Showing 30001 words to 33000 words out of 45634 words

Chapter 11 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

He was dumb founded, domin bai taba ganin abu mai kyau irin Aisha-Siddiqah ba.
Ga naivity ga innocence appearance dinta wadanda sune attributes dinta da ya fi so. Prince jinsa ya yi duk ya zama wani upset, a karshe ya kasa zaman reception din domin ji yake tamkar bafaranshan da ke bayanshi yana taya shi kallon hotunan matar tasa, sai kawai ya rufe ya tashi ya bar reception din, ya bi lift zuwa dakinsa. Kyawun wadannan hotunan ka kallesu daga kwance kuma bada alwallah ba.
Kwanciya yayi rigingine a gadon hotel din ya dora kafa daya a kan daya, ya ci gaba da bankado hotunan nan na Aisha da Kiki ta antayo masa, yayi ta kallo yana admiring kowacce kankanuwar halittar da ke tare da matarsa “Aisha Siddiqah Yunus”.
Alama ya gani na cewa Kiki ta saka sabon status, a kan whatsapps dinta.
Yana budewa ya ci karo again da zafafan hotunan nasu da suka fi wadanda ta turo masa haduwa da nuna natural beauty din Aisha. Prince har da zooming iya fuskar Aisha, yana kara kare mata kallo, wani irin abu na motsawa a zuciyarsa da illahirin gangar jikinsa, kawai sai ya samu kansa da kiran Kiki a waya ransa a mugun bace, da wani abu mai kama da allura da nan take ya soki zuciyarsa, (KISHI).
Ko mintuna biyar Kiki ba ta yi da dora status din nan ba ta ga kiran Uncle AK yana shigowa cikin wayarta kamar kiran kansa a fusace yake shiga wayarta.
Da murnarta ta daga zata soma yi masa karadinta da korafi da mita na rashin kiransu akai-akai tun tafiyarsa, Hamma yace a fusace.
“Kiki wait, ina so ki cire hotunan Aisha da ki ka dora a status yanzu, idan abokanki da samarinki maza suka gani fa? Ke ba ki san matar aure ba ce ne? Ko an ce miki daya kuke ke da ita?”
Kiki ta hau danne dariya, don bata taba jin Uncle AK na fada haka har da tada jijiyar wuya ba sai yau, fada sosai yake yi kamar ya ari baki ya kara akan nasa, bai ma dace dashi ba tunda sparking irin wannan ba halinsa bane.
“Na baki minti daya maza-maza ki sauke su duka”.
Kiki ta ce cikin kokarin boye dariyar da ta taho mata.
“Uncle I’am sorry zan sauke su yanzu”.

Hamma ya koma da baya ya kwanta, ya kasa ajiye wayar ya ci gaba da kallon matarsa Aisha-Siddiqah, wani kallo na kurillah da bai taba yi mata ba sai yau.
A zuciyarsa har tasbihi, yake domin Ubangiji ya yi halitta. Har gaya wa kansa yake wai wannan beautiful sweet 16 din matarsa ce, wane kyakkyawan aiki ya yi wa Ubangiji haka, da ya cancanci wannan kyautar da bai taba tsammanin samu ba?”.
Komawa ya yi kan status din Kiki yana saving kowanne cikin wayarsa. Sai kuma ya ga Kiki na sauke wa din. Uncle ya kasa karashe sauran kwana biyunsa a France, a kwanansa na shidda ya canza booking. Gara ya koma gida haka, kafin Kiki ta koyawa Aisha bariki. Don yaga gabadaya ta canza masa mata, fatar jikinta da tsarin kwalliyarta duk ya canza.


Ranar da Uncle zai dawo Argentina bai gaya musu ba, kuma ranar Kiki ta tuna ba su je ‘Hiking’ ba. Don haka ta kwashe su a motar Prince suka tafi Hiking (long walks na hawa duwatsu).
Ranar daga Kiki har Aisha ‘sport wears’ suka saka na mata, cikin wasu kayan Kiki ne, shaf Kiki ta manta da gargadin Uncle na dawowa da wuri, kuma dai bata da masaniyar yau Uncle zai shigo Argentina ta aza sai jibi.
Aisha da Kiki suka sha ‘sport wear’ abinsu riga da wando sakakku, suka zama tamkar tagwaye don kayan iri daya ne sai kala da ta bambanta, gasu tsaho daya, saidai kasancewar Kiki baka ce mai jiki, Aisha fara siririya maia mugun shape. Kodayake yanzu Aisha ba ta a layin siraran mata, tunda bazamu kirata mai kiba ba, haka ba za mu kira ta siririya ba, saboda samun diet na kabilar Yoruba mai kyau.
