Showing 39001 words to 42000 words out of 45634 words
Chapter 14 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt
da suke so. Kada ka manta na so Kakarku Murjanatu kamar raina. A lokacin da take raye ban taba zaton zan tsufa ba, kullum sabuwar samartaka take kara min saboda soyayya, ina gaya maka kayi gaggawar dabbaqa sunnarka kafin ranar da wankin hula zai kaika dare, wato ranar da zata gane tana son ka tayi maka bore ta hana ka kanta”.
Prince ya hau zufa daga goshi, ga kunya da ta kama shi. Ya kasa cewa komai. Amma da zai iya da yace da Kakansa sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba, amma ya fara jin sauyi a zuciyarsa da gangar jikinsa sosai a kan Siddiqah.
Sun kwana suna hira shi da Kakansa abin gwanin sha’awa, inda ya sa shi yi masa alkawarin zai kula da aurensa, zai kuma kula da Siddiqah kwatankwacin yadda Dade yake kula da Nenne. Ya kuma tabbatarwa Kakan nashi cewa shi lafiyarsa kalau ba kamar yadda mutane ke kuskuren fahimta ba. Yana jiran ya ga yadda Allah zai yi dasu ne shi da Siddiqah.
Emir kuma ya ce masa “ka yi amfani da dama a lokacin da ta ke hannunka”.
Har aka kira asubahi idonsu biyu, Kawunsa Malami Ubandoma, da mai bi masa Mufti of Ilorin suna daga shigifar farko a nan suka kwana, Prince ne kadai ya kwana tare dashi da asubah yayi masa alwallah yayi sallar asubahi daga kwance, sai ya ce da Prince yasa masa bargo sanyi yake ji. Kuma ya kunna masa Suratul Mulk a radiyonsa.
Prince yayi duk yadda Kakan ya ce cike da kauna da kulawa, sannan shi kuma ya tada tashi sallar.
A nan inda ya yi sallah kasancewar ya yi kwanan zaune barci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.
Har gari ya soma haske Abdurrasheed bai farka ba. Ashe sallamarshi kenan da Kakan nasa Emir Abdurrasheed Akanni.
Abinda ya faru yana barci shine Kawunsa Mufti ya shigo kawo karin kumallon Sarki, a lokacin da aka kawo daga cikin gida, shi ya gane cewa ran Emir ya yi kaura zuwa ga mahaliccinsa.
Sai ya tashi Prince daga barci ya yi masa nuni da abin dake faruwa. Prince ya isa ga Emir ya tallafo kansa ya tabbatar wannan ruhin da ya rayu shekaru sama da shekaru arba’in da biyu yana lelensa yana kula dashi yana kyautatawa rayuwarsa yau babu shi. He is more than shocked. Don ko kusa bai kawo wa Emir mutuwa yanzu ba, don ya saba ciwo fiye da wannan ma ya girgije ya tashi.
Shi ya san ya yi rashin da ko iyayensa ne suka fadi yau suka mutu suka barshi iyakar kukan da zai yi kenan.
A wayewar garin ranar labarin mutuwar sarkin Ilorin, Sarki Abdulrasheed Akanni, ta riski al’ummar kasar Najeriya, labarin yayi tambari ya riski duk wani jininsa, kafin kace meye wannan kafatanin zuri’arsa na garuruwan Najeriya da wajenta sau bubbugowa suke yi Ilorin. Akannis sun gigice sun dimauce baki daya, amma babu wanda ya kai Prince AbdulRasheed gigicewa, su Nenne ma da su Princess Fatima, duk a ranar suka taho Ilorin, Taiwo da ke nan Ilorin kuma akan idonta aka yi wa sarki suttura, duk a ranar suka taho masarautar, haka dukkan ‘ya’ya da jikoki na nesa da na kusa suka hallara. Sun dade basu shiga halin dimauta da gigita irin na wannan lokacin ba.
**** **** ****
Tun Siddiqah na zuba idon ganin Prince ya dawo a satinsa na biyu da tafiya har ya zamanto ta fara damuwa da rashin dawowar tasa, duk da ba wai shiri suke yi ba, ba kuma shakuwa ce ta sosai a tsakaninsu ba, amma mutum a cikin gida rahma ne. Kai ita yanzu ta fara jin tsoron zaman gidan ma, daga ita sai Dawakai da dabbobi. Ta yi da na sanin rashin yin bore na sai ta bishi kamar yadda Kiki ta ke so ta dinga yi, wato ko’ina Hamma za shi ya tafi tare da Aisha.
