Showing 15001 words to 18000 words out of 60852 words
Chapter 6 - 'YAR BARIKI Book 1 Complete Writing by Rufaida Umar .txt
kai baice uffan ba ya fita. Sai gashi dauke da akwatin kayanta da kuma dardumar dake cikin motarsa. Ajiyewa yayi kawai ya koma gefe ya tsaya domin son ganin ikon Allah. Ga mamakinsa sai yaga ta fiddo Hijab zunb'ulele ta sanya. Baki ya saki har lokacin bai bar jifanta da kallon mamaki ba. Ta lura da hakan,murmushin dai ta k'ara yi mishi a karo na ba adadi. Batace komai ba ta soma kokarin shimfid'a dardumar da hannunta na hagu wanda baya ciwo,saidai ta kasa. Ba zato taga hannuwansa sun kama mata. Ta dubeshi,bai ko kalleta ba. Yana gama shimfid'a mata ya kauce.
"Nagode."
Ta furta a sanyaye. Salloli uku dake kanta ta rama,kafin ta zauna ta kwararo addu'o'i tana hawaye. A karshe ta shafa. Tana shirin mikewa,aka soma kiraye kirayen sallar Isha'i,wannan yasa Haris ficewa zuwa masallaci.
Itama ta gabatar da sallar isha,ta had'a da shafa'i da wutri. Nan ma addu'ar tayi ta shafa duk da irin radadin da hannunta keyi bata k'i d'agashi ba yayin addu'a.
Anan kan darduman ta zauna,kafafuwanta a mik'e tana mai jingina kanta da bango. Bata fi mintuna ba,Haris ya dawo da sallamarsa. Bakinta ya motsa alamun amsawa. Ya zauna a gefen gadon kafin ya soma magana
"Nayi iyakar taimakon da nake ga ya dace nayi gareki a matsayinki na 'yar uwa a musulunci dana sameki rai a hannun Allah na kawoki asibiti. Alhamdulillah,tunda har sauki ya soma samuwa zan tafi. Ga wayoyinki nan..."
Ya sanya hannu a aljihu ya fiddo mata su gami da ajiyewa a gefenta.
"Kina iya kiran d'aya cikin abokan harkarki,anan babban asibitin kauyen danbatta kike. Batun motarki kuma,gaskiya ta samu matsala,amma tana nan a police station na nan gefen asibitin(inji ni.. Lol)idan yaso idan kun tashi saiku janyeta ku koma. Na barki lafiya."
Ya sanya hannu ya fiddo bandirin kud'i na 'yan d'ari biyar biyar ya ajiye mata. Caraf ta riko hannunsa,da sauri ya dubeta. Hawayen da yaga tana fitarwa ne ya sanyaya mishi jiki. Ta narkar da fuskarta tana mai marairaice murya
"Kada ka gujeni a wannan yanayin da nake ciki don Allah Haris. Babu wanda zai taimakeni kamar kai,babu mai bani kulawar daka bani. Da ace kasan inda na nufa yanzu,da bazaka barni ba har sai kayi kokarin sadani da muradina."
Ya dauke hannunsa ya koma ya zauna yana dubanta baice uffan ba.
"Duk tsawon rayuwata a Bariki,ban tab'a cin karo da mutumin da yayi kokarin yimin fad'a akan wani abu na daga bakar rayuwar dana zab'arwa kaina ba,sai kai Haris. Ban taba fahimtar kuskuren da nakeyi ga rayuwata ba sai a wannan lokacin dana kusan mutuwa ba tare dana kai ga neman gafarar Ubangijina ba game da b'arnar dana jima ina aikatawa ba."
Ta tsagaita gami da sanya hannunta marar ciwo ta share hawayenta kafin ta dubi Haris wanda ya zuba mata ido kawai yana sauraronta,auna maganganunta kawai yakeyi a zuciyarsa. Wai gaskiyarta take fad'a mishi ko kuwa dai barikancin ne ya dawo kanshi?
"Da wuya ka aminta da zancena,saidai don Allah ina neman alfarma agareka,ka taimakeni kada ka barni anan. Ka amince na taso mu tafi?"
