Showing 12001 words to 15000 words out of 42465 words
ƙaranci koda yaushe tana makaranta,in dare yayi kuma tayi bacci.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ga ummu cikin kwanciyar hankali ita jinior duk abinda sukeso ko babushi a nigeria inde sun nuna sunaso se Prince yasa ansamo musu shi ko menene kuwa.babu abinda prince yakeso irin yazo ya tadda ummu batayi bacci ba ƙwayar idonta kawai yakeson gani dan tabbatar da hasashenshi,uwa uba kuma yanaso magana ta shiga tsakaninsu dan yaji da wacce kalma zata fara yimasa magana,dan masoyiyarsa ta mafarki akwai wani suna da take kiranshi dashi wanda duk duniya babu me kiranshi dashi se ita.sede duk zuwan da yakeyi tana bacci inkuma yaso zuwa da yamma yanayin aykinshi baze barshi ba.
Muamala tsakaninshi da ƴarfillo kuwa ba abinda suka fasa,kullum ba ranar banza,kuɗi kuwa sanadin su ummu ƴarfillo bazata iya faɗin nawa ta mallakaba,gashi prince ya semata wani danƙareren gida acikin garin Abuja ta koma dama wanda take ciki haya takeyi.
Faɗin kyau da haɗuwar Gidan ƙauyancine dan gama babuce kawai babu a gidan.ɗakin ummu daban haka na ƙaninta,ankashewa ɗakunan dukiya bata wasa ba.
*Bayan shekaru Biyu*
Yau jummaa ummu tana gida ba makaranta dayake duk ranar jummaa basa zuwa,tsifa ƴarfillo tayimata ta gyara mats gashin sabida anjima zasuje saloon ayi mata kitso.
Sanye take cikin Riga da wando ja da fari ƴsn kanti wandon three quater ne yayin da rigar armless ce,gashinta an ɗaureshi da rimbom fari da ja,ƙafarta sanye cikin takalmi shima fari da ja.
*UMMU AYMANA*kenan baiwar Allah.
kyau iya kyau ummu tana dashi duk wani abu da ake kira kyau ga ƴa mace ummu ta mallakeshi tun yanzu da take da shekaru goma sha uku a duniya,fitowa tayi falon gidansu cikin tafiyarta me ɗaukar hankali gurin ƴarfillo ta nufa wacce ke ƙoƙarin ɗaurawa jinior igiyar takalminsa amman yaƙi tsayawa se wahal da ita yakeyi.ummu na ƙarasowa hayewa bayanta tayi wanda hakanne ta tilastawa ƴarfillo sakin abinda takeyi ta riƙeta,cike da shagwaɓa cikin gurɓatacciyar hausarta wacce kowa yaji yasan bafulatana ce tace.
"Mummy har yanzu baki gama shirya jinior ba bare mutafi da wuri,nifa kinsan banason rana wlh,shimane shegen jiniorn ya tsaya yaƙi tsayawa"ta faɗi gamida dungurewa jinior kai wanda bemasan tanayiba wasan shi yake da teddy bear ɗinshi.
"Lalalala kika zagi me sunan daddy tonide bs ruwana kuma sena faɗa masa kin zageshi".
A gigice ummu take kallon ƴarfillo kai da gani base sn faɗa makaba ta tsorata bakinta har rawa yakeyi gurin furta.
"Don Allah karki faɗa masa wallahi bazan ƙaraba,kuma dama kinga ni ban taɓa ganinsaba zakisa yace baze bari inganshi ba,nide kiyi haƙuri".
Dariya ƴarfillo tayi sannan tace, "to karki kuma zaginsa kinji ko".
Daganan gama shiryashi tayi sannan ta kwashesu a mota zuwa gurin saloon,akan hanyarsu ta zuwane Prince ya kira ƴarfillo a waya ɗagawa tayi cike da farinciki.
"Ina kuma kika kwashi yaran kukaje nazo gidan duk ba ƙwanan?kinsanfa banason yawo".
Prince ya faɗi cikin muryar dake nuna bashida walwala.
"Ayya prince wlh naje kai Aymana saloon ne ba wani guri najeba".
