Showing 6001 words to 9000 words out of 33805 words
Chapter 3 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 3 end Writing by Jamila Umar Tanko .txt
Daman
hanna ta sanarwa da kawun taranar da zasu zo
dan haka suma suka hadawa bakiabinci da abin
sha irin nasu na 'yan hutu. Harda mahaifiyar
Ramlah akazo da danginta wasu kwaidan suga
Hanna suka zo.cikin rashin sa'a basusami ganin
Hanna ba don tun 7 na safe Hanna tagudu ta tafi
can garin magarya gidan watatsohuwar kakarta ta
buya don kunyar surukantatakeji. Dangin Hanna
sai suka zama baki bude dontsananin mmk ganin
yawan lefen hanna tundasuke basu taba ganin
irin akwatinan nan ba ballekayan dake ciki. Wasu
rundima rundiman akwatinane masu santsi har
guda 6 bi da bi ta kashensu'yarkit ce a dankare
take da gwala gwalai da fashions mai tsada irin
na turawa. Leshina da shaddoji dakyana tsukewa
abun bazai misaltu ba takalmada jakunkuna
hadaddu mayuka kuwa turarruka basai na
zaiyana ba daman can ya siyo mata balleyanzu
akwatinsu suma daban. Iya haule surukartana
wajen karbar lefe hanna sai ta zama abun kallo
wasu kuma ta zamar musu abun dariya gaba
dayasaita rikice ta hau surutai. Ita abun ya zamar
matakamar wani rufa ido yanzu duk wannan kayn
nahanna ne, yanxu hanna ta dage ta tafi ta barta
tayikudi kenan bza ta iya ganinta ba balle ta sata
aiki.Allah kenan haka yake yin ikonsa ansa
ranardaurin aure sati 2 kacal sukace kuma a
ranar sukeso a zo a tafi da amarya ba sai an bata
lkc ba. Damnsun taho da kudin sadakisu d kudin
dinki duk.Msuka bayar, makudn kudi suka jifgewa
danginhanna a gabansu, wasu suka dau kukan
murna wasu suka rafsa buda suna kirari. Dangin
haisamsunji dadin yadda aka karbe su a garin
suhnna.kmar za'a hadiyesu ana ta yi musu
marhabanda wasa da dariya suka rabu akan nan
da sti 2 zasudwo su tafi da amaryar
su...............JUMA'AT KAREEM**GANGARJIKINSA
TA AURA 3**
=============9⃣=============RANAR DAURIN
AURE Ranar jumu' a ne ranar daurin auren
haisam dahanna da misalin karfe 2 na rana za'a
daura aurenbayan sallar jumu'a. Garin dashi ya
cika makil dajama'a taron da ba'a taba yin irinsa
ba a garin.Manya manyan masu kudin kano sun
halarcidaurin auren haisam, abokan babansa da
'yanuwansa abun sai wanda ya gani
hardagwamnan kano na wnn lkcn ya halarci wnn
daurinauren. Dangin hanna na nesa danakusa
sunhallara, 'yan garin kuwa da wadanda aka
gaiyatada 'yan gaiyar sodi duk sunzo su
ganewaidanuwansu kar suji ana fada su basu
ganiba. Babu abinda zaka dinga hangowa a garin
sai wasu jifgajifgan motoci bakake masu bakin
gilashi sai kumafararen shaddoji da tsadaddun ya
dika a jikinmanyan masu kudin da suka halarci
daurin auren.Kamshin turare har cikin gidajen
'yan garin 'yanjaridu tududu na nan nig daniger
suna ta daukar a hoto da bidiyo kaset. Ga
mahaifin haisam danaramlah a kewaye da
jama'a. Hiasam kuwa kohangoshi ma baza ka iya
yiba sbd jama'a kowa soyake ya gaisa dashi kowa
yana so haisam yaganshi yasan yazo donduk
dangartakarka dahaisam yace zaku bata in har
baka zo masa wnn daurin auren ba. Kafin karfe 4
har an shafafariha andaura auren haisam
yazama mijin hanna. Allahyabada zaman lfy. 'Yan
daurin aure mza sun farashiga motocinsu masu
babura da kekuna sumasun fara shiga motocinsu
masubabura da kekunasuma sun fara hawa
sunakama gabansu anci, ansha lemunan
gwangwani da ruwan kwalba kudiaka dinga
rabawa a wajen daurin auren, hakaango ya dinga
danko kudi yana rabawa mutanedon murnarda
yake ciki a ranar saida babansa yace ya isa haka
snn ya daina . Maroka duk sun cikaaljihunsu da
kudi da goro da lewa ga ruwan sanyi sun jika
makoshin su. Kowa yana san albarka dafatan
zaman lfy ango da amarya.bayan maza sun
watse motocin da zasu daukiamarya da
kawayenta da 'yanuwanta don rakatagidan
mijinta suka karaso kofar gidansu hannacikin
gidan maki yake da mata ko hanna bakahangowa
mai bidiyo kaset da kyar ya nemoamarya ya
haskata. hanna ta caba ado da wani rantsatsan
lashi baki mai adon rawayar fulawa ta sagoggoro
rawaya takalmi da jakarta baki.
