Showing 27001 words to 30000 words out of 45634 words

Chapter 10 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

Ibadan, tace rabuwar kenan, har yau ba su kara ganin juna ba.

Duka wannan ma a rashin saninsu a kunnen Prince Abdulrasheed, domin ya kasa nisa da dakin Aisha, bayan jin maganarta ta dazu, sai ya zama glued ga son jin me zata ce kuma, bayan data fahimci ya ji kallon Babanta take masa, don haka a jikin tagar dakin Aisha wadda kuma take a bude yake tsaye yana jiran isowar Pareto inda yake, domin su karasa su zaga cikin ‘Ranch’ don tabbatar da lafiyar Dawakan, don Pareto ya gaya masa a waya cewa Saheeb ba ya jin dadi.
Shiyasa ma ya kasa kwanciya ba tare da ya zo ya duba lafiyarshi ba.
Hasken fitilun lantarki na alfarma manya da kanana sun taimaka sun maida daren kamar tsakar rana a hamshakin ‘Ranch House’ din na Prince Abdurrasheed (Kehinde) Idris Akanni.
Ga dukkan mamakin Abdurrasheed, sai ya ji ransa ya sosu matuka, yana kuma cigaba da sosuwa da wannan labarin da Aisha take baiwa Kiki a kan ‘Ex’ dinta Ishaq Nafada. A ransa ya ce, ashe ma tana tsaka a kogin soyayya da wani banza can aka tsigota ni aka ba ni? Saboda cewa nayi na rasa matar aure ko? Bayan an san bata da gurbin saka kowa a zuciyarta shine ni aka bani? Irin wannan soyayyar ta kuruciya wuyar mantawa ne da ita a zuciyar mace.
Ga shi nan da aurensa ma kuma a gidansa take ci gaba da bada labarin tsohon saurayinta cikin bege mai tsanani.
Abdurrasheed ya ji wani irin bacinrai na taso masa, kafin haushin kansa mai tsanani ya kama shi, ina ruwansa da yarinyar nan nema? Balle Ex BF dinta ya dame shi? Ya girgiza kai yana ce da kansa, to tun farkoma meye nasa na jin haushi don yayi musu laben da shi yasa kansa? Allah ma ai ya hana labe.
A take Prince ya baima kansa amsa da cewa, ai ko babu komai shine mijinta a yanzu, akwai igiyar aurensa har ukku rus a kanta, wadda ko babu So, tabbas akwai ta. Aure kuma girman matsayinsa da martabarsa ya wuce duk yadda za’a kwatantashi. Darajarsa dole a jita a rai ko da So ko ba So. Ba wai don wani abu daban ba yaji haushin maganar saurayin Aisha sai don cewa shine mijinta yanzu short and simple. Kwarai kalmar nan ta Aisha “Babanta/Babban Yayanta/Uncle dinta” ta zafafe shi a rai.
Wato shi ga shi tsoho ko? Irin sa’an Babanta dinnan, don haka yaro sabon jini can shi ta ke tunawa da bege da soyayya a matsayin daidai ita. To shi yanzu in ma ba ya fada da bakinsa ba wa zai ce shekarunsa 42? Yau da babu Kiki a gidannan sai Aisha ta farraqe banbancin aya da tsakuwa, don sai ta gaya masa da bakinta yaushe ya haifeta, don kawar da komai zaiyi a tsakaninsu na rashin sabo da rashin soyayya ya nemi hakkinsa na aure, ta hakanne zai nuna mata miji ko dogara sanda yake yi don tsufa sunansa miji ne ba “Uncle” ba a gun matarsa koda kuwa ace ita matar jaririya ce don yarinta.
Isowar Pareto ne ya katse masa zazzafan tunanin, amma yaji dadin isowar tasa koba komai ya ceceshi daga sauraron Kiki da Aisha, don baya son cigaba da jin muryar Aisha, kasancewar ta jefashi a tunani da bacin rai, kuma tunaninta da Ex dinta zafi yake masa a rai, don bai saba da irinsa ba. Karfi da yaji maganganun Aisha da sanyin muryar tannan so suke yi su jefa shi a wani hali na jin radadin kishi wanda bai saba da shi ba.
Da Pareto ya iso inda yake sai Prince ya taka ya wuce gaba. Pareto na binsa a baya, suka karasa stable din Saheeb, don abinda ya fito da shi cikin daren kenan, wato ya duba lafiyarsa sosai don shima ya tabbatar Dokin ya rage walwala a satinnan.
