Showing 21001 words to 24000 words out of 45634 words

Chapter 8 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

Duk da ita Siddiqah ba abinda ya dameta da Prince a cikin gidan, harkar gabanta kawai take yi tsakanin kitchen da falo da dakinta, sannan ta riga ta kirkirarwa kanta abubuwa na debe kewa da zasu lallasheta cikin wayar da Prince ya bata, social media plarforms ta sauke iri iri ba wanda bata shiga ta ga me duniya ke ciki, bayan girke girke da take yi wa kanta don ta burge kanta da kanta kullum. Yo ta burge kanta mana, sanin da tayi Prince bazai ci ba, musamman ganin komai na girkin available kuma a wadace yasa take dafa duk abinda ranta ya kwanta dashi.
Daga baya idan ta girka ta kan ajiye bisa dining din da yake zama don cin abinci, ganin cewa da kudinsa ake yo cefanen koda bazai ci ba hakkinta ne ta bashi, musamman lokutan data ganshi a gida, ko in ta ganshi ya fito zai fita unguwa ko kuma ya dawo, sai kaji tana gaya masa cikin ladabi da sasanyan fulatancinta.
“Ga abinci Hamma Abdul, ban sani ba ko zaka daure ka ci?”
A irin wanna lokacin da Siddiqah ta kwantar da kai tana masa tayin abinci cikin kwantar da murya, jin kansa yake on top, irin yanda maigida ke ji a gidansa, ya ji shi a ransa yanzu ya cika mutum, amma sai yaji sarautar ta motsa ta hana shi amsa mata da dadin rai, sai kawai yace mata “na gode, I am okay”.
Ya kan ki kallon inda abincin yake, ya wuce ga abinda ya fiddoshi daga dakinsa, don kiri-kiri Siddiqah tasa Prince ya ragewa kansa zaman (sitting room) dinsa, bata takurawa kanta sam a zaman gidansa wai saboda shi ko don sanin cewa yana cikin gidan, tuni ta roki Ubangiji ya cire mata tsoro da shakkar Hamma, da kwarjininsa dake sata bare-baren jiki tuni Allah ya ji rokonta ya yaye mata.
A halin yanzu shine ma za’ace Siddiqah ta takurawa, don saidai in bazai zauna a sitting room din ba yayi ta zaman daki, ba abinda ke hanata bajewa a falon gidan ta kunna talbijin, bai taba ganin yarinya mara tsoro da shakkar idanunsa wadda kwarjinin sa bai sawa ta bar wuri irin Siddiqah ba.
In kaga yadda take sakewa a kitchen din tana kai komo domin shirya abinda zata ci kamar ta shekara a gidan. Sau da yawa sai ta ta gama abinda zata yi na ranar ta shige bedroom dinta ta kwanta yake iya fitowa ya zauna a sitting room din don yayi kallon labaransu na (PoloLine TV), yana kallon yana shan Chamomile Tea, wanda shine ke sashi yin barci na nutsuwa a yawancin lokuta.
Prince baya so ya zauna daga shi sai ita a falon, don sau tari kallon Siddiqah kadai idan yayi tausayi take bashi, (no any other strange feeling) bayan wannan, tausayinsa akan wannan aure da aka yi mata ne jaririya da ita da tsohon bachelor kamar shi. An kuma rabota da kasar haihuwarta da kowa nata, sannan shikuma gashi bai ko iya hira da bare ba, baren ma mace, yawanci in kaji hirarsa na fita tar-tar da Kiki ne ko Aunty Taiwo.
Koyaushe Aisha na magana da iyayenta suna kara karfafata, da kuma mutanen gidansu Abdulrasheed su kuma suna kyautata mata. Princess Firdausi ta taba turo mata lambar Aunty Taiwo tace ya kamata ta kirata ta gaisheta don taji tana yiwa Nenne korafin Aisha bata taba gaisheta ba, ko a waya, kamar bata san matsayinta ga Kehinde ba.
Amma Aisha ji tayi ko da wasa ta kasa kiran Aunty Taiwo. Tana kiran kowa na gidan musamman Dade, harda Princess Fatima kuwa mai amsa mata sama-sama. Amma har lokacin bata kira Kiki ba saboda alkawarin da ta yiwa kanta na ba dai Kiki taji maganar aurenta da Uncle dita daga bakinta ba in duk gidansu an rasa mai gaya mata to aje a hakan.
Haduwarsu cikin gidan ma ita da Prince ba sosai bane tunda baya zaman falon, wani lokacin da safe in ya fito karya kumallo in ‘yan saukin kan na kusa yakan je har kofar dakinta ya kwankwasa yace ta fito su karya kumallo tare, ta kance daga cikin dakin ba taredata fito ba Hamma ya ci, ita ba yanzu ba, don tasan na order ne in ita tayi ta bashi baya ci ai sabida ya dauka bata iya ba ko yayane oho.