fararenhannayenta da kafafunwanta sunsha
fulawar lalle.kirjinta ta da kunnuwanta da
hannayenta dambaradambara gwala gwalai ne.
babu abinda zakaji idanka matso kusa da hanna
sai kamshin turaren wuta don ta tsuma da
(dukan) tun na saura wata gudaauren kakarta ta
dinga tsumata ciki da wajeabunka da azbinawa
sunsan sirrin shirya amaryatayi tsaf ciki da bai.
an dilke fatar hanna angurgetada kayan gyara jiki
tayi sumul sumul ta kara jawur.abunka da farare
jawur jawur zaka dinga hangowa cikin gidan gashi
yalalo yalalo har bata danginhanna dai dai ne
bakake duk jajaye ne.Motar da za'a dauki
amarya tafi kowacce girma dakyau.Hanna ta
shiga ita da Hajir matar kawunta dasauran
sa'aninta 'yan uwanta dan ita bata dak'awaye
'yan uwanta ne k'awayenta.Tsofaffi suka dinga
duruwa sauran motocin kana shiga sai kaji wani
sanyi ya daki hancinka A.C ce tagauraye
motocin.Hatta manya-manyan bus din da aka
turo masu A.Cne da labulaye a wandunnan. Duk
yawan motocinda Haisam ya turo sai da wasu
suka rada waje saboda yawan jama'ar da suke so
suje Kano sugagidan Amarya.Motocin suka fara
tafiya sai Hanna ta kece da kukatana d'agowa
mutane maza da mata hannu.Har aka iso Kano
Hanna kuka take su Hajir sunalallashinta tayi
shiru. Can ta tuna da mahaifinta dama ace yana
da rai mana wannan dauka da tazomata data
taimaka masa, haka yayi rayuwarsa haryamutu a
cikin taulaci sai kuka ya kece mata.Sai da
magagriba suka isa gidan amarya a wataunguwar
jiga-jigan masu kud'in Kano gidan Hannayake mai
suna Nasawara G.R.A. Rigiji gafjin Haisam ya
tsantama gida duk layin babugida mai girma irn
na Haisam da kyau.Aka wangame jifgegen get din
gidan motocin duksuka shigo farfajiyar gidan,
amma duk da haka gafili nan fetal wasu motocin
ma fiye da biyar zasu iyashigowa ciki sbd filin
farfajiyar gifan babbane. Fulawoyi ne a shuke a
jikin katangar gidan gatsuntsaye nan da d'awisu
da talo-talo a zube afarfajiyar gidan suna ta
shawagi.Sanyi k'alau ciki sbd wasu zagayayyun
dawatsuaka gina masu 6uldulo da ruwa yana
tashi sama.Kasan da ake takawa abun a kalla ne
balle cikin gidan.Gidan 6angaren 2 ne iri d'aya ga
wani dank'arerengida a tsakiyarsu. Sai aka nuna
musu gidan Hannana gefen dama suka d'uru
ciki,wai! wai!! wai!!!Ai suna shiga sai suka ga ashe
basu ga komai a waje ba.cikingidan natsallake
shafi Guda, gashi kamar haka..Sanyi da k'amshi
ne zai fara dukan fuskarka saiwalkiyar tiles da
fitulu su fara walle maka idosannan ka fara cin
karo da kyatattun kujeru a wanikatafaren falo ga
wajen cin abinci mai dauke dakujeru da tebur a
tsakiyarsu, gefe guda kuma wani falo zaka taka
wata matattakaka tayi kasa shima agefe.Ga
makeken kicin nan mai d'auke da manya-manyan
furuj da furiza da cooker gas, da kayankicin gaba
d'ara koren launi ne aka had'a.Hatta cokulan
dake kicin d'in koraye ne har lokokin kicin din.
