Showing 3001 words to 6000 words out of 42465 words
Jameelu ba matuk'ar ina raye, kuma ko bayan Raina in kika bari Ta Aureshi ban yafe miki ba,dan haka na yanke shawarar gobe da asubar fari zani tasha in samo mota ta kwashe mana kayanmu mubar musu Garin gaba d'aya dan akan Ummu zan iya salwantar da farin cikina domin nata, dan haka kisa ranki a inuwa Mijin Umma kamili natsatstse nanan zuwa da yardar Allah".
Dan dad'i Zainabu bata san sanda ta rungume Mudi ba tana masa godiya.
Daga nan had'a kayansu suka shiga yi Dan asubanci zasu yi shiyasa suka fara shirin tun yanzu.
Maman Yusuf.
[6/29, 09:02] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*Pure Moment Of Life Writers (P.m.l)*
*page 9-10*
Da magarib bayan Sun fito masallaci da sauri su Baba Hamisu suka tsaida Mudi a k'ofar Gida.
Ba walwala A fuskarsa ya fara dubansu yace.
"Lafiya de ko kuka tsaida ni?".
Da sauri Baba Hamisu ya fara magana.
"Mudi tabbas mun san abinda aka yi maka ba'a kyauta ba kuma itama Sauden naje na sameta na nuna mata bata kyauta ba kuma ta fahimce ni dan yanzu haka Ta janye maganar Auran,dan haka Don Allah kayi hak'uri ka janye zancan barin Gidan nan"
Shu'aibu ne ya k'ara da cewa.
"Kuma Mudi in kabar Gidan nan zumuncin mu lalacewa zeyi, Yaran mu ba zasu san junansu ba, dan haka Don Allah tunda itama Yaya Saude ta janye zancan Auran Don Allah kaima ka janye zancan tafiyar".
Kallo kawai Mudi ya bisu dashi,dan yasan halin Saude farin sani bata fad'in abu ta dawo ta janye,dan haka kad'a kanshi kawai yayi sannan yace.
"To naji kuma nagode Amman yanzu bazan yanke hukunci ba se nayi shawara da med'akina tukuna in yaso daga baya shawarar damuka yanke zaku ganta,in mun yarda mu zauna zaku ga mun zauna in bamu yarda ba zaku ga mun tafi,dan haka kuyafemu duka sabida halin rayuwa".
Gaba d'aya jikinsu ne yayi sanyi da batun na Mudi amma basu da zab'in daya wuce suyi fatan alkha'iri,dan haka suka had'a baki gurin fad'in.
"To Allah ya tabbatar mana da alkha'iri Amman de ka duba maganar da idon basira".
Murmushi ya musu ya shige cikin Gidan.
Suma Gidan suka shiga jiki a sanyaye .
Koda Mudi ya yiwa Zainabu bayani akan abinda su Shu'aibu suka tare sa suna fad'amasa fafur tak'i amincewa dasu ci gaba da zama a Gidan, dan harda kukanta ita de subar Gidan, dan haka dole Mudi ya amince dasu bar Gidan shine masalaha.
Da daddare da misalin k'arfe takwas na dare Mudi yaje yiwa Mahaifansa sallama sabida asubanci zasu yi.
Koda ya musu bayanin abinda ke tafe dashi kuka Inna tasa akan bata amince ba in kuma ya tafi to bata yafe mishi shayar dashi da tayi ba.
Hankalin Mudi in yayi dubu ya tashi, rasa inda zesa kansa yayi koda yayi yunk'urin bata hak'uri mik'ewa tayi sannan tace.
"Wlh matuk'ar kabar Gidan nan bada yawuna ba Allah ya isa ban yafe maka nono na daka shaba har abada".
Tana kaiwa nan a zancan tayi shigewarta d'akinta,ta barshi shida Malam Audu.
Shima Mahaifinsa cewa yayi in yabar Gidan to ya tabbata su ya Bari ba Gidan ba.
Dan bak'in ciki Mudi har kuka yayi,haka ya baro b'angaran Iyayan nasa ya nufi nasu.
Koda shigarshi zainabu tsorata tayi da yanayin sa dan haka jiki a sanyaye ta tambayeshi abinda ya faru, be b'oye mata komai ba ya sanar da ita,itama kukan tasa daga bisani ta share hawayenta ta mik'e ta fara maida kayayyakin su mazaunin su.