Yace da Pareto dole da safe yayi gaggawar kiran Vetrenary Doctor din Saheeb ya bashi allura da magani.
Daga nan ya rufe ko’ina na gidan ya kashe wutar falon ya sa kai zuwa dakin barcinsa, yana shiga ya maida kofa ya rufe kansa. Lokacin kusan karfe goma na dare. A dakinma Prince kasa barci yayi akan lokacin da ya saba, Aisha’s low tone voice mai nuna tayi rashin abinda bazata iya mayarwa ba wato soyayyarta da Ishaq Nafada, ya tsaya masa a rai. Bai so aka hado shi da wadda zuciyarta na tareda waninsa ba.
Amma yanata sharewa da baiwa kansa tabbacin ba kishi bane ke damunsa, it’s just normal ai aure ne, tunda koma meye aurenta yake yi shiyasa yaji ba dadi, ya kuma ji tana zancen waninsa a gidansa ko wanene dole zuciyarsa ta motsa.
Duk yadda Kiki ta yi kokarin wai Aisha ta tafi ‘master-bedroom’ din Hamma ta tayashi kwana, har tana gaya mata cewa ta dinga kokarin yi masa tausa da kanta zata samu lada, don ta ga da injin tausa yakewa kansa messege, dan Polo ne dole zai bukaci yawan tausa kullum, tace ta tafi don Allah ta samu ladansa ta bar mata dakin ita kadai, Aisha tayi fumfurus ta ki amincewa, ta ce,
“Kiki ki rage karambani, da kaini inda Allah bai kai ni ba, ki bar mu yadda ki ka same mu kin ji ko malama, har gobe zamu cigaba da zamanmu ne irin wanda kika zo kika taras, a matsayin ‘Diya da Ubanta”.
Sai Kiki ta kule, dama tana da saurin shaka, ta jefa pillow a kan gado ta haye can karshen gadon, ta ja duvet din bisa gadon ta rufe rabin jikinta ta juyawa Aisha baya, tana cewa.
“Zauna nan wayiya, ki ci gaba da maida shi Baba, in kinso ma kice masa Kaka, har ranar da zai samo wadda za ta dauke shi Darling, duk girman nasa.
A gefe guda kuma mala’ikun rahma sunata kwashe miki albarka!”.
Aisha ta zaro ido tace,
“Kiki!”.
Kikin tace daga kwance, tana kara jan duvet ta rufe har saman kanta,
“Yess, gaskiyar maganar kenan. Mala’iku nata tsine miki. Kina kwarar Babana Aisha me yayi miki? Baki duba shekarun da ya kwashe babu aure ba haba, yayi auren ma bada son ransa ba amma kina raba daki da shi ba wata kulawa ba tarairaya. Ina gani fa ko magana ba kya son yi masa shikuma duk ya damu da rashin kula shi da kike yi
Am sure ba haka Nenne ta zata zaki yi ba”.
Daga haka Kiki bata kara magana ba ta soma jan rago (minshari) ta bar Aisha a zaune dungurgur, tana tunani da jin ba dadin hakan a zuciyarta. Musamman data ambato Nenne. Ta kuma tuna amanar da Nennen ta bata akansa na ta yi kokari ta canza shi daga yadda ta same shi.
Amma ba abinda zata iya a cikin abinda Kiki ke so tayi wato tafiya (master bedroom) da sunan ta biyo miji turaka. Ko wanda Nenne ke so tayi, wato ta dinga shiga rayuwarsa tana motsi, alhalin shi da yake namiji bai nemi faruwar hakan ba in one way or the other.
“Kiki kuma sai in tafi uninvited? Walk before you run Dear. Komai dan a hankali ne, kuma komai da lokacinsa, amma ni bazan je ba tareda ya nemi zuwana ba”.
Kiki da farko ta yi mata shiru, don minsharin karya take yi, tasan ta hada mata zafi, amma don Aisha ta san ta jita kulata ne bazata yi ba, sai ta kware bargon ta mike ta dauko wayarta a caji, ta kunna ta zauna gefen ta soma kiran layin Tosin AbdulNaseer, ta murguda baki tana cewa,
“ni in ki ka kara kula ni Allah ya isa, tunda ba kya son Babana”.
Kiki sai ta koma bata dariya rigimarta da giringidishinta Allah yayi yawa dasu, kamar ‘yar fari ba uata ba, ta kuma yarda kaunarta da Uncle dinnata mai girma ce don tsakaninta da Allah tayi Allah ya isan.

