Showing 33001 words to 36000 words out of 45634 words
Chapter 12 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt
shirya table din da kwalliya ta ban kaye bisa umarnin uwardakinsa Kiki-Ruqayyat. Ya shirya abincin da ya karbo order, ya aje katon cake a tsakiyar table din. A jikin cake din Kiki tasa an rubuta “Happy 43rd Birthday Uncle AK”.
Kiki ta fara zuwa wajen ta tabbatar komai yayi yadda take so ya kuma tafi yadda ta tsara. Sai tasa Pareto ya kashe mata wutar harabar wajen gabadaya. Sai wata 'yar kankanuwar ‘dim light’ ya bari.
Ta dawo daki tana cewa Aisha “Pretty biyo ni muje cikin Ranch, amma don Alah kada ki tambayeni komai”.
“Kiki ho!” In ji Aisha, da alama dramomin Kiki ba masu karewa bane. Haka tabi bayan Kiki zuwa cikin gidan gonar.
Kiki ta kama hannun Aisha ta zaunar da ita a kujera ta kuma karbe wayar Aisha ta rike don ma kada Aisha ta haska wajen da wayartata.
Komawa tayi neman Uncle cikin gidan har dakinsa, acan ta samoshi idar da sallahr isha’insa kenan yaji knocking din Kiki. Saida ya kwashi mintuna kafin ya taso ya bude don yasan bazai wuce ita din ce ba.
Casual wears dinsa ne a jikinsa kamar kullum wato shirt da dogon wandona Mark Jacobs. Harda farin karamin cazbaha a hannunsa. Yana bude kofar Kiki na kamo hannunsa.
“Uncle don Allah biyo ni, amma kada ka tambayeni komai”.
Inda sabo Prince ya saba da rigimar Kiki da dramarta kala-kala, haka ya yarda ya bi bayan Kiki zuwa bangaren data keso suje na gidan.
Bai kuma tambayeta din ba har shima ta zaunar dashi a kusa da Aisha yana cewa,
"me ya faru aka kashe wutar wajen nan haka? Ina Pareto?"
Kiki tasa lighter tana kukkunna candles din cake din, sannan ta kunna fitilar wajen haske mai ni’ima ya wadata ya gauraye wajen. Kiki na dariya tana clapping hannayenta. Ta soma wakar.
“Happy birthday Uncle AK!”.
Sai lokacin duk suka fahimci me take nufi. Da abinda ta shirya. Wato sai lokacin ma Hamma ya tuna yaune zagayowar ranar haihuwarsa shekaru 43 a duniya.
Excitement dinsa ya kasa boyuwa, domin ko ba komai Kiki ta bashi babban surprise din da ya sashi dariya, diyar nan tashi Ruqayyat tana matukar kaunarshi, ko bai haifi da ba a duniya ya godewaTaiwo data haifa masa Kiki.
Kiki tana kula tana kuma sane da komai nasa, don shi ya manta ma.
Duk da ba wai yana celebrating ranar haihuwarsa bane a baya a kowacce shekara, amma idan ranar ta zagayo, Nenne da Dade su kan kirashi suyi masa fatan alkhairi da addu’a, shikuma ya kan kara ninka sadaqarsa ga gidan marayu, a kowacce ranar birthday dinsa.
To yau wayarsa tana kashe, domin ya baiwa kwakwalwarsa hutu.
Ta cikin hasken candle lit din ya juya yana duban Aisha dake gefensa, sai ya ga ta koma masa tamkar furen fulawa don kyau. Kamar an kara wanketa an canza mata launin fata, sakamakon wannan sassanyar kwalliya mai tsari da Kiki tayi mata, serene make-up din ya amsheta sosai. At long last! Yau shi Abdulrasheed ya cika shekaru arba’in da uku tare da matar aure by his side (a gefensa).
Auren da bai taba zaton yiwuwarsa gareshi a gidan duniya ba. Tabbas aure lokaci ne dashi ga kowanne dan adam, komin tsarin daka yi masa, idan lokacinsa ya zo daga Allah ko mutum yanaso ko baya so zai tabba dashi.
Prince ya sakarwa Aisha kyakkyawan murmushinsa, wanda bai san lokacin da ya subuto masa daga zuciya zuwa fatar bakinsa ba, ganin itama kallon shi take yi yau da dukkan admiration na mace ga miji cikin idanunta.
Ta kasa ce masa “happy birthday” din ita sabida kunya, amma a cikin zuciyarta ta fada ta kuma maimaita, har ta kara da cewa,
“Allah ya karawa rayuwarka albarka the Great Prince of the Ilorin Emirate”.
Kiki ta hau hure candles din dake bisa kan cake tana cewa.
