Showing 30001 words to 33000 words out of 42465 words

Chapter 11 - Ummu aymana complete by ksm-1.txt

zata rufawa wanda yatona mata asiri asiri,shiɗin ɗan uban waye daze mata wannan keta haddin?kiramin ita yanzu"ya faɗi cikin ƙaraji.


Da sauri umma taje ta kira ummu.


"ki faɗamin sunan shegen daya miki wannan taasar da inda yake da kuma aykin da yakeyi".


cikim kuka ummu tace.


"Da badan nasan makomar me karya alƙawariba ranar gobe ƙiyama wlh da ba abinda ze hana ban tona masa asiriba,kodan baƙincikin daya sama zuciyata na guduwa da yayi ya barni,kayi haƙuri daddy,wutar me karya alƙawari daban take a lahira,ni me laifice gurin Allah bangama wanke wannan ba bazan ƙarawa kaina waniba,bazan iya faɗa makaba"ta sake rushewa da kuka.


"tashi kije"daddy ya umarceta.


Jiki a sanyaye ummu tabar gurin.


Shiko daddy ranar wuni yayi cikin takaici da baƙin ciki,ji yake daze ga mutumin da se ya harbeshi har lahira.


Washegari da rana,tawagar sarkin kano ta sauka a gidan ciroma.


yazo yima ɗan uwannasa sannu da zuwa.


Gaba ɗaya gida ya kaure da murna,haka suka keɓe shida ciroma wanda yake ɗauke da Abu Ayman a hannunsa suna hira.


"wannan ɗan waye kuma ka jajibo,kiyashi uban jayejaye?"sarki ya tambayi ciroma yana dariya.


murmushi ciroma yayi sannan ya kwashe labarin komai ya sanar da sarkin.


yadda ran sarki ya ɓaci ko na ciroma be ɓaci haka ba,faɗi yake.


"duk ranar da aka gano wannan azzalumin dole se ya ɗanɗana kuɗarsa,wlh bazamu yarda ya cutar mana da ƴa abanza ba".


Da kyar ciroma ya rarrashi sarki yayi shuru,miƙa masa Abu Ayman ɗin yayi.ya amshe shi.


A gigice ya miƙe tsaye yana kallon yaro yace.


"ciroma kaga abinda nake gani kuwa kode ido nane,?Ayman ɗana fa nake gani yana jinjiri".


Dariya ciroma yayi sannan yace.


"kamace kawai da kuma ikon Allah amman in banda abunka taya ayman ze haɗu da ummu mutumin da baya ma ƙasar".


Shide sarki yasan ana kama amman be taɓa ji ko a labari ana kama irin haka ba inde ba ɗan mutum ba.


gaba ɗaya jikinshi yayi sanyi,zuciyarshi tagaza amincewa da kamace kawai,ba abinda ya ɗagawa sarki hankali irin wani tabo daya gani a tafin hannun Abu Ayman wanda shida Ayman suma duk suna dashi kuma iri ɗaya.


"Banyarda kamace kawai ba"itace kalmar da sarki ke maimaitawa a zuciyarshi.


muje zuwa.


Surbajon kuce,pls kusani a addua.
[7/30, 17:44] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀


Zahra Muhammad Mahmud




DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION




*Liman yazo Sallah tazo,muje zuwa masoyana Allah ya sa muga Annabi,(S,A,W)*




*Page 79-80*




Wuni Sarki yayi rungume da Abu Ayman yana jin wani yanayi tattare da yaron,yanaji ajikin shi koda ga ina yake jinin sa ne.


Ba ƙaramin firgita sarki yayi ba sanda yaji an ambaci sunan mahaifiyar yaron da suna ummu,sabida inde ba mantawa yayi ba,Ayman ya taɓa furta sunan a gabanshi sanda yake roƙonsa ya amince ya auri ummu.


Gumi ne ya shiga karyo masa,da kyar yasa akayi masa kiran ummun,sannan bayan tazo ya buƙaci kowa yabasu guri zeyi magana da ita,ba musu kowa yabar gurin harda ciroma.


Jiki a sanyaye ummu tashigo falon,yayinda gefe ɗaya kuma take mamakin abinda yasa sarkin yace tazo.


