Showing 36001 words to 39000 words out of 45634 words
Chapter 13 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt
ita kuma a kwanakin nan guda hudu, Aisha babu abin da ta ke yi sai sauraron zuciyarta, tana ‘digesting’ maganganun Kiki na hankalin dana wautar. Tana daukar na hankalin, tana watsar da na shirmen.
A ciki Kiki ta ce da ita kada ta kara yarda Hamma ya barta jiran gida. Ta dinga saka su lingeries a cikin gida da sauransu.
Kiki ta manta duka wannan ana yi ne a inda akwai soyayya da kaunar juna. Ba ta haufin yau da a ce Ishaq ta aura za ta iya yin fin abubuwan da Kiki ke koyar da ita. Ita ba bagidajiya ba ce irin yadda kowa ke daukanta, ta san duk abin da ya kamata macen kwarai ta yi a dakin aurenta, uzurinta kawai shi ne Prince ba sonta yake ba, ita ma kuma haka, sannan ba ta hango musu wani canji a zamantakewarsu nan kusa ba, domin ita da shi duka danjuma ne da Danjummai. Wato babu wanda ya damu da wani abu wai soyayya, ita a kan Ishaq duk wani tsuntsun soyayyarta ya gama tashi.
Tana wannan tunanin mara adadi a zuciyarta ta ji motsin ana knocking kofarta kadan-kadan. Kafin a shiga kwankwasawa sosai, a nitse Aisha ta tashi zaune daga kwanciyar da ta ke, ta isa ga kofar ta bude don ta san babu mai yi mata knocking har kofar dakin barci a gidannan a kuma daidai wannan lokacin da dare ya fara nisa in ba shi Hamma Prince din ba.
Aisha ta taso ta bude wa Hamma kofa, ta rabe jikin kofar ta ba shi damar shigowa don alamu sun nuna shigowar yake so zai yi dakin.
Sai da ya baza manyan idanunsa yana nazarin tsaftar dakin. Ba laifi Aisha ba ta watsar da shirgi, komai nata neat. Don haka ya zabi sofa-bed guda daya dake dakin ya zauna, kafin ya dago a hankali idanunshi a lumshe ya fuskanci inda take tsaye tana gaisheshi, bai amsa gaisuwar ba yace,
“Are you alright? Kwana biyu bana ganin wulgawarki a sitting room, baki ko gaisheni, ina fatan dai lafiya?”.
Kan Aisha a sadde ta bada amsa, “Wallahi lafiya kalau Uncle, kawai ina kewar Kiki-Rukayyat ne”.
Prince ya yi murmushi ya ce, “Ni kuma da kika daina fitowa kinsan ya nayi kewar ki? Na ga alama jininki ya hadu da na Kiki, ga shi ba ki san ita yarinya ce mai kiriniya da rawar kai ba.
Kawancenku ba zai yi daidai ba, considering cewa ke din Uwa ce a gare ta.
Ba komai za ki dinga tattaunawa da Kiki ba akaina please, zan kai ki makaranta insha Allah idan nagama hutuna mun koma inda nake aiki a Qatar, domin ki samu abin debe kewa”.
Godiya sosai Aisha ta hau yi, tana jin kamar Hamma ya mata bushara da kujerar makkah, kwarai ta ke son komawa makaranta, ta dauka karshen karatunta a rayuwa kenan sakandire, amma ta san wannan shekarar dai ta shige mata, sai ko shekara ta gaba. Prince yace yana mikewa tsaye, hannunwansa biyu zube cikin aljihu,
“ina fatan gobe da safe zan samu breakfast daga hannun Ayshah? Tunda Kiki ta tafi kika daina bani, bayan kwana biyu kun shagwabani da kyawawan girke-girken nan naku”.
Ya fada yana kokarin saka idanunsa cikin na Aisha, ita kuma tana kokarin sunkuyar da kai ga barin kallonsa.