*Aymana*itace kalmar da prince yashiga juyawa akan bakinsa kamin daga bisani yace.
"Wacece kuma haka?,ina kika baro ummu da kika tafi yawon raka wata saloon?".
dariyace ta ƙwacewa ƴarfillo sannan tace.
"Prince kenan to ay ummun ce Aymanar,duka sunanta ne koda yake kai da ummu kawai kasanta to sunanta Ummu Aymana".
"Hasbunallahu waniimal wakil"itace kalmar data fito daga bakin prince badan komaiba sedan tsananin mamakin yadda akayi take ɗauke da sunan masoyiyarsa wato Aymana.
Ƴarfillo ce ta katse mishi tunani da cewa.
"Prince lafiya kuwa?".
Da kyar ya furta.
"lafiya lau,ko a ina kike please kiyi gaggawar zuwa gidana yanzu na baki 30 minutes"yana gama faɗa mata haka ya kashe wayar.
Hankali atashe ƴarfillo ta juya aƙalar motar zuwa Gidan Prince dan a rayuwarta babu abinda ke ɗaga mata hankali irin ganin Prince cikin damuwa.
Tana zuwa dayake ansanta buɗe mats get akayi ta shiga,tana yin parking ta ɗauki jinior a hannu ta kama hannun Ummu suka,shiga cikin gidan.
Muje zuwa.
taku har kullum
Maman Yusuf.
[7/5, 16:58] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad@zahrasurbajo*
😝😝😝😝😝😝
*Tun kan a haifi uwar me sabulu balbela take da farinta,Alhamdulillahi Allah shi ya haska surbajo a zukatan mutane ba wata ƙungiya ba,kuma tunda Allah shi yawa surbajo riga babu wani wanda ya isa ya tuɓe mata,wallahi nan gani nan bari dukiyar uban wani,shiga nayi dan ƙashin kaina batare da shawarar kowa ba kuma yanzu ma na fita ba tare da na shawarci kowa ba,sabida ina da ikon zaɓawa kaina abinda yadace dani,hhhhhhh lalle surbajo kina da matsayi a zukatan al-umma tunda har ake bin groups ana cireki dan kin zaɓi abinda yake dai-dai,hhhhhh lalle na yarda KUNU LABARIN WUTA YAKE JI SHI KO TSIRE ZAHIRI YA GANI,duk mesona ni kaina to mu ɗora daga inda muka tsaya,duk me sona dan ƙungiya ya kamata ka dena dan angulu ta koma gidanta na tsamiya*
*page 31-32*
Suna shida falon gidan ƴarfillo ta ajiye su ummu sannan ta shiga ɓangaran da prince yake.
Yana ganinta ya miƙe yana murmushi rungume juna sukayi sannan ƴarfillo tace.
"Prince ka ɗagamin hankali wallahi ban ɗauka,zan sameka cikin nishaɗi ba".
murmushi yayi sannan yace,
"se gashi kuma kin samenin,ina kika bar su Aymanan?".
"suna falo"
"ok to muje mu gaisa dan so nake zan fita".
dariya ƴarfillo tayi sannan tace.
"wlh prince kanada rigima yanzu dama dan ka gaisa dasu ummu ne yasa kace inzo?"
dariya shima yayi sannan ya ɗaga mata gira ya kashe ido ɗaya yace.
"Laifine dan uba yaso gaisawa da ƴaƴanshi?"
"rufamin asiri ni bance ba muje ka gaisa da kayanka" tana kaiwa nan taja hannunshi zuwa falon.
gab da,zasu shi falon Prince ya ƙwace hannunshi daga nata,juyowa tayi tana kallonshi murmushi ya mata itama ta mayar masa suka ƙarasa shiga falon,lokacin da suka shigo yayi dede da lokacin da ummu take wasan hajijiya a falon jinior yans dariya juyowar da zatayi ta faɗa ƙirjin Ayman,kwantar da kanta tayi a ƙirjinshi sabida jirin da take gani sedr ƙamshin turaren da tajine ya haddasamata ɗagowa da sauri dan ganin shi ɗinne na mafarkinta ko ba shi bane.