Cikin k'ank'ani lokaci komai yayi tsaf,sannan taje ta kawo musu abinci suka ci,shi de K'ara rarrashinta yake tayi.
murmushi kawai tayi tace,"haba Malam ay dole na taya ka yiwa mahaifanka biyayya, in ban taya ka ba waye ze taya ka?Dan haka ka dena ma bani hak'uri, Allah yasa hakan shine alkha'iri".
*Bayan Wata Shida*
Tsawon wa'innan watannin ba'a sake d'ago da zancan Aure tsakanin Ummu Aymana da Jameelu ba se yau.
Saude ce ke zubar da ruwan bala'i a tsakar Gidan tana fad'in, "wlh nagaji dayin shuru yau ko sede ayi wacce za'a yi, in ko aka hana Jameelu Auran Ummu, to wlh zan bashi damar fita yak'in neman Auran ta koda kuwa da kaifin takobin shine tunda abun ba mutunci".
Sosai maganganun nata suka firgita Zainabu dan tasan kashe Mutum a gurin Jameelu tamkar kashe kiyashine,shi yasa duk tabi ta firgita gashi acikin daji suke ko hukumar Y'an sanda babu a gurin bare su d'auki mataki.
Shiko Mudi ko a jikinshi maganar bata dameshi ba harkokinsa kawai yake yi, abinda ya sanide shine Y'a tashice Ba kuma wanda ya isa ya sashi Aurar da ita ga Wanda be dace ba.
Maman Yusuf.
[6/30, 06:46] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad @ZahraSurbajo*
*Pure Moment Of Life Writers (P. M. L)*
*page 11-12*
Koda dare yayi su Baba Shu'aibu ne suka sake zuwa gurin Mudi akan zancan Auran.
Kai tsaye yace musu.
"Ni bazan Aurawa Ummu Jameelu ba sabida be dace da ita ba, kuma wlh babu Wanda ya isa yasani yin abinda be dace ba".
Ko sauraron su be sake yi ba ya tashi ya barsu a gurin.
Gaba d'ayan su Ransu ya b'aci, dan haka daga gurinshi kai tsaye gurin Inna Saude suka nufa,suna zuwa suka kwashe k'arya da gaskiya suka fad'a mata.
Ga mamakinsu se kawai tayi murmushi tace musu, "ku kwantar da hankalinku,aure kamar anyi shi angama, ayni bana magana ta tashi a banza,inde na furta sena tabbatar, dan haka ku tashi kubani guri zanyi nazari".
Cike da mamakinta suka bar gurin.
Dare ya tsala sasoi baka jin motsin komai sena Shanun da Awakin da suke Gidan,kasancewar duk wani Bil Adama dake Garin ma yayi bacci,dan Dare ne sosai misalin k'arfe biyu na dare.
Jameelu na hango d'auke da wata sharb'eb'iyar wuk'a fuskarshi b'oye cikin rawani,ya nufi b'angaran Baba Mudi, koda ya haura ta katanga kai tsaye D'akin da suke kwana ya nufa.yana shiga be b'ata lokaci ba ya samu Dede zuciyar Mudin ya Burma masa wannan wuk'a wacce sabida kaifinta seda ta tsago jikinshi ta caki katifar da yake kwance.
Nishi me k'arfin da Mudi ya saki shine ya farkar da Zainabu daga bacci, da sauri ta kunna cocila dan ganin meke faruwa, hakan yayi dede da lokacin da rawanin da Jameelu ya rufe fuskarsa dashi ya kwance.
A razane Zainabu ta furta.
"Jameelu me ya kawo ka D'akin mu a dede wannan lokacin? me kake nema? Ko kayi makuwa....."maganarce ta mak'ale a mak'oshin ta sanda tayi arba da sharb'eb'iyar wuk'a soke a k'irjin mijnta jini se ambaliya yake.
Wata razananniyar k'ara ta Saki ta fad'i k'asa sumammiya, shi ko Jameelu jikinshi na rawa ya fice daga b'angaran, kai tsaye D'akin Mahaifiyar shi ya nufa.
Da yake tasan da zuwanshi k'ofar a bud'e take kuma bata bar Baba Hamisu ya kwana a D'akin ba, dan haka da shigar Jameelu da sauri ta tare shi tana tambayarsa
Cikin matsanancin tsoro ya bata labarin ya kashe Mudi Amman Zainabu ta ganshi wanda sanadin hakan gata can ma a sume.
Wani murmushi na mugunta Saude tayi sannan tace .
