Showing 18001 words to 21000 words out of 45634 words

Chapter 7 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

bada list, don yawanci ire-iren abincin da Hamma yake ci dinne aka kawo kayan dahuwarsu. Bata san cewa restaurant din da yake karbar abinci Pareto yaje ya karbi lissafin komai ya sayo mata ba.
Ta maida komai inda ya dace ta canza daga yadda Pareto ya ajiye shi, tazo da guzurin spices dinsu na yarbawa da sauran kayan kara aroma din girki. Nenne har yajin borkono da tasan bata rabo da cinsa ta sa an daka mata ta hado dashi cikin kayan ta, sai ta dauko su duk tayi musu mazauni a ma'adanan kitchenette din. Daga nan Siddiqah ta zage ta hau girki. Tana yin abinta cikin dadin rai domin sosai take jin dadin aikin da take yi din. kafin awa daya ta kammala duk abinda tayi niyyar yi ta taimakon injinan saukaka girki.
Ta ajiye masa nasa anan kan dining da yake zama yaci. Ta debi wanda zata iya ci ta shige dakinta ta rufe.
Prince sai sakkowa yayi ya tadda breakfast mai rai da lafiya an shirya masa, plantain, chips, da moi-moi, sai kunun acca da yaji madara wanda shima Nenne ta koya mata.
Bayan ya san ba abunda ya baiwa Pareto order kenan ba. Amma wannan din ya bashi sha'awa sosai don haka ya zauna da kyau ya soma ci.
Har yaci ya gama bai san ita tayi ba, saidai tabbas yaji dandanon abincin ya canza a bakinsa, sannan kunun ya bashi mamaki, tunda bai taba odarsa anan ba. Nenne ce kawai take yi masa, kuma wani ikon Allah bai tambaya ba.
Yaci yayi nak, with excitement ya mike, tana hangoshi daga bayan curtains din dakinta sanda yake cin abincin har ya gama ya fita jogging din safe cikin gidan gonar inda acan zaiyi excercise dinsa.
Aisha da tayi wanka wajen karfe 10 na safe wata riga t-shirt mara nauyi da dogon siket baki ta saka ta haye gadonta ta dauki wayar da ya bata tana danne danne.
Kamar yadda Prince yaki bata lokacinsa ya koya mata amfani da wayarsa ta yarda komai sai in baka sa kanka ba, amma yanayi (condition) na bukatuwarka da abin zai sa ka koya komai wahala ko rashin wahalarsa.
Don kuwa a hankali tana bin umarnin wayar sai gashi ta gane yadda zata saka lamba tayi kira, da yadda zata yi chatting ta whatsp da sauran social media platforms.
"Umman Siddiqa" wato Ummanta Haj. Zainab Yunus ita Siddiqah ta fara kira (with nostalgia).
Haj Zainab ko da taga lambobi rankatakaf na kasar waje data kasa gane ko daga ina suke jikinta ya bata matafiya an sauka lafiya a kasar Argentina.
Tun tafiyar Siddiqa take ta binta da addu'a tun komawarta Lagos daga sallamar da taje musu kan duk inda ta samu kanta a gidan aure Ubangiji ya zama gatanta, ya huwwace mata tausayin mijinta, tarbiyyarsu ta zame mata jagora.
Tana dagawa din kuwa sai taji muryar Petel dinnata. Tana fadin
“Ummana kina ina? Petel dinki nata kewar ganinki tun jiya. Na sauka lafiya a Argentina Ummana”.
“Petel dina am miyelwa mi, kada ki damu da tunanin kowa, duk muna lafiya cikin alkhairi, aure neya gaji haka kinji ko Petel dina?”
Kukan shagwaba ya zo. Aisha ta soma sheshsheko shi, Umma tayi maza tace “lala-lala Petel, in haka ne zan daina daga kiranki, Petel din Umma. Ko bangon duniya suka tura ki kije ki zauna da mijinki lafiya kinji Petel dina.
