Showing 24001 words to 27000 words out of 52381 words
"Wayyoooo Abba Mamana zafi" ta faɗa tana ƙara ƙanƙame jikinta gaba ɗaya ta rasa wanne abune hakan, Ya Heemu na son mayar da ita ƙwallon wasan sa..
Shi ko kunyar haÉ—a ido da ita ba yayi, da wanne ido ma zai kalli Arman ta fahimci Ya Heemu sam bai san kunya ba, haka kuma gaya gudun abin kunya..
Shi baya son farin ciki a rayuwarsa ne? Banda haka ƙarami yaro kamar Ya Heemu me zatai dashi, me zai ɗauke mata, gaba ɗaya nawa yake a shekarun yana jin zai iya ɗauke dukkan buƙatun rayuwarta ne?
Miƙewa tayi bayan taci kuka ta ƙoshi kamar ƙaramar yarinya riga tasa body Short mara hannu ta fesa parfume tare da ɗaure kanta ko dinner ba tayi ba ta haye bed ta kwanta, tana ƙarasa karanta SIRRIN MU domin Littafin da yazo ƙarshe sai yafi daɗi, tana zuwa ƙarshen Labarin taga Announcement na sabon littafin Anty Ni'ima mai suna *ABU_MALEEK* labarin mai tsayi ne domin zai je book 1, 2,3 littafin na kuɗi for 500 for vip, 300 for regular, sosai tai mmki domin a yadda taji tsarin labarin da kuma sabbin abin da yake cikinsa ta ɗauka zai je 1k ko 2k murmushi tayi a fili tace "Nimcyluv i like your attitude kinyi taku" Sharp-Sharp ta shiga acct ɗinta taiwa Nimcyluv transfer 5k just for appreciate, Domin littafin SIRRIN MU ba ƙaramin daɗi yay ba, amma duk wannan daɗin da yay a hakan Nimcy tace bai kama ƙafar ABU_MALEEK ba. Ganin bata jin bacci sam sbd tashin hankalin da take ciki kuma bata ƙaunar damuwa tai tasiri a ranta sai kawai ta fara karanta SAI NA AURETA littafin Nimcy na farko wanda ta fara na kuɗi.
Ya Heemu na zuwa gida ya tarar ba kowa a parlo da kuzarinsa yake taka ƙafafuwansa zuwa part ɗinsa har lokacin kuma hannunsa a ɗaure yake.
Kai tsaye bathroom ya shiga ya zare singlet ɗin ya tara hannunsa a sink ruwa ya fara zuba, kana ta sanya detol ya shiga wanke hannayensa yana dirzawa, yana gamawa ya sakarwa kansa shower ruwa ya shiga ratsa jikinsa yana dukan baƙar fatarsa wacce har hasken baƙi take, yana gamawa ya sanya kayan a washing machine kana ya wanke bakinsa tass ya shiga busar da gashin kansa da abin gyaran kansa. wasu nightwear masu kyau da taushi ya ɗauka company Panjams White colour, gaba ɗaya rigar daya sanya tun daga wuyansa har zuwa ƙirjinsa a tsage take, wandon kuma gaba ɗayansa iya guiwa ne.
Bayan ya gama ya sanya bedroom sleeper suma white ya nufi kitchen ɗin dake part ɗinsa ya haɗa coffee mai zafi, yana ƙoƙarin kai coffee ɗin bakinsa yaji wani a zabar zafi, tsaki yaja kaɗan tunawa da Moha da yay he hate her wlh gaba ɗaya Yarinyar sam bata da kunya, kamar wacce aka sangarta.
Parlo ya koma ya zauna kana ya ɗauki remote ya sauya channel zuwa Aljazeera ya fara kallon labarai domin abinda yafi kalla kenan, sai kuma kallon Ball musamman idan ABU_MALEEK ne zai gabatar da wasan gayan ya iya buga ƙwallo.
System ɗinsa ya buɗe yana buɗewa ya samu abinda ya bari da sauri ya fice a wajan a fili yace "Ƴan iska" kai tsaye ya fara operating system yaci gaba da binciken da yake domin soon yake son gabatar da komai, domin tuni ya rubuta dakardar sauya muƙami daga Chief of Army zuwa Captain Khalel Sha'aban.