"Ka kwantar da hankalin ka,kasa a ranka cewa ka kashe banza, ay ka godewa Allah daya baka jarumar Uwa me zurfin tunani,ay sanin da nayi za'a iya samun matsala gurin aywatar da aykin shiyasa na amso kan ta kwana a gurin Boka na kan tudu, dan haka yanzu zanyi Maganin komai".
Tana gama fad'in haka ta bankad'a katifar ta ta d'auko wani abu da wata k'aramar wuk'a ta fice daga D'akin ta nufi Garken Shanun Gidan wanda suke mallakin Baba Mudi ne,shi de Jameelu bin ta kawai yake da ido dan gaba d'aya ya gama tsorata.
Tana zuwa rami ta hak'a da Wata Wuk'a dake hannunta tana gama hak'awa ta d'auko wasu tarkace a wani Jan kyalle ta saka a cikin ramin Tana Kiran sunan Zainabu, seda Ta Kira so bakwai Amman a hankali sannan ta rufe ramin da kyallan a ciki,da sauri suka koma d'akinta gudun kar wani ya Gansu.
Tunda suka koma D'akin in banda dariya ba abinda suke yi sabida ta shaidawa Jameelu manufar abinda Ta burne, ashe asirine ta yiwa Zainabu wanda ita da hankali sede wani Ikon Allah ma'ana ta haukata ta hauka me tsanani.
Acan kuwa b'angaran su Zainabu,tana nan kwance a sume kamar a mintsineta se kawai ta farka, tana farkawa ta fara soshe soshe tana cire duk wata sutura ta jikinta,seda tayiwa kanta tsirara sannan ta shiga tik'a rawa akan gawar Mijin nata.
Maman Yusuf.
[6/30, 12:57] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad@ZahraSurbajo*
*Pure Moment Of Life Writers (p.m.l)*
*page 13-14*
Haka Ta kwana akan gawar Mudi tana chashewa ba tare da damuwar komai ba.
Da gari ya waye Dariyar Zainabu ce ta farkar da Ummu Aymana Wacce take ta faman shirgar baccinta,koda ta farka mamaki take na ganin mahaifiyar tata tsirara, Amman abunka da yarinta seta rufe idonta wai gudun kar Umman tata tace ta kalleta idon nata a rufe tace.
"Umma zaninki ya kwance ki d'auka kisa zan wucene".
Dariya Zainabu ta sake fashewa da ita cikin haukanta ta cewa Umma Aymana.
"kajimin tsinanniyar mata! uban waye yace miki tsirara nake?dan Kan ubanki duk tulin kayan dake jikina baki gansu ba da har kike cewa nasa zani ayko yau se naci uwarki".
Tana gama maganar ta diro daga kan gawar Mudi,tasa hannu ta finciko wuk'ar da aka sokawa Mudin ta nufi Ummu Aymana da mahaukacin gudu, ganin hakane yasa Ummu ta kwasa da gudu zuwa tsakar Gidan su inda kowa ya fito yana harkokin gabansa harda Inna Saude wacce bame cewa ta aykata wani abu mummuna duba da yadda hankalinta yake kwance.
Da gudu Ummu tayi cikinsu tun kamin suyi wani yunk'uri Zainabu itama ta fito rik'e da wuk'ar da aka kashe Mudi wacce take d'igar da jini.
Hankali atashe suka mik'e kowa ya nemi gurin b'uya da kyar su Uwaisu suka murd'eta suka amshi wuk'ar,itako se dariya take tana fad'in.
"Kisan gilla zanyi tunda na koya na iya".
Abun d'aurewa kowa kai yayi Inna Saude ce fuska d'auke da damuwa da yanayi na tausayawa kamar gaske tace.
"Ikon Allah Zainabu ciwon haukane Kuma ya kamata,watak'ila ma yanzu ne abun ya sameta bayan Mudi ya tafi masallaci".
Baba Shu'aibu ne ya katseta da cewa.
"Ay yau Mudi ya makara dan ko masallacin be jeba sede ko in asubancin tafiya kasuwa yayi".
Ummu Aymana wacce ke b'oye a bayan Inna uwani ce tace.
"Ba kasuwa yaje ba dazan fito naga suna wasa da Umma na ta haye kanshi tana rawa, shi kuma yana kwance a kan Gado".
Da sauri suka nufi d'akin abunda suka gani ba k'aramin firgita su yayi ba,su duk a tunaninsu Zainabu ce Ta kashe Mudi bayan ta sami tab'in hankali sannan Kuma ta biyo Ummu Aymana itama zata kashe.