Ta karashe tana karya wuyanta gefe idanunta a kansa. Ya tabe baki kafin ya girgiza kansa
"Ni ba d'an BARIKI bane,saidai na karanci halayyarku. Ki sani, Allah ba abin wasa bane. Yanzu idan kikace zakiyi karya da sunanSa,zai iya hukuntaki. Ba don ni zaki tsorace shi ba Tasneem. Ban hanaki aikata masha'arki ba. Saidai wannan hatsari daya sameki ya kamata ya zamto izna gareki,da ace mutuwa ta riskeki a daidai wannan lokacin,wane guzuri kika tanada da har kike ganin zai tseratar dake daga azabar Allah?"
Ya k'ara girgiza kansa,bakin ciki karara da kuma tsana ya bayyana saman fuskarsa.
"Kuna ganin cinyewa ce ga diya mace ta fad'a yawon barikanci! Kuna kallon lamarin a matsayin wayewa,alhalin babu abunda zaku tsinta ciki nan gaba sai bakin ciki idan kuwa har mutuwa ta riskeku ba tare da kun tuba ba,hakika zakuyi nadama irin wacce baku tab'a yinta ba a duniya. Babbar DARAJAR DIYA MACE,shine ta kasance a d'akin mijinta. Babu mutunci a zamowarta tamkar wata kasuwa da kowane kara da kiyashi zai shiga."
Ya dakata sakamakon sheshshekar kukan Baby Tasneem daya cika d'akin. Gaba daya a rayuwarsa ya tsani kuka,musamman ma na d'iya mace. Yanzu yanzu ne zaiji zuciyarsa ta karaya,wannan ya sanyashi mikewa da sauri ya nufi hanyar fita.
"(No Haris, please don't leave me alone,please!)."
Baiko juyo ba ya fice daga d'akin. Kuka sosai Baby takeyi,babu abunda take tunanowa sai rayuwarta. Ji takeyi tamkar tayi tsuntsuwa ta ganta a gaban mahaifiyarta kwance a jikinta. Dakyar ta share hawayenta.
Kasancewar cikin magungunan da nos ta bata harda na bacci,ya sanya ta soma hamma. Tun tana korewa har dai ya dauketa anan kan dardumar ba tare data shirya masa ba........!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(21)
Sanyin asuba ne ya farkar da baby. Duk shaidanci irin na Baby,bata wasa da sallah. Ta mike tana mutsistsika ido. Sai lokacin ta tuno abunda ya afku. Tausayinta kanta ya mamayeta,ta mike ta zagaya bandaki.
Ta jima tana addu'o'inta kafin ta mike ta dauki wayoyinta ta hau kan gado. A sannu ta shiga sarrafata tamkar bataso. Missedcalls din Kb har shida a Mtn dinta dinta,hakanan a Airtel dinma missedcalls har goma. Text message kashi kashi harda na whatsapp,duk tambayar tana ina. Ta samu missed calls daga Momi ma da kuma kawayen nata. Wato su Manal. Sai sauran wadanda ta daukesu matsayin tarkace. Murmushi tayi kafin ta kashe wayar gaba dayanta. Ta kurawa silin ido bata da niyyar bacci. Tunanin Haris ya fado mata, yanzu dagaske shikenan ya tafi ya barta? Hawaye suka kwaranyo mata, haka tayi ta tunane tunane kafin bacci na ba zato ya saceta.
**** BAKWAI DA MINTUNA(7:00AM)
Turo kofar da akayi gami da sallama ne ya farkar da ita daga baccin da takeyinsa ba don dad'i ba sai don kawai yana fisgarta. Idanuwa ciki ciki take dubansa,daman ya lumsassun idanuwanta suke a farke ballantana kuma akwai bacci cikinsu. Ta k'ara lumshesu tana murmushi duk a zatonta mafarki takeyi ba gaske bane. Saida ta k'ara jin sautin ajiye leda a kusa da 'yar dirowar gefanta,tayi firgigit ta bud'e ido ta zuba mishi.
