Showing 45001 words to 45634 words out of 45634 words

Chapter 16 - Aishah-Saddiqa book 3 complete by Takori Kabara .txt

kuma kwana a daki guda, amma Prince na kan pillow da kilishi rufe da duvet, ya sallama mata gadon, Aisha bata san irin faman da yake da kansa ba kafin wayewar kowanne gari.
Sai ya zama Prince na Allah-Allah hantsi ya dubi ludayi wato lokacin Polo lesson din su yayi, just to have that closeness da Aisha akan Doki. Sarai ya gane zata iya riding da kanta itama kuma ta fada masa yanzu ta iya, amma yace sammm, bai yarda ba fadowa zatayi in ya barta ta hau ita kadai. Duk dai don ya samu wannan kusancin da Aisha, da dan body contact dinnan mai hargitsa duk wata nutsuwa da Prince din ya mallaka cikin dare da ido biyunsa.
A sati guda da akayi ana koyon Polo Prince ya samu duk wata sha’awarsa ta da namiji ta dawo jikinsa.
Aisha bata san haka ba ta koma saka lingeries da nighties din da Kiki ta sai mata. shakuwarsu kullum daduwa take yi, they have build a good bond of friendship, a satin da ya biyo baya Prince ya soma kai Aisha yawo da shopping, ita kuma ta saki jiki da shi sosai ta sake dashi kullum tana zuba masa hirar gidansu da nasu gidan, ta fito a real Aisha dinta ta Billiri mai baki zauu. Unknown to her, komi tayi kashe shi take yi da soyayyarta cikin ransa.
A wadannan satittikan Prince Abdulrasheed ya gama sanin komai game da matarsa Aisha-Siddiqah. Itama kuma ta kara sanin abubuwa da yawa game da shi da rayuwarsa da zuri’arsu ta Akanni gabadaya.
Ya soma kiran iyayenta a waya akai-akai yana gaishesu. Ya kuma gayawa Aisha shi ya kaisu airport ya saka su a jirgin da zai maidasu arewa lokacin da suka zo Ilorin yi musu ta’aziyyar Emir kafin dawowarsa. Dade ya gabatar dashi ga Ummanta da malam Yunus. Ba karamin jin dadin wannan labarin Aisha tayi ba.
Suna cikin wannan yanayin da yafi gaban biro ya rubuta don dadinsa garesu, suka wayi gari da bakuwa a gidansu. Aisha dai Pareto ya zo ya gaya mata sunada bakuwa. Tayi mamaki. Amma tace kawai ya shigo da ita jin cewa mace ce.
Prince na dakinsa yana shiryawa zasu fita lokacin da Haseenah ta shigo falon. Aisha tayi mata sannu da zuwa fuskarta ba yabo ba fallasa. Ita kuma Haseenah sai karewa Aisha kallo take, small beautiful girl, wadda ganinta yafi jinta! Irin kallon da Haseenah ke mata, da irin shigar dake jikinta duk basu yiwa Aisha ba. suka zauna shiru a falon, Haseenah bata ce mata ga wanda tazo nema ba, ita kuma taga bai yi daidai tace mata wa take nema ba. sai suka zauna zaman kurame a falon. Haseenah na kallonta da budadden ido Aisha na neman inda zata boye kanta kada wannann bakuwa da bata san ko mayya bace ta cinyeta.
Sai ga Prince ya fito daga dakin sa cikin shirin fita, yana cewa “Aisha ina kika saka mukullin Lamborghini?” sauran maganar makalewa tayi a makwallatonsa, da yayi arba da Haseenah Ambursa zaune a falon gidansa.
Mu karasa a littafi na hudu (4)


(INA MAI TALLATA MUKU AISHA LAME ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login