Showing 27001 words to 30000 words out of 42465 words
siyar da duk wani zinari nata dan ta samu ta rufawa kanta asiri da ƙaninta, shima kamin wani lokaci kuɗin sun ƙare.
Yau Ayman yayo waya ga megadin gidan nashi wanda su Ummu ke ciki ya bada umarnin a kulle masa gidan dan aciki ze ajiye fiddah itako ƴarfillo sabo ze gina mata yadda zasu ji daɗin rayuwarsu.
Me gadin abun ya bashi mamaki sabida yadsn akwai ummu aciki,amman be ce komaiba ya amsa umarnin ogan nasa,cikin gidan ya nufa dan ya sanar da ummu saƙon oga.
Ita ko ummu tun cikin dare take fama da ciwon mara,kasancewar watan haihuwarta ya tsaya,amman dayake batasan ya abin yakeba haka tai ta murƙususu ita kaɗai har zuwa lokacin da me gadin yazo.
Lallaɓawa tayi tazo kiran megadin,koda ya sanar da ita saƙon Ayman to kawai tace,dan tasan ze iya yimata abinda yafi hakama tunda ya iya gudunta sanda ta fi buƙatarsa.
cikin gidan ta koma dakyar ta iya haɗa kayansu taja hannu jinior suka fice a gidan tana kuka ga mararta dake ciwo kamar zata fashe,dakyar take iya ɗaga ƙafa.
Sun ɗanyi tafiya me tsawo taji bazata iya ci gaba da tafiyarba,kasancewar gurin akwai yalwar bishiyoyi ,gindin wata bishiya ta ƙarasa dakyar,kuka take jinior na tayats,abun gwanin tausayi,ummu ji take kamar zata mutu.
Unguwar ta manyan masu kuɗi ce dan Anan Gidan shugaban ƙasa ma yake,inda ummu take kwance ƙofar wani gida ne,me ɗan karan kyau kai da ganin gidan kasan meshi yaci ya tada kai.
Haka ummu taita fama ga faya ta fashe amman haihuwa shuru zuwa lokacin har numfashinta yafara sarƙewa.
jin ƙarar buɗe get ɗin gidanne yasa jinior rugawa da gudu gurin,wata arniyar motace ta cinno hancin ta waje,da sauri jinior yasha gaban motar yana kuka.
Da sauri na cikin motar ya fito,saurayine,kyakkyawa na ajin farko wanda kallo ɗaya zaka masa kasan naira najin tsoronsa.
Ƙarasowa yayi gurin jinior yana tambayarsa lafiya.
Shiko jinior yana ganin mutumin ya fito da sauri ya kama hannunshi yafara janshi har seda yakawoshi inda ummu take kwance.
Agigice mutumin ya ƙarasa kusa da ita,taɓata yayi amman ina ko numfashi batayi a gigice ya ɗauketa ya nufi motarshi da ita yayinda jinior ke biye dashi abaya.
Gudu yake na fitar hankali har ya iso Asibiti.
Daga saman Asibitin an rubuta,
*Doctor Na'im Chiroma,Special Hospital.*
yana parking da sauri ya ɗauketa yayi cikin Asibitin da ita,duk wani maaikaci na Asibitin seda ya kamu da tsananin mamaki na ganin doctor ɗinsu ɗan ƙwalisa ɗauke da me tsohon ciki kuma yana kwasar gudu mutumin dako sauri be iyaba.
Kai tsaye labour room ya shiga da ita,duk wani abu daya dace shi ya mata har ya samu numfashinta ya dawo,ruwan naƙuda ya ɗaura mata.
kamin wasu mintoci ummu tafara kukan neman taimako,hannun shi ta riƙe da ƙarfi tana salati,gaba ɗaya tausayinta yagama cika shi,injin scarning ya matso dashi kusa da ita inda yafara yimata scanning ɗin dan ganin yanayin kwanciyar yaron.
Ilai kuwa yaron a karkace yake,dan haka hannu yasa ya gyara mata,ummu ji tayi kamar zata mutu,sanda yake gyara kwanciyar yaron.
