Showing 6001 words to 9000 words out of 42465 words
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad @ZahraSurbajo*
*pure moment of life writers*
*page 15-16*
Ummu Aymana tana nan zaune har dare yayi amnan Umman ta bata dawo ba kuma a lokacinne Yaron ya fara kuka wanda ko ba'a faÉ—a ba yunwa yake ji.
Hankalin ummu ne ya tashi tarasa yadda zatayi dashi gashi bame taimaka mata ay kawai itama seta fashe da kukan.
Rarrashin shi ta shigayi tana bashi ruwa a hankali bacci ya ɗauke shi be sake farkawa ba se wajan ƙarfe ɗaya na dare,Ummu rasa abin yi tayi ay kawai wata shawarace ra faɗo mata,miƙewa tayi ta ɗauƙi ƙoƙo ta nufi garken Shanun Gidan,tana zuwa ta samu me shayarwa a cikinsu ta tatsi Nononta da yake a ɗaure take bata mata komai ba.
Da sauri ta koma ɗaki tasa cokali ta dunga ɗiba tana bashi ay kamar jira yake,take Ya kama sha bada wasa ba,ci gaba tayi da bashi har seda ya fara turoshi waje inta bashi hakan ne yasa ta gane ya ƙoshine,rufewa tayi ta cire mishi zannuwan data rufa mishi ɗazu sabida yayi kashi a ciki.
Wasu ta É—auko ta rufa masa bayan ta goge mishi kashin,Allah sarki bawan Allah ay jin cikinshi ya É—auka se bacci,itama baccin tayi cike da kewar Ummanta.
Washe gari da safe tayi masa wanka ta goyashi tasa hijab ta fita barar abinda zata ci bata dawo ba se Azahar,tana zuwa ragowar Nonon jiya data rufe shi ta ɗauko taba Ƙanin nata yasha ya ƙoshi ya koma bacci.
Haka ta dunga ɗawainiya da ƙanin nata har tsawon kwanaki biyar,kuma dama tun bayan rasuwar mahaifinta Inna Saude bata sake zancan Auranta da Jameelu ba sabida dama dukiya sukewa kuma sun samu.
Gaba É—aya sun gama tsaida shawarar kashe yaron ko kuma salwantar dashi,amman basuyi shawarar dasu Malan Audu ba su eh su sukayi shiyasa su Malan Audu basu da masaniya.
Jameelu aka wakilta akan kashe yaron kuma ya amince ze aywatar.
Da daddare misalin ƙarfe goma na dare yaron cikinshi ya fara ciwo gashi cikin ya kumbura, hakane yasa tsoro ya kama Ummu ta kwantar dashi ta nufi gurin Inna Saude domin ta faɗamata ko zata taimaka mata.
Tana zuwa ƙofar Ɗakin abinda taji ne yasa takasa ƙarasawa cikin Ɗakin,muryar Saude ta jiyo tana ba Jameelu umarni akan yaje yanzu ya kasheta ita da Ƙaninta kuma ya tabbatar ya musu irin kisan da yawa Mahaifinsu.
A gigice Ummu ta baro gurin jikinta se ɓari yake yi har faɗuwa take gurin gudu, a haka ta ƙaraso Ɗakin nasu tana zuwa ta sungumi Ƙanin ta dake ta faman kuka sabida ciwon da cikin shi ke masa ko hijabinta bata saba tafice da mahaukacin gudu daga Gidan.
Tana fita ba jimawa Jameelu ya shiga ÆŠakin domin aywatar da mugun nufin shi sede yayi rashin sa'a domin sunbar Gidan.
Da sauri ya fito yabi bayan su dan ya fahimci basu jima da fita ba.
Ita ko Ummu gudu take irin na ceton Rai rungume da Ƙanin nata shiko se kuka yakeyi,Garin lokacin damina ne dan haka hadarine baƙiƙirin a sama Ruwa gab yake da sauka.
Ganin hadarin sosai hankalin Ummu ya tashi amman hakan be hanata cigaba da gudunba musammam data fahimci kamar anbiyo sawun su,a haka har ta shiga ƙurgummin Dajin Garin bata dena gudunba.
Shigarsu Dajin keda wuya Ruwa ya kece kamar da bakin ƙwarya harda ƙanƙara,amman hakan be hana baiwar Allah Ummu Aymana ci gaba da gudu ba duk da cewa ko gabanta bata gani sabida tsananin duhun dajin.
