Showing 9001 words to 12000 words out of 52381 words

Chapter 4 - AUREN FANSA Book Complete Document by NIMCY.txt

04 Dec 2024

3870

cutar ƙarya yake dan kawai Ya Heemu ya dawo yazo ya gansa, Ya Heemu cikin gidan ya shiga ya samu Matar Baffa Inna tana kallonsa tace "Oyoyo ga mijin ya dawo" zare mata manyan idanunsa yay tare da ɗan ware mata hannayensa, baya taja tace "Kufa a ƙidar turawa ta gama ratsa ku meye kuma runguma da tsakar rana haka?" Fararan idanunsa yaja ya rufe yana taune leɓansa kamar bazai magana ba yace "Ashe dai ba matar gaske bace" Inna tace "I naji ba komai Allah ya nuna mana rai da lfy sai na ɗauki baƙaƙen yaranka,dan inda kake baƙin nan babu macan da zata aureka sai baƙa kamarka" Zama Ya Heemu yay saman lallausan ladduma yana tanƙwashe ƙafafuwansa yace "Kice dai masu kama dake kikeso" ƙwaɗon zogala Inna ta ajjiye masa wanda yaji Tumatir da Albasa, ruwa ta zuba masa ya wanke hannayensa tassa kasancewar baya cin abinci da Spooy Bisimillah yay ya fara cin ƙwaɗon zogalan, Wannan dalilin yasa keson gidan Baffa yana son ƙwaɗon zogalan sosai, yana gamawa ya wanke hannayensa ya miƙe tsaye yana Shirin fita wasu ƴan mata na shigo yanayin kamaninsu zai sanya kace duk jini ɗaya ne, da sauri suka ja baya suna zare ido da ƙyar Hanna tace "Ya Heemu ina yini" banza yay mata idanunsa akan Moha wacce ta turo baki gaba tace "Ina yini" fiddo da manyan idanunsa waje yay yace "Ke dan Ubanki sa'an ki ne ni? Shegiya da fuska kamar karass" turo baki tayi tace "Ni ai fara ce kuma.." bata ƙarasa ya nufi inda take tsaye da gudu tai cikin gidan tana ihuu "Wayyoooo Inna" jikinta duk rawa yake tasan halin Ibrahimul Khalel sarai yanzu zai ball da ita, waje yay yana fidda siririn tsaki a zcyarsa yana faɗin "Shegiya mai duk ya ɓata fuska" ko yaushe ta shafa man tsabar rashin kirki irin na Ya Heemu kawai farar fata Allah ya bata irinta Safa, da wannan tunanin yay waje Excorts ɗinsa na ganinsa suka sara masa da sauri suka buɗe masa ƙofar motar ya shiga fuskarsa kamar hadari ba alamun fara'a gaba ɗaya motocin suka fara bin layi tare da barin unguwar.