Ɗago idonta keda wuya suka haɗa ido ita dashi,bakinsu ne yafara rawa wajan son furta kalma,atare kalmar ta fito daga bakunansu,Prince yace.
*HAYATI*
ita kuma tace.
*QURRATU AYNI*
Gaba ɗaya prince rasa inda zesa kansa yayi dan tsananin farincikin dayake ciki na haɗuwa da hayatinsa da yayi bayan ya kwashe tsawon shekara biyar yana mafarkinta da ita yake kwana da ita yake tashi,kullum so da ƙaunarta ke ɗawainiya dashi.
A nata ɓangaran itama Ummu tayi matuƙar farincikin ganinshi sabida shekara uku kenan tana mafarki dashi yana taimaka mata kuma yana bata labarai masu daɗi itama kullum se tayi mafarkinshi amman bata taɓa faɗawa kowaba.
Ƴarfillo ce ta katsesu daga kallon ƙurillan da sukewa junansu,da sauri suka ɗauke idanuwansu akan juna kowannensu yan murmushi.
Cike da mamaki ƴarfillo tace,
"Qurratu ayni,hayati,dama kunsan junane da jimawa?"
Murmushi prince yayi wanda tunda ƴarfilo take tare dashi be taɓa yimata irinshi ba,sannan yace.
"Kema de kinjiki da wani zance,ina na taɓa ganinta ma inba yauba,suna kuma da kikaji na kirata dashi tana kama da wata ƴsr film ɗin larabci ne to kuma jarumar sunanta kenan Hayati shiyasa kikaji na kirata dashi" .
murmushi tayi wanda ke nuna ta gamsu da bayanin nashi,sannan tace.
"Haba nifa ince,amman kaga ummu harda wani cewa Qurratu ayni,ni nasan larabcin da ake koya matane a islamiyya shine ta karramaka da sunan a farkon haɗuwarku".
Murmushi Prince yayi sannan yace,"wannan gaskiya ne"
Ranar wuni sukayi a Gidan Prince sam ya hanasu tafiya saloon ɗin da ƴarfillo ta takura cewa yayi ta kawo kayan kitson shi zema Aymanan kitson.
Dariya sosai abin yaba ƴarfillo dan ta ƙureshi seta miƙa masa jakar kayan kitson ummun,ayko kiran ummun yayi taje kan kujerar da yake kai kwantar da kanta yayi akan cinyarshi yashiga kitsa gashin,.
Ba ƙaramin mamaki abin yaba ƴarfillo ba bakinta har harɗewa yakeyi wajan yimada tambaya.
"Prince taya ka iya kitso haka? abun yafa bani mamaki sosai wlh"
Murmushi yayi sannan yace.
"ba abin mamaki bane ƴarfillo, sabida shekara biyar na kwashe ina yin wannan kitson a mafarki wanda koda wasa ban ɗauka zan iya yinshi a zahiri ba, segashi kuma nayi,wannan kitson da nayi wallahi ya ƙara gasgatamin mafarkina"
Dariya sosai ƴarfillo tayi sannan tace.
"lalle ka amsa sunanka Ɗansarki me abun mamaki,kace mu yanzu ba ruwanmu da saloon kawai da mun tsefe kai muyo nan" ta ƙarasa zancan tana dariya shima dariyar yakeyi.
Ita ko ummu aymana duk inda Prince ya juya idonta na kanshi so take yamata irin hirar da yake mata a mafarki wani sain har bacci zantukan suke sata,shima idonshi nakanta so kawai yake tamasa shagwaɓar da take masa untanjin bacci a mafarki tace se ya goyata,amman dayake shi yafita wayo yanayine da system gudun kar ƴarfillo ta ɗagosu.
ƴarfillo ko koda taga ummu na kallon Yman ɗauka tayi dan yau ne tafara ganinsa shiyasa take kallon nasa shiyasa bata ɗauki abun serious ba.
Ba su suka baro gidan Prince ba se bayan ishsha'i tare da rakiyar prince da muƙarrabansa.