Amma cikin hudubobin Kiki na arzikin wanne ta dauka? Kusan a inda ta bata su, tun tafiyarta a nan ta ajiye mata su saboda taurin kanta. Yanzu ga shi rashin Hamma a gidan ya dame ta, musamman da ko sau daya bai kirata ba.
Sati biyu kenan da tafiyar Hamma Ilorin, ranar da aka yi rasuwar Nenne ta kirata, nan ta gaya mata rasuwar Kakan nasu Fatima. Sai kuma Kiki ma ta kirata suna gama magana da Nenne. Kiki tana cikin damuwa domin makarantarsu ba za ta bata excuse din zuwa gida ba kasancewar ba ta jima da dawowa ba.
Nenne again a washegarin ranar rasuwar ta sake kiranta, ta ce, ta kira Abdulrasheed ta yi masa ta’aziyya. Domin kuwa shi aka yiwa mutuwa a kafatanin zuri’ar Akanni, ta gaya mata babu wanda ya kaishi kusanci da shakuwa da Sarkin. Kuma babu wanda Emir yake girmama sha’aninsa da kaunarsa cikin jikokinsa kamar Prince din, wadanda a kiyasce jikokin na Emir Abdulrasheed Akanni sun tasar ma (82).
Nan fa ake yinta! Don Siddiqah da Prince ya kirata bayan saukarsa a Ilorin, ya gaya mata saukarsa lafiya ya kuma tambayi yadda take coping tace masa batada matsala, ashe lokacin ko lambar Prince din bata yi saving cikin wayarta ba, tsabar yadda bata daukeshi matsayin mijinta ba face Yayanta/Babanta, wannan abun kunya da me yayi kama?
Taji kunya sosai yau, sannan da kunya ta tambayi Nenne wai lambar mijin da suke kwana gida daya. Har suka yi sallama da Nenne jikinta a salube yake, bayan ta sake yi mata tata ta’aziyyar, Nenne kuma ta kuma hadata da Dade shima tayi masa, da Princess Firdausi da Princess Fatima, ba ta iya ta tambaye ta lambar Hamma ba. Me Nenne za ta dauke ta?
A yau sai ta ga cewa ma a gabadaya zamansu wanda ya ki samun daidaito da fahimtar juna har lokacin ba laifin Hamma Prince bane, laifin ta ne. Saboda Hamma yayi iya kokarinsa da ya karbeta a matsayinsa na wanda aka yiwa auren dole, ita da take mace ita ya kamata ta canza shi zuwa yadda iyayensa sukayi fata, suka kuma dora burin hakan a wuyanta saboda kyakkyawan zaton da suke dashi a kanta. Amma me ta tsinanawa Hamma na kyautatawa tun zuwanta? Hasalima bata dauki auren nasu a matsayin aure ba sai zaman biyayya.
Bata shiga sha’aninsa yadda ya dace tayi, ba abinda Kiki bata ce mata ba wanda shi zai sa ta kusance shi su shaku da juna, ba abinda bata koya mata ba cikin dabarun abinda Bayeraben miji yake so daga matarsa, wanda zai sa ta kama zuciyar Hamma nan da nan, haka mahaifiyarsa ta dade tana bata training akan zama da shi. Amma a ciki wanne ta aikata baka da zuci?
A zahirin gaskiya bata cika expectations din iyayenshi a kanta ba, da yardar da suka bata dari bisa dari na zata iya, zata kawo kyakkyawan canji a cikin bahaguwar rayuwarsa.
Cikin watannin data yi tare da Hamma Abdulrasheed wane abun ku zo ku gani ta kulla a zaman nasu, wanda in aka tambayeta progress na zaman su zata iya adarwa da babbar murya?
Idan da ta bi shawarwarin da Kiki ta bata, duk da ake cewa Kiki bata da nutsuwa, in aka dauka a tsanake aka dubasu za’a ga cewa shawarwari ne masu kyau da za su taimaka a rayuwar aurenta. Tunda auren nan ya riga ya zama rubutacce daga Allah! Wanda babu yadda za ta yi ta guje wa kaddarar kasancewarta mata ga Prince Abdulrasheed jikan marigayin sarkin na yarbawa.
**** **** ****
Daga wannan lokacin Siddiqah ta yi kyakkyawan kudiri a zuciyarta na in Prince ya dawo daga ranar zata canza irin zaman da suke yi, zuwa zama mai armashi da ma’ana koda bazai bata hadin kai ba. ta fannin ta zata yi kokarin sauke nauyin duk da iyayensa suka dora mata, sama da komai Ubangiji ma ya dora mata.
Zata koma kyautata aurenta dashi iyakar kyautatawa.
