Showing 12001 words to 15000 words out of 45634 words

Chapter 5 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

itaba.
Su din kuma ya tabbata masu cikakken iko ne a kansa, sunada ikon canza masa rayuwa zuwa wacce hankalinsu yafi kwanciya da ita.
Don haka ya shanye komai na damuwarsa a fuskarsa, haka ya boye bacin ransa a cikinsa, ya dawo daukan abu a kitchenette ne ya ganta har zuwa lokacin a inda ya barta, mamaki ya kama shi, ita komai sai an mata umarni? Sai ya nuna mata dakin dake gefen nasa yace.
“Kiyi amfani da wanan dakin”, ba tareda yace komai ba ya bude mata dakin suka shiga, ya nuna mata wajen kunna wuta da wajen kunna room heater, da yadda zata kunna shower da tap na toilet sannan ya fita, ya dauki snacks dinda da ya fito dauka a firij yasa kai ya koma master bedroom dinsa.
Yana shiga dakin tun bai kai ga zama ba kiran Dade ya shigo wayarsa.
Da rashin kuzari Prince ya zauna a gefen gadonsa yana amsawa Dade, suka gaisa, ya gayawa Dade ta iso lafiya, kuma har ya daukota, tana tare dashi a ranch house already.
Dade don farin ciki hamdala ya saki a fili kuma da karfi, har abin ya baiwa Prince mamaki. Sai ga Dade yanata shiwa Prince albarka kwando kwando, yana roka masa alkhairori na rayuwa, zuria mai dayyiba da falalar Ubangiji.
A karshe yace “yadda yayi musu wannan biyayyar Allah ya bashi masu yi masa ninkinta da gaggawa”.
Jikin Prince Abdulrasheed ya idasa macewa murus, dan sauran shirin silent protest dinsa akan zuwan Siddiqa ya karasa tsiyayewa, ya rasa wane irin son yayi aure ne haka a zuciyar iyayensa, irin addu’o’in da Dade yayi ta jero masa yau, bai taba yi masa irinsu ba, Dade ya umarceshi da ya karbi wayarta ya hada mata layi ya loda mata credit don ta rinka kiran kowa nata a Gombe dasu Nenne.
Prince yayiwa Dade alkawarin tunda yanzu dare yayi tana bukatar ta huta, gobe in sha Allah zai bata daya cikin wayoyinsa dake hade, ba sai ya karbi ta hannunta ba.
Ina zani Dade ya goya Prince! Don farin cikin sa ya gaza boyuwa. Bai san sanda yace.
“That’s my son Kehinde! Master of all my children, the great Prince of the Ilorin Emirate!”.
Ya kare wayar tasu da cewa cikin harshen yarbanci.
“Nenne mhi Iya agba opeo toba se die”. Ma’ana Nenne da Kakarsa Nani sunaso zasu kirashi yanzu domin su bashi tasu albarkar.
Suna gamawa da Dade kuwa Nenne ta kira, ko daga yadda take magana yau dashi a sake kasan cikin farin ciki take. Cewa take cikin Fulfulde.
“Allah wanne albarka Hammansu!”. Wato (Allah yayi albarka Yayansu).
Shikuma ya amsa da “Amin Nenne, Allah beddu sabbungo!”. Wato Allah ya kara girma.
Sannan tace “na baiwa Aisha WARA mai yawa ta taho maka da ita, tana cikin kayanta a duba a cire a dumama”.
“Godiya nake Nenne, madallah!”.
Uwar da Dan cikin shaukin juna suka yi sallama, ko ince Nani Oummana ta amshe wayar ba tareda ta barsu sunyi cikakkiyar sallama ba.
Cikin fulatanci Nani Oummana ta shiga koda masa halayen kwarai na AISHA-SIDDIQAH wadanda ta nakalta a dan zaman da tayi tare da ita na gajeren lokaci.
Tace "bafullatanar usul ce don haka bata da tsoro saidai kunya. Kada kayi tsammanin zata dinga jin tsoronka duk shekarun nan naka idan ka uzzura mata, amma idan ka tausasa mata zata yi maka biyayya sannan zata ji kunyarka".
Da wannan sukayi sallama shida Nenne da Nanin Gombe.
Wayar gabadaya ya kashe ya jefa ta a tsakiyar gado, kansa har sarawa yake kasancewar yayi Magana mai tsayi, a karshe yace da kansa “so Oummana ma na son Siddiqah kenan”. Dama can bata son ya auri kabilar Babansa, ta sha fada masa yazo wajensu yayi aure ya more mata.
Yanzu kuwa tunda ta samu an aura masa 'yar Gombe ai shikenan kuma kaya ya tsinke a gindin kaba. Gara ya kashe wayarsa gabadaya don yana so ya zauna ya nutsu, ya saurari zuciyarsa, ya nemi zabin Allah sannan yayi tunani mai kyau akan zuwan Siddiqah rayuwarsa, ba wanda zai sa shi nadama daga baya ba.