“Bari toh in huresu, a madadinka Uncle!”.
Ta hure candles din duka. Tace sai Uncle AK ya yanka cake dinnan nasa da kansa.
Nan ma dai Hamma dariya ce ta kama shi, da girmansa gemai-gemai za’a ce ya yanka cake! Yace Aisha ta yanka a madadinsa.
“Lets the wife represents the husband”.
Kunya ce sosai ta kama Aisha irin wadda bata taba ji ta Hamma Prince ba, a yau da ya dangantata da matarsa.
A karshe sai Aisha da Kiki ne suka hada hannu suka yanka cake din tare. Aisha ta zaftaro katoto tayi bakin Kiki dashi, sai Kiki tayi kwana da hannun Aisha zuwa bakin Hamma Abdulrasheed (Prince).
Ta kuma yi maza ta daukesu hoto. Aisha tayi dumu-dumu da bakin Hamma da cake. Daga Aisha har Prince kunya ce ta kamasu da wannan hoton da Kiki ta dauka don idonsa yana kan Aisha, babu irin wannan shaquwa da sakewar a tsakaninsu kafin zuwan Kiki. Don haka Kiki ta zama rahma ga auren ma’auratan nan.
Kiki ta cigaba da waka a wurin tana musu hotuna tana wakar.
“Happy Birthday Uncle Abdulrasheed Kehinde!”.
Daga nan ta bubbude foil paper da aka rurrufe abincin dashi, ta zauna itama tana fuskantarsu suka soma cin dinner din tare.
Suna ci suna hira gwani ban sha’awa, Kiki nata basu dariya da hirarrakinta na wauta, suna gamawa Prince ya kunna wayarsa ya zagayo hannunsa ta gaban Siddiqah, yace da Aisha,
“dan matso nan Siddiqah muyi selfie nida ke, cikin wayata saboda tarihi!”.
Ba karamar kunya ce ta lullube Aisha ba, lokacin da Hamma ya kashe kyawawan fuskokinsu shi da Aisha da flash din dalleliyar camarar wayarsa
Idan da Kiki zata yi duba da duk abubuwan da ke faruwa yau, da wadanda suka faru tun zuwanta, sai ta godewa Allah, domin kuwa ta samu ladan wadannan ma’auratan. Zuwanta yayi riba.
Tayi silar abubuwa na farin ciki da yawa a gare su, da cigaba cikin irin zaman da ta tarar suna yi. Don kafin zuwanta wani irin zama suke yi kamar na ‘jahiliyya period’.
Don yafi gaban a kira shi na doya da manja don baza’a kira shi zaman aure ba. don kuwa alhakin juna suke dauka. Zuwan Kiki ya haska gidan. Ya hurawa zukatan ma’auratan ruhi. Sai mu ce madallah da Kiki-Ruqayyat, madallah da zuwanta gidan a wannan lokacin.
Kiki zamewa tayi ta bar su a wurin da cewa zata je ta dawo. Ganin Prince duk hankalinsa na kan Aisha. Yau Prince da Aisha ne zaune dab da juna, har ya samu kansa da janta da hira.
“Siddiqah bani labarinki mana? Tunda kikazo kin kunshe min baki, bansan kina walwala haka ba sai bayan kawarki tazo ko?”
Aisha ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran ‘yan yatsunta tace “Uncle me kake son sani a kaina?” A takaice Prince ya ce da ita.
“Komai!
Tun daga labarin iyayenki, ‘yan gidanku, samarinki, kawayenki da makarantar ku.
Yadda kika tsinci kanki a auren Bayerabe alhalin kina bafullatana mai kin yarbawa da sauransu.
Kin ga ni na tabbata kinsan komai a kaina a gidanmu, amma ni har yau bansan da wa nake zaune ba, banda cewa ina tare da matar aure na kawai”.
Aisha ta rufe fuska da zara-zaran yatsunta tana cewa cikin murmushi.
“Hamma Abdul, banida labari ne ni, gidan mu ba kanne ba yayye, nikadai ce ‘ya a gidanmu. Nice yar kaina nice kanwar kaina.
Samari kuma bana sauraron kowa sai Ishaq Nafada.
Kawayena na makaranta kuwa sunada yawa, babbar aminiyata a cikinsu Amintako ce, sai Ramatu da Ruma, don ni dinnan da kake ganina shiru-shiru a gidan ka ‘gang leader’ ce dake shugabantar fitinannun yara a makaranta.
Sunan makarantarmu FGC Billiri Gombe.
Yadda nayi na samu kaina da auren bayeraben miji bazan iya cewa ba, illah ince wata addu’a ce ta Ummanka ta filin Arfah, ta fado a kaina ni Siddiqah, kamar yadda Ummata ta bani labari nima”.