Daga nan basa kara haduwa sai ko da daddare in zai yi dinner tana zaune a sitting room din tana latsa wayar hannunta ko kallon tv, nan ma su kan hadu, kan ba yadda Prince zai yi, saidai yaci abincinsa tana zaune don baya iya cewa ta tashi.
Ta fahimci duk yammaci daga karfe hudu zuwa shidda na yamma wato bayan yayi sallar la’asar, Hamman nasu Fatima, yana kasancewa a ranch dinsa ne ya karasa wunin ranar tare da Dawakansa.
Mu’amalarsu shi da Dawakan mai ban sha’awa ce, don sau tari takan hango su idan ta daga labule don samun danyar iska (fresh air). Musamman wani babban doki a cikin Dawakan da ta ji Hamma yana kira da suna SAHEEB.
Sau da yawa ta kan jiyo basarakiyar muryar Prince idan yana magana da dokinsa Saheeb, ko in Pareto ya tadda shi a wurin suna maganar da ta shafi lafiyar dabbobin.
Ana I gobe zai tafi France din da ya shirya tafiya suka wayi gari da bakuwa a gidan ba zato, “Kiki”.
Tun kafin kamo hanyarta ta komawa makaranta, Kiki ta yanke shawarar bari ta tsaya gidan Uncle dinta tayi kwana biyu yadda ta saba tare dashi, sannan ta wuce makaranta, tayi kewar Kawun nata sosai.
Da niyyar kwana biyu kacal Kiki ta tsaya wato zatayi Asabar da Lahadi in yaso Litinin ta karasa Los Angeles daga Argentina, tuni a hakan tayi booking flights dinta tun farko.
Ko da ta sauka ma bata kira shi domin ya daukota ba, taxi ta biyo zuwa gidan nasa duk don tayi surprising dinsa.
Pareto ya tabbatar mata Master na nan, kasancewar ya san matsayin Kiki a gidan yasa ya barta ta wuce kai tsaye zuwa kofar shiga sitting room.
Kiki (Ruqayyat Toufeeq) taci gayunta kamar koyaushe, ta fito a Kikinta tsaf, ‘yar gatan Prince (Uncle AK) inji ta, tana tafe kwas-kwas-kwas akan tsinin takalminta, sanye cikin wata ruwan zumar kampala Yoruba Traditional Attire mai ratsin baki data sha dinkin bubu don Kiki kam masha Allah bul take, shiyasa da wuya kaga tayi dinki wanda zai kama jikinta, ko English wears da take yawan sakawa zaka ga cewa sakakku ne, Kiki tayi kyau har ta gaji duk da bata make-up, da ganin ta kaga ‘yar hutun budurwa mai cin lokacinta da zamaninta, bayarabiyar asali gaba da baya.
Wani dan share-sharen gyale ne Kiki ta yafa iya kafadunta da ‘yammata ke yayi, (chantily) kalar kayan jikinta ruwan zuma, a kafarta wani siririn (golden heel shoe) ne mai tsinin dunduniya sosai a santala-santalan kafafunta.
Kiki ta danna kararrawa mai sanar da zuwan bako (door-bell) a kofar shiga sitting room, tana cike da dokin ganin Uncle din nata.
Aisha na zaune a sitting room tana kallon bakaken larabawan Sudan na wakarsu ta Sudanese, shi kuma Prince yana daga can cikin Master bedroom dinsa. Kiri-kiri shi da falonsa Aisha ta gaje ta hanashi zama, ta maida shi zaman daki dole, don baya so su zauna tare na lokaci mai tsaho a falo ko mai yasa? Shima ya rasa dalili. Ya dai danganta hakan da baya so su saba, ta shiga jikinsa.
Dadin wakar larabawa da akeyi a TV dinne yasa bata yi saurin mikewa domin taje ta bude ba, ai tasan zai ji yazo ya bude tunda gidansa ne, karewa ma bin wakar take yi tana kada ‘yan yatsunta a hankali da juya dogon wuyanta don tana matukar son wakar da akeyi din. Mai kiran bai hakura ba haka ya cigaba da danna door-bell din a nitse, sannan da zaquwar son azo a bude.
Dole Aisha ta mike ganin Hamma bashi da niyyar fitowa da kansa ya karbi aiken, ta isa kofar dakin nasa tana masa knocking, don tana zaton Pareto ne, taji sanda ya kira shi ta waya ya aikeshi ya samo masa chamomile tea.
Daga ciki Hamma ya amsa da.
“Yes, I am coming”.