Suna can suna ‘hiking’ Uncle AK ya dawo gidan tun azahar. Bai taddasu ba. Har zuwa la’asar shiru ba su dawo ba, kuma bai ga sun shirya masa wani abu da zai iya ci ba. gashi sun koya masa kyankyamin takeaway. Ya kuma ki kiran Kiki a waya don ya ga iya gudun ruwansu.
Ashe dama dare suke kaiwa haka a gantalin nasu?
Aisha dama bai taba gwada kiranta ba, tun tafiyarsa, sai dai ya ce da Kiki ta gaishe ta.

Ya zauna a ‘sitting room’ ko kayan da ya dawo da su a jikinsa da ‘socks’ din kafarsa bai cire ba, don ba ya son ya tashi su shigo, so yake su shigo a kan idanunsa ya kare musu tanadi tas. Ashe lasisin gantali ya baiwa Kiki tayi da matarsa da ya bata mukullin mota shi bai sani ba?
Bai zaci ko fitar da suke yi din suna wuce azahar din da yace musu ba, amma ga shi har magriba Kiki na waje da matar aure don rashin hankali da rashin mafadi.
Wayarsa ya kunna yana amsa sakonni da kiraye-kiraye, don dai ya rage bacin ransu, nan ya jiyo dirin motar da ya tabbata su ne suka dawo gidan.
A tare suka shigo sitting room din suna hirar wata zamowa da Aisha ta kusan yi daga kan dutse, ana dariya ana maida yadda aka yi, idon Aisha ne ya fara fadawa cikin na Uncle da ke zaune a three sitter, ya dora kafa daya kan daya rike da waya, yana kallon shigowarsu rai a matukar bace.
Ransa ya kara baci da ganin kayan ‘sport wear’ din da ke jikin Aisha, duk da ta dora mini hijab, kuma kayan ba masu kama jiki sosai bane, amma sun fiddo kirar jiki da kugun Aisha sosai. Wani abu ya huda zuciyar Hamma Prince, wanda bana ko tantama kishi ne kamar yadda Kiki tace, amma sai yayi fadan nasa a jumlace, ya ce.
“Kiki am? Uban wa ya ce ku saka wannan kayan ku fita? Kwatakwata kin manta da matar aure ki ke tare ko? Sannan kin san tun yaushe na dawo gidan nan ba ku dawo ba? alkawarin da kuka yi min kenan?”
Fada sosai Hamma yake yi yau, fiyeda wanda yayi mata a waya kafin ya dawo. Yana fadan yana kallon Aisha ta gefen idonsa, wadda ta yi tsumu-tsumu, ta kuma rikice duk a lokaci guda. A nature dinta bata son fada ko daga waye, balle daga babban mutum irin Hamma. Kiki kuma ko a jikinta, sai faman rike dariya a cikinta take don fadan ma Uncle bai iya ba, bai yi masa kyau ba, musamman da bai saba ba, ta fahimci kawai dai kishin an fitar masa da mata titi da ‘sport wear’ ne ya birkita mata Babanta.
Amma a zahiri shima a nasa idanun Prince yasan Aisha ba karamin kyau tayi ba, kamar a sace ta a gudu (looking takeaway). Hamma ya kasa danne zuciyar sa da fushinsa ganin sun masa shiru, ya sake kankance ido yana kallon Aisha. Wadda take jin idanun Hamma na zaneta tamkar saukar bulala a jikinta, da wannan kallon kankance ido da yake mata.
“A irin hankalinki yakamata ku rika saka irin wadannan kayan ku fita ko, in Kiki bata da hankali sai ki biye mata? Kin manta matar aure ce ke Kuma Uwarta ce ba kawarta ba da zaki maida kanki kamarta. Duba agogo ki gayamin karfe nawa kuna waje don rashin mafadi da rashin sanin darajar aure ko Aisha?”
Wannan karon kai tsaye da Aisha yake kuma ita ya jefawa tambayarsa.
Aisha ta sunkuyar da kai, tayi tsumu-tsumu, idonta fal kwallah, karo na farko da taji Hamma ya ambaci sunanta kai tsaye. Kasa cigaba da tsayuwar ma tayi kada taje Baban Kiki ya hada da duka.
Sum-sum-sum ta wuce dakinta, domin Uncle fada yake sosai, sai da ya surfe su tas.
Sai da y agama ya zauna a kujera yana maida fushi Kiki ta ce, “Uncle kai fa da hannunka ka saya min wadannan kayan a wancan zuwan naka Ilorin, ka manta ne?”