Prince ya soma dariya kamar bashi ba, bai zaci Aisha haka take da baki ba, yace “wato Nenne addu’a tayi akaina, sai ta fado a kanki ko Aishahh?”
Ta sake rufe fuska tana dariya ta ce “exactly, sosai kuwa, wata irin zazzafar addu’a tayi a inda Allah baya juyarda addu’a, don Ummana ta ce da ta ji Nenne tana addu’ar nan a lokacin, a take a zuciyarta tace inama zata ganshi ko waye shi ta bashi PETEL dinta!
Sai Allah yayi ta tsara abubuwan daki-daki yadda ya ga dama, suka yi ta faruwa subsequently (wani na bin wani).
A rayuwata ban taba jin wani abu mai kyau game da kabilar Yarbawa ba, sai bayan da Nenne ta dauke ni zuwa gidanku a birnin Ikko.
A nan ne Yarbawa iri-iri suka goge min hadda, tun daga kan ma’aikata da masu girkin gidan, na fahimci cewa Yoruba kabila ce mai matukar daraja a Nigeria, kamar Hausa/Fulani.
Dana zo Argentina na tadda Prince of the Ilorin Emirate, sai ya karasa wanke duk wata negative hadda dake cikin kaina akan Yarbawa, don na gane cewa Prince din Bayerabene na gaske, mai alfahari da kabilarsa. Da bakinsa ma ya fada min; he’s a proud Yoruba man.
Don haka ni yanzu duk inda naga Yarbawa tsakanina dasu girmamawa ce da karya hula, sanadin kaunata dasu”.
Prince ya lumshe ido cikin murmushi, kowacce kalma dake fita daga bakianaata tana masa dadi, ya budesu a kanta yana cewa.
“Aisha frank kenan! Naji wannan, na kuma taya yarbawa bakidayansu murna da kika cire musu kabilanci daga dictionary dinki.
Bayan wannan zan so in san wane irin so kike yiwa Ishaq? Ina nufin yaya kike jinsa a ranki kafin auren ki da Bayerabe da yanzu bayan auren?”
Aisha ta hau ‘yar dariya tana cewa.
“Uncle me yasa ka tambayeni wannan? Babu kyau binciken abinda yaa riga ya wuce”.
Kai tsaye Hamma ya saka idonsa cikin na Aisha ya dan budesu cikin nata. yace “because I am extremely jealous of him!”.
Aisha ta sunkuyar da kai tana jin wani irin dadi a zuciyarta, amma tana so ta baiwa Prince wannan amsar koda zai ji babu dadi. Ba don ta goge kishin da yace yana yi akan Ishaq ba, sai don ita ‘yar keke da keke ce tun asalinta, bata da rufa-rufa (frank).
“Ina son shi sabida he is caring. Kullum muke tare sai ya gaya min how much he cares and loves me. Baya gajiya da gayamin muhimmancina cikin rayuwarsa duk da kankantar shekaruna.
Na taso na san shi a matsayin fiancé dina shikadai na saba da shi na kuma shaku da shi. Rana daya aka ce an bada ni ga waninsa kuma Bayerabe da ban ko taba gani ba.
Ka gayamin in kaine ni yaya zaka yi? Ai dole ka yi dan protest ko? Musamman daka gane cewa shi wannan da aka mallakaka gareshi din bai ma san da kai ba, bai damu da kai ba, bai san kana existing ba, kuma baka cikin lissafinsa a rayuwa”.
Hawaye suka digo mata tace “it’s not easy, ina gaya maka Hamma, it’s not easy, don ma na roki Allah juriyane, da danganar karbar rayuwa a duk yadda ta riske ni”.
Amma bayan nan ina dadewa ban tuna Ishaq ba, na yarda “he is my past, I don’t have a present”.
Ba don komai nace haka ba Uncle sai don kasancewar Uncle AK da aka aurar dani gareshi rana daya bana cikin lissafinsa.
Ya karbeni a gidansa ne kawai kan ba yadda zaiyi da umarnin mahaifinsa”.
Hamma yace cikin karfafawa.
“Prince Abdulrasheed yanada past mara dadi akan mata, kin zo rayuwarsa a lokacin da ya tsani mata, bashi da sauran hope akansu. Amma duk da haka Prince zai yi kokari ya komar da hannun agogo baya, wato ya yi kokarin manta past dinsa, ya karbeki a gidansa da rayuwarsa a matsayin present dinsa, don radin kansa ba don tursasawar iyayensa ba, hakan zai faru ne only ranar da kika daina yi masa kallon BABANKI!”