Kafin ya bude ya fito daga shi sai farar bodycon da dogon bakin wandon Jeans, Aisha ta sunkuyar da kai don ta kasa kallon sa da suttura a jikinsa, ga (8 pack) dinsa duk ya bayyana ta cikin (bodycon) din da ke jikinsa, kanta a kasa tace,
“Hamma anata sallama a kofa tun dazu”.
Prince yace “kuma ke baki iya bude kofar bane ko yaya?”
Ya fada yana binta da idanu daga sama har kasa, ita kenan kullum cikin dogayen riguna abinta, kamar ita tasa aka kera jallabiyyas, bata yin wani abu (to make him attracted to her) tsakanin ta da Allah ba kallon miji take masa ba, kallon babban Yaya ne. Ko kuma wani young kanin Babanta haka. Prince a ’yan dakikannan saida ya gama karewa kyakkyawar surar jikinta da fuskarta dake sunkuye kallo, sannan ya sauke wani boyayyen numfashi, ya ce,
“to naji, kije kisa kallabi mana, bana son ganin ki a gabansa kai a bude babu dankwali, ga Pareto ba hankali ya isheshi ba, duk da yasan kina gidan amma kullum yana faman yi min Pareti a gida”.
Kalmar tashi ta karshe “Pareto na faman yi min Pareti a gida” taso ta bata dariya. Daga haka ya wuce Aisha a wurin, tana tambayar kanta ko meye gamin Hamma da daura kallabi a kanta?
Ita batama san lokacin da kallabin ya zame akan kujerar da take kwance a kai ba. Kodayake ko ba komai daura kallabi abu ne mai kyau musamman ga matar aure a gaban wanda ba muharraminta ba. Kenan Hamma bai fada don wata manufa ba.
Tana kallo ya isa ga kofar cikin takunsa na kasaita ya bude, don da gaske ya dauka Pareto ne ya dawo daga aiken da yayi masa. Sai kawai ya ga Kiki ba zato tsammanin sa, kamar daga sama.
Lallai kuwa Kiki tayi surprising Uncle din yadda tayi fata. Don can na ganeshi rike da bakin mamaki, har fuskarshi hakan ya nuna, wato mamakin ganinta, at the same time, yaji dadin ganinta.
Kiki ta yi tsalle zata rungumeshi yadda ta saba, ga mamakinsa yau sai ya kasa rungumar Kiki gabadaya a jikinsa yadda ya saba, ko ba don Aisha dake bayansa ba, don ji yai girma ya karu masa akan nasa, (girman aure da haibar dake cikinsa).
Itama kuma Kiki sai bata damu ba ko don ta san ta girma yanzu? Duk da cewa niece din shi ce sannan al’adarsu ta Yoruba bata hana hakan ba, dan side hug ya dan yi mata a kafadunta sannan ya kama hannunta yarike cikin nasa.
"Kiki? Kece da gaske? How comes kika zo ba sanarwa, meyasa baki gayamin kin taho ba, inje in dauko ki bayan saukar ki?"
Kafin Kiki ta bashi amsa ya sake cewa "ki daina zuwa ba sanarwa, tunda kin san ba nikadai bane a gidan yanzu".
Da mamaki Kiki ta ce "Kai da waye toh a gidan Uncle AK?".
Sai kawai ya matsa ya bata hanya ta shige cikin sitting room din. Zakin muryar Kiki mai amo kamar na marokiya da taji kamar cikin mafarki yasa ta juyowa da sauri daga gaban talbijin, sai idanunta suka sauka cikin na Kiki-Ruqayyat.
Kiki saura kadan ta koma baya da gudu, don kuwa ba karamin tsorata tayi da ganin Aisha a gidan Uncle dinta Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni ba.
How dare she came here? Ta ina tabi tazo har Argentina kuma gidan Uncle dinta? To me tazo yi? Me ye gaminsu? Kodai-kodai Aisha aljana ce bata sani ba, tukunnama meye hadinta da Uncle AK da zata dawo gidansa da zama?
Iyakar tsorata da shiga rudani Kiki ta shigesu ta kuma firgita, mamaki ya kusan kasheta daga tsaye, sai ta koma daga bayan Prince ta dan rike rigarshi ta baya, tana buya tana lekowa kadan.
“Uncle AK boyeni, kawata Aisha-Siddiqah ce take yi min fatalwa a gidanka ba don ta mutu ba”.
Watakila tun zuwan Aisha gidan Prince batayi dariyar data fiddo fararen hakoranta waje ba sai yau. Da kyar Prince ya zaqulo Kiki daga bayan sa yana cewa “bana son shirme Kiki, kina nufin baki santa ba ko yaya ne? Mutuwa tayi da zata yi miki fatalwan?”
Da gudu Aisha ta taho ta janyo Kiki ta karfi daga bayan Uncle ta rungumeta. Kiki na kokarin zamewa tana dojewa tana cewa.