Kanta a ƙasa ta gaisheshi,ya amsa sannan yace.


"Ɗago kanki ki kalleni ƴata".


A kunyace ummu ta ɗaga kai tana kallon shi.


A razane ta miƙe tsaye tana binshi da kallon tsana,gami da nuna shi da ɗan yatsa tace.


"dama kaine ka badda kama ka shigo gidannan?mayaudari azzalumi,mugu,Wallahi Ayman bazan yafe maka ba ka cutar dani ka cutar da ɗanka,ka gudu kabarni se yanzu kadawo......."hawayen dake zuba a idon sarkine yasa ummu lura da kyau,ashe ba Ayman bane,kawai tsabar kamace dan se yanzu ta lura wannan ɗin ya girmi Ayman.


Da sauri tasa hannu ta toshe bakinta jikinta na rawa,musamman ganin hawaye a fuskar sarkin yafi komai ɗaga mata hankali,tsugunawa tayi a gabanshi tana kuka ta kama ƙafarshi ta soma da cewa.


"Don Allah kayi haƙuri ɓacin ran dana shigane da ƙunci yasa na ɗauka kaine Ayman,tabbas Ayman ya cutar dani kuma ya yaudareni,amman hakan bazesa na karya alƙawarin da nayi masa ba,Ayman ya shaidamin mahaifinshi babban mutum ne a ƙasarnan,haka zalika shima babban mutum ne,dan haka na rufe sirrinshi,dan kar duniya tayi tur,dashi da mahaifinshi,na mishi alƙawarin zan rufe sirrin har se lokacin daya buƙaci in buɗe,se gashi yau cikin rashin sani na karya alƙawari,don Allah ina roƙonka,ka rufawa Ayman da mahaifinshi asiri,banaso duniya ta zagesu musammam ma mahaifinnasa wanda beji ba be gani ba,don Allah kar ka tona wannan sirrin nawa na roƙeka".


Ta ɗago ido tana kallonshi cikin kuka,wanda shima zuwa lokacin gemunshi yagama jiƙewa da hawayen.


Muryar shi na rawa,yace.


"ba wanda zan faɗawa,amman se kin bani labarin komai game da haɗuwarki da Ayman ɗin,kar kimin ƙarya,dan idan kikayimin zangane".


Ba musu ummu ta kwashe komai ta sanar da sarki tundaga kan mafarkin da sukeyi ds juna har zuwa taimako daya dunga yimusu,bata ɓoye masa komaiba,ta ƙarasa bashi labarin tana kuka.


Zuwa lokacin sarki ya gaza yin kukan illah na zuci da yakeyi share hawayenshi yayi ya daidaita natsuwarshi,sannan yace.


"Gaskiya Ayman be kyauta miki ba,na tausaya miki,shiyasa nayi shaawar haɗaki aure da ɗana,guda ɗaya dana mallaka,nayi imani ze soki ze kula dake da ɗan dakika haifa batare dayayi laakari da hanyar da aka bi gurin samar dashiba".


"Nagode babah da wannan karramawa,sede wlh duk da abinda Ayman yayimin har yanzu zuciyata taƙi tayi fushi dashi ma bare ta tsaneshi,na koya mata hakan amman taƙi koya ,koda na amince na auri ɗanka,zan aureshi ne badan ina so ba sedan rufe,asirin kaina dana ɗana,Ayman kawai nakeso,kuma shi kaɗai zanso har abada"ta ɗurƙushe a gurin tana kuka.


jikin sarki rawa ya farayi sabida yayi imani shine silar faruwar komai,shine ya tarwatsawa wainnan masoya tarihin soyayyar su,shine silar wanzuwar yaron dake hannun sa wato Abu Ayman,inbe haɗasu Aureba ina zekai wannan Alhakin daya ɗauka,yayi danasani mara iyaka,da kalaman daya furtawa Ayman,wanda yasan da badan suba ko aɓoyene Ayman zeje ya Auri ummu batare da saninsa ba,amman kaucewa kalaman ya janyo jikansa yazo bata hanyar Aureba.


Share wasu zafafan hawaye yayi,sannan yace.


"ba komai ƴata nagode da amincewar da kikayi nasan a sannu zaki mance da wancan Ayman ɗin ki saba da Ayman ɗana".


