Showing 6001 words to 9000 words out of 45634 words

Chapter 3 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

tare dashi ko yanaso ko baya so.
Gashi tasan bata taki komai ba, bata da idea bata da wata fasaha akan zama da Dan su Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni, wanda alamu sun gama nuna ba ita Siddiqah kadai ba, baya maraba da kowacce mace cikin rayuwarsa balle ita diyar Mallam Yunusa.
Ko abubuwan nan da Kiki tace su suke gigita maza su so mace, ita Siddiqah bata dasu bata mallaki ko dayansu ba (frontward-backward) ta bakin Kiki. Taji da kunnenta sanda Murjanatu (Taiwo) take kusheta, Ya Allah! Murjanatu ma kenan wadda tafi kowa kusanci dashi, tafi kowa saninsa, ta san abinda zai iya so da wanda bazai taba so ba, balle ita Siddiqah da ba sidi ba sadada!
Tsabar tunani irinna rashin self-confidence, lack of motivation da inferiority complex da suka bi suka dabaibayeta yasa har aka ajiye mata abincin jirgi a gabanta bata sani ba. Abu daya take da kwarin gwiwa akansa har gobe, idan ta tuna cewa ita bafullatana ce a kansa, tanada wannan ego din na cewa kabilar data fito tafi tasa daraja (a tunaninta). Kabilarta wato (Hausa/Fulani) babu ya ita a kabilun Najeriya wannan kadai idan ta tuna shi yake bata karfin gwiwa.
Kenan ethnocentrism dinta har yanzu yana nan, bazai taba barin zuciya da kwakwalwar Siddiqah ba har abada wato perception dinta na (alfaharin kabila).
Tana cikin passengers masu tafiyar dare, da suka tashi zuwa babban birnin (Beunos Aires) din Argentina, kai tsaye tun daga Lagos, tafiya ce suke yi mikakka ba tareda transit (dakatawa a wata madakata ba).
Lokacin da jirgin su ya sauka a ‘Aeropuerto Ezeiza’, wato filin jirgin (Buenos Aires), saida kowa ya gama ficewa amma still har lokacin Siddiqah tana zaune a mazauninta kamar an kafe ta, ta rasa inda zata tsoma zuciyarta da rayuwarta taji daidai. Har saida ma’aikatan jirgin suka ankarar da ita cewa kowa ya fita ya barta.
Sannan ne ta mike ta saba Jakarta, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta dinga jan kafa, jaye take da trollies dinta guda biyu da basu cika girma ba.
Aisha sanye take da ruwan makubar Abayat da mayafinta kirar Taiwan, mai adon manyan stones da suka maida rigar mai dan nauyi, ba tareda Siddiqah ta san ina zata dosa ba kawai ta tasa kai a gabas take tafiya.
Ita tasan ba wata shaida da take da ita da Hamma zai ganeta, kamar yadda Dade yake zaton itama zata iya gane shi, bata tsammanin ko kamannin fuskarta Prince ya sani. Kodayake Dade yace wai hotonta zai tura masa na jikin pasfo ko yaya dai?
Itama kuma bazata iya tuna kamanninsa ba, don kallon shifcin gizo tayi masa a asibitin Lagoon lokacin da aka kwantar da Nenne, abunda zata iya tunawa game dashi guda daya ne zuwa biyu; na farko turarren tabon sallahr dake saman goshinsa, wanda ya ciza sosai ya nuna cewa Sajidi ne (mai yawan sujjadah). Na biyu kuma ingarman jikin sa murdadde da tsayayyun kafadunsa, wadannan ko ya juya baya ne ta gansu zata ganeshi dasu, don ba duk maza Allah yayiwa baiwar halittar da yayima Hamma ba.
Ta cigaba da wuce mutane tana tafiya a ba tare da ta san ina zata dosa ba. Don haka ba jimawa Siddiqa taji wani marayan kuka ya zo mata, ba don ta rasa Uwa ko Uba ba, amma jin kanta take yau a marainiyar karfi da yaji, mara gatan kowa. Tana ta kokarin hadiye kukan da hawayen, tana gayawa kanta Allah na nan, kuma shi zai zama gatanta a nan inda bata da kowa.
Hannayenta hagu da dama jaye da jakunkunanta ta wuce cikin terminal.
Tana tafe idanu a rufe duk hawaye ya jika fuskarta, ba tareda ta san ina take jefa kafa ba saboda rudanin zuciya da kwakwalwa, Siddiqah tafiya kawai take kanta tsaye har ta kan kusa bige jikin mutanen dake wucewa ba tare ta kula ba, sabida idanunta sun rufe ruf! Da hawaye, sai ji tayi gab! Tayi wani uban karo da mutumin dake tahowa direct gabanta.
