Showing 57001 words to 60000 words out of 65424 words

Chapter 20 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

ciki yakewa ‘yarta saboda baya son kowa ya kamo Zainab, tun da yanzu itace a
gaban goshinsa. Saboda haka a kyale mata yarinyarta itama ta auri mai arziki.
Hakan kuwa akayi. Nan kuwa ta fantsama shirin biki. Da aka tashi aka basu wani makeken gida
sai da kuwa ta cika falika uku da dakuna shida da kaya. Kaya kuwa na alfarma. Ga kuma
hidimar biki da aka tsunduma.
Zainab tayi wa Abbanta waya yake sanar da ita zancen auren kanwarta. Taje gidan da niyyar
taji me ake ciki, Momi ta zazzage ta ta koreta tana fadin bata son ganinta a harkar bikin ‘yarta.
Har tana fadin “in don ganin wan nan dan kudin na mijinki ne ya sa kikewa mutane gani gani.
Jira kiga inda ake harkar arziki. Shi iyayensa ban da kudi har mulki suna da shi”. Batayi la’akri da cewar shi kudin mahaifin sa bane, sabanin Albashir da yake da halastacciyar
dukiya ta halal.
[8/9, 14:16] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 33
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Duk abin da ake yi na shirin biki, Zainab bata da masaniya. Shi kansa dadi bai san komai ba. Ya
dai san ranar daurin aure da kuma wanda zata aura. Amma ban da haka bai san duk wani shiri
da ake ciki ba.
Tayi niyyar gudonmowa Momi ta nuna bata da ra’ayi bata son komai nata. Duk da haka ta bawa
mahaifinta kudi naira miliyan biyu da sunan ya rage hidima. Yaya A’I ce, ta kawo katin gayyatar
na bikin Salim da kuma Farisa wanda dinner ce ta gidan maza. Tare suka yi makaranta da
mahaifiyar yaron, amma sanin yadda take gudanar da lamuranta ya sanya bata mua’mala da

ita.
Amma ganin sune manyan garin ya sanya uwar angon nacewa sai ta gayyace ta, saboda duk
uwar darin ce ita da uwar amaryar. Professional class strugglers ne. ana fito da kati, Zainab
taga sunan kanwarta ajiki. Ita kuwa yaya A’I tana mitar ba zuwa zatayi ba, saboda bata son
halin mamin Salim. Umma ce tace “Maama baki da kirki yarinyar nan tana sonki tun kuna yara amma ke kin kita”.
“Umman ba son ta ne bana yi ba. Gaskiya ba zan iya hulda da ita ba. Kina ga yadda son abin
duniya ya zarme mata tayi destroying gidan mijinta gabadaya. Kwata kwata ya daina kula uwar
‘ya’yansa sai ita da yaranta kawai. Ba yadda za ayi ki ga sauran yaran ki dauka wai uban su
daya da su Salim. Su kullum suna yawon kasar waje amma ita kuwa tana faman yadda zata
biya kudin karatun yaranta anan Nigeria.
Amma ba komai kanta ta yiwa. Gata dai nata sun samu amma tarbiyya ita kuma waccan din
nata sun yi zarra. Ta dai samu duniyar, amma ni tausayin yariyar da zata auri salim din nake.
Yaron kwata kwata ba shi da dadi”.
Zainab ce tace “maama kin san su da kyau ne”?
“Tun secondary muke tare da ita”.
Sai da tayi ajiyar zuciya san nan tace “Maama kanwata zai aura”.
Cike da mamaki suka maida kallonsu gareta. Umman ce tace “yanzu ke da gidanku bikin a
gidanku kuma jibi za a fara amma baki sanar da mu ba”.
“umma kiyi hakuri nima ban san an kusa bikin ba. Farida dai ta sanar da ni an kusa auren
amma ban san komai ake ciki ba”.
“Allah ya kyauta” inji Umma. San na ta juya wajen Yaya A’I tace zaki iya samo mata katin zuwa
saboda bai kamata ace bata je ba”.