Prince ya kai bakin kofa yana cewa “Good night Ayshah!”. Amma kuma ya kasa ficewa daga dakin gabadaya, rabin jikinsa har lokacin yana cikin dakin. Wani bakon yanayi yana ziyartarsa.
Da kyar da dakiya da jan kafa da karfafa giyar mulkinsa kada ta gudu ta barshi, da maintaining class dinsa kada ya bada kansa da yawa gaban little Aisha, Prince ya samu ya fidda gangar jikinsa data makale a dakin, amma har washegari zuciyarsa na reto tsakanin dakinsa zuwa na Aisha. Ji yake kamar ya dawo ya kwana a dakin tareda ita.
A washegari kuma ya samu waya daga Ilorin cewa, Emir babu lafiya, ko fada baya iya fitowa, yau kwana uku yana kwance saidai a kwantas a tayar.
Bai yi niyyar zuwa gida nan kusa ba, ko sake yin tafiya cikin hutunsa, amma sanin kowa ne sha’ani in ya hada da Kakansa Emir daban yake a gare shi, balle magana ake ta lafiyar Kakansa Maimartaba Sarki, ba zai iya kara wasu kwanaki bai je ya ganshi ba, a take Prince ya soma neman jirgi mafi kusa domin tafiya Ilorin.
Ya tuna Siddiqah, yaya zai yi da ita idan ya tafi? Wancan lokacin da Kiki, wannan kuma babu.
A karshe ya ga gara ta zauna ita kadai din maimakon ya dauke ta yanzu zuwa Ilorin, ya yi wuri ma ta je gida nan kusa, gara ma tun yanzu Aishah ta koyi zama ita kadai, don kuwa tafiye-tafiyensa ba masu karewa ba ne.
Banda sauyukan dake faruwa dashi a ‘yan kwanakinnan a kanta, wato yanzu da ya fara sabawa da ita, ya kuma fara fuskantar dadin mu’amalar da yarinyar keda shi, da ba zai damu don ya tafi ya barta ita kadai cikin gidannan ba.
Zuwa yanzu Prince da kansa ya fara tantama a kan cikar lafiyarsa, don duk da tabbacin da yake da shi na cewa Siddiqa matarsa ce, bai taba jin darsuwar wani abu game da ita a ransa ba da ya danganci ‘sexual urge’. Ya dai fara jinta a ransa, ta manne a zuciyarsa. Watakila kuma ko don ya riga da ya saba da yadda yake rayuwarsa ne tuntuni daga shi sai shi, sai ibadar addininsa, sai lafiyar Dawakansa sai kuma zuwa Polo tournament sai aikinsa na ‘Qatar Petroleum Refinery?’.
Bai gaya wa Siddiqah maganar tafiyarsa Ilorin ba sai bayan ya gama duk wani shiri yayi (booking flight) dinsa na tafiyar, wato ana i-gobe zai tashi zuwa Ilorin.
Siddiqah tana kitchennett tana tana dauraye kofin Mug din data sha tea, ta ji motsin Prince ya shigo inda take.
Kai tsaye firij ya nufa, ya bude ya dauki gorar ruwa ya rufe. Ta gama wankin kofin tana kife shi a wurinsa taji motsinsa dab da gefenta. Siddiqa ta rusuna tana gaishe shi da irin gaisuwarsu ta ce, “Ekaaro Uncle” (wato ina kwana)”. Wannan Uncle da Siddiqah ke lanqaya masa ba ya son jin shi, har gara masa Hamma Abdul din da take kiransa dashi da fari kafin zuwan Kiki.
A kan me za ta dinga ce masa Uncle sai ka ce wata Kiki? Uncle din nan da ta ke ce masa na sawa ya ji kansa tsoho sosai a kanta sosai.