Fuskarsa a daure tamau babu alamun dariya,kallo daya yayi mata ya dauke kansa,baice da ita komai ba ya fice. Bayansa tabi da kallo tana murmushi kafin ta cije lebbanta.
Tabbas Haris yana da tausayi,mutumin kirki ne sannan Ustaz ne na hakika kuwa kamar yanda Kb ya shaida mata. Bata tab'a tsammatar yana nan asibitin ba bai tafi ba sai a yanzu daya shigo. Ta mike ta janyo ledar,murmushi tayi ganin jug dauke da ruwan shayi da batasan daga inda yazo ba,saidai yayi mata kama da sabo. Sai kayan shayin. Mikewa tayi a sannu,zuwa lokacin banda hannunta da take fama dashi babu kuma sauran wani ciwon dake addabarta. Wanka ta soma yi kafin tayi daura kirji ta fito. Kayanta ta dauka a akwati ta koma bandakin ta kimtsa cikin riga da siket 'yan kanti,bakak'e anyi musu kwalliya da fari da bulu. Ta yafa mayafin (pashmina) a kanta,saboda dukkan kayanta bata da wadataccen mayafi kwata kwata. Tana shirin ninke wanda ta cire ne nos ta shigo. Suka sakarwa juna murmushi,kafin nos ta ajiye kayan aikinta akan gadon.
"Sannu madam,bari na taimaka maki. Ai yanzu kada kice zaki dunga wahalar da hannun nan naki,ki bishi a sannu har ya warke."
Ba musu baby ta zauna tana dubanta yayinda take linke mata kayan. Cikin siririyar muryarta ta jefo mata tambaya
"Don Allah na tambayeki mana."
Nos ta juyo tana dubanta
"Inajinki madam."
"Wannan yayan nawa daya kawoni yana nan har yanzu?"
Ta danyi dariya
"Yana nan madam,ai bazai iya tafiya ya barki a wannan halin ba. A masallaci ya kwana yanzu haka ya sanya a wanke mishi motarsa da alama dai yau zaku wuce don likita yace zai iya baku sallama a yau."
Baby ta gyada kanta,ita kanta ta k'agu tabar wajen nan,don ma dai babu laifi,suna kula da tsaftar asibitin nasu. Tana kallo nos dinnan ta k'ara yi mata dressing na hannunta tare da yin allura,sannan ta fice bayan ta gargadeta akan tasha magungunanta.
Ta hada shayin kad'an tana tunanin ko Haris ya karya? Ta daure ta ci ta sha.
Daidai lokacin da take b'allar magungunanta zata sha,ya shigo da sallama likita yana biye dashi. Duk iyakar kokarinta na ganin sun had'a ido bai yarda ba,gashi sai faman d'ad'd'aure fuska yakeyi. Hakan duk ya sanyayar da jikinta.
"Sannu ko? Ya jikin?"
Ta maida dubanta ga likitan,wanda ba shine wanda ya dubata da farko ba. Dakyar ta iya amsa mishi
"Alhamdulillah."
Ya aunata kafin ya duba takardunta sannan ya dubeta
"Akwai inda keyi maki ciwo?"
Girgiza mishi kai kawai tayi domin a zahiri hankalinta yana ga Haris dake danne danne a waya. Batasan dalilin daya janyo bata gajiya da dubansa ba. Haka kawai ya zame mata tamkar farin wata,wani irin kyau da kwarjini ya k'ara yi mata. Zancen likita ya katse tunaninta a inda ya dubi Haris
"Alhamdulillah,zamu iya bata sallama yanzu. Jikinta yayi sauki sosai. Saidai ta kula da shan magunguna hakanan kada ta takurawa hannunta da aiyuka."
"Ok."
Daga haka suka fice tare da Doctor din.
Kafin tayi wani yunkuri,wayarta ta soma k'ara. Ta duba,Kb ne. Dauka tayi tana mai karawa a kunnenta batace uffan ba.
"Hello,hello babyna. Kina jina? Don Allah kiyimin magana kafin na fita a hayyacina."
"Na'am,ina sauraronka Ka..."