Cikin jimami suka Fara y'an koke koken su na munafurci wanda zahirin gaskiya murna suke giwa ta fad'i zasuci nama.
Cin k'ank'anin lokaci gari ya gama d'auka Zainabu ta kashe mijinta kuma tana neman kashe y'arta a sakamakon haukacewa da tayi.
Ayko jama'a se zuwa kallo sukeyi,haka mutanan Gidan suka bar Zainabu ba Kaya kowa yazo haka ze ganta tsirara,tana ta surutai.
Ummu Aymana ko kuka kawai takeyi gwanin tausayi,abunka da farar fata tuni har tayi ja sabida kuka,kowa yazo seya tausaya mata,haka aka yiwa Mudi wanka aka sallaceshi aka kaishi makwancinshi, ita kuma Zainabu aka kwashe kayan D'akin tas sannan aka sata a ciki aka mata tirke kamar Wata Akuya aka d'aureta kuma har zuwa lokacin basu suturtata ba.
Haka akai Ta zaman makoki har zuwa lokacin da akayi rabon Gado inda sabida da zalinci Ummu Aymana da mahaifiyarta, suka tashi da Saniya daya da Raguna guda biyu acikin Shanu sama da d'ari biyu da Raguna sama da guda hamsin iya gadon da suka samu kenan,sauran ko harda su Saude a cikin jerin magada inda kasonta yafi na kowa yawa dan ko Furera Shanu biyu aka bata.Koda aka ba Ummu Aymana nasu bata damu ba dan bata san me hakan ke nufi ba.
Duniya sabuwa ta dawo a Gidan kowa ya samu dukiya se walawa yake yi, sab'anin Ummu da Umman ta kullum tana mak'ale da ita tana kuka gashi ko abinci ba'a ba Umman tata wai a cewar su mahaukata basa cin abinci a k'oshe suke,shiyasa a cikin nata wanda ake bata seta k'i ci ta kawowa Umman nata ga mamakinta seta ga ta cinye tas tana neman k'ari.
Kullum Ummu cikin tausayawa mahaifiyarta take kasancewar Zainabu ba Y'ar Garin bace Y'ar Asalin jihar Adamawa ce shiyasa babu wani nata daya san abinda ke faruwa, shiyasa Ummu ke tausayawa mahaifiyar tata.
Kwanci tashi rayuwa tayi tsanani garesu dan yanzu ko lomar abinci babu me basu sede tafita bara tasamo ta kawowa mahaifiyar tata,gashi babu Wanda yatab'a yunk'urin nemawa Umman tata magani, d'an Gadon nasu ma wayar gari tayi taga babu su a tirken da suke kwana, koda ta tambaya cewa akayi barayine suka sace haka dole ta hak'ura.
Yanzu D'akin da suke kwana tsutsotsine ke yawo ko ina sabida Umman ta tunda aka d'aureta tsawon wata shida koda wasa basu tab'a kwanceta ba a gurin take kashi take fitsari,Ummu Aymana kuma bazata iya gyara mata ba kuma tayi iya yinta ta kwanceta Amman ta Kasa, gashi daga alamu Umman tata bata da lafiya dan ta lura cikin Umman nata se motsi yake gashi lokaci zuwa lokaci cikin na k'ara girma.
Ta rasa wanda zata fad'awa sede tai tayiwa Umman nata Addu'a akan Allah ya bata Lafiya.
Abinda Ummu bata saniba tun kamin rasuwar Mudi, Zainabu ke d'auke da ciki na Wata biyu wanda ko ita kanta batasan tana dashi ba bare wani na Gidan.
*Bayan watanni biyu*
Ummu Aymana ta dawo daga barar abinda zasuci kwatsam Ta sami mahaifiyarta a cikin wani mummunan hali na ciwo gaba d'aya ta fita hayyacinta,a gigice Ummu taje cikin Gidan neman suzo su taimaki Umman ta Amman ba Wanda ya kulata dan Saude asiri tayiwa kowa na Gidan akan ya tsani su ummun.
Ganin bame Taimako ne yasa takoma gurin Umman tata kamar wasa ta Fara kwance igiyar da aka d'aureta kawai se gani tayi ta kwantu.