Dukuna uku ne a gidan, d'aya a k'asa kowanne
daband'akinsa a ciki da gado d'an kamfani da
madubida waduruf.Biyu kuma a sama makad'a-
makad'an had'd'd'ungadaje ne ya fi na kasa,
suma da bad'akansu a cikida wani katafaren falo
a saman. Duk kusuwar gidan an ajiye fulawuyi
irin na robarnan masu kama dana gaske.Ga
kayan kallo nan dana jin kid'a a
falukan.....kowanne d'aki kuma akwai talabijin an
had'a ta datauraron d'an adam (settelite).Tunda
Hanna ta shiga gidan kukan dad'i take a
zuciyarta kuma tana hamdala tana yiwa Allah
kiraritana gode masa.Allahu akbar.K'arfe 8 dai-
dai bayan duk sunyi salloli sai Hasamyayiwa
Hanna waya ya ce ta shirya ita dak'awayenta
kawai banda tsofaffi da yara zai turo motoci azo a
d'auke su matar gwamna ta shiryamusu liyafa a
Tahir quest place har mutane sun farazuwa tayi
sauri.Hanna ta shaidawa k'awayenta nan fa duk
sukafara shiri.Ita kuma ta fad'a wanka ta fito ta
tarar Haisam ya aiko da mota da wasu kaya da
takalmi da jakarsuda ribon duk kalarsu d'aya ya
ce inji matar gwamnata ce ta saka.Kayan kansu
abun kallo ne wata shadda-shadda,leshi-leshi
mai surfani riga da zani aniywa zaninkwalliya
d'ankwalin kayan kuma an nad'oshi kamar
goggoro irin kayan nan ne da ake d'inkowadaga
Senegal to wannan na musamman ne sai
irinmatan gwamnonin ne suke iya siyansu.Hanna
ta saka kayan nan ta tufeke gashinta daribon
kalar kayan ta d'ora goggoron kayan bayanhoda
da jagira da janbaki da tasha tazo ta saka
tsadaddun sarka da d'ankunne irin kalar kayan,
gatakalmi da jaka ta d'ana.Sai kowa ya bude baki
yana kallon kyau dagaAllah.Hanna ta zama kamar
wata tauraruwa mai haske acikin taurarin masu
disheshshen haske. Sai walkiya take,Hajir ta
fesheta da turaruuka designers saik'awayenta
suka take mata baya suka fito sukashiga motocin
suka nufi Tahir quest place dakeLamido
cresent...A bakin get din hotel suka iske Haisam
da tulinabokansa suna zazzaune akan motocinsu
sunajiran isowar su Hanna.Hanna na iso suka
bud'e baki suna kallon ikonAllah. Ko a mafarki
basu d'auka zasu ga amarya Haisamkyakykyawa
kamar balarabiya ba.Musamman da suka je
d'auren auren suka gawannan 'kauyen sai duk
suka raina bikin sukacewa banda soyayya ma ne
Haisam zaiyi da matark'auyen nan a bayan
idonsa amma fa. Ashe wannan 'yar k'auyen ta
linka matansu nabirni had'uwa.Suna ganin Hanna
kamar idan kayi mata hausabazata iya mayarwa
ba tsabar babu wata surartaguda d'aya data yi
kama da bahaushiya.Ta k'aso ita da k'awayenta
wajen da su Haisam suke tayi 'yar siririyar dariya
ta duka kadan tagaishesu duk suka amsa.Haisam
kam ko amsarwama ya kasa yi saimurmushi yake
ya k'ura mata ido.Ya mik'a mata hannu wai su
gaisa sai Hanna tasaHannu ta rufe ido. Abokansa
suka hau cewa ai yanzu Hanna amaryakomai yazo
karshe babu kunya Haisam ya
zamamijinki.Haisam ya diro daga kan mota ya