Arman zubewa yay saman Sofa yana sauke wahalallan numfashi he can't believe abinda idanunsa haka gane masa, abun har gizo yake masa ya kasa gogewa daga cikin idanunsa, ƙarar motar mahaifin nasa yaji da sauri ya miƙe ya nufi part ɗinsa, yana barin Parlon Abban Arman na shigowa ƙamshin turarensa kawai yaji ɗan nasa ya dawo kuma dawowarsa bata rasa na saba da auran da yay, shima bai damu da ganin Arman ɗin ba dan bashi da abinda zai faɗa masa, kai tsaye upstairs ya haura yana sakin Murmushi, yana zuwa ya kwanta saman bed zcyarsa fess har yanzu ɗanɗanon bakin Safa yana nan zaune daram a bakinsa, wayarsa ce ta fara ƙara ganin sunan Mannal yace "zaki gane baki da wayo wallahi sai na rama iskancin da kikai min" yana faɗin haka yana Answering call ɗin, daga can ɓangaren Mannal tana cikin wasu haɗaɗɗun ƙana nan kaya tai fess da ita idan ka ganta baza ka taɓa cewa ita ta haifi Arman ba, tana sanye da 3gauther sai half vest kyawawan brest ɗinta wanda suke tsaye cirrr babu alamar zubewa a cikin half vest kasancewar bata sanya bra, fuska ta marai-raice tare da turo baki gaba tace "Wai irin baka damu da dawowata gida ba?" Dry mata yace "Why? Meyasa zan damu kuma?? Bayan ina tare da samuwar matata dall a kwali, ai Mannal kinyi kuskuren ko mata biyu nai niyyar aura i can sbd ina da halin yi kin gane" juya idanunta tayi tama rasa abinda za tace Sbd damuwa ga wani zillo da gudan jinin ta ke mata a ciki tace "Abban Arman ni kake gayawa haka? Wane ya faɗa maka baƙin ciki nake da auran Safa da kayi? Hasali ma ban ɗauke ta kishiya ba, kawai nai haka ne sbd kare mutun cin kai na" dry ya ƙarayi yace "Au har wani mutucin gareki? Look! Ina sonki bai taɓa yiwa wata ƴar mace son da nake maki ba amma dole ne na rama abinda kikai min dan haka kije na sakeki saki biyu" ƙirjin ta ne ya buga da ƙarfi tana son mijinta domin shi ne sukai aurane saurayi da budurwa, bakin ta na ɗan rawa idanunta tuni sun cika da hawaye cikin rashin fahimta tace "Me...me kake cewa ne hak?" Hannu ya wara irin ke kika sani ɗin nan kana yace "Ni kada kimin ihu kije sai sanda na nemeki nasan babu wanda zai iya Auranki a haka kin zama cusss, Ni Da kaina yau na tsinke igiyoyin aure na guda biyu a kanki enjoy yourself Mannal Haidar Babagana" ɗiff jinta da kuma ganinta ya ɗauke sakin wayar tayi idanunta a rufe ta fara lalubar hanya harta ƙarasu bakin strains cikin rashin Sa'a ƙafarta ya goce ta fara gangarowa ƙasa, shigowar sa garin kenan yazo duba muhimman aiki a nan Kano, cikin nutsuwa da kamala haɗi da jarumta yake taka ƙafafuwansa jin shiru kuma yay yawa a gidan yasa ya ɗan ƙara turo kansa ciki, tsaki ya saki ya juya zai fita ya fara jiyo ihunta tsayawa yay cak, sai kuma ya juyawa da wani mahaukacin gudu ya nufi wajan strains ɗin tana gaf da faɗuwa yana ƙarasawa ya zube a ƙasa ta sauka a jikinsa, numfashinta na sama idanunta na rufewa ta riƙesa sosai sbd a zabar ciwon da marar ta take mata dubansa yakai zuwa kayan dake jikinta fiddo idanunsa waje yay sbd ganin jinin dake zuba, da ɗan zafin nama ya miƙe da ita gaba ɗaya a jikinsa buɗe ido tayi bakinta na rawa tace _"Ya...Ya Heemu!!"_ sai kuma numfashinta ya cakk.






🤕🥲As my wish and your wish gashi nan nayi, wlh billahi idan babu COMMENT da SHARE na ajjiye rubutasa tabbas, kuyi share ɗinsa please fisabilillahi zuwa grp 🤙�🤙�🤙�🤙� idan naga haka akwai hot page gobe, idan kana son grp na ka amince zakai share da comment chat me up https://wa.me/+2348119237616