Kamar jira tana kwanceta umman tata ta kama hannunta ta rik'e da k'arfi tana kuka me tsuma zuciya gami da wani nishi me k'arfin gaske,kwatsam Ummu Aymana se ganin Jariri tayi ya fad'o yana tsala kuka.
A gigice ta kwace hannunta daga ruk'on da Umman nata tayi mata ta matsa gefe jikinta na rawa kamar mazari, ita ko Umman D'an na fad'owa ta koma ta kwanta tana maida numfashi sabida ta wahala..
Shi ko Jaririn in banda kuka ba abinda yake yi ga shi kwance cikin kashi tsutsa ta Fara bin jikinshi,tausayin Yaron ne yasa Ummu Aymana d'auko wankakken zani tazo ta d'aukeshi ta lullub'eshi bayan ta cire tsutsar da ke binshi ayko take yanke yaron yayi shuru.
Ajiye yaron tayi akan shimfid'a tafita tsakar Gidan tace Umman ta ta Haihu.
Ay ila hirin Gidan ba wanda be razana dajin zancan ba,da sauri suka nufi D'akin kowa yana toshe hanci, abinda suka gani shine ya firgitasu wato Yaron babu ta inda ya baro kamannin Mahaifinshi, hakan ke nuna Dan Mudin ne, kuma hakan na nufin Gadon da suka ci na Mahaifinsa sesun dawo dashi ma'ana de ya koresu daga cikin Magadan Baban shi.
Ko cibiya basu ji tausayi Sun yanke masa ba haka suka baro D'akin cike da zullumi akan in suka Bari duniya taji labarin haihuwar D'a Namijin da Zainabu tayi,sun bani.
Ummu ko tasa Yaron tayi tana kallo k'aunarshi na ratsa zuciyarta, ita ko Zainabu bacci kawai takeyi na huce gajiya.
Ummu naso Ta goya yaron Amman wannan mahaifar da zaranta sun hanata yin hakan, kuma taga intaja da niyar ta cire Yaron kuka yake duk da a hankali take jan, kawai seta yanke shawarar ta rage masa tsawonta zefi kawai dan haka Reza ta d'auko sabuwa tazo ta yanke cibiyar,tana yankewa se taga jini na zubowa da sauri ta sami bakin d'an kwalinta ta yanka ta d'aure masa sosai seda taga jinin ya dena zuba sannan hankalinta ya kwanta.
Goya shi tayi tafita yin Icce dan tana tsoron ajiye shi Ummanta ta dukar mata shi,da yake tasa hijab kowa yaganta da goyo d'auka yake y'ar tsanace haka har ta isa daji tayo itacen ta dawo gida,had'a wuta tayi ta d'orawa Ummanta ruwan wanka dan ita gani take yanzu Ummanta ta warke zata iya yin wanka,seda ruwan ya tafasa ta kwashe a bokiti sannan ta nufi D'akin domin tashin mahaifiyarta ta a bacci tazo tayi wanka.
Abunda ta gani shi ya firgitata wato ba Umman nata a Dakin ba alamarta, Da gudu ta fita waje tana dubawa nanma ba ita, seda tayi tafiya me nisa goye da yaron a bayanta tana neman Ummanta Amman bata ganta ba kowa ta tambaya sede yace yaga tawuce da gudu ba kaya a jikinta.
haka Ummu Aymana tagaji ta dawo Gida tana kuka tana addu'ar Allah yadawo mata da Ummanta lfy.
Ruwan Data dafa domin Ummanta shi ta juye a baho ta tsunduma yaron a. ciki ta fara yi masa wanka abun ba k'aramin mamaki ya bani ba ganin yadda take masa wankan kamar wata uwar mata,amman dana tuno wayo da dabara irin na bafulatanin mutum kuma mazaunin k'auye se abin yadena bani mamaki ya koma burgeni.
tsaf tamasa wanka shiko se kuka yakeyi na alamar yaji dad'in wankan.
Duk abinda takeyi gani take yanzu Ummanta zata dawo dan haka guri tasamu a gefe ta kwantar da yaron bayan tashafa mishi man kadai ta lullubeshi da zannuwa guda biyu,seta shiga gyara D'akin dan kar Ummanta Ta dawo taga bata gyara ba.
Ummu akwai juriyar ayki kamin lokaci me tsayi ta gama gyara D'akin fess bame cewa shine me tsutsa sede warine har lokacin be dena ba, d'aukar yaron tayi suka shiga D'akin suna jiran dawowar Umman su.
Maman Yusuf .
[7/1, 08:34] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*