“ai ko kati dari na nema zan samu, saboda hadaddun mata take so a wajen bikin”. Take kuwa ta
buga mata waya akan tana bukatar more cards for her family. Tana nan gidan kuwa sai ga
driver ya zo ya kawo mata about twenty cards, amma fa dangi an hana su saboda ‘yan gayu
ake so a bikin. Umman kuma ta sanya ta ta aikawa har mamanta da kanwarta da kuma wasu friends dinta.
Gayya dai suka saka tayi sosai. Bayn nan Yaya A’I ta nemi wata kawarta dake Lagos, tace mata
hadaddaiyar souvenier take so kuma nan da two days take sonta. Ta aika mata details din
amarya da ango da kuma sunan presenter. Ranar Thursday za a gabatar da dinner ta gidan maza, saboda haka Zainab da tawagar ta, ta
kusan mutum ashirin ta isa venue din. Da gani kasan bikin na manya ne. kuma ita dai yaya A’in
ta bawa MC sunan Zainab. Har announcing arrival dinta akayi. Su kuma su ka biyo ta cikin
rausaya na kidan da mc ya saka musu. Ga kwalliyarta tadaukar hankali, kamar itace amaryar don kuwa tama fi amaryar kyau, saboda
ita farisa iyayi yayiwa a kwalliyar tata yawa sai taki yin kyau. Da kyar momi ta danni zuciyarta
saboda bakin cikin yadda taga Zainab tayi stealing show din bikin.
Ga kuma VIP seat da aka ware musu ita da jama’arta. San nan ga kuma dinbin souvenier mai
dan Karen tsada da kyau data raba. Wani set ne na kayan wanka da ya kunshi bath robe da
towel na fuska da na jiki da kuma nakai an nade su da kyau aka saka acikin wata jaka mai
daukar hankali. Duk kuwa wanda yazo fita daga gidan bikin nan sai da aka mika masa tsarabar nan. Biki dai

yayi biki. Mata kuma an sha shagali. Saboda tsabar duniyanci, uwar amarya da ango suka taka
rawa tare. Ga barin kudi da aka dinga yi kamar ba gobe. Su dai Zainab da convoy dinta da suka
yi gracing occasion sukayi sallam suka tafi.
Washe gari ma ranar wuni umma ta sake tilasta ta akan sai taje. Tunda ta ga take taken Momi
taje ta gyara dakin boysquaters inda baba Laure ta tashi. Nan ta shirya ajiye dangin mijinta.
Kafin ta taho kuwa, sai da ta bada sallahun yaran da suke kamata aikin catering dinta suka
hada mata variety na abinci mai yawa, saboda har da mutan kera tayi saboda suma ta san ba
lalle Momi ta mutunta su ba.
To cikin hukuncin ubangiji abinci nata shi ya rufawa Momi asiri saboda wadanda taba wa aikin
nata abincin sun yi disappointing dinta. Amma kusan ba laifin su bane ita ta bada dokar kar a
kawo mata abinci da wuri saboda ta fi son sai mutan kauye da kuma locals sun tafi san nan ta
fito da better for her special guest. Hakan kuwa akayi. Su kuwa dangi Zainab ta ciyar da su, sanna ta bawa kowa kyautar atamfa
irin ta kamfanin mijinta, san nan tayi oder hummer masu kyau domin su mai da ‘yan uwanta
gida.
Sai goshin magariba kuwa aka dinga shigo da variety, amma Momi tayi rashin sa’a saboda da
yawa daga mutanen da take expecting basu samu zuwa ba, saboda a ranar kuma bikin ya hade
da na wata ‘yar perm sec. Saboda haka can akayiwa rubdugu. Kunsan harkar bariki ko zumunci
is for the highest bidder. Nan dai taro ya waste ya barta da tulin abinci da sai dai a zubar ko a bawa alamajirai.
Washegari kuwa dinner Momi ce itama kuma an kashe mata makudan kudi. Ga guri yayi kyau.
