Showing 42001 words to 45000 words out of 45634 words
Chapter 15 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt
dinga kiransa don jin ya jikin Maimartaba. Amma ba ta yi hakan ba sai yanzu?
Bai san cewa ita Siddiqah ko digits dinsa bata yi saving a wayarta ba, saboda bata dauki auren nasu da wani alkibla a baya ba. Bayan zama na biyayya.
Amsar da Hamma ya bata nan take, duk da a gajarce ne, showing nothing, shi ya ba ta kwarin gwiwar kiransa.
Kirjinta da zuciyarta baki daya suna harbawa a cikin kirjinta, don yau ji ta ke Hamma na samun wani special reception a gunta, data dangata shi da tausayinsa.
Yana kallon lambobin Siddiqah suna shigowa da mamakin kiran kamar ta san me yake sakawa a ransa, shi yana da lambobinta ai, kasancewar layin da wayar duka nashi ne a baya.
Kuma daya bata din, sai ya yi saving da sunanta, sunan da zuciyarsa ta ga damar bata a lokacin, wato “Baby”, don a wurinsa Siddiqah jaririya ce kamar yadda Kiki take a idanunsa.
Sai da kiran ya yi dab da katsewa Prince ya amsa,
Aisha ta tausasa murya tace.
“Assalamu alaikum!”.
Sai kuma ta yi shiru tana shirya abin fadi, don duk wata hikima da ta ke da ita a lokacin subucewa ta yi. Prince ya ciccibe ta, ta hanyar amsa sallamarta.
Sai ta samu kwarin gwiwa ta yi masa ta’aziyya ta fatar baki. Hamma ya yi godiya sannan ta ce a raunane,
“Uncle yaushe za ka dawo?”
Shi kuma ya amsa, “Ranar dana tashi daga Uncle dinki!”.
Siddiqah sai ta yi wani murmushi mai kyau kamar Hamma yana ganinta. Yace “Ko ba haka kika ce ba, kallon kamar Babanki kike min ko Aishah?” Girgiza kai kawai tayi kamar yana kallonta amma ta kasa amsawa. Prince yace “To yaya gidan ince ko babu matsala?” “Babu matsala Hamma, gidan kawai yayi tsit da baka nan babu dadi”. “To ko in aiko miki ticket ki taho duk da gashi ina shirin komowa?” “Tunda zaka dawo soon ai bai kamata kuma in taho ba, zan yi hakuri harka dawo”. “Yaushe har kika damu da presence dina ai ba wani banbanci da ina nan da bana nan a gunki Aisha, ba kya sakin jiki dani tunda Kiki ta koma”. Aisha taji wani irin dadi a ranta, (something more of excitement). Hamma ashe yana yinta, koda ita bata damu dashi ba.
Murmushi Aisha tayi ta sake rike kan wayarta sosai a kunnenta, tace “ina kara yi maka ta’aziyya Hamma Abdul. A gaidasu Maman Kiki”.
Prince ya amsa da cewa, “Za ta ji, yanzu ta bar nan, ina fatan idan na dawo inga canji, kuma duk abin da kike so Pareto was there to help, he is always at your service”.
A tare suka ajiye wayar, Prince na ajiyar zuciya ya ce a ransa, ita Aunty Murja din tana nan tana binki da mummunan kulli, ke kina cewa a gaishe ta Aisha.
Tana fatan kada a hada zuri’a da ke, ‘yar mallam shehu. Tana neman kariya daga hada jini da ni, don matata bata yi daidai da ra’ayinta ba.
In ya ce bai ji zafin abin da Taiwo ta fada ba ya yi karya, amma ya zai yi? Dole ya hadiye tunda Taiwo ce. His very own twin, his one and only Taiwo.
Ranar lahadi Prince Abdulrasheed ya dawo gidansa, Siddiqah tana can wajen Doki Saheeb, bata da masaniyar dawowarsa.
Ta kama sirdi ta haye, shi kuma ya soma tafiya da ita a hankali, tana tafe kan Saheeb tana rangaji irin na tafiyar doki a hankali zuwa karshen ranch. Kawai sai Saheeb ya hango shi daga nesa ya harde hannuwa a kirji yana kallonsu.
Saheeb ya fara kokarin gudu da haniniya har yana neman jefo Siddiqah, da karfi ta ce, “Saheeb!” Dan saura kadan ya jefo ta kasa, amma tsawar nan da ta yi masa ya sa ya koma cikin nutsuwarsa, ya fasa fudun ya kuma daina haniniyar.
Abun ya kashe Prince da mamaki daga tsaye, ta yaya Siddiqah ta yi ta samo kan Saheeb cikin sati biyu haka, har da bashi umarni kuma ya bi? The Prince was dumb-founded. At the same time, abin ya burge shi matuka gaya.