Kawai sai ta samu kanta da dagowa a hankali, da bude ido jikakkun idanunta da suka kankance don kuka ta dubi mutumin, bata san sanda ta saki marikin jakunkunan hannunta kasa ba.
Don kafin taga komai ta hango tabon sujjadar dake saman goshinsa, kafin ta sauko da rinannun idanunta akan faffadan kirjinsa wanda shine ya bashi suffar da za’a kira shi da INGARMA…
A yawan hirar Kiki akan Kawunta, ta kan ce mata wai mazan duniya aji-aji ne su, a kamanni na halitta da kasaita, amma cikinsu da wuya a samu irin Uncle dinta….
Kiki tace “Uncle dinta zatinsa da kyawun surarsa ya zarta yadda duk zata misalta mata su ta gane baiwarsa mai yawa ce, ta dauka Kikin koda Ubannata kadai take yi a wancan lokacin, don ita bata ga komai da zata iya noticing har ta karar a tare dashi ba, a dan ganin data yi masa.
Amma yau ta ga zahirin maganar Kiki-Ruqayyat, saboda ta yi masa kallo ne sak na rahma da salama, bana cikin halin taraddadi ba (ba irin wanda tayi masa a ganinta na farko dashi a asibiti ba). Ga cikar zati da kamala irin na jinin sarauta tsantsa da Allah ya yi masa, sannan kwarjinin fuskarsa a bayyane yake duk da a hade ta ke tamkar hadarin da ya nausa yayi gabas, sun nuna cikakken basarakensa, bayeraben usuli mai surki da ruwan jikin fulanin Gombe, wanda shine ya hadu ya maida shi tamkar ruwa biyun kasar Habasha, wato kamar dan kasar bakar fata ta Ethiopia, wannan kadai da kallon kyarr da ido da yake mata ne yasa ta gane cewa ba kowa bane a gabanta; HAMMA PRINCE ne……
Bata bukatar sai wani ya fada mata cewa ya ganeta, ko sai ya gabatar da kansa cewa shi dinne kafin ta yarda ta bishi. Shima kuma bai ce komai ba, sai kawai ya sunkuya yana daukar jakunkunan da ta saki a kasa ….
Kafin Prince ya dago daga sunkuyon da yayi don daukar jakunkunanta, Aisha Siddiqah taji mararta ta cika taf! Da wani fitsarin razana da ke shirin balle mata daga yanzu zuwa kowanne lokaci, saboda tsabar kidima hade da rudewar da ta sameta lokacin da Prince ya dago manyan maganansa ya dubeta suka hada ido.
Hamma ya wara manyan idanunsa a kanta, kallon da yake mata kamar yana son karanto dalilin wannan bewilderment din da ya gani a tare da ita.
Ga hawaye na babu gaira babu dalili dake ta tsere a fuskarta wani na korar wani, Aisha ko damuwa bata yi data sharesu, ga jama’ar dake wucewa suna kallonta. Prince ya dan juya hagunsa da damansa a sace, kamar yana son ganin kota jawo masa hankalin mutane da wannan kukan nata, a dauka ko bata son binsa ne, ko batan hanya tayi.
Sa’arsa daya sai yaga ba wanda ya basu hankalinsa wucewa kawai ake yi hagu da dama ba tareda an kula da ita da koke-kokenta ba.
A cikin jikakkun idanunta kadai ya karanci cewa ta ganeshi, domin bayan rudewar ganinsa daya mamaye idanunta har da kallon sani dana bakunta a gareshi, da kuma kallon rashin sanin kalmar data dace ta furta masa mai nuna cewa ta gane shi din.
Don duk wata kalma data kama a kan halshenta don furta masa, sai taga bata yi daidai ta furta masa itaba, har gara ma tayi shiru ta bishi da ido.
Sai kawai taga ya juya dauke da jakukunan nata a hannunsa yayi gaba abinsa, ya kasa furta kalmar "biyoni" ko "follow me" don bai san yaren data ke ji sosai ba, tsakanin hausa da fillanci ko ingilishi, ya san dai Nenne tace daga Gombe ta ke, balle yayi mata tsammanin yarbanci.
Kalarta da shigar jikinta da komai nata yafi nuna na ‘yan garinsu Nenne din, wato typical 'yan matan arewacin Najeriya.
Aisha ta kasa cira kafa tabi bayan Hamma Prince tunda dai bai mata umarnin hakan ba, kada ta bishi ya zama ta zaqe, ita kuma a rayuwarta ta tsani zaqewa, kawai taga ya dau jakunkunanta ne yayi gaba. Ba tareda yace mata komai ba.
Har sai da ya dan yi nisa ne ya ankara da cewa ashe bata biyoshi ba. A sannu ya juyo don ya tabbatar, sai ya ganta kuwa tsaye standstill a inda ya barta, bata ko cira kafa ba.