Ga abincin an hada shi kamar ba gobe. Amma fa amarya da uwarta basu zoba sai bayan tara
na dare. Albashir dai da ya kawo Zainab ya tokare jikin kofar da take zaune ya hana ta fitowa. Fatu tana
tsaye tana musu dariya na wan nan kankagewa da yake mata. Shi kuwa fadi yake yi “mh mh
barni Fatu. Kinajin sanyin da ake a garin nan in barta ta fito wan nan filin. Ina ba zan iya ba”.
Bayan dai dogon zama da aka bar mutane suan jira, sai ga Momi ta shigo cikin rakiyar
kawayenta ta sun sha kwalliya sun gaji, sai ya zamana kamar ma sune amaren. Da rawa suka
shiga, amma basu fi minti biyar da fara rakashewaba, sai ga wata iska ta taso.
Kafin minti biyar wuri ya harzuke. Decoration sai fadowa kan mata yake. Ban Ankara ba sai na
hango gwaggwarayen kan mata yana tashi a fili. Wuta ta dauke. Bakajin komai sai hayaniya. Du
iskar nan bata fi minti hudu ba, amma ta’adin da ta yi saika dauka ‘yan daba ne suka kai farmaki
filin. Abinci cike da chaffing dishes duk ya bude da kura. Shi dai Albashir ya maida kofar motarsa ya rufe ya sa su Fatu suka shiga domin ya ajiye su a
gida. Tun da suka dau hanya yake tintsira dariya. Har Zainab ta gaji ta ce “wai dariyar me ka
keyi ne kai kadai”?
Sai da ya sake sakin wata dariyar yace “dariyar hadaddadiyar dinner da ban taba halarta irinta
ba nake. Fatu baki hango Momi ba kafin a dauke wuta ta dafe dankwali tana kukan na ganin
yadda akayi fata fata da hidimar da ta hada”.
Dukan wasa ta kai mishi. San nan tace “Momin tawa kake wa dariyar mugunta”?
“ni na isa in yiwa surukata dariya, murna kawai nake taya ta. Ni na isa in yiwa Momi dariya. Ai
tana da value a wajena sosai. Ki tuna fa har mai gwanjo na zama saboda kawai in bi dokar ta ai
kuwa kinga ina mutunta ko”? ya fadi tare da sakin wata dariyar.

Haka bayan ya sauke su fatu nan ma ya daddage wajen bawa Umma labarin crises da ya faru a
gidan party. Yana dariya kuwa har da sukewa ita ma Umman na taya shi.
“kai Umman har da ke a tsokanar Momi”.
Cikin dariya tace “yi hakuri matar dan uwana. Ai duk wanda yace tukunyar dan uwansa ba zata
tafasa ba, Allah ba zai sa, tasa tayi ko dumi ba. Ta dauka haka zata share kalau. Ai da saura
ma”.
A can kuma cikin motar amarya da ango, masifa yake zuba mata kamar zai daketa a wajen yan
fadin data fito da wuri bata tsaya bata lokaci ba ai da duk haka bata faru ba. Ita dai Farisa kukan
abu biyu take. Ga na bakin ciki biki ya baci ga kuma na bakin cikin masifar da Salim yake mata.
Ya ma mai da ita gida a kawo ta washegari kamar yadda aka tsara, yace in har bata bishi sun
wuce ba a lokacin to kuwa sai dai auren ya rabu. Haka ta hakura ya wuce da ita gidan sa yana
duddura mata ashar kamar ba sabuwar amarya ba.
Washegari kuwa Abban su Albashir ya aiko da sakon kayan gara komai goma goma gidan su
Zainab. Suma dai wan nan din ne ya rufa mata asiri, saboda duk abin data karba ta narkar da
shi a ganin ta yi haddaden biki, har kuwa da kudin garar. Tayi haka da tunanin zata samu
gudummowa saboda haka sai tayi almubazzaranci da kudin hannunta. Liki ma kawai ranar
dinner gidan maza ta lika sama da 300k.