Amma wannan ba shi ne abin da ya kawo shi yanzu ba da yayi korafi, ya zo ne ya gaya mata batun tafiyarshi duba Emir gobe. Tun shekaranjiya rabon shi da ganin Siddiqah. Jiyan da shekaranjiyan duk bai karya kumallo a gidan ba, ya wuni ne a ‘Cathedral of Polo’, shi ya sa bai ga gilmawarta ba, don ko babu komai koda bazata saki jiki dashi yadda yakeso ba yanzu, yana son ganin gilmawarta a kitchen don dai ya tabbatar da lafiyarta.
Murya a tausashe ya ce, “Siddiqah, in baki ganni ba ba kya nemana cikin gidannan ko? In ma mutuwa nayi cikin daki ko bani da lafiya duk ba damuwarki bane ba ko Ayshah?”.
Kiran sunan nata da ya yi har sau biyu yasa ta bashi hankalinta, don yau ne karo na biyu da Prince ya ambaci sunanta. Ya kara matsowa dab da ita, ita kuma ta dan ja baya.
Ya ce, "daina ja da baya ba rike ki zan yi ba Pretty, so nake na gaya miki zan je Ilorin, zan dubo jikin Kakana.
Ba na fatan in wuce kwanaki bakwai ban dawo ba, ko akwai abubuwan da ki ke bukata?”
Siddiqah kamar ta ce masa za ta bi shi, to amma ita ma tasan ya yi wuri su Nenne su ganta yanzu, duk da cewa ba abin da ke hada su cikin gidan ta san akwai mutum, idan yana nan. Don haka ta samu kanta da rashin jin dadin zancen tafiyarsa, haka ta daure ta ce,
“Bana bukatar komai Uncle, ka saya mana komai, ina maka addu’a Allah ya kiyaye hanya ya bawa Emir lafiya, ina duba shi da jiki, in ka karasa wajen su Nenne, ina gaishe su bakidaya, Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya”.
Prince ya ji kamar ya riko hannayenta ya sumbata, ganin damuwa karara a kyakkyawar bafullatar fuskarta. Ashe haka mutum yake ji idan iyalinsa sun masa addu’a?
A zuciyarta kuwa hudubar Kiki ke ta mata aiki, na ta daina yarda yana tafiya yana barinta gadin gidan gona, to amma kwarjinin Hamma da girmansa da ta ke gani cikin idanunta ya sa kowanne hukunci ya yi ba ta da ja a kai, musamman a kan zuwansa Ilorin dinnan itama ta san ya yi wuri a ce ta bi shi yanzu.
Ta kalle shi a raunane, shi ma kallonta din yake yi da wani sabon yanayi cikin idanun Hamma Abdulrasheed Prince, ya zuba dukkan hannayensa cikin aljihun wandonshi ya juya ya bar kitchen din, yana kokarin maida wani abu da ke neman fita daga bakinsa, wato kalmar ‘I will miss you’ da yake ganin bata dace ya furtawa Aisha ita ba. Amma tabbas zai yi kewar tata, gashi yana son ya zauna tare da Kakansa a wannan lokacin ya kula da shi da kansa.
Prince ya tashi a washegarin ranar litinin Siddiqah ta tashi da azumin tadauwa’I a bakinta, wajejen karfe sha daya na rana ta kammala shiryawa ta fito zuwa falo.
Ta kunna TV da taimakon remote tana kunnawa din kuma tashar Polo ta ‘PoloLine TV’ ce ta kama, ga dukkan alamu ita ce tashar da ya fi kalla. Ta tarar ana gudanar da wasan tseren Doki. Ta sha jin Nenne na ce mata Hamma yana polo, bata taba ganinsa a profession din ba sai yau, gashinan tsaf ya fito cikin kayansa na polo. A lokacin ana gudanar da wasan ‘Concacap World Polo Championship’. Kasancewar Helmet din kansa budaddiya ce ya bata damar gane fuskarshi sosai cikin mahaya dawakan.
Dokin da yake kai wani farin kosasshen doki ne mai fatsi-fatsi, wanda a halin yanzu Prince baya wasan Polo da shi, tun wancan lokacin da suka fadi tare shi da dokin nasa.