Ta gaza k'arasawa sakamakon shigowar Haris. Ya dubeta ta dubeshi kafin ya dauke kai ganin yanda tayi yanayi da marar gaskiya. Akwatinta kawai taga ya bude zif dinsa,ya dauki kudaden daya bata ya sanya mata ciki. Sannan ya dauke dardumarsa yayi gaba tare da akwatin. Ranta yayi sanyi.
"Hello,me kike cewa ne?"
Sai sannan ta tuno da ashe fa waya takeyi
"Look kabir,yanzu ba lokacin magana bane. Zan nemeka."
Ta kashe wayar gaba dayanta. Tana shirin mikewa ya dawo,ledojin magungunanta ya dauka sannan ya ajiye mata silifas dake a hannunsa sabbi fil. Har yakai k'ofa yayi magana tamkar bayaso
"Kina iya tasowa."
Ya ficewarsa,ta mike ta sanya silifas din tana murmushi. Komai na Haris burgeta yake, a tun ranar data soma ganinsa.
*****
A harabar asibitin ta hangoshi yana kokarin mikawa wani kud'i da alama dai shine wanda yayi mishi wankin mota. Kallonta da yayi ne ya sanyata soma tafiyar nan nata mai kama da yanga ta nufeshi bayan ta dauke idanunanta a kansa. Zagayawa yayi ya shiga motar, itama ta zagaya ta shiga gidan gaba. Ribas yayi ya fita daga asibiti
"Barka da asuba Haris."
"Barka. Ya jikin?"
Ya fad'i tamkar dole akayi masa,
"Alhamdulillah,na samu sauki sosai."
Baice uffan ba,kai tsaye police station dinnan ya nufa. Anan baby taga motarta a ajiye.
"Ina zuwa."
Ya fice, magana taga sunyi da wani sanye da kayan 'yan sanda kafin ya fiddo kud'i ya bashi. Sai kuma taga sun zaro waya,Haris na magana mutumin yana kwafa hakan ya fahimtar da ita cewar lamba ya bashi. Tayi tsai tana dubansa,ta tsani yawan kallo,batayi hakanan batason ayi mata. Amma menene da Haris wanda ke daukar hankalinta ga kallonsa.
"Kefa banza ce, keda ake ganin kin fita daban ko cikin kawayenki da sauran hadaddun 'yan barikin da kuke tare. Menene na yawaita kallon wanda a kyau babu abunda zai gwada maki?"
Zuciyarta ta kwab'eta,wannan yasa ta gyara zamanta ta maida dubanta ga gabanta. Saidai kamar jan idanunta akeyi,sai gashi suna komawa ta gefe gefe suna duban Ustaz Haris. Ganin ya taho yasa ta daure ta sunkuyar da kanta har ya bud'e motar ya zauna. Sai anan ya dubeta....!
'YAR BARIKI
©Rufaida Omar(Hannu da Yawa Writers)
(22)
"Zan mik'a ki tasha. Idan yaso saiki hau mota ya k'arasa dake. Nima naje ga abunda ya kawoni."
Bai saurari cewarta ba yaja motarsa ya soma tafiya.
"Nagode da taimakonka gareni,fatana Allah Yasa zumuncinmu ya..."
Kallon daya watso mata ne hanata k'arasawa. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta murmusa
"Wai har yanzu ba'a bar fushi dani ba? Ya dace kayimin uzuri,tunda kaji nace maka nayi na damar ayyukan da nake aikatawa wanda daman tilastani akayi,toh iyakar gaskiyata na fad'a maka. Ban iya rantse rantse ba,nafiso mutum ya yarda dani. Banga wanda zan yiwa karya ba Haris, ba halina bane."
Ta kauda kanta gefe tana wani d'an tunani,shi kuwa nanata maganarta yakeyi. Tilasta ta akayi tayi karuwancin kamar ya? Haka yayita juya maganar,zuwa yanzu zai so yaji tarihinta saidai bayason yiwa mutum shishshigi a sha'anin rayuwarsa.
"Baka tambayeni inda zanje ba?"
Ta jefo mishi tambayar tana dubansa da wannan shu'uman idanuwan nata. Ya dan kalleta babu laifi ya dan saki fuska kad'an.