Washe gari tun da safe Mannal ta gama shirinta na barin garin zuwa Kano, domin dukkan abinda zai sanya ta haÉ—u da Ya Heemu yan zun kam gudunsa take.
A hankali ta fara sakkowa daga upstairs zuwa downstairs tana sanye da wani light purple É—in lace mai White É—in Flowers, anyi mata nrml É—inkin duguwar riga mata brest_cup sai stones da aka jera mata a saman wuyan rigar har zuwa baya, rigar ta É—an buÉ—e hakan ya baya faffaÉ—an west É—inta damar juya son ransa ba tare da takura ba.
Ta sanya nrml passion ɗin neakless da ear-ring fuskarta fayau ba zaka taɓa cewa ta kwana tana kuka ba, ta murza ɗaurinta na gaban goshi bayan ta sauke gashinta a ƙasan wuyanta, hannunta riƙe da Iphone 12 max pro.
Cikin nutsuwa ta gama sakkowa tana nufar dinning area, cak ta tsaya sbd jin ƙamshin turarensa tsoro da fargaba suka saukar mata, haka nan taji bata yarda ba ƙilan abinda ya faru jiya yasa ta kejin hakan.. kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna, abin mmkin tana zama taji tamkar ta zauna inda turaren yake, Arman dake zaune yana cin soyayyan dankali with vegetables source ya kalli mahaifiyar tasa shi kansa yana mmki ace ita ta haifesa shiyasa da yawan friends ɗinsa basa yarda sai sun tambayi Ya Heemu, ajjiyar zcy ya sauke kafin yace "Ina kwana Mumy?" A hankali ta ɗaga kanta tare da watsa masa Idanunta wanda sukai jaa kana ta ɗauke tana jan mug domin haɗa tea shi kawai take tunanin zata iya sha, cikin jan ajin daya zama jikinta tace "Yaka tashi hope ba wata matsala" Arman yace "Yes Mumy, Mgnar matsala kuma kin san akwai" tana zuba milk tace "Ok dear ina jinka" ya marai-raice fuska yace "Mumy how can you imagine life without you a gidan Abba, and ba wannan ba tayaya kike tunanin zan iya jure ganinki a gidan wani bana Abba ba, dan Allah Mumy ki koma sbd ni da kuma soyayyar da kike min" tunda ya fara mgn take shan tea ɗinta a hankali tana rufe idanunta, Yes tana son Abban Arman amma ta ina zata fara? Zata ƙasƙantar da kanta ne Just sbd she want come to him, this is difficult abu ne mai wahalar gske haka kuma bashi ya buƙaci hakan ba.
Jin tayi shiru ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa kamar zai kuka yace "You're my mother kinfi kowa sanin soyayyyar da nake maki Mom! Dan Allah sbd ni, ban san mene matsalar ki da Abba ba, amma koma mene ina son ya zama tarihi ko koma kamar da asalin masoyan Gsky, Mom! Yanzu duk kwalliyar ki da iya girkin da tsaftar ki sai dai wani ya mura?" Kamar daga sama taji saukar Muryarsa yana faɗin "Kai kuma kana baƙin ciki" girgiza kai Arman yay yace "No Ya Heemu is not like that, kai ma zaka tayani kishin Abba ai,dan Allah kasa baki" Mannal kam tuni tayi suman zau ne, da sauri ta juya ta kalli inda yake no wonder ashe yana left hand ɗinta shiyasa gaba ɗaya ƙamshin sa ya gana gundirarta, yana zaune kai ba zaka taɓa cewa shi yay mgnar ba sbd yadda ya ɗauke yana duba wayar hannunsa, yana sanye da wasu blue ɗin suit, wanda sukai masifar haska baƙar fatarsa ya manna wani baƙin glasa a idanunsa ba zaka taɓa cewa ga halin da yake ciki ba.