Ci gaba tayi da gudun har takai dede inda tagaza ci gaba da gudun dan tana zuwa dede gurin taji kamar an riƙe mata ƙafa tayi tayi ta ɗaga ƙafarta amman abun yaci tura hakanne yasa ta durƙushe a gurin tana kuka tana roƙon Allah akan ya kawo musu agaji,gashi daga ita har ƙanin nata ruwa ya musu shegen duka wanda hakanne yaja ƙanin nata ya suma sabida wahala.
Tana nan durƙushe ruwa na dukansu taji wani abu me santsi yana bin jikinta hannu takai tana shafawa dan ta gasgata tunaninta ilai kuwa abinda take zargine wato *Maciji*
muje zuwa.
Maman Yusuf.
[7/1, 15:36] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad @zahrasurbajo*
*pure moment of life writers*
*page 17-18*
Runtse idonta tayi taci gaba da shafa micijin har zuwa sanda tazo dede kanshi da sauri ta shaƙi wuyan macijin sede ga mamakinta seji tayi babu komai a hannunta.
Da sauri ta buɗe idonta abun da tagani shine yayi matuƙar bata mamaki gami da farin ciki,umman ta tagani zaune akan wata kujera ta alfarma cikin shiga ta alfarma tana mata dariya.
Da gudu ummu ta miƙe ta ƙarasa gurinta tana kukan murnar ganinta,tana zuwa rungumeta rayi ita kuma tasa hannu ta amshi yaron dake hannun ummun.
Ga mamakin ummun ruwan da akeyi yadena sauka akansu sannan gurin ya wadata da haske tamkar rana,koda ummu takai dubanta gaba ƙaton kogin garinsu ta hanga wanda da ace taci gaba da gudun da takeyi ba makawa ciki zata faɗa dasu.
Gidiya tayiwa Allah sannan takai dubanta gurin ummanta wacce tun É—azu inbanda murmushi ba abinda tace mata,cike da murna ummu tace.
"Ummana da badan Allah ya taimakemu kinzoba da tuni mun mutu dan Allah tunda kinji sauƙi kar ki kuma cire kayanki kuma yaronki se kuka yakeyi".
Murmushi umman kawai tayi sannan ta kamo hannun ummun ta zaunar da ita akan cinyarta,zamanta keda wuya se ganinsu tayi ita da ƙanin nata a wata bukkar kara ga wani abinci me rai da lafiya se kuma madara me kyau itama,kuma abinda ya bata mamaki shine ita de da tasan darene yanzu kuma safiyace kuma tana jin ƙarar motoci daga inda take.
Ta duba ko ina bata ga umman tasu ba ƙanin ta kuma gashi cikin ƙoshin lfy harda kayan sanyi a jikinshi,se ɗaga ƙafa sama yake yi yasa hannunshi a baki yana tsotsa.
Lokacinne ummu ta gama yarda Allah ne ya turo wannan aljana ta taimakesu dan ko shakka batayi da aljana ta haɗu,godiya ta sake yiwa Allah sannan taja kwanon abincin batare da tunanin komaiba ta kama ci har ta cinye tasha ruwa,shima ƙaninta madarar ta bashi amman yaƙi amsa alamar a ƙoshe yake ,daukarshi tayi sede ga mamakinta tana ɗagashi se taga ashe akan kuɗi yake kwance ƴan dubu dubu guda goma da sauri tasa hannu ta ɗauki kuɗin ta ƙulle,a zaninta sannan ta goya ƙanin nata ta fito daga cikin bukkar.
Koda ta fito se taga ashe a bakin titi suke motoci se wucewa sukeyi.abun sosai ya bata mamaki kuma daɗin daɗawa titin ba irin na garinsu bane,ƙara ɗaure ƙaninta tayi a baya da kyau ta saka hijab ɗin da tagani a rumfar ba me cewa ɗane a bayan nata kasancewar tana da girman jiki duk da cewa shekaranta goma sha ɗaya lokacin.
Ƙarasawa tayi bakin titin se ta hango wata tasha daga can gaba kaɗan dan haka can ta nufa,tana zuwa taga motoci da mutane a ciki ita kuma gashi batajin yaran hausa bare ta fahimci inda kawai wata mota da taga ta kusa cika ita taje ta shiga itama, dama mutum ɗaya suke jira tana shiga akazo karɓar kuɗin mota,Ayko ansha fama kamin ta fahimci yawan kuɗin da zata bada sabida kaf gurin bame fahimtar yaranta itama kuma bata fahimtar nasu ,a cikin kuɗin da aljana ta bar musu ta bada kuɗin motar,sannan direba yajasu suka tafi inda ummu batasan inda zasu ba.