Ba jimawa Allah ya sauketa lafiya,inda ta haifi ɗa namiji tamkar Ayman ne yayi kakin yaron.babu,wata halitta ajikin yaron wacce ba irin ta Ayman bace.
muje zuwa.
surbajon kuce.
[7/23, 18:58] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Hameedan Hamman ɗinta,Ummu faix,Bilshop(Hizba one😜)wannan shafin nakune nagode da irin kulawarku gareni,adduoinku sunamin daɗi,Allah yabarmu tare cikin aminci*
*page 73-74*
Murna sosai Doctor yayi da nasarar daya samu,ta ceton ran ummu da abinda ke cikinta.
Shiko jinjirin se tsala kuka yakeyi alamar dake nuna yana cikin ƙoshin lafiya.
Ummu tayiwa Allah godiya daya turo me taimakonta,ta kuma gode masa daya rabata da cikin lafiya.
Dayake Asibitin private ne komai akwai a ciki dan haka kayan jarirai doctor ya bada umarnin a kawo,ayko ba jimawa nurse har ta gama shirya babyn ta kawowa doctor shi.
Gurin ummu ya kaishi wacce fitowarta daga wanka kenan.
"madam hala haihuwar fari ne wannan naga tunda yazo duniya baki buƙaci a kawo miki shi ba,kinajin kunyar shi ne?"doctor Na'im ya wurga mata tambayar yana dariya.
Ɗago ido ummu tayi ta kalleshi,ji tayi gabanta ya faɗi da sauri taƴi ƙasa da idonta tana murmushi.
miƙa mata yaron yayi,hannunta na rawa ta amsheshi,tana amsar yaron ya buɗe ido yana kallonta,yana turo harshenshi waje.wani matsanancin kukane ya kufcemata,rungume yaron tayi cikin kuka take faɗin.
"Na gode maka Allah daka bani shi,babu bsƙin ciki a zuciyata na game da samun shi,Allah ka gafartamin laifin dana aykata na samar dashi,ya Allah albarkacin naƙudar haihuwar sa danayi,da rainon cikinsa da nayi,ya Allah ka dubeni ka gafartamin na tuba ya Allah natuba"ta ƙarasa zancan cikin matsanancin kuka.
Gaba ɗaya kan doctor ya gama ɗaurewa gameda furucin na ummu,yana buƙatar ƙarin haske game da hakan amman ya barwa cikin shi.
Miƙewa yayi ya fice yaje ya shigo da jinior,da gudu jinior yaje ya rungumeta yana kallon babyn yace.
"lah Aunty kin siyo mana baby ne?".
kai ummu ta ɗaga masa wasu hawayan na ƙara biyo fuskarta.
Ɗakin hutu aka kaisu,se a lokacin ummu ta ciro nono taba babyn ay kamar jira carab ya cafke yafara sha,tanajin zafin tsotson da yakeyi amman ta daure sabida tasan in ta shayar da yaron ma Allah ze ƙara yafe mata.
Da daddare doctor ya shigo ɗakin,lokacin jinior har yayi bacci ummu da babyn ta ne kawai idonsu biyu,tana riƙe da hannun babyn tana kallonshi shima ita yake kallo abin gwanin sha'awa.har doctor ya samu guri ya zauna ummu batasan ya shigo ba hankalinta nakan babynta wanda da gani zeyi wayo sosai.ba abinda yake ƙara faranta ran ummu se kama da yaron yakeyi da Ayman,wanda tasan ko giyar wake yasha be isa yace ba nashi bane.ɗauke babyn da akayi shi ya dawo da ummu cikin hayyacinta a gigice takai raruma zata kwace ɗanta,ganin doctor tsaye akanta riƙe da babyn shi ya haddasa mata jin kunya.
"wannan kalar soyayyar da kike nuna masa ita zata sa ya ganeki da wuri mu kuma uncles ɗinsa ya dunga yimana ƙiwya".
Ummu de murmushi kawai takeyi,ta kasa magana,har seda doctor ya sake jefo mata tambayar data hargitsa kayan cikinta.
