Showing 33001 words to 36000 words out of 52381 words
ke zaki zauna dashi, a yanzu kuma nina zaɓa maki miji wanda zaiyi dai-dai da rayuwarki, na san har abada bazan taɓa dana sanin wannan auran ba koda ke zai zamana anyi maki ba dai-dai ba, wannan bai daman ba in dai ba wanda aka aura makin bane yace baya so"
Ita dai kanta a ƙasa amma sam bata gane komai abu ɗaya ta fahimta shi ne Dad ɗinta ya ɗaura mata Aure da Sufyan.
Kasa motsi tayi sai Ajjiyar zuciya da take saukewa, kafin ya ta É—aga kai tace
"Dad kana da ikon yimin komai, nasan cewa baka son Abban Arman amma soyayyyar da nake masa ne yasa ka amince dashi, Dad indai zaka samun albarka ka daina fushi dani na amince da Sufyan matsayin miji"
Tattausan Murmushi Dad Yay mata yana shan coffee É—insa ya kalli Anuty Lubna yace "My dear explain to her"
Yana faɗin haka ya miƙe tsaye tare da nufar part ɗinsa.
Shiru Anuty Lubna tayi sai kallon juna kawai da suke, jin shirun yay yawa yasa Mannal cewa
"ki faÉ—a min menene, me kuke hiding keda Dad?"
ÆŠauke kai Anuty Lubna tayi tace
"bada Sufyan aka É—aura maki Aure ba da Captain Ibrahimul Khalel ne"
Miƙewa tsaye Mannal tayi tana nanata sunan can kuma tace
"Kamar dai na san sunan amma waye haka nakasa fahimta waye ne Captain"
Cikin tausayi da kuma rashin adalcin da akai mata tace
"Chief of Army Ibrahimul Khalel Ibrahim, wanda a yanzu ya sauya matsayi zuwa *Flight Officer* ma'ana dai (Ya Heemu)".
Girgiza kai Mannal ta fara idanunta ya sauya kala fuskarta ta sauya kala tai jajir.
Jikinta ya É—auki rawa tana jin zcyrta a cunkoshe idanunta ya fara duhu yana janyewa, bakinta na rawa tace
"Khalel? Ya Heemu my son?"
Sai kuma tai baya ta faɗi saman kujera babu numfashi, salati Anuty Lubna ta sanya da sauri ta fara kiran Dad ɗin Mannal kafin ta ɗauki ruwa mai sanyi ta shiga sheƙa mata, Dad kam yasan za'a rina yasan dole za taji wani iri amma bashi da wani zaɓi wanda ya huce haka.
Yana da tabbacin wata rana zatai masa gdy wannan auran zata zo masa da yaran data haifawa ɗan riƙon nata kuma mijinta a yanzu.
Mumy zama tayi kamar mahaukaciya ta shiga ihu tana fasa dukkan abinda tayi karo dashi.
Fitowa yay cikin nutsuwa da kamewa haɗi da kwanciyar hankali amma fuskarsa a ɗaure take tamau ba walwala kamar baƙin hadari.
A karo na farko yana sanye da wani tattausan farin voyal fari ƙal mai manyan zane sumar kansa sai sheƙi take sai kwance har ƙasan wuyansa.
Ya zura Dukkan hannayensa cikin aljihun wandon kasancewar rigar half body ce mai ƙaramin hannu.
Kana ganin kuma farar singlet É—in dake jikinsa.
Sai baza ƙamshin turaren Arabian Ohud yake.
Duk abinda yake idanun Ummi a kansa da Anuty Meera wacce zuwanta kenan.
Sam bai kula dasu ba ya nufi downstairs zai sauka yaji Muryar Ummi tace.
"Ohh hello!"
Tsayawa yay tare da zaro hannunsa na dama yana É—an sosa kansa da key É—in motarsa.
Zama yay a armchair yana taune leɓansa tare da fesar da iska a tattaushe cikin sabuwar miskilar Muryarsa yace "Ummi"
Kallon tsaf tayi masa fuska ba walwala tace.
"Ashe baka da hankali Ibrahim? Ashe nice bani da hankali da nake tunanin kasan me kake?"
Lumshe idanunsa yay kana ya buÉ—e kamar bazai mgn ba yace "Ya rabb! Me Ibrahim yay da wannan sanyin safiyar Ummi?"
Haɗe fuska tayi tace "Kayi aure ba tare dana sani ba, amma ba wannan ne matsalar ba ace ka rasa wacce zata aura sai sa'ar uwarka? Kace kayi aure kenan? Kaga bana baƙin ciki da auran infact ma Am happy billahi amma wanne abu kayi me kaiwa Arman a matsayinsa na babban abokin ka? Wannan adalci ne ko mene ace ka auri mahaifiyar Amininka Goodness"
Ta ƙare maganar tana sauke numfashi sbd sam bata iya faɗa ba bata kuma jure masa.
Zamewa yay ya ɗura kansa saman cinyarta tare da kama hannunta ya ɗura saman sumar kansa Muryarsa bata fita sbd abinda ya keji a zcyarsa wanda yake fama dashi Shekara da shekaru baya jin kuma zai iya rabuwa da abun domin mganin abun ya suɓuce masa.