Washe gari kuwa da za akai garar nan bata da ko dubu dari a tare da ita. Tana cikin wan nan
tashin hankali ne sai ga sakon surukin Zainab ya iso.
Momi ce ta sa Farida ta sanar da Zainab labarin wan nan sakon sai dai kuma babu kayan
dangin ango. Tayi maula by stle. Da kuma an kawo tace bata so. Zainab bata yi fushi ba ta je ta
sayo super goma Holland goma da shadda getzner guda goma.
Albashir ne ya debo wasu shaddoji presidenta da ya sayo wa kansa suma goma yamika yace
“gashi nan ba dan halinta ba kar azo ana yi wa 'yarta gori”.
“kai Ya Al B. ni Kenan gori ka ke min na rashin zuwa da gara”?
Sai da ya jawo ta jikinsa san nan yace “ai ni dake Putri bamu yi auren don abin duniya ba. Baki
aure ni don kudi ba haka nima banyi neman aurenki da kudi ba. Soyayyace zalla da mutunta
juna a tsakaninmu. Kuma ke baki san irinki, idan ma da bashi a kanta aka kawo wa miji da gudu
zai karba, ya kuwa dage kodago don ya fanso ki. Don a lokacin dana ke nemanki ko faskare
akace in yi saboda ke zan yi shi, balle sai da gwanjo mai sauki”.
“To naji ya Bala mai gwanjo dan bani excuse inje kai garar nan”.
Dada narkewa yayi a jikinta yana fadin “saboda Allah naje daurin aure kinje yini kinje dinner kin
kuma zuwa wadda iska ta wargaza, amma duk da haka sai kin kuma fita yau”.
Itama murya cike da shauki tace kayi hakuri. Nayi ma alkwarin da wuri zan dawo”.
“Ni ba wan nan damuwata ba kar kije iska ta dauke min ke. Kin ga ba wani nauyi ne dake ba,
san nan …….” Dukan wasa ta kai masa ya goce cikin dariya.
To sun kai gara, amma fa sai da aka yaba musu bakar Magana, saboda sun yi lefe akwati
ashirin suna expecting gara sama da haka.
Momi dai aka dawo ana bata labara bakin ciki kamar tayi yaya. Duk yadda taso tsara bikin ba
haka yazo mata ba. Ga shi anji jiki, kuma kususu ba riba, saboda ko kwatar abin da aka kashe
ba a samu ba. Komawar yara makaranta ma sai da taci bashi suka koma, saboda Dadi yace ba
zai kara ko kwabonsa ba, saboda ya bata kudin komai nasu ta narkar da su a bikin nan. Balle dama ya dada jin haushin labarin da ya samu a wajen Mallam ya dada bata masa rai. Shi

ya shaida masa yadda akayi neman auren Zainab da kuma shawarar da ya ba wa Abashir na
yayi basaja, da kuma irin yadda rayuwar Zainab ta so baci a sanadin rashin sa ido da aka ringa
yi mata.
Dadi yayi nadamar rashin sanya ido a harkar gidansa kwarai da gaske, wanda kuma shine
major problem din mazan yanzu. Sun dauka in dai sun tafi nema shi ke nan hakkinsu ya tsaya
daga nan. Sun dauka wadata iyali materially is all that is needed. Su bar mata suna son ransu.
Allah yasa mu dace. [8/9, 14:19] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 34
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haka dai Zainab taci gaba da yin rayuwarta cikin jin dadi da walawala. Ga tsananin kauna da
mijin ke nuna mata. Ga kuma yadda mahaifiyarsa da sauran ‘yan uwansa ke tattalinta. Ko da
auren Fatu ya tashi wanda kuma shi ya hada auren nata da daya daga cikin abokansa, shi yayi
mata komai na hidimar auren. Mama Hajjo saboda tsabar murna ta kasa yi masa godiya, sai dai
da sun hada ido ta fara hawayen murna. Ga kuma gallalen mijin da ya hada ‘yarta tata da shi.