Hmmm me karatu nasan ya ƙosa da son sanin waye Wannan prince ɗin,to muje zuwa.
*WAYE PRINCE AYMAN*
Taku har kullum
Maman Yusuf.
[7/6, 09:26] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad@zahrasurbajo*
*page 33-34*
Ayman Abu Ayman shine sunanshi,saurayine ɗan kimanin shekaru talatin da uku a duniya.
Ɗa ne ga Sarki Abubakar,Amman tundaga ranar da aka haifi Ayman mahaifinshi yamaida sunan shi Abu Ayman shiyasa yanzu kowa da wannan sunan yasanshi,sarkin dake mulkar masaurata mafi Girma a faɗin ƙasar nigeria,wato masarautar kano.
Abu Ayman adalin sarkine me tsoron Allah,yanada mata biyu da ƴaƴa huɗu dayake Allah be bashi haihuwa da yawa ba shiyasa yake tsananin son ƴaƴan nashi.
Hajiya Zaituna itace uwar gida wacce ake kira da Hajiya babba,ƴaƴanta uku duka mata,Zainab,khadeeja,Hafsa.
Se Hajiya Jameela wacce ake kira da gwaggo amarya itace mahaifiyar Ayman,shi kaɗai Allah ya bata,kuma shine ƙaramin gidan dan sauran duk sun girmeshi.
Gidan babu kishi acikin shi shiyasa gaba ɗaya kulawar Ayman ta koma hannun Hajiya babba tana sonshi kamar ita ta haifeshi dan seda yayi wayo ne ya gane ba itace mahaifiyar shiba,haka suma sauran yaran gwaggo amarya na nuna musu soyayya ta aynihi.
Gaba ɗayan yayyan nashi sunyi aure dan haka shikaɗaine yarage yanzu a cikin gidan,se kuma ƴaƴan yayyan nashi da suke gidan.
Tun tasowar Ayman mutumne da beson hayaniya ko kaɗan dan koya hayaniya take yanzu kanshi ze fara ciwo shiyasa Mahaifinshi ya turashi Oxford University dake turai yayi karatun shi acan bayan ya gama primary da secondry ɗinshi a Nigeria.
Zuwan Ayman Turai karatu be lalata tarbiyar da iyayenshi suka bashi ba har yagama ya dawo gida,babu wani abu daya sauya daga ɗabiunshi.
Bayan ya dawone ya nuna yanasom shiga aykin soja,fafur Abu Ayman yaƙi amincewa sabida acewarshi in Ayman ya shiga aykin soja aka turashi yaƙi aje tsautsayi yasa akashe shi acan shikenan ya rasa magaji dan haka shi be,amince ba.
Duk yadda Ayman yaso shawo kan mahaifinnashi amman fafur yaƙi amincewa,hakanne yasa Ayman dena cin abinci har na tsawon kwana biyu,ganin,Ayman na ƙoƙarin kashe kanshi da yunwane yasa Sarki Abu Ayman amincewa da buƙatar Ɗan nashi,kuma ya tsaya masa har yasamu matsayi babba a gidan sojan.
Tunda Ayman yafara aykin soja mutumne shi me juriyar wahala dan har mamaki yake ba abokan aykinnashi dan inyana ayki babu me cewa daga gidan sarauta yafito,hakane yasa ya dunga samun promotion har zuwa yanzu dayake riƙe da miƙamin Conel.
Anyi mishi transfer daga wannan jaha zuwa wannan kuma yaje yaƙe yaƙe da dama inda daga ƙarshe de aka ajiyeshi a garin Abuja wanda har yanzu acan yake aykin.
Ayman ba iya aykin soja da mulkin mahaifinshi ya dogara dashiba,Ɗan kasuwa ne inda A halin yanzu har kamfani gare shi guda biyu,da na yin takalma da jaka,dakuma nayin atamfofi,sosai Allah yasa albarka acikin harkokinsa shiyasa yake da tarin dukiyar da koshi kanshi besan yawanta ba.