Wanka ya fada ya sakarma kan shi shower mai dumi. Yana wanka amma yana zufa, don iyayensa sun gama daureshi da jijiyoyinsa.
Da ya fito daga wankan ya zabi kayan barci farare marassa nauyi ya saka ya sha zazzafan chamomile tea dinda ya saba sha kullum kafin ya kwanta, don chamomile din yana bashi barci na nutsuwa duk daren daya sha shi.
Prince ya kwantar da kai a wuyan kujerar da yake zaune yana tunanin me ya kamata yayi akan zaman Siddiqah tare dashi a gidansa? Ya duba ya hanga ya ga ko ta ina babu wata mafita bayan mika wuya ga hukuncin Ubangiji da Kuma abinda iyayensa ke so yayi, hukuncin su na karshe kenan akansa, don ga dukkan alamu basu dauki al’amarin rashin aurensa da saukin da yake zato ba, ta yadda zai tunanin mayar da ita ba tareda sunyi mummunan sabawa shi da su ba.
To amma shi ina yaga lokacin zama da mace a rayuwarsa. Abar ta tsanarsu da ya riga yayi bakidayansu, da kudin goron da ya riga yayi musu na maha'inta, marassa godiya, marasa tarbiyya, marasa tsoron Allah, mazinata, masu kwadayi da rashin halacci, sannan (gold diggers).
Kullum a tafe yake kamar tsuntsu daga wannan kasa zuwa waccan, in ba jela zai mayar da Siddiqah ba yaya zai yi da ita?
Yadda Prince Abdulrasheed yayi kwanan zaune yana tunanin mafita da wadda zata fishsheshi, haka Aisha Siddiqah ma tayi kusan rabin kwanan zaunen akan kujerar sofa kwaya daya dake dakin da Hamma ya sauketa.
Ta kusan kwana a zaune dangargar tana kewar gida da iyayenta da Nenne. Amma a karshe ta lallashi kanta ta baiwa kanta baki tunda bakin alkalami ya riga ya bushe, gata ga Hamma Prince a cikin gidansa.
Ta baiwa kanta shawarar daina takura zuciyarta akan komai ko asarar hawayenta, ta fuskanci reality din dake gabanta kawai, wanda shine zaman aure na fisabilillah tsakanin ta Abdulrasheed Kehinde wanda shi Allah ya zaba mata madadin Ishaq, iyayenta suka ga shi yafi mata alkhairi akan nata kabilan, alhali sun san bata son wannan kabila ta Yoruba ko digo.
Tace tunda iyayenta shi suka zaba da saninsu na cewa Yoruba dinne, ta kuma gane ko su waye kabilar yarbawa yanzu a dan zamanta dasu a Lagos da makaranta, it will be easier for her to live with this arrogant Prince.
Ya kamata ta baiwa kanta farin ciki ta maida komai ba komai ba, ta kuma baiwa kanta ‘yanci a zama da Prince.
Abu na farko kada ta yarda ya raina ta wai don ita yarinya ce sosai a kansa, ta girmama shi yadda Allah yace a matsayinsa na mijin ta kuma babba sosai a kanta, ta shiga duk inda take so a gidannan ai gidanta ne da aure ya riga ya bata, ta kuma cire duk wani tsoro-tsoron nan nasa wanda take dan ji a baya dalilin rashin sakin fuskarsa gareta.
Zata fara rayuwarta cikin sukuni da walwala daga safiyar gobe, ta daina bari kwarjinin Prince Abdulrasheed yana yi mata dabaibayi.
Saka kai a damuwa kan abinda baka da maganinsa aikin banza ne, gara ma ta nemowa kanta farin ciki da sukuni a cikin gidan, ta hanyar yin duk abinda taga zai bata nishadi.
Tunda auren Baban Kiki yanzu aka fara, kuma ya zama dolen da bazata iya gujemawa ba har illa masha Allahu.
Aisha Siddiqa ta mike bayan gama wannan tunanin, ta shiga bathroom ta daura alwallah sai ta kintaci inda hakalinta yafi kwanciya da cewa shine gabas, ta tada sallah, ta sauke duk sallolin da suka risketa a hanya.
Sannan ta koma tayi wanka da ruwa mai zafi sosai ta sanya wata doguwar rigar barcinta sabuwa kar mara hannu da dan kauri. Ta zauna taci abinci ta koshi don yunwar cikinta kadai ta isheta kasancewar bata ci abinci a jirgi ba.