Shi da kansa sai da ya ji kunya, tabbas shi ya sayawa Kiki kayan, bai san ba ya so a saka din ba ya sayo mata sai da matarshi ta saka, Kiki da bai saba da yi mata fada akan sanya suttura ba itama wannan karon ta shaka, don shi da kansa ya sayo mata kayan ya kai mata har gidansu.
Aisha ta shiga daki ta zumbulo katon hijabin sallarta ta fito ta wuce su a falon har yanzu suna wajen suna kaftawa ta wuce zuwa kitchenette don ta samar musu abin da za su ci, bata ga alamar ya ci komai ba sai fada, gashi daga tafiya ya dawo. Jikinta har bari yake da fadan Hamma.
Kiki kuwa daga baya ganin da gaske yake ta daina boye dariyar ta koma sai hakuri ta ke bashi, duk da ranta ya sosu. Sai ga Aisha ta fito Hijabi yana binta yana jan kasa ta wuce ta gabansu zuwa kicin, Prince bai san sanda dariya ta kufce masa ba.
Wai hausawa suka ce ta baya ta rago. Ita dai fatanta ya kyalesu haka da fadan nasa don har ga Allah ya kidimata.
Itama Kiki dariya ta saka da ganin hijabin da Aisha ta zumbudo, don Hamma ya daina fada. Bayanta ya bi tana firar dankali tana share hawaye, because she hates to offend someone, balle babban mutum kamar Uncle AK.
Daga bayanta ta ji motsin mutum da kamshin turaren Uncle AK, ba ta juyo ba ta ci gaba da fere dankalinta jikinta da hannunta yana rawa, space din da ke tsakaninsu bai fi taku biyu ba. Ya kuma fahimci hawaye Aisha ta ke yi kadan kadan saboda yadda fadansu ya rikitata.
"bar firar nan, baiwa Kiki tayi, kiyi a hankali kada ki yanke". Inji Hamma.
“Haba Aisha, am, ni ban ce ki je ki sako hijabi a cikin gidanki ba. Bayan kin gama nuna wa mazan waje abubuwan da ni kadai addinin musulunci ya yarda in gansu.
Sai kuma ni a zo a zumbuda min hijabi me kenan akayi?
Fita ce nace bai dace a yi da wadannan kayan ga matar aure ba. Amma ba a cikin gida ba. Ba ki ga yadda kayan suka yi miki kyau ba ne, looking ravishing!”.
Da sauri Aisha ta juyo don ta tabbatar wa kanta Uncle ne yake wannan maganar a kunnenta? Kuma a tausashe? Shi ma kuma cikin borin kunya sai ya juya ya bar wurin don kamar subutar bakin ba-zata ne ya same shi.
Ko da Prince ya koma dakinsa ya rasa me ya sa duk ya koma upset saboda Aisha, wani irin emotional ya tsinci kansa. Sai da ya nutsu ne ya gane kukan da ya sa Aisha ne ba komai ba ya birkita nutsuwarsa.
Kiki kuma a daren ta hau hada kayanta, da ma a gobe ne za ta wuce makaranta. Ga haushin fadan da Uncle ya yi mata don kawai tana kokarin maida Aisha ‘yar gari, ta daina tsangwamar zaman kadaicinta. Ai dai yasan ba za ta kai Aisha inda za ta cutu ba ko a cutar masa da ita.
Tana cikin hada kayan Aisha ta shigo dauke da tray din abinci da ta gama girka musu, bayan ta ajiye na Uncle a kan dining, express ne tayi musu chips ne da agada (plantain). Ta ajiye tray din a gaban Kiki, hankalinta duk ya tashi da ta fahimci Kiki tafiya za ta yi.
“Amma Kiki ya kamata ko sati daya ne ki kara, kin ga ni ban saba da Hamma ba har gobe, zuwanki ne ya sa muka dan saba har muke cin abinci tare, ni in ki ka tafi ki ka bar ni daga ni sai shi takura zan yi”.
Kiki ta harare ta tana cewa, “Aisha da sauranki, nikam ban iya zama daku alhalin kuna wannan rayuwar mara ma'ana, sannan taurin kaine dake bakya jin shawara, alhalin kuna matsayin ma'aurata amma kin kasa jan mijiki a jikinki. Sabida wauta da rashin wayo kin zauna Uncle ya maida ke hoto a gidansa ba matar gida ba.
Na farko kin barshi yana kwana shi kadai a dakinsa, ke ya ware ki a nan kamar kanwarsa Fatima.
Yana tafiya wata tournaments yana barinki gadin gidan gona, halan maigadi aka kawo masa daga Gomben?