Ayman a ɓangaran addininshi mutum ne me tsantsar ruƙo da sallah baya wasa da ita sam kome yakeyi aka kira sallah ze ajiye yaje yayi sallah sannan ya dawo.mutum ne shi me tsananin tausayawa na ƙasa dashi yanada tausayi sosai dan ko a hanya yaga wani na buƙatar taimako yana tsayawa ya taimaka masa
Yau Jumma'a yaune Ranar da Ayman ya shirya dan zuwa Ganin gida kano,dayake shi be fiye son tafiya a jirgi ba shiyasa yake da masu tsaron shi har mutum ashirin da biyu motocin dake take masa baya guda huɗune kowacce mota akwai mutane biyar a cikinta se tashi wacce ke ɗauke da mutane uku direba me buɗe masa ƙofa se shi kanshi.
Haka motocin suka jeru akan titi daga Abuja zuwa kano inda suke ta sharara gudu,gab,da zasu shiga garin Kano dede wani titi daze sadaka da garin kofa in ka wuce ƙauyen gwarmai kaɗan kamar ance Ayman ya waiga.
Wata mace ya hango kwance agefen hanyar tana murƙususu wanda ke nuna alamar bata da lafiya,da sauri yabada umarnin a tsaya, ba musu duka motocin sukayi parking a gefen titin,shida kanshi ya fita yaje inda matar ke kwance tana ta kuka,sallama ya mata,amman da ƙyar ta amsa sabida halin da take ciki,umarni yayi da a ɗauketa asata a mota.
Nan da nan akasata a motar da yake ciki,suka ja zuwa cikin garin kano kai tsaye Asibiti aka kaita likitoci suka rufu akanta kamin wani lokaci har ta dawo cikin natsuwarta inda ta buƙaci likitan daya kira mata wanda ya taimaketa dan tayimishi godiya.
Dayake koda suka kaita Asibitin Ayman be tafiba dan haka likitanne yafito yace masa.
"Ranka ya daɗe mara lafiyar da ka kawo tanason magana dakai".
Batare da damuwar komaiba Ayman ya miƙe yabi bayan likitan zuwa ɗakin da matar take.
muje zuwa
Maman yusuf.
[7/7, 08:54] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad@zahrasurbajo*
*ONE WITH GOD IS MAJORITY*
*Page 35-36*
Koda shigarsu ɗakin matar tana zaune tana kallonsu.
Likitan juyawa yayi yafice yayinda Ayman ya matsa kusa da ita yamata ya ƙarfin jiki,cikin faraa ta amsa da cewa.
"Jiki Alhamdulillahi yayi sauƙi,nagode da taimakon dakamin bazan taɓa mantawa dakaiba,kai mutumin kirkine wanda yadace da abun kirki,banida da abin biyanka,sede ka faɗamin abinda kake nema a duniya na tayaka da adduar samun shi"
Murmushi Ayman yayi sannan yace.
"Nagode sosai da wannan yabon da kikamin,kuma ni azahirin gaskiya jin daɗin rayuwar duniya Allah be rageni da komaiba,na farko ya yoni musulmi,yabani kyau,ya bani ilimi,yabani mulki,yabani ƙarfi da lafiya,ya bani dukiya,sannan yasanyamin sonsa da ƙaunarsa a zuciyata,kinga Allah yamini komai,abu ɗaya nake fata tamin kuma yanzu shine ya bani matar aure tagari domin samun zuria tagari,na ƙarshe shine yasa in ajalina yazo yasa na mutu cikin imani,shine kawai burina".
ya ƙarasa zancan yana kalon matar.murmushi tayi Sannan tace.
"Duk mutum nagari dole nagartacciyar mace ze aura,dan haka zantaya ka da addu'a nagode da karamci irin naku na bil adama".
Tana gama faɗa masa haka ta ɓace a gurin.
A razane Ayman ya miƙe yafara waige waige amman ba bu ita ba dalilinta.
Da gudu yafice daga ɗakin sede bekai ga inda yakeson zuwaba ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme.
Da gudu securities ɗinshi suka nufoshi yayinda wasu kuma suka nufi ɗakin,da matar take amman basu gantaba,da sauri suka ɗaukeshi zuwa Asibitin da yake ganin likita.