Cikin dakewa da juriya yace
"Ayyah! Ummi kada ki fara da haka ki shafa kaina ki sawa Ibrahimul Khalel ɗinki albarka, kada ki manta hakan ba kaifi bane domin shekaru number ce, kuma hakan bazai taɓa zama haramun ba, sau tari ni mutane suke haramta abinda ya zama halak ga mutane, miye laifin Ya Heemu dan ya auri age mate ɗin Umminsa, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama shima ya auri wacce ta girmesa kinga hakan ba laifi dan Allah Ummi kada kice komai ki sawa Abokin ki Albarka, kuma na wannan Auran...,"
Sai kuma yay Shiru Anuty Meera tana jan numfashi tace "Khalel kalle ni nan?" Kallonta yay yana jiran yaji ita kuma mene za tace
"Ina biye maka ne sbd sanin halinka, na sanka sanin da kai kanka baka san dashi ma, mai yasa a gabanka kuma akan idanunka kana ji kana gani zaka bari Aysuhtul humaira ta auri waninka ka sanya ido ka zama masu sheida aure ko?"
Miƙewa yay ba tare da yace komai da sauri ta Miƙe tace "mgn nake kana jina"
Ba tare daya kalleta ba yace "Ke ba'a gidan Mijinki kenan ba ne? To ita jiƙata zaki kisha da ba zaki aurar da ita ba?"
Gabansa taja ta tsaya idanunta cike da ɓacin rai tace
"Kai kasan a girme na girme ka, na kwana da sanin kana hana idanunka bacci akan zazzafar soyayyar da kakewa Moha, ko kuma so kake ka cutar da kanka akan abinda kake da iko akai? Nasan ciwon zcyr daya kamaka duk a dalilin Aysuhtul humaira"
Da sauri Ummi ta miƙe tsaye tana dafe ƙirjinta jikin ciwon zcy yasa hankalin ta ya tashi kuma ma wai Ya Heemunta keda wannan wahalallan ciwon.
Ya Heemu kam ƙuri Yay wa Anuty Meera da ido kafin ya ɗan taune bakinsa ya saka hannayensa ya ɗaga Anuty Meera cak ya matsar da ita gefe da sassarfa kuma ya fara taka strains ɗin yana haɗa bibbiyu.
Yana shiga motarsa Wayarsa tayi ƙara connecting yay da bluetooth cikin fesar da iska ya shiga danna wani mahaukacin horn kana yay waje da gudu yana faɗin "Uhm Wasallamu Alaika Dad"
Dad yana zaune yana jin yadda Mannal ke fashe fashe yace "Ibrahimul Khalel ka hanzarta zuwa ɗauka kan matarka, domin dukkan abinda data ƙara fasa min a gida kai ta ɗurawa nauyi domin saika biyani, idan ka ɓata lokaci kuma zaka zo ka sameta a waje"
Yana faɗin hakan ya kashe kira, wani ƙyakƙyawan tsaki Ya Heemu yaja domin shi ya gama da wannan shirin barin ƙasar yake ma, domin idan ya zauna Tabbas zcyarsa zata iya yin bindiga.
Amma dole ya zame masa ya É—auko ta tunda abu yake nema gareta.
Gidan Baffa ya nufa domin yi masa sallama, yana shiga yaga ba kowa tsakar gidan juya idanunsa yay kamar zai koma sai kuma ya nufi cikin É—akin Baffa a ciki ya samu Inna Shoona da Hannah sai Amatu budurwar Areef.
Idanunsa ne ya sauka akan Moha tana kwance jikin Baffa yana mata tofi yana shafa mata, jikinta gaba É—aya ya saki numfashinta na wani irin fita da sauri kallo É—aya yay mata yasan cewa ciwon ta ne ya motsa wanda ta gajesa wajan mahaifiyarta.
Inna tace "Yawwa Mijin yanzu ake ta ƙoƙarin kiran mijinta number baya tafiya wai yaje Zaria"
Bai ce komai ba ya juya zai fita sbd he can't wait any longer idan yace zai tsaya za'a iya samun matsala, salatin da Inna ta rafka shiyasa Ya Heemu jiyowa a 180 bai tsaya jiran komai ya sunkuce ta zuwa jikinsa ya riƙeta sosai jinta jikinsa yasa ta numfashinta ƙara sarƙewa ba kin Ya Heemu na rawa yace "No please Humairahhhhhh!" Sai kuma yay waje kai tsaye asibiti ya nufa da ita aka sanya mata drip akai mata injection yana zaune yana ganin Ummi dasu Kawo Shuriem na kiransa yaƙi ɗagawa daga ƙarshe kuma Alhj Al'mustapha ya kira shima yaƙi ɗagawa, ana gama yi mata komai har lokacin bacci take ya ɗauke ya nufi Kano da ita tana kwance a saman kujera ya ɗura kanta a cinyarsa.