Banda rashin karar nan taki da nasanki da shi da keke da kekenki, watarana ‘ya’yanki zasu yi miki fiyeda wannan biyayyar da kika yi mana in sha Allahu”.
Da kyar ta samu Petel ta hadiye kukan shagwabar suka koma hira. Ta tambayeta ya ta samu bakon wurin da maigidan nata?”
Siddiqah ta soma magana cikin tsananin gaskiyar dake ranta cikin fulatanci.
"Uncle AK yanada kirki Umma. Kinga har wayarsa ya bani, don in sake in ji dadin zaman gidan, kuma in nayi masa magana yana amsawa. Amma Umma idan na tuna shi din bayerabe ne, duk kyawunnan nasa irin na Nenne, sai inji wani iri a raina….”.
Bada niyyar labe Prince yazo dakin nata ba, yazo ne ya tambayeta koda abinda babu na cefane da shoppping yasa a karo mata saboda zai yi tafiya har ta tsayin sati daya. Sai kawai ya tsinkayi tana fadar hakan ga mahaifiyarta a waya cikin harshen fulatanci.
Bai fasa shiga dakin ba yasa kai ya shigo da sallama, duk kunya ta kama Siddiqah.
Umma na fadin.
“Akul Petel, ko Allah hoddiri fe’an, be tagu fe’an (wato abinda Allah ya riga ya rubuta mata kenan wanda babu makawarsa). Zaman aure ba ruwanshi da kabilanci.
Tayi maza ta kashe wayar cike da fargabar ko Uncle yaji me take gayawa mahaifiyarta akansa? Sai kuma ta cewa kanta ai ba lallai ya zama yanajin fulatanci ba yarbanci da turanci kawai ya ke ji.
Da wannan Siddiqa ta karfafi kanta ta mike daga kwanciyar, ta boye wayar a kasan filonta duk guilt ya baibaye fuskarta.
Hakika Prince yaji abinda take fadi din don shi yama fi jin fulatanci sosai har fiyeda harshen Yoruba, don dashi Nenne ke masa magana tun yana yaro har girmansa haka Nani Oummana.
Har ransa yaji wani iri shima, kwatankwacin abinda kanwarsa Fatima ta gaya masa kenan akan Siddiqah wato har yanzu kabilancin nata da saura. Ba tareda ko a fuska ya nuna mata yaji ba, sai kawai yace,
“Madam din gidan nazo in miki sallama, koda abinda kike bukata? Zan dan yi balaguro na wani lokaci".
Siddiqah wadda ke ta fama da kayan guilt dinta, wanda ya kusa nutsar da ita cikin kasa don kunya kasa amsawa tayi. Nan dai ta hau 'yan mutsu mutsu na rashin sanin abin cewa, da ya ga ta kasa bashi amsa duk ta takura da guilt, sai yayi murmushi kawai ya juya ya fita abinsa.
Kai tsaye dining ya nufa, ya zauna yana kokarin hada coffee, amma koda ya hada din ya kasa kaishi bakinsa sai juyawa yake da cokali a hankali.
Tambayar kansa yake ko ta yaya zaman aure zai yi dadi tsakaninsa da Siddiqah tunda ita ga alkiblarta akan kabilarsa?
Ya tambayi kansa yaushe ne za’a daina nunawa juna kabilanci tsakanin hausa Fulani da yorubawa ne? Yoruba da yawa da ya sani ko a cikin Akannis akwai wadanda basa cin abincin hausawa, da an ambaci bahaushen mutum kallon wani jaki, dakiki suke yi masa.
Shikuma a matsayinsa na bilingual babu wanda zai ce ya fifita tsakanin wadannan kabilun, duka yana girmama kowanne saboda Nenne da kuma Dade dinsa da suka fito daga cikinsu, don haka Hausa/Fulani da Yoruba, basu da banbanci a wurin Prince.