Da sauri ta ɗago tana kallonshi jin yace sunan ɗanshi Ayman.


Murmushi yayi dan ya fahimci mamaki takeyi.


"tabbas sunan ɗana Ayman,wanda yanzu haka baya ƙasar ze dawo nan da ƴan watanni,da tuni ma yadawo to an ƙara masa lokaci ne shiyasa be dawoba,ina fatan kinyi farinciki da zaɓin nawa?".


kai ummu ta ɗaga tana murmushi,cike da jin kunya.


Janta da hira yaytayi abun har mamaki ya dunga bata,sabida ta ɗauka sarakuna ko magana ma wuya take musu.


sun jima suna hira yayinda sarki cikin hikina ya dunga recording video na ummu da ɗanta,a wayarshi batare da ta gane ba daga bisani ya sallameta ta shige cikin gida.




Koda sarki ya tuntuɓi ciroma game dason Aurawa Ayman ummu,sosai ciroma yay murna gamida fatan alkhairi,itama umma murna tayi,shiko naim ji yayi kamar duniya aka ɗora masa akai sabida nauyin da zuciyarshi da kanshi suka masa.


Tunda ya fara ganin ummu ya kamu da sonta ya za'a yi masa shigar sauri?,shi Ayman ko labarinta be taɓa jiba bare ya ganta kuma yana da matar shi amman kuma za'ace za'a ƙara masa da ummu?,gaskiya ba'a masa adalci ba.




*WAI INA AYMAN NE?*




Surbajon kuce.
[8/1, 09:03] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀




Zahra Muhammad Mahmud




DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION




*Saƙone zuwa gareku members na duka groups ɗina,nace novels kawai nakeso a group ɗina baya gashi banason komai,duk wanda ya turo abu saɓanin novels komai ƙanƙantarsa zan cireshi,batare dana kalli kusancina dashiba,kuma inna cireki karki biyoni pc,neman baasi,kina ganinki a waje kije ki bincika kin karya doka ne,ko wannan abun da ake cewa duk meson book kaza yasa sunansa a ƙasa to banda groups ɗina,dan inkinturo zan turaki waje,naga kunfarayin na ummu aymana ma,to shima ku dena karku tura groups ɗina kar ku tura na wani,ni na yarda da soyayyarku gareni base kunsa sunanku ba,dan inaga tunda kuka shigo group ɗina ay no need kucemin ku masoyanane,tunda kuke aciki nasan soyayyarce ta kawoku,ba komai yasa nasa wannan dokar ba se danmu masu siyan datar naira ɗari ɗari da hamsin,in ana ture turennan saurin ƙarewa takeyi,dan haka akiyaye nagode*


*page 81-82*




Ayman anashi ɓangaran.




Yanzu ƴarfillo ta baro inda take ta dawo gurin shi a garmany,tare suke kwana a hotel ɗin dayake,ya mance da ummu da duk wani abu daya shafeta,fiddah ko haushinta yakeji wanda ya rasa dalilin dayasa yakejin haushinnata,sede duk ƙarshen wata yana ayka mata da kuɗi,ta hannun drivern sa dan tayi amfani dasu.


Son da yakewa ƴarfillo yanaji duk wanda yanemi taɓa masa ita ze iya kawar dashi a doron duniya,sone na hauka wanda da gani ba tambaya kasan na Asirine.


Ƴarfillo ansamu duniya,an kuma samu abinda akeso wato zuciyar Ayman,dan yanzu har kuka yake mata akan tabarshi ya kusanceta,sosai yake kusantarta ba dare ba rana,tade zama tamkar matarshi,ga wani matsi da tayi amfani dashi na hanashi jin daɗin kowacce mace a duniya inde ba itaba,shiyasa in yana kusantarta,har ihu yakeyi dan daɗi,duk da wannan sheƙe ayar bata taɓa tunanin yanada aureba.


Fiddah baiwar Allah tayi kuka tayi kuka har ta dena yi,gaba ɗaya tayi baƙi ta lalace ta fita hayyacinta,ko abincin kirki bata iya ci,sabida baƙin cikin Ayman,ta rasa inda zata sa kanta,ta nemi number salmab amman bata samuba kullum cikin try take,yau ko taci saa ta sameta.


bugu ɗaya salmab ta ɗauka,tana mata tsiya.