“Ba wani hugging dina da zakiyi. Ba wannan a tsakaninmu yanzu. Nayi fushi, nayi fushi sosai Siddiqah.
Ki gayamin kawai saboda Allah me kike boye min haka tuntuni?”
Kiki ta juya ga Baban nata cikin rudewa tace “Uncle AK, ku fiddani duhu, I am perplexed, that means Aisha-Siddiqah is your wife since?”
Prince rasa amsar da zai baiwa Kiki yayi, don sosai yaji nauyin ‘yar tasa ta yadda zai ce mata kawar tata da basu fice shekaru daya ba matarshi ce ta sunnah, ba wani (age gap) ma tsakaninta da Kiki. Duk da haka yayi mamaki da bata sani din ba.
Sai kawai ya zuba hannayenshi a aljihu yana kallon Kiki tana murje ido wai dai ta tabbatar ba mafarki take yi ba, Hamma ya samu hannun kujera ya zauna, ya mika mata hannu yace.
“Come on my darling daughter, zo ki zauna kusa da ni, ki gayamin yaya hanya? Uncle missed you for long!”.
Kiki taki zama, ta soma kukan dadi daga tsaye, tana bubbuga kafa a kasa na shagwaba don zuwa yanzu duk da bai furta ba ta gama gane komai.
Cewa Kiki take daga inda take tsaye cikin kukan da ya wuce da dariya, “wayyo ni Kiki! Wayyo ni Ruqayyat! Uncle AK kawai kace min kayi aure, ashe inada rabon ganin wannan ranar?
For how long akayi toh da har ni ban sani ba???
Auren ma kuma da Aishata! Itace na dade ina yi maka sha’awa fah!”
Ta koma Yarbanci ziryan tana fadin “God so kind, yau da wace kalma zan godewa Ubangijina?
Uncle dina yau da matar aure a cikin gidansa a Ranch dinsa?”
Sai ga hawayen farin ciki na gudu daga idanun Kiki-Ruqayyat. Siddiqah ta kamota tana tirjewa ta zaunar da ita a gefenta, sai Kiki ta matsa can nesa da ita tana zumburo baki.
“Daga yanzu ai nasan irin zaman da kike dani Aisha, baki daukeni aminiya yadda na daukeki ba, tunda har kika iya rufeni a bai-bai irin haka.
Ni me aka dauke ni? Hayagaga rariya uwar Magana ko? Ko kuwa Aku-Kuturu sarkin zance ko? Shi yasa baza’a gaya min wannan abin alherin ‘officially’ ba aka yi ta yawo da hakalina? Aisha abokin kuka ba’a boye masa mutuwa”.
Kiki mita da korafi da kyasci kamar ta ari baki, nan dai Aisha duk ta karbi laifin ta shiga baiwa Kiki hakuri itama kamar ta ari baki, tace “ai ba ni ya dace in gaya miki ba Kiki, nima kunya nake ji, a inda ya kamata a gaya miki daban Kiki ba’a nan ba. Kiyi hakuri kada ki ga laifina, to me zan ce miki ni a lokacin da kika zo Lagos? Bayan ni kaina bansan matsayina a gidan Nenne lokacin ba?
Ina dai zaune ne kawai tareda Nenne. Ban kuma taba ganin Baban naki ba ko a hoto, saboda Allah me kike tsammanin zan iya ce miki akai a lokacin banyi azrbabi ba?”
Kiki ta yarda da kariyar da Siddiqah ta baiwa kanta. Amma tace da Uncle dinta daga yau itama ta saka shi a bakin littafi.
Tace itama daga yau ta daina masa zancen Tosin, tunda shima ya boye mata soyayyarsa da matarsa kawarta Aisha.
Kiki ta ce “daga yau Aisha kece Uncle dita, kece kuma Aunty na, nayi fushi na daina Uncle da Uncle AK!”.
Kai yau Hamma yaga boni da rigima iri-iri daga Kiki. Sai murmushi yake kansa a sunkuye yana latsa wayar hannunsa. Da ya gaji da mita da korafinta ya dago kai a hankali ya dubeta da manyan idanunsa tamkar ruwa ya kwanta a cikinsu.
Don duk korafinnan da mitar nan da Kiki take yi kan Hamma Prince yana duke akan wayarsa ko dagowa bai yi ya kale su ba, amma tsaf yake jinta. Yana kuma murmusawa tarin kuruciyarta. Muryar Aisha dake ta kare kai kuma tana masa dadin saurare. Da kyar yace.
“Kiki kinsan Uncle dinki care for you koh? Ba abinda zan boye miki wanda yakamata ki sani.
Na aza kin sani. Yanzu dai duk kiyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login