Da sauri Aisha ta rufe ido da tafukanta cikin jin kunya daidai lokacin da Kiki ke tahowa garesu. Tana karasowa tace “Uncle AK zan dauki Uwata haka, lokacin barcinmu yayi, in ya so ka kawo kayan zance sai in barka zuwa tadi!”
Hamma ya zaro ido yace “Kiki, kina maida ni Kakanki koh? Zan yi maganinki aure zan yi miki soon”.
Koda suka koma cikin sitting room Aisha da Kiki kallo suka kunna a falon, suna kallon girke-girke a Netflix. Hamma dakinsa ya wuce cikin wani yanayi. Domin maganganun Aisha bakidaya na yau sun zame masa food for thought.
Ya kasa barci a daren nan ya samu kansa da kallon selfie dinsu shi na birthday shida Aisha, da tuna hirarrakin da suka gudana a tsakaninsu. A daren yau Prince yayi abinda bai taba yi ba, wato yin rubutu a shafukansa na social media.
Domin bayan ya kasa daina kallon selfie din, sai ya budo status dinsa na whatsapp, yayi wani rubutu mai matukar jan hankali da shikadai yasan ma’anar kayansa, a kasan hotonsu shi da Aisha, bayan yayi covering fuskar Aisha, amma gangar jikinta ta fita gaban candle lit cake.
“Happenings at 43rd Birthday ….. !!!
The wife that is slowly becoming the centre of my universe”.
**** **** ****
Wani ikon Allah Taiwo ce ta fara ganin status din brothernta. Ta sha mamaki ganin yau Kehinde ya dora status don baya yi sam. Don haka da doki da zaquwa ta bude don taga me Kehinde zai daura?
Ta kuwa ci karo da wannan magana da hotonsa shida Aisha, da suka yi matukar daure mata kai. Me Kehinde ke nufi? Ya folawa wannan yarinyar ko yaya ne? Nan take tayi screenshot cike da takaici da tsegumi ta turawa Haseenah.
Washegarin ranar Kiki tayi musu sallama ta wuce makaranta bayan Kawun nata ya cikata da duk abinda zata bukata, har ma da wanda yafi karfin bukatunta.
Bayan wucewar Kiki Aisha duk ta canza wa rayuwar gidan, dan fitowa falo da take yi duk ta daina. Aisha ta maida kanta daddawar daka, gabadaya walwalar nan da ta ke yi sanda Kiki ta ke nan ta dauke daga fuskarta ta komar da kanta yadda suka saba zama ita da Hamma tun kafin zuwan Kiki.
Duk inda miji yake sunansa miji, da soyayya ko babu, to hakan ce ta faru Prince Kehinde, bayan tafiyar Kiki da canzawar yanayin Aisha, duk sai ya ji ya damu. Ya shiga takura da canzawarta da rashin fitowarta falo yadda suka saba. Ko da ma can shi Aisha tausayi ta ke ba shi, balle yanzu daya fara sanin wacece AISHA-SIDDIQAH.
Zaman Kiki ya haifar mata da walwala mai yawa, ya fara bankado masa asirin dake kunshe a zuciyar Aisha, ya ga excitement a tare da ita, irin wanda bai taba gani a tare da ita ba, kafin zuwan Kiki. Sai Hamma yaga cewa zai yi kokari ya maye mata gurbin Kiki, wato ya zame mata babban aboki kuma dan uwa, wanda zata iya yin dariya da walwala tare da shi idan har zata yarda da hakan. It’s not easy a rabo ka da iyaye, dangi, kasarka da kowa naka sannan a barka cikin damuwa.
Yau kwanan Kiki hudu da wucewa, kuma tun lokacin ganinsa da Aisha sau daya ne tak! Ya zauna a falon har ba adadi domin ya ga gilmawarta ko don ya tabbatar da lafiyarta amma ko kamshinta bai ji ba.
Aisha wadda ta koma daddawar daka tun bayan tafiyar Kiki Ruqayyyat, ko kiraye-kirayen waya data ke wuni tana yi da jama’ar gidansu dana gidan Nenne yanzu ta rage. Ta fi yin tilawar Alkur’ani da nafilfili a cikin dakinta, sai ta tabbatar Hamma ya fita ‘Ranch’ ta hanyar hango shi cikin stable din dawakansa ta tagar dakinta take fita kitchen ta dafa taliyar indomie da bakin ruwan tea, tayi maza ta juye a flask ta shige daki shikenan.
Dama Kiki ce ta matsa suke cin abinci tare dashi. A rashin Kiki kuwa, sai ta maida musu rayuwarsu ta tun asali irin yadda suka fara ta.
Duk iya juriyar Prince da dakewa da jin sarauta, ya kasa yin biris da wannan silence din na Aisha. Da canjin data kawo musu. Because it’s killing him inside.
A can dakinta