Kiki ta kira a lokacin da take tsaka da wannan juyayin, Kiki na cikin alhinin babban rashin da suka yi don itama Emir yana sonta albarkacin son da Abdulrasheed ke mata.
Yau sai ta ji hatta Kiki din abin kunya ne babba ta tambaye ta lambar Hamma. Amma har gara ta murje ido ta tambayi Kiki, a kan dai ta tambayi Nenne.
“Kiki am, nace ba, ko zaki ba ni lambar Hamma don Allah, ina cikin damuwa, tunda ya tafi ya kirani sau daya bai kara kira na ba, ni ma kuma nayi wani kuskure da ban kira shi ba, na dauka nayi saving no. din tun a lokacin, ai yanzu na duba ban ganta ba, a tsammanina zai kira again, sai inyi saving to amma yanayin da yake ciki nasan shi ya hana bai kira din ba”.
Kiki was shocked da wannan ganganci zata ce ko childishness na Aisha. Ta ce,
“Aisha me ki ke cewa? Sati biyu ba ki ji motsin mijinki ba, kuma ba ki kira shi ba ke? Sannan ba ki da digits dinshi a wayarki?
To kenan ashe duk shawarwarin da na bata lokacina na baki ma babu wanda ki ka dauka kika gudanar kenan?
Aisha me ke damunki har haka na tabbata ba kiyayya bace. To menene? Kin san girman hakkin Uncle AK da ke wuyanki kuwa? Haba Aisha, kankantar shekaru da rashin soyayya ba hauka ba ne, domin bayan dukkansu akwai abin da ya kamata mace ta yi la’akari da shi a zaman aure, shine sanin yakamata da sanin girman hakkin mijin duk da Allah ya rubuta shi ne mijinta”.
Jikin Aisha duk ya idasa macewa, dama kuma ko kafin ta kira Kiki Rukayyat, duk ta yi wadannan hasashen itama, Kiki ta ce,
“Lallai ne yanzu Uncle ke bukatar kulawarki da soyayyarki Aisha. Ya yi rashin masoyin da bai da kamarsa”.
Nan Kiki ta shiga bai wa Aisha labarin irin kaunar da ke tsakanin Sarki da Hamma. Ta gaya mata hatta dokinsa Saheeb data gani yana matukar so, da daya matashin ‘Criollo Horse’ din, duk kyauta ce ta musamman daga Emir zuwa gare shi. Abubuwa da yawa da bata sani ba a kan rayuwar Prince, a ranar yau duk ta ji su a bakin Kiki. Aisha daga karshe kashe wayar tayi tun kafin suyi sallama da Kiki, saboda zuciyarta tayi rauni, tausayin Hamma Abdulrasheed Prince, hade da wani sabon ni’imtaccen feeling da ke sauka a kasan ranta a kansa.
Kiki ta turo mata lambobin ta hanyar text message, ta kara da turo mata sakon text.
“Text him. And call him tonight’.
A take ta rubuta sakon text ta tura wa Prince. Sakon ya kunshi ta’aziyyah zallah a kan rashin da ya yi, da fatan Allah ya bashi hakuri da danganar musulunci, ya kuma jikan Maimartaba Sarki.
A kasan sakonta ta rubuta sunanta;
“Aisha-Siddiqah Yunus”.
Prince bai bude wayarsa ba sai da ya zo kwanciya barci, bayan fitar Taiwo kenan daga masaukinsa, yau ne aka yi sadakar bakwai, kuma har ya soma shirin komawa Argentina.
Yanzu Taiwo ta bar masaukinsa tana masa wasu maganganu da suka ba shi haushi da mamaki, ko dai Taiwo ta manta irin rashin da yayi ne da ta zo tana masa wannan shirmen?
“Kehinde, yanzu saboda Allah don zubar da aji da barar da kima, yarinyar nan mai kama da kazar mayu ka dau hoto da ita ka dora a status? Ka san iya mutanen da zasu bude? Me kake nufi da kalaman daka rubuta a kanta? Abu daya ma yanzu ni nake son sani, tunda aka tura maka ita ‘have you ever touched her?”
Dan bude idanu ya yi a hankali wadanda duk sun kankance, yana kallon ‘yar uwar tagwaitakarsa Taiwo Akanni, his very own twin sister Taiwo. Sai ya rasa amsar da zai bata, domin tambayarta ta fi kama da crossing limit da shiga personal marital affair dinsa.
Taiwo ta ce, “Don in baka tabata ba in ba ka shawarar amfani da kwararon roba, tunda naga alama ta fara samo kanka, na san it will not be easy for you to be using condoms, yadda ka dauki lokacin nan ba aure, ace ka daure ka iya hakan. Amma Kahinde ka sani ba ta isa mu hada zuri’a da ita ba, make her your sex slave kawai, Allah ya gani ba zan taba son yaran da za ta haifa ba”.