Sai ga Siddiqah ta fito falon kamar mara gaskiya. Prince don ta saki ranta da kansa ya ja mata kujera yace ta zauna. Zamanta keda wuya ya juya harshe zuwa fulatanci gangariya, yana tambayarta me zaya zuba mata cikin kalolin abinci na kasaita da yasa aka kawo wajen dake jere bisa tebir?
Shikuma Prince abinda yaji ta fada ne yasa yake son tabbatar mata yana jin fulatanci fa, ba ita kadai ce bafullatana ba, yanaso dai ta sabawa ranta da kasancewar asalinsa Yoruba ne ba canji. Yanada kyau tasan cewa Bayerabe ta aura (a proud one)!”.
Abinda tayiwa kanta alkawarin ta daina a gidan Hamma, wato kuka, shine ya dawo mata yanzu domin tasan tayi kuskure. Siddiqah sai ta kifa kai a saman tebur din daya raba tsakaninsu ta fara rera masa kuka babu gaira babu dalili, wani irin kuka na zallar shagwaba da ya nuna kuruciyarta a fili, kukan wanda yafi kamata a kirashi ‘na borin kunya’, a dalilin ganewa da tayi cewa Hamma Prince ya jita tsaf, a lokacin da take cewa tana jin wani iri a ranta da kasancewar sa ‘Bayerabe’ ga Ummanta mahaifiyarta.
Shi kuma gani haka wato ganin guilt yayi mata yawa sai ya saki fuska sosai, daga dan dauretan da yayi, don baya son kukan mace a gabansa taba shi yakeyi sosai, Hamma ya koma magana cikin turanci, da dan murmushin bagararwa a fatar bakinsa, don ya kwantar da hankalinta.
“Me akayi miki na kuka? Share hawayenki ki ai bakin alkalami ya riga ya bushe miki, ki shirya zama na har abada da Bayeraben miji, don wani abu muhimmi a al’adar gidanmu babu ‘sakin aure’. In akayi anyi kenan har abada, da so ko babu.
Munada kishi mai tsanani akan iyalanmu, kishi irin mai lasting har gaban abada. The Akannis’ sun san ciwon matansu sosai. Bama taba auren mace mu hada irinmu da ita, daga baya mu barta wani ya aura. Ke ko ko bamu hada iri ba wato ko ba’a samu rabo a takani ba in dai mun aureta bama taba sakinta.
A takaice sai ince miki Bayeraben mutum yafi bahaushe/bafullatani kishi da rukon aure da kyau. A wurin bahaushe ne kawai zaki ga ana saki da sake-saken aure anyhow.
Nima biyayya na yiwa Dade na karbeki a gidannan as a Fulani girl, but I never planned it. Duk da ni bani da preference na matar aure daga kowacce kabila. But honestly what Hausa/fulanis are doing to Yoruba tribe is extremely bad. Islamically (a musulunce) mun san cewa Ubangiji yace “Inna akramakum indallahi Atqakum”, above all kuma kalmar shahada ta riga tayi binding us together. Then why the disgust?
Idan aka duba ta fuskar kishin kasa ma, ya kamata a daina kabilanci gabadaya tsakanin kabilun Najeriya. Mu yarda cewa mu din duka WA-ZO-BIA ne. Idan muka yarda muka karbi hakan zamu zauna lafiya cikin girmama darajar kabilar juna".
A cikin muryarsa akwai maturity na yawan shekaru, akwai amo (tone) mai nuna sanin ciwon kai, sannan at the same time a cikin muryar Prince din akwai lallashi, sabida kukan data soma yasa yaji tausayinta sosai. Domin ya fahimci kalar nata kabilancin kamar nature dinta ne, tanada kabilanci sosai da ya kasa boyuwa a ranta.
“Ai kuwa in baki yimin shiru haka ba, ni kuma daga yau zan fara yi miki magana da Yarbanci kullum, har sai kin kware kin fini iyawa".