Sai lokacin Siddiqah ta ankara da Hamma, fuskarta ta haskaka da ganinsa, Hamma ya rame sosai a idonta, ta jefa masa murmushi (full of innocence), a idonsa she looks pure and angelic, ta kada linzamin Saheeb suna tahowa inda yake tsaye. Murmushinta na kara fadada, domin harr anta taji dadin ganinsa, tace “Uncle shine baka gayamin yau zaka dawo ba? Sannu da zuwa Hamma Abdul! Sannu da hanya Uncle!”
Cikin dan lokacin nan zuciyar Prince ta shiga wani yanayi na raguwar radadi, ya dan mance da zugin da zuciyarsa keyi na gajeren lokaci, ganinta kawai kuma akan Saheeb ya zama tamkar haske maganin duhun da zuciyarsa ke ciki, ya samu kansa da takowa domin ya cimmasu.
Suka game a tsakiyar filin wajen, hamma yace “ashe haka kike da karambani? Idan kika fado fa?” Aisha tayi murmushi kawai tace “sannu da dawowa” tana kokarin saukowa daga bayan Saheeb, Hamma ya shagala da kallonta ya mika mata hannu ta kama cikin jin nauyi ya kama kugunta ta sauko, sai lokacin yaga takalmin sa na hawa Doki ne a kafarta (chukka boots) duk da ya mata yawa.
Bayan ta sauko Hamma ya tsaya yana kallonta tana dan manne a jikinsa, Siddiqah ta sunkuyar da kai duk ta rikice ta kasa kallon idon Prince, haka ta kasa gasgata abubuwanda ke faruwa yau.
Ganin rikicewar data yi dinne yasa Hamma ya cikata, yana dan tsokanarta da cewa.
“Inye Siddiqah, yaushe na baki takalmin da kika dauka mun, haaa!” Siddiqah na murmushi kamar ta nitse a haka suka jera a tare yana rike da hannunta suka shige cikin gidan.
A sitting room ya zauna yana nazarin yadda Siddiqah ta gyara shi, ta canza zaman kujerun zuwa yadda ya fi yi mata daidai, ga kamshin turaren wuta na tashi mai dadin kamshi.
Siddiqah ta tsugunna tana masa barka da zuwa tare da sake yi masa ta’aziyya, ya tambaye ta ko ina Pareto? Ta ce, ta aike shi cefane.
Daga haka ya shige dakinsa bai kara fitowa ba har la’asar. Siddiqa ita kadai a kitchen tana girki duk ta bi ta damu da rashin jin motsinsa. Ganin Hamma yau ko abinci bai nema ba, sannan ba ta kara jin motsinsa ba har yamma.
Don sai yanzu ne ma bayan ya dawo ya kadaice a dakinsa. Mutuwar Kakan ta soma taba shi, rayuwarsa da Emir ta dinga dawo masa filla-filla tun lokacin da yake yaro, da moments dinsu tare, da karfin soyayyar Emir a gare shi.
Ya tabbata ya yi rashi irin wanda ba zai taba mayar da shi ba. Prince sai yau yake kuka da hawayensa tun bayan rasuwar Sarki Abdulrasheed.
Domin sai yau ne ya samu kadaici, a can gida Ilorin koyaushe yana tare da jama’a, ga Dade da Uncles dinsa da basa bari ya bar kusa da su sai lokacin barci.
Idan ma ya shiga barci Taiwo na biyo shi ne ta taya shi hira, kasancewar tunda aka yi rasuwar tana nan main house dinsu ba ta koma gidanta ba. Toufeeq ma ya zo ya musu gaisuwa ya koma UK.
Da taji shirun nasa yayi yawa ta kasa daurewa ta isa ga kofar bedroom din nasa tana knocking a hankali. Prince ya share hawayensa da hankacif yace “Yes!”
Sai Siddiqah ta bude kofar ta shiga a hankali, karonta na farko da shigowa masterbedroom din na Prince, dakin ya tsaru iya tsaruwa, komai ya zauna a muhallinsa cikin tsari mai ban sha’awa, ga kamshin turarukan Prince da suka hadu suka cakude dana room freshner. Aisha taji wata irin nutsuwa na shigarta karo na farko da shigarta turakar mijinta, shima kuma Hamma ganin Siddiqa yau a dakinsa sai wani bangare na zuciyarsa yaji contentment na cewa yau gashi ga macen Sunnah a dakin barcinsa, lallai da gaske yanzu ya yarda yanzu an masa aure.
Kallo daya Aisha tayi masa ta gane kuka Hamma yake yi, taji wani irin damuwa ya tsirga a ranta, da kyar ta daure tace dashi cike da kulawa.
“Uncle na ji ka shiru ne, are you okay?”