Washegari da safe ma sun sha gardama ita da Kiki, don Kiki ta dage sai ta bi Uncle daki ta gaishe shi da safiya.
Aisha ta ce, “Kiki ki bari sai ya fito (sitting room), ki fahimceni bana son wuce gona da iri, tukunnama kan ki zo kin san ya muke zaune da yanzu za ki bi ki dame ni a kan abinda bazan iya ba, ba kuma zai taba yiwuwa tsakaninmu ba?”
Kiki ta shaka, ta yi kwafa ta kyale ta, ko girkin safe da Aisha ta fara Kiki wanka ta shige ta ki taya ta, ta ce tunda ba ta je ta gaida Babanta ba bazata kuma taya ta girki ba.

Da misalin karfe goma na safe Prince Abdulrasheed ya fito (sitting raoom) din. Yana sanye da kayan barci farare sol. Daren yau ne zai tashi zuwa kasar France wasan tseren Doki na Concacap Polo Championship.
Aisha ya hango a kitchennette ita kadai, tana kai da komowa, don kokarin hada musu karin kumallo.
Motsin Uncle da kamshin turarensa ta ji a bayanta yana shigowa madafin. Da hanzari ta juyo sai ta ga Uncle ne cikin kayan barcinsa, da alama ko wankan safe bai kai ga yi ba. Aisha sai ta tsugunna ta gaishe shi, ya amsa a dake yana cewa,
“Ina bakuwar taki ta barki da aiki ke kadai?”
Aisha ta amsa da cewa, “Kiki ta shiga wanka”.
Ya ce, “Yau zan yi tafiya zuwa tournament, zan yi akalla sati guda kafin na juyo.
Kiki ta gaya min ta fasa tafiya gobe za ta zauna dake har sai na dawo.
Sai ki kula da gidan, da komai, kada ki manta ban da zuwa wajen Horses don suna harbi da kafafunsu.
Musamman Saheeb, ba ya so kowa ya je inda yake in ba ni ko Pareto ba, he is very Anti Social”.

Kafin Aishata bashi amsa Kiki ta fito ta sha gayunta kamar koyaushe, ta tadda su suna maganar tafiyar tasa. Ta ce,
“Uncle sai ka bamu kudi, kudi sosai fa, muna da activities masu yawa nida Pretty. Kama daga Shopping, zuwa su Hiking da Camel Riding. Tunda Aisha ta zo na tabbata ko sau daya ba ka fita da ita ta ga kasar nan ba”.
“Ke ba sai ki fito da itan ba, uwar ‘yan kankanba da kilbibi, baki kamar na Aku-kuturu, halan ba’a gasa bakinki yayin omogwu ba?”.
Kiki tasa dariya tace, “ka tambayi Maman Hakeem (Aunty Taiwo). Nidai kawai Uncle ka yi mana izini muna da wuraren zuwa mu mike kafa tunda baka nan”.
Katin cirar kudinshi na daya daga cikin bankunan da yake ajiya ya ciro ya mika ma Kiki, ya ce, su sayi ko me suke so har ya dawo.
Sannan zai bar masu mukullin mota daya Kiki ta kai su ‘tour round the city’.
“Banda kai wa dare Kiki, kin ji na gaya miki”.
Kiki ta amshi credit card din ta yi godiya, ta ce, “Insha Allahu Uncle ba za mu dinga yin dare ba”.
Aisha dai tana gefe tana jera abincin da ta gama bisa tebir ba ta saka musu baki ba.
Kiki ta ce, “Aisha ki yi mana godiya mana, an bamu dama mu je shopping, kuma in kai ki tour cikin gari”.
Dan murmushin gefen baki Aisha ta yi ta ce, “Kiki ni ba abinda zan saya, sannan kuma bana son yawo, gajiya zan yi”.
Kiki ta ce, “Ai da ma ban tambaye ki ko za ki sai wani abu ba, ni na san duk abin da ki ke bukata kuma ni zan dauko miki”.
Hamma bai saurare su ba, ya ja kujerar dining daya ya zauna, yau ma a tsakiya suka saka shi, Aisha na dama Kiki na hagu, suka soma cin abincin.
Bayan Kiki ta yi serving dinsu kamar jiya. Jefi-jefi Kiki da Uncle dinta na magana cikin yarbanci akan abin da ya shafe su.
Maganar Kiki kullum guda daya ce, ‘yasa baki Maman Hakeem ta yarda Tosin ya iso gida, tunda dai shi da take kafa hujja da shi din yanzu ya kama Dahir”.
Aisha ta kudire a ranta zata kara zagewa wajen koyon harshen yarbanci da gaske daga ranar yau, don ta lura Prince ba ya so ta ji ko me suke tattaunawa, shi ya sa ma ya koma magana cikin kasaitaccen yarbancinsa.
Kiki ta ce,
“Uncle AK da ban zo ba kenan haka za ka tafi ka bar Aisha a gidan nan ita kadai?”
Prince ya harare ta, ya ce,
“Kiki ke ce uban ne ko ni ne?”
Dariya ta yi, Aishama saida ta murmusa, ta ce, “Amma dai Uncle amarya ba’a barinta ita kadai a gida, son samu a ce tafiyar nan France tare ku ka yi ta, (as in honeymoon a tsakiyar birnin masoya irin Paris) koh?”.
Kunya ta nuna a fuskar Uban Kiki. Yayi maza yace “na gaya miki amma tournament za ni je ko? Kiki why are you disturbing me?”
Kiki ta bar zancen don bata son bata masa rai, ta ce,
“Shi ke nan Uncle, Allah ya kiyaye hanya. ‘yar ka zata kula maka da Aisharka har sai ka dawo!”.
Prince ya tashi da daddare, Kiki ta tsara musu duk abubuwan da za su gudanar yadda za su mori satin sosai, kafin ya dawo.
Tana so Aisha ta san gari, ta kuma daina bakunta da rashin sakewa a gidanta.
Washegari suka shirya ko break fast ba su yi a gida ba, suka tafi shopping. Kiki ita ce mai diban kaya Aisha mai tarawa. Kiki ta daukar wa Aisha lingeries, English wears da nighties kala-kala data lura bata dasu, ta ce,
“Daga yau bake ba kara saka atamfa a cikin gida, musamman in yana gidan, sai wadannan da na zabar miki in dai kinason zaman lafiya da ni”. Aisha tayi dariya tace “wasa kike yi Kiki, kema kinsan bazan iya ba”. Kiki tace “to ki ajiye ki boye, can gaba in kin yi kilin zasu yi miki amfani”.
Sosai Kiki ta bata dariya.