Sarauta
11/30/21, 9:02 AM - Ummi Tandama😇: *AURAN FANSA*


_��9-10_


SHARE fisabilillahi🤲�


Kallon yadda jikinta ya saki Ya Heemu yay ga kuma jinin dake zuba daga jikinta, bai tsaya jiran komai ba ya Miƙe da ita a jikinsa kai tsaye ya nufi hanyar fita daga shashin nata, yana gab da fita daga babban Parlo yaci karo da Anut Lubna kallonsa tayi da mmki tace "Ya Heemu me kuma ya samu mahaifiyar taku?" Da gajiyayyun idanunsa kawai ya kalleta ba tare da yace komai ba sanin ba lallai yay mata mgn yasa tace.
"Ok barta a nan bari na kira Family Dr namu"
Fararen idanunsa ya juya ya kalli Anut Lubna dasu kana ya kalli Mannal dake jikinsa sai kawai ya fice da ita da sauri ba tare daya aikata abinda Anut Lubna tace ba.
Yana fita Excorts suka miƙe kallo guda yay masu suka ja baya tare da bashi waje, da kansa ya sanya (Mumy) a baya kana ya amshi key car da wani irin speed yaja motar tare da barin gidan gaba ɗaya.
*Aminu teaching hospital*
A nan yay parking nurses da yawa suka zagaye motar sa tare da gadon marasa lafiya, yana tsaye yana lumshe idanunsa tare da fesar da iska daga cikin bakinsa time to time hakan shafa lafaffan cikinsa, yana kallo har suka nufi Emergency room da ita.
Cikin nutsuwa da kamala ya juya zai shiga reception wanda daga nan zai ƙarasa emergency room ɗin da aka nufi Mumy dashi yaji hayaniyar mutane, tsayawa yay cak tare da juyawa a hankali ƙara ware manyan idanunsa yay sbd wanda ya gani abun har mmki yake masa, ba aikin sane bane kama masu laifin amma a yau zai fara domin idan tunaninsa ya bashi dai-dai wannan shi ne guy ɗin da suka jima suna nema.
Fesar da iska yay da sauri kuma ya zaro lafiyayyiyar wyarsa cikin ƙwarewa ya fara latsa ta.
Not too long yay dailing wata number, ringing É—in farko akai pic sauke numfashi yay idanunsa akan mutumin a hankali cikin bada umarni yace "Uhm, You guy's duk inda kuke kuzo nan" ya faÉ—a yana gaya masu inda yake a yanzu yana faÉ—in haka ya buÉ—e motarsa tare da cilla wayarsa ciki.
Fuska ba walwala kamar ko Yaushe ya fara tafiya inda ake hayaniyar yana zuwa yaja ya tsaya tare da kallon wani da yake cewa.
"Wannan mutumin duk sanda yazo Asibitin nan sai an nemi jariri sabuwar haihu an rasa, yanzu haka wani babyn ya ƙara ɗauka dan ban yarda da wannan jakar ta bayansa ba" .
Ɗaya mutumin yace "Haba Musty ance zato zunu bine baka da hujjar faɗin haka ai,tunda ba'a taɓa kamasa da jariri a hannu ba" kafin Musty yay mgn wani mai suna Omar yace "Haba Lawan, ai kallo ɗaya zakaiwa mutumin kirki kasan cewa na gari ne, kana kallon Wannan bawan Allan kasan cewa shi ɗin student ne, ka kalli shigar mutunci da kuma kamala a tare da shi" Wanda aka kira da Lawan yace "Uhm! Ɗan yau ne fa? Nidai wlhe ban yarda da shi ba" Wanda ake ta mgn a kansa yana tsaye sai raba ido yake,sanye yake da riga da wando na shadda ruwan madara ya ɗura hula a kansa ga kuma handcovers ba wasu littattafai a hannunsa yace "Nifa nazo practical ne a wannan Asibitin ne ba wani abu ba" taɓe baki Ya Heemu yay domin duk surutun su ya cikasa ga wani bacci daya keji.
Tashin farko ya ƙara ware manyan idanunsa akan guy ɗin yace "What's your name?" Kusan mutuwar tsaye matashin yay domin sai yanzu ya kula da Ya Heemu ha faɗa girman halittar jikinsa ya zautar dashi ga kuma kwarjininsa.
Lokacin ɗaya kuma ya fashin ci wani Ya Heemu, juya kai ya fara ya rasa me zai ce ta ina kuma zai fara, A karo na biyu Ya Heemu ya saki Murmushi wanda kana ganinsa kasan cewa bai saba yi ba wannan ba iya jajayen laɓɓansa ya tsaya, Cike da kuzari ya ɗauko I.D card ɗinsa ya nunawa matashin yace _" Ibrahim Khalel Muhammad Jalal my name"_ sai kuma yay Shiru tare da jan numfashi ya ɗura da faɗin _" It's my I.d card I'm the chief of Army staff (COAS)_ dan haka last question what's your name and where is your I.d card?" Gumi ne ya fara yan kowa matashin ya juya ya kuma juyawa yaga dai no way da zai gudu dan haka yace "Sunana Anas anace min Nas" sai kuma yay Shiru Ya Heemu kallonsa kawai yake domin duk wani jami'in tsaro kallo guda zaiwa Nas ya san cewa bashi da gsky.
Ganin kamar Ya Heemu baya ganinsa yasa ya ɗaga ƙafa zai gudu cikin zafin nama Ya Heemu ya ta ɗesa tare da riƙe hannunsa ya lanƙwasa bayansa nan take hannun Nas yay ƙara ƙassss alamar karyewa, wani ihun a zaba Nas yay a dai-dai lokacin kuma Sauran Soldiers wanda suka kasance Excorts a wajan Ya Heemu suka ƙarasu wajan, kai tsaye jakar bayansa Ya Heemu ya cire tare da miƙawa na kusa dashi yace _"Check it_ da sauri ya buɗe jakar abunda ya gani ba ƙaramin tsora tasa yay ba domin jariri ya gani wanda ko cibiya ba'a cire masa ba, an ɗaure masa baki da plaster sai ɗaga hannu yake sbd Numfashinsa da baya fita sosai.
Captain Daniel yace _"Oga it's a Baby"_ Ya Heemu sam bai mmki sai kallon Nas da yay yace "Wa kakema aiki?" Shiru Nas yay Ya Heemu ya ƙara cafkar ɗaya hannun nasa nan take shima ya karye cikin tsawa Ya Heemu ya ƙara maimaita masa tambayar bakin Nas na rawa zai faɗi wanda ya kewa aiki nan aka sakarwa Nas harbi a gadon bayansa.
Da sauri Excorts É—in Ya Heemu suka fidda guns É—in su abin mmki ba mai harbi sannan ba alamar ta inda harbin ya fito.
Ya Heemu kallon gawar Nas yay da sauri ya juya zuwa cikin motarsa dan harga Allah ya kanta cewa Mumy (Mannal) ya kawo asibiti, kai tsaye hanyar Abuja ya É—auka ba tare da Excorts É—in ba,su kuma Excorts É—in gawar Nas suka É—auka suka nufi headquarter Kano ita.