rike hannunHanna abokansa da k'wayenta suka
take musubaya suka dunguma zuwa wani
katafaren d'akin taro (conference hall) inda ake
gudanar da liyafar,ashe jama'a jingim sun taru
isowar ango da amaryakawai ake jira. Hall d'in
haske ne tar kamar safiya ga wani sanyinna'urar
sanyaya d'aki wasu dogayen teburan netafka-
tafka a jejjer a cikin d'akin taron jama'a mazada
mata zazzaune.Kwalayen lemune da kofuna
tangaran da robarruwa a gabansu, gefe guda
kuma masu kid'a ne da gangunansu a gefe 'yan
police banda suna d'ankadawa a hankali kafin a
fara gudanar da biki,Hanna na shiga taga
idanuwa cununu akanta gabad'aya an tsaya ana
kallonsu.Tebur guda Ramlah ce da k'awayenta
had'ad'd'un'yan boko duk sun zubo mata
ido.Hanna ta d'ago ta kalli Ramlah sai taga
Ramlah tayi mata murmushi itama ta mayar
mata.Koda kuwa ta had'a ido da sauran
k'awayenRamlah sai harararta suke da kallon
banza.Hanna ta sunkuyar da kai k'asa suka
wucehannunta gam a hannun Haisam suka nufi
kanwani k'ayataccen dogon teburi akan wata
matattakala (high table) da k'ayatattun
kujeruguda 2 irin na ango da amarya.Anan suka
zauna sannan kowa ya d'au tafi.Abokan ango da
k'awayen amarya suma sukasamu kujeru suka
zazzauna.Baban abokin Haisam wani mai surutu
mai suna Jibril (Jibson) shine take jawabi a
lasifika.Bayan ya bud'e taro da addu'a ya ce ga
matar maigirma gwamna nan da tawagarta suna
shigowawace ta had'a wannan taron itama tazo
taya angoda amarya murna.Kowa ya zauna yayi
tsit ana kallon k'ofar shigowa wad'anda basu
ta6a ganinta a fili ba suna so sugayaya take a fili
wad'anda daman sun ta6a ganintasuna so suga
wanne irin kayane a jikintamusamman mata
masu tsegumi ana jira aga wanneirin leshi yau
zata saka, wacce irin jaka kuma zatarike. Dan
daman an san uwargidan maigirma gwamnaakwai
iya tsala kwalliya kuma irin ta had'd'u 'yanboko,
ga gayu ga kyau.Mai girma uwar gidan gwamna
ce ta sako k'afartacikin katafaren dakin taron
gefenta matarmataimakin gwamna ce d'aya
gefenta kuma wasu daga cikin kwamishinonin
gwamna suma sundoshi goma bayansu kuma
wasu mata ne guda 2inyamurai suna sanye da
riga sut da d'an gajerensiket iyakar gwiywowinsu
sune body guards d'inta(S.S).Dogon tebur guda
aka ware mata datawagarta.Suka zazzauna itace
a tsakiya. Kayan jikinta irin nahanne ne shima
ready made ne komai sak danahanna saikalarce
ta bambanta, na hanna green nena matar
gwanma kuma komai nata pink ne.Hanna ta kalli
matar mai girma gwamna ta juyo ta kalli hanna
suka hada ido tayi mata murmushi.Hanna ta juya
takalli haisam taga shima murmushi.Tace yaya
amma matar gwamnan nan tayi kama dawata
kwata. Haisam yace kawarki. Nusaiba ko?Tace
ashe kaima ka gani wlh sak nusaiba idris.
Yayimurmushiyace ai ba kama bace nusaiba ce
cewa tayi kar in gaya miki saidai kawai ki ganta.
