Showing 42001 words to 42465 words out of 42465 words
ƴarfillo zatayi ummu bazata mance taba,dan haka ummu na kallonra ta shida ta da sauri tanufeta ta rungumeta tana faɗin.
"mummy kece kika dawo haka?"
Aruɗe ƴarfilli tabi ummu da kallo se alokacin ta ganeta,kuka tasa tana neman gafarar ta,itama ummun kuka take tana faɗa mata ta yafe mata.
koda Ayman ya ƙaraso yagansu a haka beyi mamaki ba dan yasan akwai tsaftatacciyar soyayya a tsakaninsu,sharrin fiddah da na shaiɗanne kawai yashiga tsakaninsu,dan haka jan ummu yayi zuwa mota sannan yadawo ya tura ƴarfillo zuwa bayan motar ta shiga yasa keken nata a boot yaja motar suka dawo gida.
koda ƴarfillo tagane sunyi aure harda ɗa ba ƙaramin daɗi tajiba,cigaba tayi da neman gafararsu su kuma suka yafe mata.
wata biyu tsakani,suka ɗaga zuwa ƙasar egypt inda zaayiw ƴarfillo ƙafar roba,anyi mata cikin nasara inda Ayman yanarkar da dukiya me yawa dan amata me kyau dan ya faranta ran ummu,ayko anyi matan,sarai take tafiya akanta.
Tun tana iya godiya har tazo ta kasa sede kuka,tsoron Allah ne yakamata sosai,tashiga tubarwa Allah akan abinda ta aykata abaya.
Daga egypt saudiyya suka wuce da ita,acan ta duƙufa neman gafarar Allah tana kuka .
koda suka dawo nigeria,har yola suka kaita gurin ƴan uwanta suka basu haƙuri,irama ta nemi yafiyarsu suka yafe mata,taci gaba da zama a yola tana roƙon yafiyar Agurin Allah.
Itama fiddaj tasamu dakyar da taimakon ummu Ayman ya yafe mata,inda ahalin yanzu tayi aure,agidan gomnan sokoton,inda take auren gomnan.
Salmab itama,tayi danasanin shawarwarin data ba ƙawarta,har sokoto taje ta nemi gafarar fiddah ta yafe mata.
ummu ce kwance akan gado Ayman namata tausa ita kuma tana masa shagwaɓa.
cikin wasa tace masa.
"se wani matsamin kake da ƙarfi salon na tsufa da wuri ka auro wata ko?"
Dariya Ayman yayi yajawota jikinshi ya rungume,ya raɗa mata a kunne.
"Hayati inda ke arayuwata,duk sauran mata mazane,ke kaɗaice macen danake kallo a matsayin mace,ba tsufaba ko mutuwa kikayi zanci gaba da sonki har ƙarshen numfashina,akanki nasan so akanki narufe"
Mirginowa tayi sosai itama ta rungumeshi tana dariya,shima dariyar yakeyi ya ƙara da cewa.
"Ummu Aymana ta Ayman,mummyn Abu ayman,sirikar Abu Ayman,fara me farar aniya,anbuga dake anbarki kainuwa dashen lillahi"
"Kai qurratu ayni wannan kirari haka kode fadanci kakeyine"taƙarasa maganar tana dariya.
"Hhhhh ashe kingane,gaisuwace da roƙon iri"yafaɗi sanda yakamota yafara ayka mata sakonni na maaurata.
*ALHAMDULILLAHI*
*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH ME KOWA ME KOMAI,TSIRA DA AMINCI GA ANNABIN MU MUHAMMAD S,A,W*
*ANAN NAKAWO ƘARSHEN WANNAN LITTAFI NA UMMU AYMANA KUSKUREN DANAYI ACIKI ALLAH YA GAFARTAMIN,ABINDA NAYI DAIDAI ALLAH YABANI LADAN,ALLAH YASA SAƘON DANA TURA YA ISA GURIN WAINDA YADACE,ALLAH KUMA YASA MUDACE AMEEN*
*KU BIYONI CIKIN ƳAR BAUTAR ƘASA*
*TAKU HAR KULLUM,ZAHRA SURBAJO*.
Masha'Allah, Allah yaƙara basira da hikima
Mun yaba sosai bisa wannan namijin ƙoƙarinki a cikin wannan littafin naki ummu aymana,
Allah yasa mu amfana da fadakarwa da kikayi a ciki,
Daga ɗaya daga cikin dubannin masoyan wannan littafi
Muhammad Kabiru,Admin na mk, hausa novels group.
08160112181.
Sai munji sabon littafinki dake hanya.fatan alkhairi.