Data kammala ta dauko wayarta ta saka a caji, ta ce ita kadai "bari in roki Baban Kiki ya karba ya hada min network". Amma koda ta fito don duba shi babu shi a falo bata tadda shi a sitting room din ba, ya dade da kashe wutar lantarki da duk kayan wutar dake falon ya shigewarsa dakin barcinsa.
Komawa dakin tayi ta maida wayarta ta saka a caji, ta cigaba da kallon ko’ina a dakin tana tazbihi, don ita dai bata taba ganin gida mai shan kai irin Ranch House din Hamma Prince ba, wanda tun saukarta ta kudire daga yau ta daina kiransa Hamma sai Uncle AK. Ba don komai ba sai don kwana daya da sukayi yau a gida daya yasa kwarjininsa da kamalarsa sun karu a idanunta.
An kashe dukiya da lokaci wajen tsara wannan gidan gonar Dawakan nashi ba kadan ba, komai na gidan daban yake daga wanda ta sani, ko ta saba gani a Gombe da Lagos.
Ga caji ta samu waya ta cika full, kuma bata jin barci, amma bata da password din da zata yi amfani da WiFi din gidan. Sannan bata da kudi a wayar ma balle tayi kira na kai tsaye, kwarai take son kiran Nenne da Ummanta ta gaya musu yadda ta sauka lafiya. Son samu har Dade mai sonta da son kwanciyar hankalinta ta kira don ya tabbatar ta kwantar da hankalinta.
Anan kan kilishin da tayi sallah da waya a hannu barci mai nauyi ya dauke Aisha Siddiqah Yunus a gidan Prince Abdulrasheed (Kehinde).
Barci take yi na gajiya da tsamin jiki wanda zaman jirgi na awanni masu yawa ya haifar mata, ba ita ta samu farkawa ba sai asubahi.
Ta saba ji a jikinta idan asubah tayi, ba tareda kowa ya tasheta ba ko taji kiran sallah. Yau dinma jikinta ne ya bata cewa asubah tayi, Siddiqah ta bude ido a hankali tana salati da mika.
Ta fadawa kanta;
“Kwana na farko a gidan Bayeraben miji na!”.
Tun daren jiya ta yi wa kanta alkawarin bazata kara kuka ba, ta karbi auren Prince a matsayin kyakkyawar kaddararta. Ta amince babu nadama kuma babu kaico a cikin bin iyaye kowanne iri.
A can dakinsa Prince Abdulrasheed shi ko baccin ma bai samu ba, yadda ya ga rana haka yaga dare. Bai samu mafita ta yadda zai mayar da Aisha Lagos ba, in yaso shi ya takura kansa ya dinga zuwa akai akai. Babu mai yarda da wannan shawarar tasa tsakanin Nenne da Dade don sun san bazai jure zuwan ba, su basa rabuwa da juna sai dole don haka suke so shima ya mayar da Siddiqah abokiyar rayuwarsa.
Don haka ya qudurce raino zaiyi musu in sun gaji sun san nayi da ita don shi kalubalantar lafiyarsa ma yake yanzu akan mace. Da talatainin dare yace bari kawai ya gayawa Allah, yafi shi sanin yadda zaiyi da Siddiqah a cikin gidansa da rayuwarsa.
Ya dauro alwallah yayi cikakkiyar nafila raka’a biyu ya roki Allah ya sassauta zuciyarsa akan tsanar da yayiwa mata, idan yarinyar nan alkhairi ce a gareshi, rayuwarsa da addininsa, ya roki Ubangiji ya bashi juriyar zama da ita, don maganar mayar da ita bata ma taso ba, ba idea bace karbabbiya wa iyayensa illa wadda zata tarwatsa zaman lafiyarsa da su. Don haka koda wasa ba zai yi ganaganci ko kuskuren mayar da ita Lagos nan kusa ba.
Sai da yayi sallahr asubah da mintuna kusan talatin kafin ya samu barci, bai kuma farka ba sai wajejen karfe goma na safe.
A sannan ne ya tuna da mace cikin gidansa, kuma bai bata breakfast ba. Don ko Pareto ya kawo bazai buga masa kofar ba sai ya tashi don kansa. Prince ko dabbobinsa da tsintsayensa baya so a bari da yunwar safe, balle Dawakansa, balle kuma mutum dan adam mai amsa sunan matarsa.
“Ya salaam!”
Prince ya furta a fili, a gurguje yayi wanka da brush, da riga da wando three quarter na barci a jikinsa ya fito zuwa kitchenette, yana tunanin me zai bata taci mai sauki kafin yayi order a kawo breakfast. In yaso zuwa yamma sai yasa Pareto yayo mata cefane ta dinga dafawa da kanta, in tanada ra'ayin hakan, don ya san mata bisa al'ada su suke girkin abinci da kansu, ko daga mahaifiyarsa wadda duk matsayin ta na sarauta, bata bari a yiwa iyalinta da ita kanta abinci bata saka hannu wajen girkawar ba.