Hanna tadafe krji don mkk tana cewa wayyo Allah
yanzuwnn nusaiba idris ce ashe zan sake ganin
nusaiba aryw ta?Hall ya cika ya tumbatsa da
hamshakan matanmasu kudi a hnkl hanna ta
dinga hango wasu dagacikin kawayensu 'yan
mkrtr su ta hango rauda maa zaune a gefen
nusaiba. Tace ashe ruda zata girmatayi tsawo da
kib? Bodane yake cashewa kannenramlah da
haisam ne suke cashewa su amratu. Sai jibril mai
jawabi a lasifika yace a bawa amarya daango fili
su fito su cashe. Kowacce ta komata
zauna.Hanna ta kalli haisam shin yana kallonta
taji waninauyi yaya za'ayi tafito fili ta yi rawa ita
da yayahaisam a matsayintana malaminta wanda
takemutukar jin kunyar. Sai taji ya kamo
hannunta suka mike gaba daya suka fara
saukowadaga kan stage.Ramlah ta
aikawanikaninta wajen masu kida tacepolice band
ne zasu kdawa ango da marya wakarsarmadan
kauna in tayi dadewa mutuwa ce kerabawa. Haka
kuwa akayi police banda suka sakikida da waka.
Ango da amarya ne kadai a tsakiyar fili. Ango ya
tsaya cak yana kallon amarya. Itamamaryar a
tsaye. Take ta daga kai tana kallonhaisam. Sai
hawayeyake zubow daga idanuwanta,yasa
hannuyana goge mata. Sai shimahawayen yafara.
Diso masa, sai ramlah ta tasotazo tana ta
zubamusu kudi abunka damata sarakan bidi'a
nan fa kowacce tanaji da kudi ta budebakinjaka
tanufo filidon ta yiwa ango da amarya liki. Jidda
(hidaya) akaki kiranta dashi matar yaya habib. Ta
karakarasowa filin ta Dinga yiwa ramlah liki da
'yandubu dubu ita kuma ramlah tana likawa
mijinta daamaryarsa kudi. Matar gwamna haj.
Nusaiba ta dinga liki ai kuwa police band da suka
ga ruwankudi sai suka saka himma suna
sakedukanganga.lall ai bikiyayi biki hanna ta
rungumenusaiba da rauda sai hawayen farinciki
sukeyi. Ba'atashi daga taro basai karfe 1:30 na
dare. Bayanancinshaan cashe.Kwanan dangin
hanna 2 a gidan amarya kawisuna shakatawa sai
da kawu ahmad ya aiko yacemaza maza su hado
su dawo sudukansukar a ragekowa snn
sukatarkato suka tafiba'a son ransu ba.Hanna
kuka suma kuka suka shigamotocisuka tafi.A
hanyane dangin hanna sukayiwa iya haulehabaici
ganin duk jikinta yayi sanyi ganinAllah ya
sakawahanna da gidan tangaranma banasiminti
ba. Wata kakar hannace ta fara cewa allahya bwa
hanna gida, gida kamar ba'a duniyaba.Wata ta
sake cewa oh har daake tadajijiyar wuyawaibaza
a kai hanna gidan sumuntiba ashe gidan
tangaran ma Allah zai bata, sauran suka
tsomabakisuna yabawa inna haule mgn.inna
haule tayi tsurutsuru a zaune a mota tasan daita
ake tasantayikuma ba sharri kayi mata ba.