Ya sunkuyar da kai, jin wasu sabbin hawayen na kara fito masa bayan wadanda ya share kafin shigowarta, amma yayi kokarin hadiyesu. Yace “No Aisha. But Alhamdulillah!”.
Aisha ta sake yiwa Hamma sabuwar ta’aziyya, ta bashi hakuri, Prince yana mai yabawa da hankalin Aisha a ransa yace “ya gode”.
Aisha tace “don Allah ka dai na kuka haka Uncle, in babba na kuka abun yana tada mun hankali sosai”, itama tayi narai-narai da ido nata hawayen na shirin zubowa.
Abin ma sai yasa shi dariya, yace “to na dena, jeki cigaba da abinda kikeyi”.
Tace “tau abinci ne nake maka dama, bansan yau zaka dawo ba, ai zaka ci don Allah ko?”
Aisha tayi maganar a shagwabe da zuciyarta daya, bata ma san tayi ba.
Hamma yace “tohh!”.
Sai ta fita ta saka karatun Al’qurani a falon Suratul Noor, tana girkinta tana sauraron karatun har ta gama. Lokacin taji ana kiran Magriba, shiru har lokacin Hamma bai fito ba, ta sake isa ga kofarsa ta sake yin knocking, sai taji shiru, ta bude a hankali ta shiga sai ta ganshi akan sallaya yana barci. Aisha tayi tsaye a kansa yau tana karema Uncle kallo. “A beautiful man, with a beautiful heart” ta fada a ranta.
Bata san lokacin da Hamma ya bude ido ba, sai muryarsa taji yana fadin “Aisha, yaya dai kiketa kallona?” Taji kunya sosai ta juya masa baya, tace “anyi maghrib ne, na jika shiru nazo in ga ko lafiya?” Yace “subhanallah!” sai yace mata “bari nayi wanka nayi sallah ina zuwa”. Aisha tace “toh, na gama abinci ma, inyi setting table yanzu?” Hamma yace “no, jeki yi sallah ki gama, nima wanka zanyi inyi sallah tukunna”.
To sai ta koma dakinta ta shiga wanka, ta fito ta saka ‘lounge wear pink and white’ wando da riga sakakku da basu kama jikinta ba, wandon kamar pallazo amma mai taushi, samfurin ‘duvet days collection’ sunbi jikinta sun kwanta, Aisha ta saka ‘plush slipper’ na cikin gida shima pink ta zama tamkar angel don kyau, ta shafa turare mai sanyin kamshi, daman tayi jan lalle a yan yatsunta, ga gashinnan bata dade da wanke shi da steaming dinsa ba, Aisha ta jima tana shan SABAYA da Ummanta ta bata lokacin da taje gida Gombe sallama so Aisha ta kara cikowa sosai. Saida tayi sallah magrib da isha da shaf’I da wutr sannan ta fito falon, taje ta shirya table ta sake kunna oil burner na turare. Ga sanyin AC ya hade dana turaren, taje ta zauna akan 3 seater tana kallon PoloLine TV.
Nenne kamar ta san halin da Prince ke ciki a daidai wannan lokacin sai ta kira Siddiqa.
Siddiqah ta amsa kiran Nenne alhalin ta saka wayar a handsfree. Da damuwa a muryarta Nenne ta ce,
“Aisha ya kuke? Ya Hamma din?” “Nenne yana kokari ba laifi” “yaci abinci?” “na dai gama masa pounded yam (Iyan) da Afang Soup shinake jira ya idar da sallah ya fito” Nenne tasa mata albarka, tace “ki kasance tare da Hammanku a wannan lokacin kin ji, yana bukatar mai karfafa shi da ba shi kwarin gwiwa. Na san halinsa sai yanzu ne zai soma nashi ‘mourning’ din. Ki tausashe shi, kin san yadda yake da Kakan nasa”.
Aisha cikin jin kunya ta amsawa Nenne da cewa “Insha Allah Nenne zan kula da Hamma”. Bayan da idonta har lokacin bata ga Hamma din yanada alamar fitowa ba, yau dai Hamma tunda ya sauka ko Ranch dinsa bai shiga ba, ko kula Dawakan nasa bai yi ba tunda ya kama mata ta sauko daga Saheeb, komai ya fita kansa saboda rashin Sarki.
Aisha bata kula da fitowarsa ba harma yana jinsu itada Nenne, daidai sanda Nenne ke fadin, “to ko zaki bishi da abincin daki? Kamar kinsan yana son Afang Soup, ki ta lallaba shi a haka har ya ware ya koma sha’anoninsa kin ji ko Aisha-Siddiqah?”.
Sukayi sallama da Nenne tana ta saka mata albarka.
Sai taji Hamma daga bayanta yana cewa.
“toh ni baby ne da Nenne ke checking up on me haka, kuma through another baby din like you za’ayi checking up din? Lallai!”