"Madam zuwa yanzu ya kamata ki sanar dani inda ƴan uwanki suke domin aje a sanar dasu halin da kike ciki musamman baban yaron nasan yana can cikin damuwa".
kuka ta rushe dashi me tsuma zuciya,cikin kukan take faɗin.
"Dama duk abinda ka tambaya ina dasu dana shaida maka inda suke,wannaɓ ɗan da kake gani babanshi be damu ɗashi ba,hasalima ya gujemu tun cikinshi na wata biyu bamusan inda yake ba,ƴan uwa kuma bani dasu ksga kenan babu wani wanda hankalinshi ke tashe da rashin ganin mu,da ace mahaifiyata na kusa dani shine zan iya faɗa mata komai game da ɗana,dabida uwace kawai zata iya share kukan ƴarta"ta karasa faɗi cikin kuka.
Tausayinta ne ya mamaye zuciyar doctor,cikin sanyin murya yace.
"na gamsu da bayananki,amman ina roƙon,alfarmarki da ki bari in kawo mahaifiyata gareki domin ta share kukanki,mahaifiyata mace ce me tsoron Allah,dason ɗan da ba nata ba fiye da kanta,namiki alƙawari inde ta muamalanceki zaki iya mantawa ma da taki mahaifiyar"ya ƙarasa zancan yana dubanta cikin tausayawa.
"ko baka yabi mahaifiyarkaba nasan mutuniyar kirkice ta lura da irin kirkin ɗanta,na amince ka turota gareni,amman batun mantawa da tawa mahaifiyar abune me wuya"ta sake fashewa da kuka.
"to nagode da damar da kika bani,yanzu zan wuce zan tafi da wannan ƙaramin dan,asamu ayimasa wanka,amman se kin amince".
"Doctor kenan!ay tunda ka iya ɗaukomu batare danasan inda kaina yakeba kataimakemu baka cutar damuba to banajin zaka iya cutar damu sanda na dawo cikin hayyacina,dan haka kaje dashi ɗin".
Murmushi yayi sannan yace, "to nagode da yarda dani".
Miƙamata babyn yayi sannan ya ɗauki jinior yafice daga ɗakin.
Kai tsaye gida ya nufa,yana parking ya ɗauki jinior ya shige dashi cikin gidan a falo ya sami mahaifiyar tashi se safa da marwa takeyi.
yana sallama ta nufeshi a gigice tana faɗin.
"Haba ɗan umma yanzu dan Allah abinda kayi ka kyauta kenan taya zaka tashi ka kashe wayoyinka kuma kaje kayi zamanka a waje har ƙarfe goma na dare"ta faɗi cikin damuwa.
Se a lokacin ta lura da jinior dake rungume a kafaɗarshi,da sauri ta miƙa hannu ta karɓeshi,tana tambayarsa ina ya samo ɗa.
Shiko jinior matar na karɓar shi a hannu doctor ya buɗe idonshi a firgice,ƙureta yayi da ido,itama kallonshi take cike da mamakin irin kallon da yaron yake mata,zuwa can kuma se jinior ya saki ajiyar zuciya yakwantar da kanshi a ƙirjinta gamida riƙe mata riga alamar dake nuna yana gudun a kwace mishi ita.
Murmushi doctor yayi sannan ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar da ita,Allah sarki baiwar Allah harda kukanta,sallama doctor ya mata ya wuce ɗakinshi ita kuma ta haura sama ɗauke da jinior.
Ko cikin dare al amarin jinior ci gaba yayi da ɗaure mata kai,dan gama miƙa hannu yake cikin rigarta,kamar yadda yara suke in suna buƙatar nono,gefe ɗaya kuma hannun shi ɗayan na riƙe da rigarta,tausayin shi ne ya kamata gamida sonshi,tabbas ta fahimci yans cikin kewar mahaifiyarshi ne shiyasa yake mata hakan,rungumeshi tayi sukayi bacci.
washe gari da wuri suka tashi sabida zasuje asibiti gurin ummu.
gurin me gadi doctor yaje yasashi ya ɗauko jakar kayan su ummu,wacce suka bari tun jiya a ƙofar gidan.