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
GANGARJIKINSA NA AURA 3 Part 2
Posted by ANaM Dorayi on 05:39 PM, 30-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
Bayan tafiyarsu masu iki matasuka shigo
bagarenhanna suk hau kalkelewa suka wanke
bandakunasukashishshinfida sababbinzannuwan
gado sukafashe gidan da turarrukan kanshi. Wani
kuku ne akicin yna ta shirya mataabincin kala
kala.hanna tayikuri a zaune. Katafaren
dakintdake sama itakadai sai talabijinta rasa
meke damunta murna takekobakin ciki. Taji ana
kiran sallar magriba sai tatashi ta shiga bndaki ta
dauro alwalla tazo tashinfida abin sallatayi sallar
mgriba da nafilfilo dtasaba. Ta zauna tana lazumi
har sai da taji ana kiransallar isha'I snn ta tashi
ta kawo sallarisha'I. Ta idartana linke abin sallar
ne tji wayar dake ajiye agefen gadonta tana kara
ta dauka a hnkl gamidacewa hello sai taji muryar
wani bagwareneturanci yake yi yce madm nine
kukun ki dagakicinmake yi miki waya na gama
abinci ne jera mikiakn dinning table zn iya
tfybabu wani abu da za'a dafa miki? Hanna taji
wani abu banbarakwai waninamiji d suna hajara,
Abu na frko daya bata mmkwi yu itace madam ke
shida mata ngama abinci tazotaci kawi inhrma
akwai wani bunda takeso adafamata ta fada,
mmk na 2 kuma shine yaya za'ayi abar garjejen
namijibama ba haushe bane ya shiga gidan
matar aure yana dafa mata abinci daga ita saishi
wnnba tsarinmusuluncibane. Hanne yace zi
iya.Tfy banu wani bu da zaiyi mata.
Tajimotsinbudekofarsa ya fita. Ta zauna a gefen
gadotayishiru tana tnn.can ta tun she fa yanzu
itamaryace,kuma tund babu kowa wata kila
haisam ya shigo bari taje ta yi wanka ta sake
tsala kwalliyairinta matan dasuka san darajr
mazansu. Tayi sauri tafada bandaki ta dinga salla
wanka ga sabulai nankala kalahar dana ruwa.
Tana fitowa ta zauna kanmudubin dake shake da
kayan shafe shafe ta fararangda kwlliya dafesa
turarurruka suk jikinta. Tasha hoda da janbaki da
gazalta zubo gashinkanta har baya bata tsrke ba
ta barshi bazai. Tasaka wanidogon siket na jeans
da wata yaryaloluwar riga bulawusmi dogon
hannu dabuddden kirjin. Tsa wani takalmi mara
nauyi maikama da sosan katifa ta fara saukowa
daga kan bene. Tana isowa babban falon dake
kasa saitajiwayar dake ajiye a falon tana kra.
Hnna ta karsa knteburin dawayar take. A jiye tasa
hannu ta daukasai tji muryar ramlah ce take
fara'a tace helloamarya yaya kadaici ke kadai yau
kowaya watseanbarki ko? Aiya don't worry haka
rywr aure take sai a hnkl zaki saba. Amma yau
bazan barki kikwana kadai ba zan kawo mikimai
raya ki kwanagamu nan zuwa. Hanna tayi
murmushi tace antyramla ina yini ramlah tace lfy
lau kanwata gamunan ma zuwa saimu gaisa
sosai. Suka ajiye kanwaya. Hanna tyi jigum a
tsaye tana mmkn yadda ramlah take fara'a da
nuna mata so da kauna tace aranta Allahkenan,
ya hadani da duk abind zanjisanyi a ryw ta. To
wa anty ramlah zata kawomin tatayani kwanina
jin amratu ce kai ko dai haisam ne?Hanna ta
dubi matsatstsun kayan dake jikinta tagagsky
baza ta iya sakewa ba a gaban hisamba. Sai ta
koma sama ta doro doguwar riga baka mai
dankwali kafin t sauka sai taji muryarramlah
tanasallama a fallon kasa. Hanna ta sauka
tanarangwada ta karaso wajen da ramlah
dahaisamsuke tsaye tayi dariya tace sannun ku
da zuwakuzokuzauna suka zazzauna dukkan su
fuskarsu cike da fara'a. Hanna ma ta zauna a
kunyace tagaishesu, suka amsa ramlah tace
munzomuciabincin don yau a nan zamu ci abinci
intaya ku hirain tafi in barku, ko bakiyi abincin
damu bane? Sai alkcn hannata dubi dinning table
taga katan teburincike yake da manyan foodflask
din abincitayimurmushi tace antyna isa in ki yin
abincidaku, da ku akayi. Suka mimmike sukanufi
dinningare. Haisam ne a tsakiya ramlah a gefensa
na hagu,hanna na daya gefen, suka fara
zuzzubawa a filetsuna ci suna hira. Ba sosai
hanna dahaisam sukacika mgnb, ramlag ce take t
zuba surutusun jinta suna satar kallanjunansu.