Maganarsa ta baiwa Aisha dariya sosai. Ta yi ‘yar dariya tace “saboda ta damu ne ai, nima dazu ai ka bani tsoro da naga kana kukan” Prince yace “Oh! So you are genuinely worried about me, not because of Nenne?” Aisha bata bashi amsar wannan ba, tayi murmushi ta karasa tashi tace
“muje kaci abinci toh Hamma”.
Ashe dankwalinta ya zame ta baya akan kujerar data tashi bata sani ba. Nan Prince yaga wani zallar bakin gashi mai laushi da sheki yana zagin idonsa.
Wani abu Hamma ya hadiye a makogaronsa, kafin yayi ta maza ya zauna ya fara kwasar daddadan girkin amaryarshi Aisha.
Koda suka gama cin abincin ma haka tayi ta lallabashi. Da taga ya zauna shiru zata fara yi masa hira.
Har lokacin kwanciyar Prince yayi, ya mike ya na ce da Aisha.
“Ko zan samu ‘yar tayin kwana? Banason kadaici yana dawo da damuwata baya, please Aisha”.
Sunkuyar da kai Aisha tayi, kamar mai tunanin taje ko a’ah?
Hamma ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye yana fadi cikin lallashi, “I only need your presence, ba abunda zan miki Aysha. In baki son jina ma a kusa dake ba sai na kwana akan gadon ba”.
Don haka da Prince ya saka hannun shi cikin nata suka soma tafiya, sai ta kasa resisting offer dinsa.
Hamma ya cika alkawari, domin kuwa Pillow ya jefa akan kilishi ya bar mata ni’imtaccen gadonsa, ba jimawa da kashe wutar da yayi barci ya daukeshi dama ga gajiya ya tara.
Saida Aisha taji numfashin Uncle na sauka a nitse ta tabbatar yayi barci sannan ta samu sakuni a ranta, daga wata irin fargaba data shiga ranta a dalilin kwananta a yau master bedroom tareda Prince.
Washegari tare sukayi sallar asubahi. Prince ya koma barci Aisha ta fita zuwa dakinta tayi wanka ta shirya ta koma kitchen tana hada musu abin kari.
Da hantsi ya daga ma suna tare a parlor amma har zuwa lokacin fuskarsa da damuwa. Duk dai don ya daina damuwar Aisha tace
“Hamma please, yau zaka fara koya min Polo”. Ya juyo with attention ya kalleta. Magana in ta Polo ce dama Hamma na sonta, don haka gladly ya amince su fara. Amma yace ‘riding’ zai fara koya mata kafin Polo. Dama kuma itada Saheeb sun riga sun saba sosai.
A haka Prince ya fara koyawa Aisha ‘horse riding’, yana ajiye damuwarsa a gefe.
Rana ta farko data biyu tare suka hau bayan Saheeb, don yanata koya mata amma ta kasa ganewa, saida ya hau tareda ita ya saka ta a gabansa.
Rana ta biyu suna cikin yi Aisha ta kusa fadowa, Prince yayi saurin tarota da hannu daya, inda unintentionally hannunsa akan dukiyar Fulani ya sauka. Da sauri ya saki, itama kuma haka ta saki linzamin, duk suka daburce suka zamo tare daga bayan dokin.
To da yake ba gudu Saheeb din yake yi ba, ga uban tausasan grass carpet sai basu ji ciwo ba. Saida suka fado ne Prince ya tuna abinda ya cafko, sai ya fashe da dariya, itama kuma haka.
Ya fuske yace “to daga yau an gama, tunda fadowa zaki dinga samu muna yi”.
Ya dinga tsokanarta don yayi shaking off the awkwardness.
Sai bayan ya kwanta ne a daren, kafin shigowar Aisha, duk sanda ya tuno irin laushin da yaji sai hankalinsa ya tashi.
Lokacin ne ya tabbatarwa kansa ashe dai lafiyarsa kalau, bai zama abinda shima yake tababar ko ya zama ba. Something strange deep down inside him is working like ignition or arousal.
Sha’awa tace salamu alaykum, shiyasa koda Aisha bata zo taya shi kwana yau ba itama saboda kunyar abinda ya faru yau, shima bai je bikonta ba.
A rana ta uku ma da kyar suka yi one hour ana koyon Polon, gabadaya ya zama aware of her body, da son taba ta da gangan, a wajen rike linzami da sukuwa da hawa da sauka daga doki jikinsa a gugar nata yana kara birkita shi, kamshin jikinta da laushin fatar jikinta inda duk yayi kuskuren kai hannunsa sai ya kidima shi, gabadaya Prince ya kasa gane kansa a wannan koya Polon da Aisha ta saka shi. A haka a daddafe aka yi kwana biyar ana yi. Suna