Siddiqah aka gyara zama ana kallon duk wani motsi na Prince Abdulrasheed Kehinde . Gudu yake da doki cikin kwarewa da iyawa, kamar zai yi fiffike ya tashi sama.
“Wannan shi ne ake kira Polo kenan!” Inji Siddiqah. Kuma a koyaushe ta kalli wasan da aka nuno zata ga cewa kusan Prince shi ne jagaban wasan, wato shi ne a sahun gaba na wadanda ke neman isa goal.
Abin ya burge Siddiqa matuka don kuwa a wannan daren kusan kwana ta yi tana mafarkin Prince Abdulrasheed a kan doki, yana mata murmushi da helmelt dinsa mai ban sha'awa a a kansa.
Shi kuma Hamma tunda ya sauka a Ilorin bai samu sukunin da zai tuna kowa da komai bama don jikin Emir ya yi tsanani, ko wayarsa bai iya ya bude ba.
A washegarin ranar ne Aisha ta fara fitowa ainahin kwaryar ‘Ranch house’ din, sabida kadaici daya dameta, kallo sosai Siddiqah take na dabbobi kala-kala masu daraja, harda wadanda ko a talabijin bata taba ganin irinsu ba.
Tana tafe a sannu itace har wurin stable din dawakai. Daga ganin farin doki mai fatsi-fatsi “Saheeb” Siddiqah ta gane shi saboda irin kebewa da killacewar da aka yi masa. Wato an ware shi daga ragowar. Ba wanda ya isa ya je inda yake ba tare da Saheeb ya harbe shi ba, daga Prince sai Pareto.
Amma daga nesa Pareto ya hango wani abin mamaki, wato Siddiqah ta isa har gaban Saheeb bai harbe ta ba. The beautiful royal horse “Saheeb”, duk ya fi sauran dawakan girma da mulmulallen jiki mai kyau.
Ga tsafta ta kama jikinsa saboda kulawar Pareto. Farcensa kansa tsaf-tsaf yake, sannan yana zaune cikin korran ciyayi masu taushi da tsabta.
Nan Siddiqah ta shashance har lokacin sallar azahar tare da doki Saheeb a stable dinsa.
Pareto sai komawa ya yi da baya don ya ga tana jin dadin zaman wajen, sauran ma’aikatan gidan gona kuwa kowa yana bisa aikinsa babu wanda ya ba ta hankalinsa.
Sai ya zamana daga ranar kullum da safe sai Siddiqah ta je stable din Saheeb, har dokin na Prince ya fara gane ta. Da ya ga tahowarta zai fara haniniya yana daga kafafu sama irin yadda yake yi idan ya ga Prince. Ba da sanin kowa ba cikin kwanaki hudu kacal da tafiyar Prince Ilorin Aisha da Saheeb suka yi developing good bond.
Har wajen shanun Prince ta ke shiga inda ake tatsa (milking) mai kula da shanun yana mata bayanin madarar sayarwa kamfanonin sarrafa madara suke yi. Pareto ya sha mamakin sabon da ya ga ya shiga tsakanin Siddiqag da Saheeb cikin dan lokaci. Sosai abin ya burge shi. A rashin abin yi Siddiqah ta mayar da Ranch din dawakan wajen shakatawarta da debe kewa da shan iskarta.
Wani zubin kuma ta tsaya kallon dramarsu shi da Pareto. Daga irin dramar da ake bugawa tsakanin Saheeb da Breeder din nasa Pareto Siddiqa ta ji doki Saheeb ya kara shiga ranta. Koyaushe ta zo gun Saheeb sukan gaisa da Pareto ta zauna a kujera a gefe tana kallon yadda al’amuransu ke gudana tsakanin Saheeb da mai kula da shi, tamkar saheeb wani dabba ne mai tarin hikima da baiwa, duk mai kula da shi ya sanshi farin sani.