Ɗauke kai tayi Uncle yay dry yace "Ya Heemu baku gaisa da Mumynku ba" idanunsa akan Wayarsa yana tsotsar strowbeery a bakinsa cikin tattausan Muryarsa mai kwarjinin gske irin ta ƙasaitattun maza yace "Mrng Mumy" Mannal wani baƙin ciki ya kamata ganin kallon da Uncle ke mata yasa tace "Ibrahim Ya gida" ajjiye wayar yay gaba ɗaya ya juya gareta yace "Mmy i miss You so much baki ko nemana" ya faɗa yana bata side hug kan Uba ta faɗa a ranta lallai Ya Heemu bashi da kunya ji yadda yake acting like duk abinda yake faɗa Gsky ne, Khausar tace "Ya Heemu kwana biyu Mmynka sai addu'a" ɗan Murmushi dole tayi kana a hankali ta ɗan rungome sa tare da shafa fuskarsa tace "Sorry Heemu na" tayi hakan ne domin ta nuna ta fishi iya tsiya, Arman yace "Mmy ni ko kiss ɗin da kike min a kumatu kin dai na" Ya Heemu na ɗan ɗauke kai tare da juyar da kansa dai-dai fuskarta yana aikata mata da wani kallo mai kashe jiki kafin a hankali yace "Nikam yanzu za'a rama min" zare ido tayi shima ya zare mata nasa idon yace "Ohhh!! Mom" runtsa idanunta tayi ta ɗura bakinra gefen baƙar fuskarsa ta masu small kiss, tana shirin ɗauke fuska yasa tattausan softness hands ɗinsa ya riƙe fuskarta mai taushi da laushi sai ƙyalli take yace "Ohhh Ya rabb! Uncle Mom cewa idanu take ne?" Uncle yace "Waya sani, tunda ta rabu da mijinta take cikin damuwa" Shiru Ya Heemu yay gani ta haɗe rai tamau fuska ba walwala dai-dai kunanta yace "Get ready, Soon you're going to be Mrs Ibrahimul Khalel Sha'aban the richer young man" yana faɗin hakan ya zame fuskarsa yana taɓe baki kafin yace "Allah ya dai-dai ta" da sauri Arman yace "Amen Ya Heemu, Abba ma yace kije office ki samesa kuyi mgn" Ya Heemu ya ɗauki wyarsa ya ɗura a kunne kafin ya ɗan ɗaga Murya yace "Don't ever try to go" sarai tasan da ita yake kallon Arman tayi tace "Ok My son" tana faɗin haka ta miƙe ko tea ɗin bata gama sha ba, upstairs tayi Uncle ya bita da kallo kafin yace "ita wannan halan bata san ta girma bane, shekaru sama da 40 ba wasa ba fa" Murmushi kawai Khausar tayi Arman kuma yay waje yana faɗin "Ya Heemu bari naje" ko inda yake Ya Heemu bai kalla ba sai da ya fice sannan Ya ɗan kalli Uncle yace "zan amshi abu gun Mumy" yana faɗin hakan yay upstairs yana ɗan shafa ƙirjinsa tana tsaye a parlon sama sai kai koma take tana ɗan yarfe hannu. Buɗe ƙofar yay ya shigo bata juya kamar zata ari baki tace "Ya Heemu ka fita a idanuna, idan baka da kunya ni ina da ita" waje yaja ya tsaya yana Kallonta yana kuma jin me take faɗa, wajansa ta ƙarasa inda yake tace "Let's talk Ya Heemu, dan Allah dan Annabi mene yasa kake haka, kai baka san cewa Namiji ne wanda yake da ikon samun dukkan matar da yake so ba, look at you Son, kana da kyau hankali ilimi ga kuɗi kaga ko ƴar sarki kace kana so billahi zaka samu...," Saurin kai tafin hannunsa yay saman bakinta hakan yasa bata ƙarasa faɗin abinda tayi niyya ba, matsawa yay sosai kamar zai shige jikinta ɗaya hannunsa ya ɗura west ɗinta daga baya ganin tana ƙoƙarin faɗuwa, fuskarsa dab da ta ta, ya shiga sauke mata numfashi yana fesar da iska daga bakinsa kamar bazai ce komai sai kuma yace "Hate me or love me baya tsarin Khalel ina son amincewar ki, kisan cewa idan nayi niyar auran ki koda baki so sai nayi, why kike ƙoƙarin wahalar da kanki Mumy? Am your son, and you're my Mom dan haka period sunayen mu zasu sauya daga haka zuwa miji da mata, ki dai na wahalar min da kanki" hannu tasa zata hankaɗa sa amma ko motsi bai ba, sai ma ƙara matse ta da yayi yana kallon tsakiyar