Dan night dressing din nan na gayu da gyaran gashinki yadda za ki bada kala ki dimauta uban nawa duk ba kya son yi, kullum sai uwar atamfa da leshi da jallabiyya a cikin gida, haba Aisha shi ya sa fa ‘Yoruba Demons’ ke raina matan Hausawa.
Dazu kuma saboda Uncle na fada kika wani je kika sungumo hijabi kina asarar hawaye, in ni ce ke wallahi shigar da tafi ta farkon fitsara zan yi in kara fitowa in yi juyi a gabansa, in kada masa bombom, ke in makaleshi ma in masa kyakkyawar sumba, in yaso ya yi gunduwa-gunduwa da ni karewar fada.
Don abin haushi har da wani kuka-kukan ki ke ga ki mai Uba ko? Na ce Babanki ne shi da za ki tsaya kina kuka don yana fada? Ko ni ‘yar sa kin ga na yi kuka?
Haba mana kada ki bada Aishoshi. A sanina duk Aishoshi ba matsorata bane, ba wawaye bane. Duk inda na san Aisha na san mace ce mai karfin zuciya da kwatar kanta wurin miji ta hanyar kissa da iya kisisina. Sannan ta bada misali ga sauran mata saboda iya tarairayar miji, ta riga ta sha gaban mijinta duk shekaru da sarautarsa.
Kada ki manta kannen Nana Aisha kuke. Wadda kankantar shekarunta basu hanata zamowa tauraruwa a idon Ma'aiki SAW ba, ke saboda kankantar shekarun nataa ne ma yasa yafi biye mata".
Haka Kiki ta yi ta kwankwadawa kwakwalwar Aisha hudubarta, irin ta wayayyun ‘yammatan yarbawa.
Wani abun ma in ta fada Aishar ta ke bari da jin kunya, wato sai ta barta da ji mata kunyar duniyancin da ta ke so Aishan ta koma yi wa Hamma, da cirewa kanta rauni da tsoro a zamanta da Prince Kahinde, musamman in yana fada.
Ta ce, “Baban nan nawa sai kin yi da gaske Aisha, don zuma ne ga zaki ga harbi, sannan ya kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure, yanzu da ya samu bazai rike shi da wasa ba kishinsa akan matarsa yanzu ya fara.
Ki yi duk abin da ki ka san zai sayo miki martaba da kima da soyayya a idanunsa”.
Aisha ta zumburo baki, ta ce,
“Kiki, ni na ce miki ina son soyayya daga Babanki Hamma Abdul? Ai ki bar mu yadda ki ka zo ki ka same mu kawai, ba abinda zai iya canzawa a tsakaninmu don duk zaman biyayya muke yi ba neman canji muke ba”.
Kiki ta ce, “Taurin kanki shi yake ba ni haushi dake, amma na tabbata Uncle ya fara kamuwa da sonki. Ko daga kishinki muraran da ya soma nunawa ba tare da ya san yana yi bama.
Tunda nake Uncle bai taba yi min jan ido ba sai yau a kanki. Wanda ke nuna zuciyarsa ta fara sauyawa positively a kanki”.
Aisha bata ce komai ba, rokon Kiki ta ke a kan ta kara kwanaki, Kiki na cewa lokacin komawa makarantarta ya yi. Zadai ta Kara kwana daya saboda gobe akwai wani surprise data keson yiwa Uncle AK. Tsabar fadan sa na yau yasa ya manta (tomorrow is his 43rd birthday).
Washegari tunda safe Kiki ta soma shirye shiryenta a boye na shiryawa Hamma Candle Lit Dinner. Na farko ta bada order din birthday cake mai kyau da tsada ta kuma sa Chef a kusa dasu su shirya mata dinner na abinci da abin sha na alfarma, na iya mutum biyu zuwa uku, tun kafin karfe bakwai na magariba aka kawo mata komai.
Ta sa Pareto ya kai mata karamin dining table na farar roba da kujerunsa zagaye dashi a wani bangare na korran ciyayi dake cikin Ranch din.
Aisha na fitowa daga wanka Kiki ta zabo mata wata gown ta wani jan material da ratsin baki, budaddiya sosai daga kasa amma ta kama kirjinta sosai, cikin kayanta da tazo dasu daga Lagos, tace tayiwa Allah su zata saka yanzu, sannan ta zaunar da ita bisa stool din mudubi tanaso zata yi mata kwalliya.
Kiki ta fara zizara mata sassanyar make-up, wato irin light make-up dinnan ba mai daukar ido ba. A
isha dai tana kallon ikon Allah don Kiki bata gaya mata ko me take shiryawa ba.
A can kuma Pareto ya gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login