Hajiyar shi ya kaiwa ta buɗe ta cirowa jinior kayan daze saka sannan ta ciro na me jego tamayar ta rufe,da kanta tayiwa jinior wanka dan so ds tausayin yaron tun daran jiya suka gama cika zuciyarta,shirya shi tayi tsaf ts bashi abinci yaci,sannnan doctor yazo ya ɗauki kayan abincin da ta shiryawa me jego na abinci,suka fice zuwa Asibitin.
Koda suka iso Asibitin maaikatan Asibitin se duƙawa suke suna kwasar gaisuwa gurin mahaifiyar doctor ahaka suka nufi ɗakin da ummu take.
Ummu wacce ke tsaka da baccinta ita da babynta a gigice ta farka,kamar wacce aka tsoratar,gabantane ya shiga faɗuwa da ƙarfi,miƙewa tayi tsaye,hakan yayi daidai da shigowar su doctor.
Kallon kallo suka shiga yi tsakanin ummu da mahaifiyar doctor,kallo irin nason gano a inda suka san juna,a lokaci guda suka tuno.
ƙara ummu Aymana ta ƙwalla tana faɗin,
*UMMA NA !!!!!*.
bata ƙarasa faɗi ba duka suka yanke jiki suka faɗi sumammu.
muje zuwa.
Surbajon kuce.
[7/24, 09:49] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*banida lfy pls pray for me*
*duk meson book ɗina ko wanne irine ya nema a group,ko yaje page ɗina na whattpad ze samu acan amman kar abini pc ace inturo,nadena turawa dan wlh ina rasa inda zansa kainane,na rasa wa zan kula,so pls wanda suka nema ban tura musu ba kuyi haƙuri ku kuma masu shi don Allah in,an nema ku dunga bayarwa pls*
*page 75-76*
A gigice doctor ya nufi mahaifiyarshi yana kiran sunan ta amman ina ko motsi batayi, a sukwane ya fice a ɗakin zuwacan se gashi ya dawo da kayan ayki da nurse na biye dashi da gudu.
Kai da ganin yadda doctor ya ruɗe ya gigice kasan akwai soyayya me ƙarfi tsakaninshi da mahaifiyar tashi.
Ceton ransu suka shigayi gaba ɗaya,wanda ba jimawa dukansu suka farka.
Ummu kuka umma kuka,rungume suke da juna dukansu,ba abinda sukeyi se kuka ganin hakane yasa doctor ya tattara su gaba ɗaya suka wuce gida,Dan karsu tara masa mutane.
Koda suka isa gidan basu bar kukanba ,gaba ɗaya sun saka doctor cikin damuwa da ƙyar ya samu sukayi shuru sannan umma ta fara magana.
"Haƙiƙa na yarda Allah maji roƙon bawane tunda Allah ya bani lafiya nake nemanki ƴata,Allah be haɗamu ba se yanzu nagode masa daya sadani dake,sede na shiga damuwa ganinki ɗauke da yara har guda biyu wanda ban sanki dasuba ko kinyi Aurene?".
Kuka ummu ta fashe dashi ta rungume mahaifiyarta,ta kamo hannun jinior tasa ana umman tace.
"Umma wannan ɗanki ne na cikin ki,ke kika haifeshi,ranar da kika haifeshi kika ɓace ban sake ganinki ba se yau,shi kuma wannan jinjirin....."se ta rushe da kuka ta kasa ƙarasa maganar.
da kyar tasamu kukan ya barta tace.
"shi kuma wannan jinjirin umma ɗana ne wanda na sameshi bata hanyar aure ba"ta sake rushewa da kuka.
Ba umman ba doctor kanshi seda ya faɗo daga kan kujera.
.Kuka umman tasa me tsuma zuciya tace.
"Nasan haka zata iya faruwa dake ƴata,nasani,wlh banyi baƙin ciki ba ,da ace kashe shi kikayi ko kika zubar da cikin ko kika yardar dashi wlh zuciyata se ta buga da baƙin ciki,ƙaddarace wacce tana iya samun kowa,Allah ya gafarta miki zunubin da kik aykata shi kuma in rayayyene Allah ya albarkaci rayuwarsa".