Tafiya suke amman taƙi ƙarewa Ummu har gajiya tayi da zama ga ƙaninta se ƴan koke koke yakeyi, sakkoshi tayi ta rungume ta bashi madarar da yaƙi sha a bukkar nan dan taho mishi ds ita tayi dan tasan ze buƙata anjima, Jama'ar cikin motar se mamaki suke daga ƙarshe se suka dena sabida kama ta jini da suka gani se duka suka ɗauka ɗantane sabida sunsan fulani da auran wuri.
Basu isa inda zasu ba se cikin dare gaba ɗaya Ummu ta gama gajiya,haka suka iso tashar garin da suka zo kowa ya sauka itama saukar tayi tasake goya ƙaninta a baya ta lulluɓeshi da hijab,cikin tashar ta shiga tana ta waige waige wanda kowa yaganta yasan ƴar ƙauye ce.
Ganin bata gane kan tashar bane yasa ta fito ta bi wani titi me yawan hasken fitulun kan titi abin yayi matuƙar burgeta, nan ta shagala da kallon fitulun har dare ya tsala bata sani ba,ci gaba tayi da tafiya a ƙafa har ta iso wani guri me yawan mata sanye cikin shiga ta zubar da mutunci duk,wani me tsoron Allah in ya musu kallo ɗaya baze ƙaraba sabida tufar dake jikinsu ita da babu duk ɗaya.
Kasancewar Ummu batasan meye karuwanci ba shiyasa ta É—auki shigar tasu a matsayin al-adar Garin, haka taita binsu da kallo,yayin da gefe É—aya kuma motoci ne na alfarma ke fakawa suna É—aukarsu.
Can É—an nesa dasu taje ta zauna tana ci gaba da kallon ikon Allah, tanason fahimto abinda hakan ke nufi,dan ita de taga kamar masu motar wacce tafi fitar da surarta suke É—auka, hakanne yasa Ummu fahimtar ashe al-adar Garin me kyauce tunda masu kuÉ—in garin ma masu irin shigar suke taimakawa,FCT ABUJA KENAN
take taji itama tanason kasancewa É—aya daga cikin matan da ake É—auka a motocin,domin a taimaka musu,waige waige ta farayi na inda zata hango inda ake siyar da irin kayan dan ta siya itama
Carab idonta ya hango mata wani boutique daga can nesa dasu kaɗan, ayko da sauri ta miƙe ta nufi gurin domin siyan irin tufar da ta gani a jikin waincan matan.
Muje zuwa
Maman Yusuf
[7/2, 08:47] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*Follow me on whattpad@zahrasurbajo*
*pure moment of life writers*
*page 19-20*
Gudu gudu sauri sauri Ummu take yi har ta ƙarasa boutique ɗin.
Da sallamarta ta shiga,da yake ba musulmai bane ba wanda ya amsa mata,sema binta da ido da sukayi azatonsu ma mahaukaciyace.
Ido Ummu tashiga warewa tana kallon kayan dake ciki,can ta hangi wata riga ayko seta musu magana da fulatanci akan tanason rigar,ayko gaba É—ayansu suka kwashe mata da dariya,dan basu san me tace ba.
Wata sassanyar murya taji daga bayanta cikin harshen fulatanci tana mata magana,da sauri Ummu ta waiga inda ta jiyo muryar,wata kyakykyawar budurwa ajin farko ta gani zaune akan kujera tana mata murmushi.
Sosai Ummu taji daɗin ganinta sabida itama sanye take cikin irin shigar,dan inba idon Ummu bane yay mata ƙarya ba, to da tace shigar wannan budurwa tafi ta kowacce acikinsu muni, dan kayan dake jikinta daga kan na shanunta se gabanta kawai suka rufe amman sauran jikin duk ana gani.
Cikin harshen filatanci budurwar tacewa Ummu.
"Ƙanwata me ya fito dake da daddare haka?sannan waccan Rigar da kikeson siya me zakiyi da ita? ko ke matar aurece?".
Idon Ummu ne ya kawo ruwa sharewa tayi sannan tace.
"Ni ba anan nake ba mota na hau kawai ta kawoni nan,kuma ni ba matar aure bace,inaso in siya ne in saka inyi kamar yadda kikayi sabida nima masu motocin can da suke taimaka muku nima su taimakamin".
Ta ƙarasa zancan cikin kuka.
Dariyace ta ƙwacewa wannan budurwa cikin dariyar tayiwa sauran na shagon bayanin da Ummu tai mata ayko suma gaba ɗaya dariyar suka sa, sun jima suna dariya sannan sukayi shuru.