Kadan-kadan Saheeb ya fara gane fuskar Siddiqah, watarana cikin dari-dari ta kai hannu ta fara shafa jikinsa da kyakkyawan gashin wuyansa, har Pareto ya tsorata ya zo da sauri zai hanata, sanin halin Saheeb da yayi, na ba ya barin kowa ya zo inda yake bai yi harbi ba.
Amma abin mamaki sai ya ga Saheeb ya kwantar mata da kai kasa tana shafa shi yana dada kwantar da kai.
A haka a haka har karambani ya sa rannan ta ce da Pareto tana so ta hau bayan dokin. Pareto ya gaya mata cewa ba ya bari a hau bayanshi in ba mamallakinshi ba. zaiyi tutsu a ita.
Aisha ta dage cewa she wants to give it a try. Dole Pareto ya kyale ta ya saka mata sirdi ta hau Saheeb, ya rike mata linzami suka shiga zagayawa cikin Ranch din. Sune har kofar fita ‘ranch’ da wajen BQ din Pareto, daga nan suka juyo suka dawo stable dinsa. Siddiqah ta sauko lafiya.
Sai hakan yasa ta kara sabawa da Saheeb sosai, kullum nan ne wajen wuninta. Kusan ba ta da damuwa a yanzu, don Saheeb ya debe mata kewar kowa da komai.
Siddiqah na nan tana fama da Saheeb, Prince yana Ilorin jikin Kakansa Sarki Abdulrashed Akanni ya rikice.
Likitoci har uku ne ke tsaye a kansa a gidansa na masarautar Ilorin, tare da ‘ya’yansa (Ten Akannis). Ciwon cikin wuni uku daya firgita zuri’ar Sarki Abdurrasheed gabadaya. Prince kwana yake tare da Kakansa a turakarsa don ko matansa na aure basa bari dashi.
Yau da dare jikin nasa da sauki sosai, don an masa allurar barci, amma cikin dare ya farka ya ga Prince a zaune a gefen kansa yana gyangyadi, lokacin kowa ya je ya kwanta.
Sarki Abdurrasheed Dan Abdullateef Akanni, ya ce da jikan nasa Prince.
“Kehinde! Barci kake yi a zaune?”
Kamar cikin mafarki ya ji muryar Kakan na kiran sunansa, tuni ya wartsake ya matso daidai kansa. Sarkin ya kamo hannunsa ya rike cikin nasa, ya ce cikin harshen yarbanci, “Kehinde Jikan Sarkin Ilorin, jika mafi soyuwa a gareni, me yasa baka zo min tare da matarka na hada ku na sa muku albarka ba? Ina fatan zuwa yanzu komai ya daidaita tsakaninku yadda muke fata? Ka karbi zabin mahaifiyarka da hannu bibbiyu? Nan bada jimawa ba zaka ajiye min mai sunana? Wanda zai gaji gidannan tunda ba kwa son gadona kai da Ubanka?”
Prince rasa amsar da zai baiwa Emir ya yi, sai cewa yayi cikin yarbanci “tana lafiya Allah ya ja zamaninka, na baro ta lafiya cikin koshin lafiya, kuma maimartaba na dade da karbar matar nan da kuka zaba min da godiya da yabawa. Tana da attributes na matan kwarai da ban san su a tare da ‘yammatan wannan zamanin ba”.
Sarki Abdulrasheed ya gyada kai cikin gamsuwa da jin dadi, sai kuma yace.
“A yadda nasan ka kullaci mata, da yadda giyar mulki ke hanaka sakewa, ina da yakinin har zuwa yanzu ba ka dora mata idda ba. Ko Qur’ani zan dafa akan ba ka dabbaqa sunnarka ba har yau, me yasa? Donni in za’a shekara ana cewa ba ka da lafiyar aure ba zan taba yarda ba, na san lafiyarka kalau, baka samu wadda kake so bane, kuma bazaka iya hada jiki da matar da baka so ba shine babban dalili, tunda na san yaya halittar sarakuna take a kan matan