Suka koma bangaren kayan wanka ta daukar mata su feminine wash, deosprays da su body scrub, daga nan suka je ‘sight seeing’.
Ba su dawo gida ba sai yamma lis.

Haka washegari suka sake ficewa zuwa ganin Penguins, waterfalls da wajen Camel Riding.

Ana saura kwana uku Prince zai dawo kiki ta kai ta aka yi mata SPA da Moroccan Hammam (wajen gyaran jiki na mata na Moroccan Hammam).
Nan aka wanke Aisha tas, aka yi mata spa, body scrubing, pedicure da manicure, har da gyaran gashi, aka wanke gashin Aisha aka yi steaming dinsa, sai ga fatar Aisha har sheki ta ke yi abin gwanin ban sha’awa, dama ga ta fara tas, to sai ta koma pinkish, har wani jaja-jaja fatarta ke yi.
Kiki da aka kammala gyaran Aisha ta saita camera ta kashe ta da kyawawan hotuna, kuma bada saninta ba kawai Kiki ta tura su wayar Uncle dinta, ta (whatsapp application) dinshi.
Saura kwana biyu Prince ya dawo da yammaci suka ga wani guri ana YOGA. Don haka washegari tun da safe suka shirya suka tafi YOGA.
A can suka wuni sur! Aisha ta ji dadin session din nasu a can, waje ne na motsa jikin mata zallah, sai yamma lis suka dawo gida.
A YOGA ma sun yi hotuna masu kyau, kawai Kiki ta hau turawa babanta hotunan da suka dauka na charming lady dinsa AISHA-SIDDIQAH ba tare da Aisha ta sani ba.
**** **** ****

Prince yana reception na hotel din da ya sauka a kasar France yana hutawa kafin ya haura sama zuwa dakinsa, kawai sakon Kiki ya cimmasa.
Yana budewa kyakkyawar surar ta bayyana kamar da an tabata jini zai yi tsartuwa. Gabadaya fatar jikin Aisha ta canza daga yadda ya santa. ‘Moroccan Hammam’ din da ta sha da SPA sun karbeta, gashin kanta ya sha steaming da gyara na musamman ya kwanta a dokin wuyanta, gashi bakikkirin da shi, sai sheki yake yi.
Wani bala’in murmushi da ta sakarwa Kiki a hoton, sai daya kusa kashe idon Prince Abdulrasheed Kehinde.
Bai taba yi mata kallon da har zai ga natural features dinta a fili ba, sai yau a hoton nan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login