"Amarsu kenan an manta damu kode ɗan babane ya ɓoyeki?"


Kuka fiddah ta rushe dashi,tana faɗin.


"na shiga uku salmab,na lalace,ina cikin ƙuncin rayuwa,inkika ganni zeyi wuya ki ganeni,Ayman ya azabtar dani,fiye da tunaninki,tunda muka iso ƙasarnan ban sake ganinshi ba ya ajiyeni yayi tafiyarsa"ta ƙarasa zancan cikin kuka.


"ke kika bashi dama fiddah rashin wayonki ya fara damuna, sekace ba mace ba,da duk matsala ba kya iya warwarewa kanki ita sede ni,inna mutu kuma,waye ze dunga yimiki,?,to wlh tun wuri in zakiyi hankali kiyi,kicire tsoronsa aranki,ki ɗaura ɗamarar ƙwatarwa kanki ƴenci da kanki sabida kema macece".


"To yanzu salmab ya zanyi,nace miki ko ganinsa banayi,taya zan kwaci ƴencina,sede fa duk ƙarshen wata ya turo driver ya kawomin kuɗi,taya kike tsammanin zan ganshi?"


"kaji sakarya,au dama har akwai ɗan ayke a tsakaninku amman kike cewa bakisan inda yake ba?to duk ranar da driver ɗin yazo kibishi yakaiki wajenshi,kuma duk balai karki kuskura ki baro gurin,kicire tsoro aranki na faɗa miki".


Daga haka sallama sukayi kowa ya ajiye wayar.


Shuru fiddah tayi tana tunanin baiwa da basirar da Allah yayiwa salmab,ita kods wasa bata taɓa tunanin bin driver ɗinba se yanzu da Salmab tasa ta a hanya.


Ayko acikin satin driver yazo kawowa fiddah saƙo da sassafe,dan haka batayi wata wata ba tace yakaita gurin ogan nashi,ba musu ya ɗauketa suka tafi.


Sanda suka isa hotel ɗin lokacin Ayman yana tsaka da saduwa da abar ƙaunarsa,se gurnani yakeyi,dayake hotel ɗin,ɗakunan jerasu akayi rukuni rukuni,dan haka base kabi ta reception zaka isa ɗakunan ba.


Har ƙofae ɗakin driver ya raka fiddah sannan ya juya ya tafi,nucking ta shiga yi amman shuru ba a zo an buɗeba.


Kasa kunne tayi dan taji kamar kuka daga cikin ɗakin,ilai kuwa gurnanin Ayman tajiyo,ɗauka tayi bashida lfy ne dan haka ta shiga dukan ƙofar,suko basu sanma tanayiba,murɗa hannun ƙofar tayi ga mamakinta se tagama ashe a buɗe take dan haka ta tura tashiga da gudu ɗakin,ba kowa a falon dan haka ɗakin da gurnanin yake fitowa ta nufa.


taku har kullum surbajo.
[8/1, 10:31] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀




Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*




*ƘUNGIYAR MU TAIMAKI KANMU MATA!!! WANNAN SHAFIN NAKUNE,ALLAH YA CI GABA DA DAFA MANA AKAN MANUFARMU TA ALKHAIRI,DUK WANDA CUTACE A ZUCIYARSHI YA ALLAH KADA KA KAWOSHI CIKINMU DOMIN TSARE DUKIYARMU DAGA FAƊAWA HANNUN DA BE DACEBA,AMEEN*




*Page 83-84*




Tana zuwa shiga tayi ɗakin.


Abinda ta ganine yasa ta fara ganin jiri na ɗibarta,Ayman kwance da wata mace wacce ba tashiba acikin yanayin dako ita da take matarshi basu taɓa kasancewa a hakanba




Basusan ta shigo ba Ayman andage se rabawa ƴarfillo duty yake,yana zuba santi.