idanunta wanda ya karanci ƙarancin rashin baccin dake damunta, ganin bashi da niyyar sakinta yasa ta sakar masa kuka ya riƙesa tare da tura fuskarta ƙirjinsa shiru yay domin babu wata ƴar mace data taɓa samun so close to him kamar Mannal, sai Moha wacce sai yaci ubanta yay mata doka taga babu sarki sai Allah shi ne take maƙale masa, sosai Mannal take kuka tana dokan Ya Heemu shi kam bai san me ake ba domin bai wani iya rarrashin mace ba, hasali ma kukanta bai damunsa ko kaɗan, ganin yadda take kuka wanda ya tabbatar daman ta daɗe tana tara kukan bata samu damar inda za tayi ba ne, sai yanzu da ƙirjinsa ya zame mata mafaka, sosai take kukan a wannan lokacin baƙin cikin abinda Abban Arman yay mata ya dawo mata sabu fil, ga rashin kirki da yaywa Dad ɗinta amma duk da haka zuciyarta shi take muradi tasha try kiransa amma kullum idan ta kirasa dry yake mata yana faɗin ta rasa mijin aure tsuhuwar mace like her babu wanda zai aureta, dan haka idan tana son ta koma gidansa dole sai tazo ta durƙosa akan ƙafafuwanta ta basa hqr akan idon ɗan ta, hakan zai sanya ya ƙara wanke laifinsa tunda ya shaidawa Arman cewa ita tace ya saketa.
🤔ANYA YA HEEMU ZAI SAMU DAMAR AURAN MANNAL KOWA? TEAM MANNAL ME KUKACE?
TEAM MOHA AND YA HEEMU BAN MANCE DAKO BA INA SANE DAKU KUN SAN CEWA NIMA INA TEAM ÆŠIN KU MANNAL OLD WOMAN CE KAMAR YADDA ABBAN ARMAN YA FAÆŠA.
*SIRRIN MU*
YA ZAMA COMPLETE DUCOMENT BOOK 1 2, DUK MAI SO ZAI BIYA 500 TA WANNAN ACCT NUMBER 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616💃�🌚
11/30/21, 9:04 AM - Ummi Tandama😇: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*AURAN FANSA*
NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv
🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
19-20
Wani kuka ne ya kwacewa Mannal Lokacin data gama tuna irin ɗibar albarkar da Abban Arman yay mata, wani baƙin ciki da take kaici da keji.
Ace mutumin da tafi ƙauna fiye da kowa idan ka ɗauke ta mahaifinta shike nuna mata rashin daraja, mijinta Uban yaronta Arman gashi dalilin wulaƙanci da yay mata har hakan na sawa ɗan cikinta yace yana sonta?.
Yau Ya Heemu ke mata abinda yaga dama abinta a mafarki bata kawo wannan bare a zahiri? Ɗan yaro kamar Ya Heemu har yashe ya gama girman ta gama yi masa wanka ta goyashi a gadon bayanta, ta bashi abinci yay mata tunbuɗi yay mata tsari amma yau shike mgnar yana son auranta? Ina sam ba zata iya wannan abun kunyar ba ta auri Ya Heemu tace ta auri me? Yay mata me? Bayan shi kanshi ta raina sa banda shirme shida Arman mene suka iya? Yadda take kukan sosai iya ƙarfin ta sai riƙe Ya Heemu take sbd yadda take jin zcyarta na zafi tana harbawa kamar zata fito waje.
Idanunsa ya buɗe kaɗan yana kallon yadda take kukan kana ganin kukan kasan bawai iya na yanzu bane, ta daɗe tana tarawa kuma tana neman inda zata sanya kanta tayi kukan wanda zai gamsar da zcyrta, hakan yasa faffaɗan ƙirjinsa ya zame mata mafaka.
Ƙara matsota yay sbd zafin da ƙirjinsa ke masa.
Bai san yaya ake ba bai san kuma ta inda zai fara ba, sam sam bai san yadda zai rarrashi mace ba, baya ƙaunar yaga kukan mace, amma a yanzu kukan Mumy yaushi ma yake basa, ya ɗauka Moha ce kawai mai baki kuka sai gashi yaga kakar Moha na kuka da Dukkan ƙarfinta kasa mgn yay sai hannunsa kawai daya sanya a bayanta ya shiga bubbuga bayanta alamar rarrashi can maƙoshinsa yace "It's okay Mumy na!" ya faɗa yana janyeta daga jikinsa, hawayen fuskarta ta share tass tai kamar batai kuka ba sai �oyayyiyar ajjiyar kawai da take saukewa a fakaice.