Bayan sunkammala sukadawo kan kujerun falo
suka zazzauna suna kallonwani film da akeyina
gefensa rmla na daya gefennasa duk a doguwar
kujerar suke.Haisam ya nisa yayi gyaran murya
yace uwargida ramla tare da amarya hanna babu
abindazance dku sai gdy ina fatan alheri a rywr
mu gda 1ina fatn Allah ya bamu zman lfy. Ramla
kece babba.Kuma Alhmdl kin nun halin
manyakinyimanahalaccibabu abunda zance
mikisai Allah ya saka miki da gidan aljannah.
Ramlakin kasance mai tsananinhnkldatnn
donhaka don allah inarokarki dakicigaba da
yaddda kika fara kicigaba danunawakanwarki
kuma abokiyar zaman ki hannakaunar da kike
nunamata kadakisaurari mazugamasu zuwasuyi
zuga don suhargitsama'aurata. Ramlah
tayimurmushi tacehabahaisamy akamataka
fahimce ni idan nasa raina ncezanyi bu gskybabu
mai zugani in fasa. Ina sonka dayawa nagadace
inso dukabindakakeso dan haka najihar
rainainason hanna musamman na lura hanna
nadaladabi dason zman lfy. I S Azamu zunalfy.
Haisan yajuya ya klli hanna wacce kanta yake a
sunkuyeakasa tanawsa dadan yatsanta yyi
murmushi yaceamarya ke baki ce komai ba?
Hanna ta dagokai tayimurmushi tace I S A zamu
zaunalfy zan zama maibiyayya a gareku kuma ni
tsakninadaku sai gdyAllah ya saka da
alheri.Ramlah da haisam suka ce amin. Ramlah
tayunkura ta mike tsaye fuskarta cike da fara'a
takalli haisam ta juya ta kalli hanna tace to
amaryyada ango zan tafi in barku sai da safe.
Haisam yaceuwar gida tfy zakiyi bari mu rakaki
har gidanki ko?Hanna ta mike suka dunguma
suka fita suka nufi bangaren ramlah. Haisam na
tsakiya suna tafe sunahira har kofar shiga
bangarenta suka raka ramlah.Ramlah tayi
murmushi tace torakyar ta isa haka kukoma ni
dai gidunmawa tada zan baku anan itacena bawa
kanwata kwana 10 da angonta ku hutasosai.
Hanna tayi. Murmushi ta sunkuyar da kai tace
a'a anty ramlah kwana ma 2 ya isa. Haisam
yaharari hannayace
maimakonkiyigdyshinekikekihar guduna kike? Su
duka sukatuntsire da dariya. Ramlah ta juya ta
shiga gida taceni dai na barku lfy sai da safenku.
Tanashig ta turokofa ta rufe tasa mukulli ta bame
sai ta sulale ta zube a kasa yayin dawani
zazzafan hawaye yadinga zubo mata tsananin
kishiyakamata sbd tanason haisam matukar so
babu yadda taiya dole tasoabunda
yakeso.kishikumallon mata.Haism da hanna
sukajuya sukanufi bangarenHanna, suna tfy a
hnkl suna hira. Hisam yakai hannuzai rike mata
hannu sai yaga ta goce tayi gefe.Haisam yayi
murmushi yce Allah ya bakihkrhannata na fasa
rike mikihnnun tunda rowa akeyimin. Suka shigo
cikin gida haisam yajawokofarfalon ya datse.
Haisam yace da hannazo muje sama muyi sallah.
Hanna talangwabe kaicikin siriyar murya taceyaya
nayi sallar isha'I tundazu. Haism yayi
murmushiyace ai nafila zmuyi. Tamike kanta a
sunkunye akasata wuce gab hasm nabiye da ita
suka hau sama. Daki hnna ta wuce kai tsaye ta
shiga bandaki, haisam kuma sai