Emmergency aka kaishi tuni likitoci suka rufu akanshi dan bashi taimakon gaggawa,wanda seda suka kwashe awa uku akanshi kamin su samu numfashinshi ya dedeta.
Sanda labarin ya samu ƴan gidan su hankali a tashe suka iso Asibitin,halin da suka,ganshi seda suka zubar masa da ƙwalla.
Tsananta bincike akayi akan a gano matar daya taimaka,ko ina jamian tsarone akan tituna suna bincikar ababen hawa😝domin kamo matar.
Wasa wasa seda Ayman Yayi wata biyu a kwance ba magana,abun ba ƙaramin ɗaga hankalin duk wani me sonshi yayiba,daga ƙarshe de na gargajiya aka koma yimasa inda Allah yasa aka dace yafara samun sauƙi,kamin sati uku ya,warke sarai ba me cewa yayi jinya,koda aka tambayeshi abinda ya firgitashi be ɓoye musu ba ya sanar dasu komai,ayko kowa seda ya girgiza dajin batun.
Daga ƙarshe de addua suka shiga tayashi akan,Allah ya tsare shi,aduk inda yake.
Tundaga wannan Lokaci Ayman yafara mafarki da wata yarinya ƙarama tana kuka gata a tsakiyar zakuna tana miƙo masa hannu akan ya taimaketa.
Kusan kullum seyayi mafarki da ita,sannu sannu har takai ga ya taimaki yarinyar har soyayya tashiga tsakaninshi da ita,kullum inya kwanta da kalar mafarkinta da zeyi,tun abin be damunshi har yafara ɗaga mishi hankali,Hajiya babba ya sanarwa,addua tace ya dunga yi Allah ya tabbatar da alkhairi.
Sannu a hankali son yarinyar ta mafarki yafara shiga zuciyarshi,har yayi girman da yakejin inde ba ita ya aura ba baze iya rayuwa ba.
Kullum cikin nemanta yake ko ze ganta sonta na wahal da zucuyarsa,kuma duk sanda zeyi bacci se tazo masa a mafarkinsa sunsha hirarsu ta masoya ta tafi,ganin hakane yasa Ayman siyo maganin bacci ya ajiye duk sanda kewarta ta dameshi se yasha ya kwanta bacci dan ya ganta.
Gaba ɗaya yafice daga natsuwarshi burinshi kawai ya ganta,ba abinda ke burgeshi da ita irin blue ice ɗinta,uwa uba shaawarta kullum ƙaruwa take a zuciyarshi,Addua kullum yinta yake dan ganin burinshi ya cika.
Ganin halin dayake cikine Magaifinshi ya yanke shawarar yimasa Aure ko ze samu kwanciyar Hankali,koda ya tuntuɓi Ayman da zancan son yimasa Aure,fafur ya tubure akan shi ba yanzu zeyi Aure ba.
Tun Mahaifinshi na ɗaukar abun wasa harde yaga da gaske yakeyi dan haka ya yanke shawarar ɗaura masa Aure da yarinyar takwaransa sarkin sokkoto,wacce ta gama karatu amman har lokacin Allah be kawo mijin aure ba,
*FIDDAH*kenan ƴa ga sarkin sakkoto.
Muje zuwa
Taku har kullum.
Maman Yusuf.
[7/7, 22:13] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*DA BAZARMU WRITERS*
*ASSOCIATION*
*Page 37-38*
Lokacin da Ayman yaji hukuncin da mahaifinsa ya yanke na haɗashi aure da fiddah har suma yayi,duk da besanta ba amman ya tsaneta.
Kuka ya dunga yi da idanunshi kamar ba soja ba akan mahaifinshi ya fasa auran dolen da yake shirin yi masa,kunnen uwar shegu Sarki Abu Ayman yayi da roƙon da Ayman ɗin yake masa.
Memakon Ayman yaga an fasa se gani yayima anata shirye shirye har kuɗin gaisuwa ankai,ba abinda ke ɗaga masa Hankali irin,alƙawarin da yayiwa Aymana wato hayatin sa na cewa shi mijintane ita