Farisa kuwa tana zaune a gidan mijinta. Duk da dai zaman nasu ba wani dadi ne da shi ba. Yau
fari gobe tsumma. Kusan duk waanda ya kamata ya sa baki ya gaji da shari’a a tsaakaninsu.
Shi ba shi da hakuri ita kuma bata da kunya. Idan fadan su ya tashi haka zaka gansu kamar
‘yan daba har da fashe fashe. Duk kayan alatun da aka narka musu sun farfasa su. Haka nan idan ya. debi cakunsa zai zo
kan dan abu kadan ya rufe ta da duka. Ga dai gidan hutun nan an samu an shiga, amma fa rai
da jikin ba su huta din ba. Barinta uku na sanadin dukan da yake mata.
Sai kuma daga baya ya dawo yana bata hakuri. Ita kuma tsabar sonsa haka zata hakura. Balle
da ta gwada nuna wa Momi halin da take ji bata dau wani mataki ba ita dai burinta ta binne
zancen kar Dadi da kuma sauran mutane suji suyi musu daraiya.
A hakama kuwa gwanda ita da Sakina. Saboda ita auren ma ya gagara gabadaya. A yan
shekarun nan auren ta hudu. Ga ta da saurin samun miji, amma fa bata dadewa auren ya ke
karewa. Aurenta hudu.’ya’yanta hudu kowa da ubansa. Zaman gidan Momi ya gagareta saboda
last auren da Dadi ya daura mata sharadin daya gindaya mata ke nan. In dai ta fito ba gidansa
ba.
Haka ta hakura ta koma birged gidan ubanta da zama. Nan kuma suka dasa da matar uba.
Kullum cikin tashin hankali. Zainab kuwa bata da matsala. Karatun ta take cikin kwanciyar
hanakali. Idan lokacin jarrabawa yazo mijinta ya saka ta a gaba suje ta gama jarrabawa su
dawo tare. A haaka har ta gama degree dinta tana goyon ‘yarta mai sunan Ummansa suna kiranat da
Amma. Dai dai ta gama degree ne kuma a lokacin bata dawo ba, Farida tayi zuwan hanzari
daga Sudan. Haka ya faru ne sakamakon shayen shayen da khalil ya sanya kansa a ciki. A
daure aka sako shi a jirgi a haka kuma ta shiga dashi gidan. Dadi yayi tsanannin bakin ciki da
wan nan abu. Take kuwa jininsa ya hau ya yanke jiki ya fadi. Sanadin samun stroke dinsa ke
nan. Momi saboda kawai bata son kowa yaji ta kaishi psychiatric ta sa aka kulle shi ta manta da
shi a a wajen.
Halinta ne ya sanya kusan duk matsalar ‘ya’yan wasu a bakinta zaka ji tare da kuma nuna

sakacin iyayen na abin da ya samu dansu. Kullum ita ce kadai ta iya tarbiyar yara, to yanzu da
abin ya zo kanta, sai ta ke kokarin boye tata wutar mai dan Karen hayaki.
Abin da bata sani ba, ba ma acan ya koyi shaye shayen ba, tun a nan yana yi. kusan kuma duk
wanda ke tare da ita ya sani itace bata sani ba. Saboda haka da wan nan ya faru sai take ganin
ba wanda ya sani. Ba ta san tas asirin ta a bude yake ba. Inda ma kuwa ta dinga tallata na
mutane haka itama aka dinga tallata nata. Amma wan nan yanzu ba shi ne damuwarta ba. Maitaining status dinta a society shi ya dameta,
saboda ko ba komai yanzu Dadi aljihunsa yayi kasa. Ita kuma bata yi niyyar ritaya daga karyar
da ta daukar wa kanta ba. Nan kuwa ta likewa wata kawarta da akayi mijin senator akan zai
samo mata aiki a Abuja. Kullum tana zirzirga zuwa can. Har dai tayi sa’ar samun aikin. Ta kuwa tattara ta yi gaba abinta
ta bar dadi da su Halim su kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login