Budurwarce taci gaba da magana.
"Ƙanwata ay ko kin siyi Rigar bazata miki kyau ba sabida ke yarinyace baki da cikar halittar da Rigar zata miki kyau,sannan wa'incan da kike kallo ba taimakonsu ake yiba kasuwace in masu motar suka zo wacce ta musu ita suke siya seta shiga su tafi,dan haka ko kinsa kinje bazasu zaɓe kiba".
Abunka da bafulatanin mutum ay gaba É—aya tsorone ya kama Ummu najin cewa siyan matan dake gurin akeyi.
Budurwarce tace.
"ya sunanki ?"
"Ummu Aymana"
"Da kyau,ni kuma sunana Husna,amman anan kowa da Ƴarfillo yake kirana,ni ƴar Garin Yola ce karatu ne ya kawoni nan Garin".
Ido Ummu ta bita dashi kawai dan bata jin zata faÉ—a mata daga inda ta fito.
Ƴarfillo ce taci gaba da cewa.
"Ban taɓa yin taimako ba a rayuwata amma yau na tsinci kaina da son taimaka miki,sede kuma ni ba yanzu zan tafi Gida ba, dan nazo gwada sa'a tane nan,akwai wani ɗan sarki da yake wucewa tanan duk bayan wata uku,to sometimes yana tsayawa anan ya ɗauki wacce zata tayashi kwana dan baya iya bacci seda mace a kusa dashi, to na jima ina zuwa amman ban taɓa sa'ar ganinshi ba, sabida ina zuwa a makare shiyasa yau na fito da wuri,dan haka kimana addu'a Allah yasa ya zaɓeni in ya zaɓeni kema zakiji daɗi dan zan ba wata ƙawata ke ta kaiki Gidana seki dunga yimin shara da gyaran Gida ina biyanki".
Farin cikine ya bayyana akan fuskar Ummu da sauri tace mata.
"Allah yasa ya zaɓe ki in kuma ya zaɓeki Allah yasa daga kanki ya gama zaɓar wata kuma har abada".
Jin daÉ—in addu'ar da Ummu tamatane yasa ta rungume Ummun sede tudun goyon da taji a bayan tane yasa tayi saurin sakinta gami da É—aga hijab É—in Ummun,Jaririne yake ta faman shan baccin shi hankali kwance.
"Ummu Aymana Jaririn waye a bayanki?".
Cikin kuka Ummu tace.
"Ƙanina ne".
"Ƙaninki kamar ya?ina Mamanki take da zata barki ki fito mata da Yaro?".
Kwashe labarinta tayi kaf ta sanar da Ƴarfillo amman bata faɗa mata sunan Garinsu ba.
Sosai Ƴarfillo ta tausayawa Ummu da Ƙaninta dan har kuka seda tayi,gyarawa Ummu goyon tayi da kyau suna cikin hakane suka jiyo ƙarar motoci alamar Ɗansarkin yazo, da sauri Ƴarfillo taja hannun Ummu suka nufi gurin dandazon karuwan.
Duk inda ƴarfillo ta wuce sede kiji ana tsaki badan komaiba sedan tafisu kyau da haɗuwa,zuwansu gurin ba jimawa tawagar Ɗansarkin ta ƙaraso, nanfa mata aka shiga gyarawa ko za'a dace.
Motocine guda biyar huɗu iri ɗaya se ɗaya daban,guda huɗun baƙaƙene Range Rover new model se ɗayar kuma fara Bugatti.duka baƙin glass ne ajikin motocin,suna ƙarasowa gurin parking sukayi ba kuma wanda ya fito,zuwa can se wani mutum ya fito a ɗaya daga cikin baƙaƙen motocin kai tsaye inda su Ummu suke tsaye ya nufa,yana zuwa gurin ƴarfillo yaje yace mata.
"you are lucky, yallaɓai yace ki biyoni".
Yana gama magana ya juya ya tafi,Ƴarfillo wata shewa tayi yayin da sauran karuwan suke jin haushinta hannu Ummu taja zuwa gurin Shema'u Duniya ƙawarta, tana zuwa cikin sauri tace.
"Don Allah ki kaita Gidana gobe zan miki manni inna dawo".
Bata jira amsar ta ba tajuya tanufi motocin Ɗansarkin, tun kamin ta ƙaraso wani ya fito ya buɗe mata bayan motar da Ɗansarkin yake ciki ta shiga ya kulle suka ja motocin suka bar gurin.