Daga ummu ta kwashe labarin komai ta faɗawa ummanta,Cikin kuka umma ta rungume jinior tana faɗin.
"Allah sarki ɗa na tun jiya kake nunamin alamar ni mahaifiyarkace amman ban fahimta ba sabida nasan ban haifa ba se yanzu nagane hakan se yanzu naga kamannin mahaifinka a tattare dakai,Allah na gode maka daka kuɓutar da zuriata daga sharrin masharranta,na gode daka bani ƴa maabociyar imani nagode ya Allah".
Haka sukai ta kuka dakyar umma tafara bada nata labarin bayan ta baro ƙauyan su.
*waiwaye*
Tunda na baro ƙauyan bansan inda nake nufa ba,bansan me nakeyi ba.
haka na dunga rayuwa cikin daji da bakin titi,har Allah ya kaini garin kano,na jima a garin kano sosai ina yawon haukata.
Kwatsam rana ɗaya nazo tsallaka titi motar ciroman kano kuma gomnan bankin nigeria ta bugeni.
Basu wuceba seda suka kaini asibiti,anan aka dunga bani kulawa,ƙarƙashin jagorancin ciroman,seda nayi shekara guda a Asibitin mahaukata na dawanau amman kullum ba sauƙi se na Allah.
Ba inda ciroma be kaini neman maganiba amman ban warke ba,seda wata aljana tazo ajikina ta shaidawa ciroma asiri akamin sannan ta faɗi inda aka birne asirin,acikin gidan,mu na ƙauye,kuma tabashi shawara akan ya ayka da mota aje garin a zuwan anzo siyan takin kashin shanu na gidan,wanda inde aka tashi ɗiba zaa ɗebo harda asirin.
Ayko haka akayi ciroma ya ayka dayake idonsu rufe yake da son kuɗi shaf sun mance da mugun ƙullin da sukayi,haka aka haƙo harda asirin da suka burne,koda aka kawo kashin shanun ciroma da kanshi yadunga tonawa har yagano asirin ya ɗauka yaje ya ƙona.
faruwar haka shine sanadin samun lafiyata,ciroma yaci gaba da bani kulawa.
Ana tsaka da hakane Allah yayiwa matar ciroma rasuwa wato mahaifiyae na'im,tun bayan rasuwarta,se ciroma ya nemi na amince da ya aureni sabida ya samu me kulawa da ɗansa ƙwaya ɗaya da ya mallaka wato naim,sabida mutuwar mahaifiyarshi har so tayi ta taɓa kwakwalwarsa.
To na amince mukayi aure da ciroma,tunda mukayi aure ciroma yaso aje akamo su jameelu,ni na hanashi sabida ina tunanin kina hannunsu kar su illatamin ke.
Yanzu haka na haihu da ciroma inda na haifi ƴanbiyu,duka maza,amman yanzu suna kano,gidan sarkin kanon kasancewar sarkin shida ciroma uwa ɗaya uba ɗaya suke,to shine yanemi alfarmar in an tashi yayesu akaisu gidanshi to yanzu sunacan.
murna sosai ummu ta taya mahaifiyar tata gameda ci gaban da tasamu.
Ranar wuni sukayi cikin farinciki inda umma tayiwa ummu wankan jego na asali kuma ta wanke jikanta wanda Naim yayiwa huɗuba da sunan sarkin kano kasancewar sarkin yana nuna masa ƙauna sosai amatsayinsa na wan mahaifinsa.suna kiran yaron da Abu Ayman🤔.
Ummu batasan Ayman ɗan sarkin kano bane dan tunda suke be taɓa bata labarinshiba.shiyasa bata kawo komaiba a ranta.
Shiko doctor,kamannin da Abu Ayman yake masa da na ɗan uwansa Ayman yafi komi bashi mamaki,amman ya danganta hakan da ikon Allah ne.
muje zuwa.
surbajon kuce.