Lokacin da aka shigar da Mumy cikin room ɗin kai tsaye Dr dake dubata ya gano matsala, da ƙyar ya samu jinin ya tsaya amma duk ƙoƙarin da yay sai da gudan jinin ta ya fita, daman ba wani ƙwari yay ba dan haka tuni cikin jikinta yabi jini shima ya fice, drip suka sanya mata tare da blood suka ɗauki dai-dai jininta, daman Ya Heemu yace suyi mata komai duk abinda ya dace.
Anut Lubna da mmki tabi Ya Heemu da kallo idan da sabo yaci ace tuni sun saba da halin Ya Heemu, amma a yau sai taga kamar bashi ba.
Cire komai tayi na mmkin Ibrahimul Khalel ta É—auki key car É—inta ta shiga mota kai tsaye Hospital É—in ta nufa dan tasan ba lallai ya kaita wani ba.
Bata wani sha wahala ba ita special room ɗin da aka kwantar da ita, tana kwance samɓal ruwa da jinin na shiga jikinta a hankali, cike da tausayinta Anut Lubna ta ƙarasa wajanta tare da zama a gefenta, sosai taji tausayin Mannal musamman da likita yay mata bayanin ɓarin da Mannal tayi.
Wayar Anut Lubna ce ta fara ringing da sauri ta É—auka ganin sunan _MY HEART_ Na yawo akan screen É—in wayar.
Answering call ɗin tayi cikin ƙasa da murya tace "My heart Baban Mannal fatan ka kwantar da hankalinka, babu abinda ya samu gudan jininka sai ƙaddara" daga can ɗaya ɓangaren yana cikin mota dattijon mutumin mai shigar kamala da haiba kana ganinsa kasan shi ne Mahaifin Mannal sbd kamar da sukai cikin nutsuwa yace "On my way dear zan zo naji abinda ya sanya farin cikin Nuraddeen damuwa" da mmki tace "Wai aikin naka ka bari ka tawo?" Murmushi yay yace "Kina wasa da mijinki dear, tayaya hankalin Nuraddeen zai samu nutsuwa bayan farin cikinsa na cikin ɗimuwa da tashin hankali? Ki bari tuni na siyi online ticket na dawo yanzu haka ina hanyar zuwa Asibitin" Jinjina girman so da ƙaunar dake tsakani uba da ƴarsa tayi kana tace "Allah ya dawo mana dakai lfy cikin Aminci" ya amsa da "Ameen" kana sukai sallama.