Hawaye ne ke bin fuskar Fiddah na baƙin ciki,rasa me zata musu tayi kamar ance waiga ay kawai se ta hango,wata sanda kakkaura a ajiye a gefen gadon irin ta sojojin nan,batayi wata wata ba ta ɗauki sandar ta bugawa Ayman A tsakiyar kanshi,wata ƙara yasaki ya gamida ɗaga ƴarfillo ya faɗi ƙasa sharab jini na fita akanshi.


A gigice ƴarfillo ta miƙe sede kamin tayi wani yunƙuri tuni fiddah ta runtuma mata sandar,dukanta fiddah tashigayi d sadar iya ƙarfinta Ihu ƴarfillo takeyi amman fiddah ko alamun tsayawa bata dashi.


Tuni fiddah ta karya hannun ƴarfillo gamida yimata targaɗe a wasu sassan jikinta,Ayman ganin fiddah na shirin kashe mishi ƴarfillo ne yasa ya ƙoƙarta da ƙyar ya miƙe ya cakumi fiddah ta baya ya dannata toilet yayi maza ya kulle ƙofar da key.


Zuwa lokacin tuni ƴarfillo ta suma dan azaba,d kyar ya iya samata kayant shima yasa sannan yay waya asibiti akazo da Ambulance aka kwashesu zuwa Asibitin.


Fiddah ko ihu take tana jijjig ƙofar amman a banza ba me jinta,ganin hakane yasa ta haƙura ta zuna a toilet ɗin tana ci gaba da kukanta.




koda suka isa Asibitin anyi musu duk abinda yadace,ƴarfillo tafi shan wuya dan targaɗe har huɗu da karaya ɗaya fiddah ta mata ajikinta,baya ga faffasa mata jiki da tayi ya kumbura kamar wacce tayi hatsari.


A daran aka sallami Ayman danshi ciwonshi kaɗanne,kuma anyi dressing ɗin gurin.


kai tsaye hotel ya nufa ya buɗe fiddah,tana fitowa ta ɗaga sandarta zata ƙara runtuma masa,da sauri ya kwace sandar,sannan ya wurgar da fiiddah ɗin ya shige toilet ya tsarkake jikin shi ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa.


Afusace fiddah ta miƙe ta ɗaukeshi da mari har guda biyu sannan tace.


"Fasiƙi, mazinaci,wanda baya tsoron Allah,wallah kaji kunya,dama abinda kake aykatawa kenan,shiyasa ka kasa sauke nawa hakkin dake kanka,to na godewa Allah da ban taɓa haɗa shimfiɗa da ɗan akuya kamarka ba,wlh bana ƙaunarka kasake ni kawai,wawa bunsuru kawai".


Ran Aymam inyayi dubu ya ɓaci dajin kalaman fiddah,dama a cike yake da ita game da dukar masa ƴarfillo da tayi,


"Ke dan kan ubanki har kin isa ki kirani da wainnan sunayan?waye ubanki,mekike taƙama dashi?".


"sede ubanka,kuma ubanka shine ubana,ina taƙama da duk wani abu dakake taƙama dashi,ɗan akuya"fiddah ta bashi amsa batare da tsoron komaiba.


"Ubankine ɗan akuya baniba,dan a gurinshi na koya"Ayman ya faɗi sanda yake tunkarota cikin fushi.


ja d baya fiddah tayi sannan tace.


"hhhh me ya haɗa biri da gada kuma da zakace a gurin ubana ka koya?Ay kowa yaga abinda kake aykatawa ko tambya baze yiba agurin,bunsurun ubanka ka koya".


*Tassssssssssss!!!*


Ayman ya ɗauke fiddah da mari gamida rufeta da duka seda ya mata lilis sannan yace.


"Tunda nace ubankine ya koyamin akuyanci kin ƙaryatani to bari innuna miki da gaske shiɗin ya koyamin,dan nacire miki tantama،abinda zanmiki yanzu inkinje gida ki tambayi uwarki zata tabbatar miki da haka ubanki ya mata ta samar dake".


Be jira komaiba ya cire tawul ɗin dake jikinshi yacirewa fiddah kayanta,kuka take takasa hanashi,tanaji tana gani yana ƙoƙarin kusantarta,amman tsamin da jikinta yayi yasa ta gaza hanashi.