Abdulrasheed sai ya bude idanunsa gaba daya yana kallon ‘yar uwar tasa da mamaki da tsoro. Da kyar ya iya motsa bakinsa da yayi masa nauyi, don magana ma wahala ta ke masa tun bayan rashin Emir, yace,
“Maman Kiki, bana son yadda ki ke min maganarta. Alaqata da ke daban, wadda ke tsakanina da ita daban”.
Ya hadiyi wani abu da kyar da ya tsaya masa a makoshi, a dalilin dacin da ke zuciyarsa na rashin Kakansa, ya dubi Taiwo sosai ya kauda kunya yadda itama ta iya kauda kunya ta yi masa wannan zancen. Yace.
“Shin Maman Kiki in tambayeki please. Zaman zina nake yi da ita da zan yi amfani da kwararon roba a kanta? Ko Concubine (kwarkwara) aka kawo min itaba matar aure uwargida ba I will never do this. Kamar na wofintar da umarnin Nenne da Dade ne.
Kin ce bazaki taba son ‘ya’yan dana haifa da ita ba don kawai diyar talakawa ce. Ni kuwa kin ga ko da ‘Kare’ ki ka haifi su Kiki bama mutum dan Adam mai kima ba, banida kamar su, ba zan taba kin son ‘ya’yan da na tabbatar daga jikinki suka fito ba”.
Da wannan Prince ya maida bakinshi ya dinke. Ya ki kara kallonta. Ya maida hankali ga kunna wayarsa dake kashe tun safe.
Taiwo sai ta ji kamar bakar magana ce Kehinde yau ya gaya mata a kan mace. Macenma wannan mara aji irin Siddiqah, wadda ba diyar kowa ba.
Wato Kehinde ya fara sanin dadin mace har ya dube ta yau ya gaya mata baqar magana irin haka akan Siddiqah?
A take Taiwo taji ta kara tsanar matar dan uwanta. Kwafa ta yi ta mike tana cewa,
“Kehinde maida wukar I came in peace in dai akan ‘yar Malam Shehu ne. Abinda ya kawo ni gareka ma ba zancenta bane rabon in samu rabon bakar magana ne.
Inata so in gaya maka tuntuni cewa I met Hasina coincidently. She explained to me all what happened between she and Tukumbo. She made a mistake and she realized it. She is haunted. How much she hurt you had been haunting her. Tana ta neman yadda za ta ba ka hakuri but to no avail. Daga baya ta yi aure har sau biyu a UK ta fito, ta ce min ta tabbata alhakinka ne ya hana ta zaman aure. Ina rokonka ka yafe mata, ta ci albarkacina”.
Prince ya ce a dan hassale,
“Maman Kiki ba ni da say a kan wannan batun da ki ka zo da shi, sai dai in ce, please! Please!! Don’t mention that bitch again to me, idan kin yafe mata is okay ni ma na yafe, domin kada ki manta abin da ya yi Kehinde shi ya yi Taiwo”.
Da sauri Taiwo ta ce, “A da ba… kafin ka samu abun hutawa, amma a yanzu kana neman canzawa ne completely daga Kehinde dina”.
Kehinde din sai ya yi shiru har Taiwo ta yi tsaki ta wuce yana mamaki. Me ya shiga kan Taiwo dinsa ne? Tunda aka yi masa auren nan ta ke acting kamar ta samu tabin hankali a kan matarsa.
Ya yi nafila raka’a biyu ya sha zazzafan chamomile tea, ya kunna wayarsa kenan sai ga sakon Siddiqah ya shigo.
Ya karanta ya maimaita, sai ya samu kansa da tura mata reply da kalmar, ‘thank you’, a fili kuma ita ma haushi ta bashi. Ko da ya san ba auren so aka yi musu ba amma fisabilillah yana iya kokarinsa wajen kyautata mata a gidansa.
Bai tsangwame ta ba, bai kuma rage ta da komai ba. Amma ace ya yi tafiya irin haka har tsahon sati biyu Siddiqah ko sau daya ba ta kira shi ba, sai da ta ji ya rasa Emir?
Saboda shi Prince a mulki irin nasa matarsa ce ya kamata ta dinga kiransa don yana son respect mai yawa daga matarsa.
Kusan wannan dabi’a ce ta mazan Yoruba, suna da tsananin son respect, musamman daga matan su. Musamman a wannan lokacin da yake ganin jinyar Kakansa ya zo, ita ya kamata ta