"Mahaifiyata zanje gani."
Baisan sadda yayi mata duban mamaki ba,tana murmushi yayinda hawaye suka kwaranyo mata ta gyada mishi kai
"Eh Haris,mahaifiyata zanje gani. A yau bana bukatar komai sai ita. Rabona da ita shekaru uku kenan."
Ya shanye mamakinsa yana maida dubansa ga titi
"A wane gari kenan?"
"KAZAURE."
Ya gangara ya sauka gefen titi,bayan mamaki daya bayyana a saman fuskarsa har da d'an murmushi. Haka kawai yaji dadin kasancewarsu 'yan gari guda. Ita kam kamar a mafarki haka take ganin murmushin da yakeyi gareta. Wannan yasa ta dan lumshe ido ta budesu domin tabbatarwar,saidai har zuwa lokacin basu gushe ba.
"Menene ya baka mamaki na kasancewata 'yar Kazaure?"
Yabar kallonta,fuska a sake yace
"Kasancewata d'an Kazaure shiyasa nayi mamaki."
Itama baby ta d'an bude ido cike da mamaki kafin ta langab'ar da kai tana marairaice murya
"Daman garinmu d'aya amma kake kyamatana?"
Yayi tsai yana dubanta,ita kam wayewar har tana neman yi mata yawa. Yanayinta ne a haka ko kuwa dai tsabar kwarewa a bariki ne?
Ya kauda wannan tunanin ta hanyar fad'in
"Ban tsanar dan uwana musulmi saidai na tsani wani hali nasa. Me kikayimin da har zan tsaneki Tasleem? Hakikanin gaskiya gurb'atacciyar rayuwa irin wacce kikeyi ne na tsana,bana kaunar dukkan mabiyanta. Babu wani burgewa a cikinta face tsantsar nadama a karshe wanda wasunku ma alokacin komai ya k'are maku babu damar tuba. Ki godewa Allah da akwai sauran numfashinki,yaci ace kinyiwa kanki fad'a da karatun ta nutsu. Kisa misali idan da ace ya zamto mutuwa ce ta riskeki yayinda kikayi hatsarin nan,wani guzuri zaki tafiyarwa Ubangijinki dashi da kikejin ya isheki kufcewa azabobinSa?"
Ta share hawayen da tun soma maganarsa suke ambaliya,idanunta yana ga kallon titi tace
"Nasani dukkan abunda ka fad'a babu k'arya aciki. Hakika rayuwar dana zab'arwa kaina ba rayuwa ce ta abun tutiya da tak'ama ba. Rayuwa ce tamkar ta dabbobi,inda mutum yake da damar yin kowane kalar sab'o ba tare da tunanin makomarmu ba. Na tafka kuskure a rayuwata Haris,saidai kamar yanda na fad'amaka,tursasani akayi."
Tun soma maganarta idanunsa ke kanta,maganarta ta karshe ta chanja yanayin duban da yake mata zuwa na rashin fahimta.
"Har ila yau,bangane manufarki ba Tasleem. Daman akan tursasa mutum ya sab'awa umarnin UbangijinSa shi kuma ya amince yabi?"
Tayi murmushi mai ciwo,ta jinjina kanta
"Bacin rai da bakin cikin kazafi da akayiwa mutum bada hakkinsa ba,ya sanyani fad'awa wannan yanayin. Abun bakin cikine ace makusantanka sune basu yarda dakai ba,har suke gaskata sharrin makiyanka. Meyasa wannan bazai dameni ba? A halitta irin tawa,na kasance mai saurin fushi da zuciya. Duk da cewar inada saurin sauka kamar yanda wasu suka fad'a,saidai na rasa yanda akayi na kasa barin abunda ya faru ya wuce a rayuwata. Babu wanda na tsana tamkar mahaifina,duk duniya babu wanda yafi bani mamaki kamar d'an uwana da muka fito ciki d'aya dashi."
Ta tsagaita ta dubi Haris wanda shima idanunsa ke kanta cikin rashin sanin inda ta dosa da maganganunta.