[7/25, 08:41] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Da badan zan roƙi addua daga bakunanku ba da ba abinda zesa nayi typing,pls kusani a addua wlh banida lafiya amman ko wuƙa aka nunamin bazan iya faɗin abinda kemin ciwoba,kawai ni de naji banda lfy,ku taimakamin da addua don Allah*.
*page 77-78*
Rayuwa tayiwa ummu daɗi sam ta mance da damuwarta,Ayman ne kawai in ta tuno take shiga damuwa.
Shiko doctor son da yake nunawa Abu Ayman koshi ya haifeshi iya abinda zemasa kenan,kullum ya fita se yadawo masa da abin wasa,ko sutura,bashi da ayki inyadawo daga Asibiti se na rainonsa.
Yau ciroma ze dawo daga tafiyar dayayi,ya jima baya ƙasar,dan besan ma anga ummu ba.
Gidan gaba ɗaya ya kaure da gyare gyare da dafe dafe,kowa beda sukuni,sabida ciroma mutum ne da bayason ƙazanta,kuma ba laifi mutum ne shi me zafi,shiyasa kowa ya,shiga taitayinsa kamin ya iso.
Da Azahar ya iso gidan,Umma se murna take da ganin mijinnata,haka shima dan ya gaza bari su keɓe tunda tazo taryarsa ya rungumeta,abun kunya yaba ummu Aymana.
Bayan yayi wanka ya kintsa ya sauko ƙasa domin yaci abinci,anan yaci karo da Naim goye da Abu Ayman yana jijjigashi azuwan dole se yayi bacci,shiko abu Ayman inbanda ware ido ba abinda yakeyi alamar dake nuna bashi da niyyar baccin.
Dariya ciroma yayi sannan yace.
"ikon Allah naim ina kuma ka samo yaro ɗan turawa haka harda goyashi?"ya ƙarasa tambayar cikin dariya.
Saukeshi yayi abayan yana dariya shima yace.
"daddy jikankane yake wahal dani wlh".
"jikana kuma?to kawoshi inganshi inga jikan nawa".
Kaimishi shi yayi ya karɓeshi,yana duban fuskar yaron,ya waigo da ssuri yana tambayar naim.
"Ah ah wai matar Ayman harta haihune,basu faɗaminba,?yaushe sukazo nigeriar ba suna germany ba?".
Dariya naim yayi sannan yace.
"Daddy kenan ay wannan kamace kawai da ikon Allah amman wannan ba ɗan Ayman bane,hasalima jikan mommy ne na gurin ummu Aymana da ta ɓace".
Fuska ɗauke da faraa yace.
"Amman kai da mommyn taka baku,da kirki yanzu har wannan abun farincikin ze faru amman baku faɗaminba?,ina ƴar tawa take? tazo na ganta mana".
Da sauri naim yaje ya kira ummu tana zuwa ta durƙusa tana gaisheshi.
Fuska cike da faraa yake amsawa,sannan ya mata barkar haihuwar da tayi sannan ya tambayeta a inda tayi aure da kuma wanda take auran.
da gudu ummu ta miƙe tabar gurin tana kuka,jiki a sanyaye ciroma yakai dubansa fuskar umma itama kuKan takeyi.
miƙawa naim Abu Ayman yayi,naim na amsarsa yabar gurin.
Shi kuma ciroma yafara tambayar umma meye matsalar.
Bata ɓoye masa komaiba ta sanar dashi,duk abinda ya faru.
.Runtse ido ciroma yayi yana huci kaida ganin yanayinsa yakai ƙololuwa gurin ɓacin rai.
"yanzu wanne mara imaninne ya aykatawa ƴata haka,waye shi?!!!!!"ya faɗi sanda ya buga tebur ɗin dake gabanshi da ƙarfi,idonshi yayi ja gashin jikinshi duk ya miƙe.
Da kyar umma ta shawo kanshi ya zauna,yana huci.
"Ranka ya daɗe wlh wannan tambayar munyiwa ummu ita tun kamin kazo amman taƙi bamu amsa sede tace tayi aƙawarin rufa masa asiri dan haka bazata karya alƙawarinba,wai se randa shi da kanshi ya buƙaci ta furta".
"wannan ay zancan banzane,taya