Dan murmushi ya subucewa Siddiqa tasa bayan hannu ta share hawayen, taji dadin yadda bai dauki abin da zafi ba shi kamar Fatima. Kodayake dama hankalin namiji irin Hamma dana yarinya mace kamar Princess Fatima ai ba daya bane.
Suna haka hankalinsa ya rabu biyu sakamakon ana ta kiransa a waya ya kasa dauka sabida Siddiqah taki daina matsar ido, mai kiran kuma bai fasa kira ba, da kyar ya daga wayar ya amsa sai yaga ashe Aunty Murjanatu-Taiwonsa ce.
“Kehinde wai da gaske ne?”
Abinda Aunty Taiwo ta fara tambayarsa kenan. Ya ce.
“Menene fa?”.
“Fatima ta gayamin su Dade sun turo maka yarinyar nan har Argentina?”.
Yace “Exactly, gata nan ma a zaune a gefe na”.
Taiwo kamar ta kundumo masa ashar shida wadda yace take kusa dashi din, sai ta tuna Dade da kansa aka ce ya tura ta, karewa ma shi yaje yasa ta a jirgin Argentina ta tafi ga Prince din. Taiwo ta rasa me ya samu iyayensu akan yarinyar nan. Duk girman Dade ace shi da kansa yaje ya saka ta a jirgi. Taiwo tayi shiru kamar zata yi kuka, can kuma tace.
“Kehinde kuma ka yarda ta zauna a gidanka? Harda wani gata a gefenka, to uwar me take maka a gefen naka, wannan bakauyar yarinya haka?
Kehinde kada kace min zaka iya kwanciyar aure da kucakar yarinyar nan?”
Dariya sosai da kunya maganar Taiwo ta baiwa Prince Abdulrasheed. To in bai yarda ya karbeta a gidansa ba yaya zaiyi da ita? Bayan saida ta taso ma aka gaya masa ba shawarar sa ko amincewarsa aka nema ba?
Prince yace da Taiwo “wace irin Magana kike haka? A matsayin Dade da Nenne garemu, kin ga ya kamata in sakota a jirgin da ya kawota ne in maido musu ita? Kigayamin tsakanin Dade da Nenne waye abokin sa'in'sa na?”
Taiwo ta kasa magana na ‘yan dakikai, don ta san Kehinde ya fita gaskiya, amma in itace zata iya yin bore ta maidata din, saidai suyi hakuri su bi ra’ayinta, Kehinde yanada gudun zuciyar Dade da Nenne fiyeda kima shiyasa iyayen nasu ke samun damar takura masa.
Ita da yake sun san halinta ba irin nasa bane wa yake shiga rayuwarta ko ace lallai ga abinda zata yi har a nemi tursasata alhalin tana cikin shekaru in her forties? Tsoron da take daya ne da zaman yarinyar nan kusa dashi a gida daya, tasan maza basu da hakuri akan sex, balle Kehinde da ya kusan fita shekarun kuruciya ba aure babu sabon Allah ta wannan fannin, tana da yaqinin cewa Kehinde baya neman mata a waje, duk yadda suke binsa kuwa as a celebrity, Taiwo tana cikin fargabar kada tsautsayi yasa Kehinde ya hada jiki da yarinyar bisa rashin kauda kai da matsuwa da rashin sanin darajar kai akan sex irinna maza, yaje haka kawai su yi masa surkullensu na Fulanin kauye da basu waye basu san komai ba sai kwadayi, don bazata yi jimilla a fulanin ba, su wadannan wato (Siddiqa da iyayenta) irinna kauye take kallon su, haka kawai taje a mallake mata dan uwa, don dai bata tashi taga bangaren su Nenne na surkulle ba, gashi kuma dai ance itama yarinyar daga Gombe ta fito. Kafin ayi haka Taiwo taji wani mikakken tsaki ya kwace daga bakinta, tace.