Cikin ƙarfin hali da juriya irin na jarumar mace wacce bata son ko kaɗan aga rauninta ta tsare Ya Heemu da gajiyayyun idanunta wanda sukai ɗan ja kafin ta ɗan cije baki tace.
"look at you! Gaba ɗaya baka gama kaiwa minzinlin wanda za suce suna son aure ba, bare har kayi tunanin yi, amma kai ne za kazo kace kana son...," Baƙin cikin ƙarasa maganar take sai kawai ta ɗauke kanta tana mai fesar da iska daga bakinta.
Juyawa tayi ta fara ɗaukan Vail ɗinta kana ta ɗauki sauran abunta ta ɗauki trolley dinta ta fara janta zuwa baƙin ƙofa, ta ɗauki niyyar a yau komai dare sai tayi aure da dai ta zauna wannan ɗan cikin nata ya tuzarta.
Ya Heemu kam ko buɗe idanunsa bai ba bare ya san abinda take aikatawa, haka kuma dukkan Mgnar da tayi yay watsi da ita a gefe da baya son iyaye Yes! Yasan Mumy a haife ta haifesa domin idan bai manta yanzu shekarunta kusan 47 a yadda take faɗa to yanzu suna ƙarshen shekara kenan gab take da shiga shekara ta 48, taɓe baki yana ɗan shafa ƙirjinsa sbd tunawa da yay gaba ɗaya shi bai huce 22, kenan ta ninninkasa a shekaru da komai ma.
Da ace zata san dalilin auranta da sam bata tsaya tai masa dugun surutu ba infact ma zai iya sakinta idan buƙatarsa ta biya.
Jin ƙarar buɗe ƙofa yasa ya buɗe idanunsa tare da saukesu a kanta, tayi rolling kanta da Vail hannunta riƙe da hand-bag ɗinta sai phone ɗinta ɗaya hannun kuma tana janye da trolley ɗinta.
Mumy nada ƙiba mai ɗaukan hankali mara muni hakan yasa duk kayan da zata sanya suke bala'in yi mata kyau..
Gata ƴar wanka sam bata yarda da ƙazanta ba, kullum cikin gyara jikinta take da mgani masu kyau irin na gyaran brest, da taushin fata ga yawan shan fruits masu gina jiki, gashi tunda tayi ɓarin nan tasa akai mata ɗinki kullum cikin kula da wajan take tana shan maganin matsi dana Ni'ima badan komai sai tunanin wata rana zata iya komawa gidanta wajan mijinta abin alfaharin ta.
Kallonta yay yaga fuskarta cike annuri ko kaɗan baza ka taɓa cewa tayi wani abu wai shi kuka ba, ta haɗiye dukkan ɓacin ranta ta barshi a Zcy, cikin takon ƙasaita cike da kuzari da nuna shi ɗin Namiji mai cikakken iko wanda yake zaune akan ra'ayinsa idan yace zai yi ba shakka sai yayi dan haka a nasa ɓangaren shima ya ɗauki alwashi sai ya aureta no matter what happen!.
Tana ƙoƙarin buɗe ƙofa yay saurin sanya tattausan hannunsa ya riƙe trolley dinta da sauri ta kallesa fuska ba walwala ba tare kuma da tace komai ba tasa hannunta saman nasa da niyyar zame hannunsa yay saurin riƙe hannunta yace "Uhm sai ina?" Banza tai masa bayan ta zame hannun nasa ta buɗe zata fita yay saurin sanya hannunsa ya danne ƙofar idanunsa ya cilla cikin nata ba tare da shakka ko fargaba ba yace "Tabbas ni Ibrahimul Khalel zan nuna maki na haifu wlh billahi sai na aurenki idan ki kaga hakan bai faru ba to Tabbas sai dai HUKUNCIN ALLAH!" hannu tasa ta wankesa da mari buɗe ido yay sosai this is the first time da aka taɓa marin baƙar fuskarsa mai cike da haiba da Kamala, kafin ya ƙara wani tunanin ta ƙara sauke masa wani marin cikin warning ta shiga nunasa da hannu tace "You're mad Khaleel, idan ƙwayar da ake baku wajan aiki tasa kake min haka to You