Ayman ko be saurara mata ba harseda ya rabata da budurcinta,ta ƙarfin tsiya,ya dirjeta son ranshi,duk da baya jin daɗin komai amman yasha alwashin seta gane kurenta akan abinda tayi masa tayiwa ƴarfillonsa.


Seda ya gaji dsn kanshi ya ɗagata ya shige toilet ya sakarwa kanshi ruwa.


Fiddah kuka take wanda tunda aka haifeta bata taɓa yin irinshi ba,tayi danasanin,auran Ayman ba iyaka tana nan zaune yafito ya shirya ya fice ya kyaleta.


Da ƙyar ta iya rarrafawa zuwa toilet ta tsaftace jikinta,ba abinds yake ƙona ran fiddah kamar ganin Ayman be jima da Aykata zinaba yazo ya kwanta da ita wannan abu koni ya bani takaici.


Ta jima a toilet ɗin sannan taji daɗin jikinta ta fito ta maida kayanta ta fice daga hotel ɗin gidanta ta nufa ta haɗa duk abinda tasan natane,ta nufi Airport cikin ikon Allah tasamu jirgin yawo danhaka ta biya kuɗi masu yawa ta samu visa ta shiga jirgi ya ɗago da ita zuwa gida nigeria.


Shiko Ayman daya fita Asibitin ya koma inda ya tarar ƴarfillo ta farka se masifa take akan se ya sanar da ita wacece tamata wannan aykin,dakyar a tsorace ya shaida mata fiddah matar sace.


ba ƙaramin firgita tayi dajin cewa yana da mata ba,ashe ta kashe maciji ne bata sare wuyanshi ba,hakanne yasa ta tada mada da darun akan cewa sede a ɗaura musu aure a yau ko ta tafi tabarshi,Ayman ji yake in ƴarfillo ta tafi ta barshi tamkar rasa rayuwarsane,dan haka haƙuri yadunga bata itako taƙi yarda.


Ganin hakane yasa yaje yasamo wasu musulmai su biyu ya biyasu sukazo suka ɗaura musu aure a Asibitin.


Wannan alamari yasa ƴarfillo da Ayman cikin farinciki mara iyaka,burin ƴarfillo yacika,a sannu zata nunawa fiddah da duk wani wanda ya nuna baya sonta da Ayman banbancin dake tsakanin,tagari da ƴarbariki.


Muje zuwa,Surbajo ce.
[8/1, 18:53] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION




*Page 85-86*




Cigaba sukayi da rayuwarsu har zuwa lokacin da ƴarfillo taji sauƙi,ko ƙuda Ayman bayaso ya taɓa masa ƴarfillonsa,sosai yakejinta Aransa.


Cigaban labari.


Naim duk yadda yaso yaga ya hana auran ummu da Ayman amman ina abu yafi ƙarfinsa,dan gama ummu na gama jinin biƙinta aka ɗaura Auranta da Ayman bisa jagorancin Sarki da ciroma.


Ɗaurin Auran daya sami halattar jamaa da dama.


Se bayan an ɗaura aurene sarki ya tara matansa ya musu bayani,gamida nuna musu video na ummu da ɗanta.


Kuka gaba ɗayansu suka sa suna faɗin.


"kaine silar komai,da ace kabarshi ya aureta tun farko da wannan abun kunyar be samemuba".


"Tabbas nine sila sabida dama komai be faruwa seda sila,tun farkon rayuwar yarannan Allah ya rubuta se hakan ta samesu kunga ko babu me ja da hukuncin Allah,kude kawai kubar maganar muyi musu,fatan alkhairi".


"to munji amman de kasan akwai azumummuka na kaffara da zakayi ko?"inji hajiya babba.


Dariya yayi sannan yace.


"na fiki sanin haka tunda nine nayi rantsuwar,tun ranar dana sawa raina zan aura masa ita nafara yin Azumin wanda ahalin yanzu na gama".


Hakade sukai ta tattaunawa gameda Alamarin Ayman ganin yanzu kwata kwata ma be damu daya kirasu su gaisaba saɓanin da da kullum se sunyi waya,fatan alkhairi suka masa.


a ranar da aka ɗaura Auran ummu da Ayman a daran fiddah ta iso nigeria,wanda kuma Aranar aka ɗaurawa Ayman Aure da ƴarfillo a germany,sede anriga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login