Prince ya dakata yana tambayar kansa wannan wace irin yarinya ce kamar ‘yar goye Nenne ta kawo masa?
Domin koda ya juyo gani yayi tana ta share ido bata taho ba din, tana jiran sai ya gaya mata me ya kamata tayi ita bata san facial expression ba?
To idan kuma bai iya yaren data ke ji bafa, don shi ba wai ya kware da Hausa bane. Bayan dama cikin haushin an masa katsalandan da zuwanta gareshi ya wuni, alhalin yazo Argentina ne yin dogon hutun karshen shekara don ya samu ya huta, ya rage stress, yanzu ga rainon 'yar goye an kawo masa, yo raino mana! Don wannan a shekaru ai bata fice sa’ar Kikinsa ba. Budewar ido kawai Kiki ta fi ta.
Ko Kiki fama yake da ita har gobe akan shirmen kuruciya, balle wannan mai ruwan ‘yan fulanin cikin garin Gombe. Dawowa yayi inda take tsaye yana kokarin hadiye fushinsa, don yasa a ransa cewa ba laifinta bane zuwan da tayi, umarnin iyayensa ta bi.
Prince ya dan hade giran saman idonsa ya cure su, yace.
“Are you waiting for my command? If yes, then follow me!”. (Kina jiran umarnina ne? In haka ne ki biyo ni toh).
Aisha ba wai bata jin turanci bane ko yaya, tanada turancinta ba laifi tunda ‘yar makaranta ce, amma wannan karon kwakwalwarta ta kasa fassara turancin nasa, domin sak yake furta shi kamar na turawan yamma, wato accent din bata saba jin irinsa ba ko yaya ne dai ita dai bata gane me yace ba.
Shikuma Prince sai bai kara cewa komai ba ya juya ya cigaba da tafiya, jinin mulkin ya motsa, yana cewa a ransa in bata biyoshi wannan karon ba baisan ya zaiyi da ita ba kuma. Don kuwa ya tabbata ta ji shi saidai in shakiyanci ne kuma abin nata, tunda ya tabbata ba kurma bace ai ya santa a zuwan da yayi Lagos tana gidansu.
Tafiya yake a nitse akan marbles din wajen da jakunkunanta, bai kara waiwayota ba, ya barta a wurin tana zare jikakken idanunta ta rasa me zata yi takamaimai, don rudewa tasa ta kasa fassarawa kanta umarninsa ba rashin jin turanci ba.
Kafin ta baiwa kanta shawarar kawai ta bi shi, shi ya fiye mata alkhairi fiyeda cigaba da tsayuwa a wajennan. Idan ya bace mata cikin mutanen da batasan kowa ba sai shi, tabbas zata gayawa aya zakinta.
Sai kawai ta cira kafa da hanzari ta bi bayan Prince, harda hadawa da dan gudu-gudu, domin ya fara yi mata nisa.
Prince sai jin motsin gudun-gudunta da sassarfarta yayi a bayansa, ya dan tsaya har ta cimmasa, kafin su jera tare zuwa parking lot na filin jirgin, yana gaya mata ta tafi a sannu akan santsin wurin, kada ya kada ita.
Motar da Prince yake budewa Siddiqah ta bi da kallo domin da fari ta dauka ba mota bace wani abun ne daban, domin gani tayi murfin ya dage sama da kansa, wato kofar motar ta daga sama automatically, sannan samanta a yaye yake. (Sport Car, Toyota Supra) duk iyaka dauriyar Siddiqah da dakewarta na kada ta nuna kauyanci ta kasa karfafawa kanta gwiwar ta shiga motar nan, ba don komai ba sai don tsoron ganin cewa samanta a bude yake gabadaya.
Idan iska ta daukota tayi wurgi da ita akan titi Ummanta kadai za'a yiwa asara. Shi a gatan da yake dashi a gobe za'a auro masa gomanta. Goman Siddiqah harda kwarori.
Don haka shiga wannan motar ai tsautsayi ne da ganganci a ganin Siddiqah. Sai ta kara jin tausayin kanta na wannan rayuwar bakon wuri, da kasaitaccen basaraken bayeraben mijinta data samu kanta rana daya. Siddiqah ta kasa tsayar da hawayen ta sam.
Prince bai lura da halin da take ciki ba ya sanya jakunkunan nata a bayan motar, sannan ya bude bangaren direba ya shiga ya zauna, har zuwa lokacin tana tsaye kikam. Shi tunda yake bai taba sanya mace a gidan gaban mota ya tuka ta ba inka cire Fatima ko Firdausi ko Kiki. Amma haka ya daure ya mika hannu ya budewa Aisha kofar barinta ta hanyar danna wani madanni a jikin allon motar, yana lallashin kansa da kansa, yana gaya ma kansa yarinyar nan taci albarkar DADE dinsa da NENNE. Iyayen da bai hada alfarmar su data kowa.