Ya Heemu kai tsaye Abuja ya nufa ransa a matuƙar ɓace, a yau ya ɗauki niyyar nemu dukkan mutanan da suke aikata irin wannan aikin dan haka zai ajjiye matsayinsa na Army staff ya koma nrml captain kamar kowa yadda zaiji daɗin binckensa hankali kwance da wannan tunanin yay parking motarsa a babban compound na gidan su, cikin nutsuwa yake taka ƙafafuwansa cike da jarumta kamar wani babban mutum nan kam ko 26 bai kai ba.
A parlon ƙasa ya samu Anut Meera kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, Murmushi tayi tace "Wlcm back son" haɗe fuska Ya Heemu ba tare daya kulata ba, Anut Meera na sane ta ƙara cewa "My son yaya akai naga ranka a ɓace?" Marai-raice fuska yay tare da dawowa wajanta da sauri yana zuwa ya zauna daf da ita tare da ɗura kansa a shoulder ɗinta cikin ƙasa da Murya kamar sangaltacce yace "Ke kam baki sanin ana ɗaga maki ƙafa uhm?" Dry Anut Meera tayi sosai tana shafa sumar kansa tace "Wacce ƙafa kake ɗaga min ɗan nan? Nida ka raina baka gani na matsayin Uwa bayan inda wacce ta kusa kamaka tsayi" lumshe idanunsa yay yana jin yadda take surfa masa mgn kana ya buɗe narkakkun idanunsa yace "Uhm ko? Nawa ne shekarun ƴar taki?" Kai tsaye tace "Moha wai?" Taɓe yay idanunsa akan jaririn hannunta mai kama dashi sak har baƙin yace "idan akwai wata bayan ita to" Murmushi Anut Meera tayi tace "A'a ita ɗaya gareni sai Lil Khalel, sai kuma Babban yayansu Ibrahimul Khalel" miƙewa yay tsaye yay ba tare daya kalleta ba yana tafiya yana faɗin "Soon or later zaki gane ina respect naki, banda haka babu wanda ya isa ya kalli idon Ibrahimul Khalel yace ya haifesa" yana faɗin haka ya haura upstairs kai tsaye ya nufi part ɗinsa,bai wani daɗe ba ya shirya cikin ƙananun kaya wanda suka amshi baƙar fatar jikinsa wacce take wani ƙyalli sbd baƙin ta, System ɗinsa ya buɗe nan da nan ya tura Muhimmin saƙo ta email ɗinsa, yana gamawa ya miƙe ya ɗauki lemon power horse a fridge ɗinsa ya fara sha a hankali yana lumshe idanunsa wanda suka ɗan janye sbd yanayin da yake ciki, a hankali ya kalli zanan Tattoo ɗin jikinsa kana ya lumshe idanunsa yana yadda mood ɗinsa ke sauyawa, banda shi babu wanda zai iya gane rubutun dake tsakiyar Tattoo ɗin da aka rubuta I&A shafa Tattoo ɗin yay kana a fili kuma yace _"My Shatuu"_ sai kuma yay saurin girgiza kansa shi kaɗai yasan me zcyarsa take raya masa, a duk sanda mutum ya sanya mace cikin lamuransa sai ya zama lazy very lazy ma weakness ɗin sa su bai yana a zahiri cikin ƙaramin lokaci a fahimci rauninsa,sam bai shirya hakan ba, saman bed ya faɗa tare da ɗaukan pillow ya rungome a ƙirjinsa. Ummi ce ta fito daga cikin part ɗinta ta samu Anut Suwaiba da Anut Meera zaune suna hira, kallonsu tayi tace "Ku shirya tafiya gida bikin an gama ai, Amarya kuma Ya Heemu zai kai ta" kwaɓe fuska Anut Meera tayi kamar yarinya tace "Nifa Daddyn Moha baya nan gsky sai na ƙara kwana Ya Ruma" Anut Suwaiba kuma tace "Ya Ruma nifa na tambayi kwana uku daman, kuma bani da matsala da mijina tunda mu biyu ne matansa dan Allah ki ramu damu" Murmushi tayi tana jinjina sakalcin ƙanan mijin nata tace "Bazan sake mgn mai maganin ku na nan ai" Anut Meera tace "Ai shi Ya Heemu matsala garesa, sai ta haɗewa mutane rai kamar shine gaba damu bayan muna da shekaru masu tazara" dry Anut Suwaiba tayi tace "Ai yana duba da ƙirar jikinsa irinta samudawa shiyasa yake bawa mutane umarni son ransa" Ummi murmushi kawai take masu dan ita kanta halin Ya Heemu mmki yake bata, Miƙewa Anut Meera tayi tace "Ya shigo yana ta zanyyana min surutu,yadda wani yana ɗaga min ƙafa ne" Ummi tace "To kada ku cinye min ɗa da baki ƙilan ko ruwa baku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login