“Kabi a sannu dai, wannan yarinyar kwatakwata ba ajinka bace Kehinde, class matters a lot in marriage, know how to relate with her don gaskiya da sake”.
Ta kuma kashe wayarta cikin kunan rai. Kamar ita aka yiwa auren dolen, auren zubar da class ta bakinta. Yadda Prince ya dauki al’amarin da sauki, ba haka twin dinshi Taiwo ta daukeshi ba, gani kawai take an cutar da Kehinde dinta.
Yau ba don tana tsoron iyayensu ba, ko kuwa da ace ba su suka auro masa Siddiqah da kansu ba, sai ta raba aurennan ko ta halin kaka.
Dariya sosai Taiwo ta baiwa Prince da daukar dumar magaji da nishinta.
Ya tambayi kansa dama ashe aure yanada class ne? Shi bai taba sanin haka ba. A saninsa Sarakuna har bayinsu da ‘ya’yan bayinsu suna aura suyi (sa-dakoki) dasu su haifi ‘ya’ya kuma tare dasu.
Eh toh, ita Taiwo tana nufin yarinyar irin ‘ya’yan malam Shehu ce, tunda kuwa yaji ance yariyar ba ‘yar sarauta bace, ba kuma ‘yar masu arziki ba, irin wadanda ya kamata ya aura a matsayinsa na Prince of the Ilorin Emirate, amma a saninsa duk ba wannan ne ya hanashi aure tuntuni ba shi, tunda kuwa ta kowanne bangare tafi Haseenah da yayiwa hakikanin SO na soyayya akan radin kansa cikar martaba, asali, da kyakkywar nasaba.
Ko babu komai ita duk sanda aka ga dama za'a je aga iyaye da danginta, koda basu da komai ya tabbata sunada asali, tunda har Nenne da kanta ta ga dacewar auro masa ita saboda kwadayin wata nagarta data gani a tareda mahaifiyarta.
A kwana shidda kadai da zuwan Aisha tsarin kitchen da sitting room din Prince ya canza, komai ta maida shi yadda tafison ya kasance. Aisha ta canzawa kanta da kanta rayuwa a gidan Prince Abdulrasheed Kehinde.
Kullum zaka sameta cikin tsafta da wanka da shiga mai kyau kuma ta mutunci. Taga cewa zaman me zata yi in bata motsa jikinta? Koda take son cikowa bata son irin kibar Fatima. Ta soma koyawa kanta gyaran sitting room din da kitchennette din, da kawar da duk abinda suka ci abinci ta wanke ta goge ta kife. Sannan ta fara sanyawa gidan turaren wuta masu tsananin dadin kamshi da Nenne ta hado mata.
Ba'a jima ba ta gane yadda ake amfani da daukacin electronic appliances na gidan su dish washer, kunna dispenser, washing machine don wanke kayan ta data yi amfani dasu, ta hanyar karanta manuals dinsu.
Cikin kwana na bakwai da zuwanta Aisha ta fahimci da yawan abubuwan amfanin gidan, ba tareda an koya mata ba, ta fara goge kauyancin data zo dashi kaso hamsin cikin dari, sai dan abinda ba’a rasa ba.
Idan Aisha tayi girki ta kan tambayeshi idan ya fito ko zai ci? Sai yace yayi order. Don Prince ganin Aisha yake bazata iya wani girki da zai iya ci ba har guda nawa take? Siddiqah bata wai damu ba, sai ta dafa iya na cikinta ta kwashe a warmer tayi shigewarta daki da abinta.
Prince ya zo Argentina ne domin ya huta, don haka zuwan Siddiqah na bagatatan dinnan baya ciki abubuwan da ya tsara a hutunnan nasa, don haka satin siddiqah biyu kenan amma abubuwa sunki yi masa normal, na farko ji yake tamkar a kansa take zaune tsabar ya kasa sabawa da zaman matar aure da motsinta a cikin gidansa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login