A komai ma zata cigaba da cin albarkacinsu, tunda sun zabeta gareshi sama da kowacce mace, har gobe sun kasa gane uzurinsa na bashi da gurbin adana kowacce ‘ya mace a ransa da cikin rayuwarsa.
Amma Siddiqa ta ki shiga don kauyanci da rashin sabo na shiga gaban mota daga ita sai katon namiji, gani take motar babu sirri, kowa yana ganinsu, sannan yadda take babu nauyin nan iska zata iya daukota ta jefota waje in aka fara tafiya.
Prince ya fara zama bored da kauyancin Aisha don kiri-kiri kana iya karantar tsoron motar take ji a kwayar idonta, bayan kasancewarta cikin takurar zuciya har a kan fuskarta, har ila yau, kana iya ganin kauyancinta baro-baro. Shi bai ga dalilin kukanta ba ko sau daya, tunda da yardarta akayi komai, koda yake ya kamata yayi ma kukan nata uzuri, rabuwa da kasar haihuwarka rana daya da iyayenka bakidaya da danginka zuwa inda baka san kowa ba baka taba zuwa ba ba wasa bane.
Amma in banda haka ai ba’ayi wa bakunta kuka in ma bakunta ce.
A ganin Prince shi ya dace ya dora hannuwa aka yayi ta rafsa ihu yau ba ita ba, shi da aka turo masa mace bagatatan, macen da ya riga ya rufe babinta aka sako yau cikin gidansa da rayuwarsa.
Watakila kuma tana kuka ne kan an aura mata tsoho kamar shi, yarinyarta da ita danya sharaf, gata nan santaleliya son kowa kin wanda bai samu ba.
Amma ya kamata ta duba cewa bai je inda take da kansa yace yana sonta ba, balle ta yi kukan auren dole dashi.
Inda wanda zata tuhuma akan hakan to nata iyayen ne da suka yarjewa nasa iyayen, ba tareda sun ko gan shi ko a hoto ba balle a zahiri.
Ya tuna abinda ya faru jiya. Yana zaman zaman sa Dade ya kira shi a waya. Inda cikin raha Dade din yace.
“Kehinde, me kake yi daga yau zuwa gobe ne?”
“Dade it's month end ai ka sani (kuma ya kama Asabar din karshen wata), so nafi zama a gida a duk rana irin wannan, Pareto yayimin lissafin abubuwan da suka kare a gidan, da abincin dabbobi da sauran bukatunsu, muna checking lafiyarsu kuma, sannan in biya ma'aikata albashinsu na wata, sannan muna yin lissafin abincin Horses da zamu ajiye na tsayin wata guda. So I will be busy the whole day, daga yau zuwa goben har in samu in kammala da duk wannan”.
Cikin tsokana Dade yace "kawai kace min “The Prince and his ranch activities dai, to Allah ya taimaka, inaso yanzu ka ajiye komai ka sa a shiryawa Aisha-Siddiqah dakin da zaka sauketa, jirginsu ya taso zuwa Argentina yanzu daga Lagos, zasu sauka a (Ezieza International Airport Bueunos Aires) nan da awanni ashirin da biyu”.
Saida ya baiwa kwakwalwarsa aiki na wucin gadi yana son gane me Dade ke magana akai, kuma wacece Aisha Siddiqa din, har saida ya ga cewa ya gaza wajen ganewar ya tambaya cikin girmamawa mai hade da mamaki.
“Dade wacece Siddiqah kuma wajen wa zata zo?”
Sai Dade ya juya harshe zuwa (native language) yana masa bayani don dai Prince ya yarda cewa seriously yake magana dashi yanzu. Cikin harshen Yarbanci yace ma Prince din.
"Na gaji da jiran zuwanka na sako maka matarka Siddiqah a jirgi, ta taho, so nake ku rayu tare rayuwar sunnah a gidanka da duk inda zaka shiga, daga nan har karewar numfashi.
Tunda naga alama baka san zuru ba, da irin sacrifice dinda iyayenta masu dattaku suka yi mana, suka baka aurenta ba tareda sun ko gan ka ba".
Sai Prince ya tsaya sakatoto! Da waya a hannu, jin Dade ya kashe wayarsa ba tareda ya bashi damar kara yi masa tambaya ko neman karin bayani ba.
Ya koma ya zauna a hankali bisa kujerar da ya mike daga kai lokacin da zai amsa kiran mahaifinsa.
Prince bayan gama sauraron Dade sai ya kasa cigaba da aikin da yake yi, zufa sai yanko masa take yi daga goshi, ya koma ya zauna yayi tagumi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login