Shema'u Duniya Ranta a ɓace taja hannun Ummu suka nufi Gidan Ƴarfilon, ta kai Ummu Gidanne badan komai ba sedan tasan Ƴarfillo bata ƙaramar kyauta.
Suna zuwa Gidan tayiwa Maigadi bayani shi ya buɗewa Ummu ƙofar falon ta shiga ita kuma Shema'u Duniya ta juya ta wuce.
Maman Yusuf.
[7/2, 20:11] Zahra surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*follow me on whattpad @zahrasurbajo*
*pure moment of life writers*
*page 21-22*
Shiga cikin falon tayi ta nemi guri ta zauna tana kalle kalle alamun ƙauyanci,kwanto ƙaninta tayi a baya wanda shima ya tashi daga bacci yanason abinci amman hasken daya gani ya hanashi yin kuka sede turo harshe waje da yake yi.
Kwantar dashi tayi tafara neman inda zata ga abinci ko ruwa,a tsorace take zaga gidan har Allah ya kaita dinning area,tsyawa tayi tana kallon kulolin dake jere kan dinning É—in batasan ko menene amfaninsu ba amman haka kawai taji tana shaawar ganin meye a cikinsu.
Ƙarasa tayi gurin hannu tasa da niyar ɗagawa se kawai taga ta buɗe dayake baa kulle ba ande kawai ɗora murfinne,ganin abincine aciki Ummu batasan sanda dariya ta ƙwace mataba ɗauko kular tayi gaba ɗayanta ta dawo falon ta zauna.
Har zata soma cin abincin se ta tuno da ƙaninta fasa ci tayi ta miƙe ta koma inda ta ɗauko kular dubawa tayi tsgani ko zata sami abun bashi,flaks ɗin data gani akan table ɗin ta ɗauka jin shi da tayi da nauyine yasa ta fara kici-kicin buɗeshi har de Allah ya bata saa ta buɗe,murfin flaks ɗin ta tara sannan ta,juyo abinda ke cikin flaks ɗin,damammiyar costard ne tasha madara amman dayake Ummu batasan ko meye ba ɗan dangwalowa tayi a hannunta ta ɗanɗana jin ɗanɗanonta ne yasa ta amince ƙaninta ze iya sha batare data cutar dashiba.
komawa tayi gurinshi ta ɗaukeshi tafara bashi ayko bawan Allah jin,sabon ɗanɗano ay tuni ya buɗe baki yana amsa,bata ƙyale shiba seda ta fahimci ya ƙoshi sannan ta kwantar dashi itama taci abincin ta ɗanɗanon da taji har addu'a tayi akan Allah ya bata irinshi a Aljanna,tana gama cin abincin tafara neman gurin alwala amman bata ganiba haka ta haƙura ta dawo falon ta rungumi ƙaninta tana tunanin inda Allah kuma ya jehosu.anan bacci yay awon gaba da ita da Ƙanin nata.
Ƴarfillo.
shigar ta motar keda wuya taji wani sassanyan ƙamshi wanda bata taɓa jin irinshi ba,dubanta takai gun Ɗansarkin wanda ke kwance a lungun kujerar motar yana latsa wayarshi,bata iya ganin fuskarshi sabida rufe take cikin rawani idonshi ma sanye yake cikin baƙin glass,maana hannunshi kawai take iya gani.
matsawa tayi kusa dashi ga mamakinta se taga ya É—aga mata hannu alamar dakatarwa batare daya kalli inda takeba,jiki a sanyaye ta koma gefenta ta zauna cike da mamakin wannan bawan Allah,dan ita de tasan duk cikakken É—an barikin daya É—auketa tun,a mota yake fara wasanni da ita amman taga wannan ko kallo bata isheshi ba.
Basu É—auki wani lokaci me tsayiba suka iso guest house É—inshi,faÉ—in haÉ—uwa da tsarin gidan ze É—aukemu tsawon lokaci bamu gama ba.
Koda suka isa ƙofar Ɗansarkin aka fara buɗewa yafita,seda ya jima da fita sannan aka buɗewa Ƴarfillo ƙofa ta fice itama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar ɗansarkinne yamata jagora zuwa ɗakin dayake,amman kamin su barta ta shiga seda suka amshi wayarta da jakarta sannan sukayi serching ɗinta sosai suka tabbatar daga ita se kayan jikinta take sannan suka bata izinin shiga,shigar ta ɗakin seda kanta ya kusa juyewa sabida tsabar haɗuwar ɗakin,ga wani ƙamshi na musamman dake tashi a ɗaki dubanta takai kan doguwar kujerar dake ɗakin,jikake tim ƴarfillo ta faɗi ƙasa