Kasancewar shi ba ma'abocin ajiye abinci bane. Yana saya ne a sanda yake da bukata kawai yaci ya tashi. Ko Pareto ya karbo ya kawo masa gida. Ya tuna cakes dinsa da baya rabo dashi a firinjinsa da choculate doughnut, sai ya jona ruwan zafi a butar dafa shayi ya hada duk wasu kayan shayi na kasaita akan tray, ya juye ruwan zafin a karamin tea flask ya hada cakes din da doughnut din waje daya, yana aikin yana gayawa kansa rayuwa mai juyi, yau shi Abdulrasheed (Kehinde) ne ya zama boyi-boyin mace.
Siddiqa ta ko kasa hawa gadon dakin ta kwanta tun bayan idar da sallarta take zaune a inda tayi Salah din, kwarai take son yin magana da Ummanta da Nenne har da Dade da Firdausi, ta gaya musu tazo lafiya tana cikin kewarsu.
Idanunta suka yi tarwai bata ko jin komawa irin barcin safennan da Prince ya samu don bata saba komawar ba, anan kan kilishi ta kishingida tana latsa wayar hannunta tana karanto azkar din safiya daga cikin (Muslim Muna Application). Sai taji alamun ana taba mata handle din kofa.
Da sauri ta daga Ido ta dubi kofar, kasancewar ko kwan lantarkin dakin bata kashe ba, haka ta kwana cikin tsananin haske abinta.
Prince ya murda kofar kadan, ya fara shigowa ya aje tea flask, kafin ya koma ya shigo da tray din hannunsa, ba tareda ya kalli inda take ba ya dora farantin kan centre table. Yana dagowa daga sunkuyon ajiyewa da yayi suka hada ido ta cikin hasken kwan fitilun da suka dallare dakin.
Kwarjinin Prince da kamshin turarensa da ya cika dakin yasa Siddiqah bata iya ta amsa masa daga kwance ba, with respect ta tashi zaune daga kishingidarta, tana amsa sallamar da yayin. Irin dan durkuson su da Nenne ta koya mata na gaida maigida ko Uba tayi daga inda take zaune, tana ambatar kalmar gaisuwa da ake yawan amfani da ita a gidansu Nenne, har itama yau da gobe yasa ta tsinta wasu daga cikin kalmomin Yarbanci masu sauki ta rike wato tace dashi.
“Ekaaro”.
Don dai ita Hamma din, ko kusa bai yi mata kama da mai jin harshen Hausa ko fulatanci ba, kamannin sa basu nuna ya san kalmar “Zo” ba, ta san dai zai kasance daga native language sai kuma turancin nan nasa mai sarkakiya da yayi tayi mata jiya.
Shima ya mayar mata, fuska babu walwala, sannan babu yabo ba fallasa. “Yaya gajiyar hanya? Thank you, and good morning”.
Sannan yace mata “please manage this tea, (yi maleji da wannan shayin kafin a kawo karin kumallo)”.
Ya juya ya fice ba tareda ya jira amsawarta ko ya dubeta ba. Har ransa tausayin Siddiqah yake ji.
Aisha sai ta samu kanta da bin umarninsa, ta tashi ta shiga toilet ta kunna famfon wanka (shower), tayi wankanta fes da kalkale jiki da sabulu, kasancewar akwai sabulai na ruwa (bath gels) kala-kala a wurin wankan masu tsananin kumfa da dadin kamshi.
Saida tayi wanka ta ji ta sakayau ta zauna shan tea din da ya aje mata. Ta ci cakes din sosai da dadin rai, kunnenta har motsi yake don dadin dandanonsa. Domin cake ne na musamman da Prince ke sawa bakery suyi masa mai dan yawa, sai ya aje a firji yana ci kadan kadan in baya son cin abinci mai nauyi.
Zaka samu Sau tari yana cinsa da yamma haka yana korawa da ruwan gahwah mai zafi (hot coffee). In kuma da dare ne yafi shan chamomile ko lavender tea.
Ta gayawa kanta bazata ke tambayar Prince ya koya mata amfani da wani abu a gidannan mai sha mata kai ba kada yaga kauyancin ta. Da kanta zata koyi amfani da komai ta hanyar amfani da basirar ta, na yadda zatayi surviving in this amazing and wonderful Ranch House.
Wanda ya hada da budewa kanta kofar fahimtar amfani da komai na gidan, ko in ta samu ya hada mata wifi ta dinga tambayar google yafi mata sauki akan ta dinga yawan tambayar sa watarana yace mata 'yar kauye.
Aisha saida ta tabbatar ta koshi, kafin ta zauna ta fidda kayanta daga cikin jakunkunan da ta zo dasu tana mayarwa tana jerawa a wardrove, zuwa lokacin in ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login