Bai isa Kano ba sai bayan Asr lokacin harya kashe Wayarsa sbd kiran da Ya Omer yake masa.
Yana fitowa daga motar tana farkawa ba tare da yace komai ba yay gaba ganin hakan yasa ta shiga taka ƙafafuwanta a hankali tana jin jira na ɗibanta, a bakin ƙofar shiga parlo suka haɗu da Dad, Dad ko sauraran Ya Heemu bai ba ya fice abinsa.
Mumy har lokacin fashe fashe take duk ta yayyanke ta fita hayyacinta sai faɗin ɗan cikina shi zai zama mijina hauka ake? Harɗe hannayensa yay ya tsaya cak tsakiyar Parlo yana kallon ta yasan cewa tana sane take dukan haukan ta ɗauka hakan zai sanya Dad wargatsa auran, Wata jibgegegiyar mage ce ta fara ihu sbd Glass ɗin daya cake ta kai tsaye kuma magen ta nufi inda Mannal take, cak Mumy ta tsaya da abinda take idanunta ya firfito da sauri ta juya zatai waje suka haɗa ido da Ya Heemu wanda yake raɓe sai Moha da take gefensa kana Kallonta kasan cewa tana cikin halin jinya.
Tsayawa Mumy tayi shi kam Kallonta kawai yake da kayan jikinta domin ko bra babu tun kayan baccin data sanya jiya ne ƙilan ko sallah ma ba tayi ba.
Wani kuka magen tayi tana jijjiga hakan yasa Mumy ƙara yin gaba idanunta a rufe tsoro ya kamata don a duniya babu abinda take tsoro irin mage, kusan hakan take ga Moha domin tunda taji kukan magen hawayen tsoro ya fara zubu mata ta ƙara matsawa bayan Ya Heemu kamar zata riƙesa amma tana jin tsoron ruwan masifar sa.
A hankali ya fara takawa zuwa inda Mumy take yana gab da ƙara sawa magen tai wani ihu tare dayin tsalle.
Mumy da Moha a tare suka saki ihu kowa yayo kan Ya Heemu a dai-dai lokacin kuma magen ta sauka bayan Mumy hakan yasa Mumy tayi kan Ya Heemu tana sakin wani firgitaccen ihu, Moha ma tsoran ne ya kamata tayo wajan Ya Heemu a tare suka rungomesa Mumy ta rungomesa ta kama Moha ta rungomesa ta baya da sauri ya runtse idanunsa yana fisgo Numfashinsa tare da ƙoƙarin zare Mumy daga jikinsa ita kuma tana ƙara shigewa jikinsa tana tura fuskarta a ƙirjinsa.
Team Mannal And Ya Heemu
Or
Team Moha And Ya Heemu?
Kowa wanne team su faÉ—i ra'ayin su.
Dan Allah share fisabilillahi
*ABU_MALEEK*
WANDA BAI PAYMENT YA GAGGAUTA YI DOMIN SAMUN DAMAR SHIGA VIP AKAN 500 MA DADIN 1K WANNAN BUNONZA CE KAFIN NOVEMBER YA ƘARE 08119237616
11/30/21, 9:05 AM - Ummi Tandama😇: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*AURAN FANSA*
NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv
I'M HOT🔥LIKE A HEATHER😂 LIKE BOM🙌��
She's called me *Piano*, *Snow* har dasu *Muciya* 😂 And i like the name nasan duk cikin so ne, to this page da mai page ɗin da page ɗin duk na kine🥲� _DEDICATED TO YOU_ DEAR SHALELE UWAR ƊAKI, OUR MENTOR🥰 *RAMLERH MAI_DAMBU* MUCH LOVE STAY BLESSING😉
Runtse idanunsa Yay yana mai jin yadda zaratar matan sukai masa ƙawanya ta gaba da baya.
For the frist time daya ji wani kalar abu na tsarga nasa tun daga yatsarsa ta ƙafa zuwa tsakiyar kansa.
Ba komai yadda haddasa masa hakan ba sai yadda babbar mace ajin farko ta bashi wata ƙyakkyawar rungoma ta gabansa.
Yayinda yarinya ɗaya shakaf mai jini a jiki mai cike da ƙuruciya ta bashi wata lafiyayyiyar rungome ta bayansa duk a lokaci guda.
Yana jin yadda Moha ta lafe a bayansa tana sauke wahalalliyar ajjiyar zcy jikinta sai rawa yake sbd razanar da tayi.
Cikin wahala kuma take fusgar numfashinta jikinta ya ɗauki rawa ga wani zazzafan zazzaɓi daya kawo mata ziyara lokaci guda wanda zafin zazzaɓin ke fita yana ratsa rigar jikin Ya Heemu yana shigewa cikin jikinsa.
Mannal kam tsoran yawa yay mata ga yunwa ga gajiyar data tarawa kanta duk ya saukar mata ya fara tambayar lfyarta.
Tsananin firgicin data shiga ne yasa numfashi fara fita da saurin kusan suman tsaye tayi lokacin da magen tayi dirar mikiya a saman wuyanta ta shiga gurnani tana É—aga jela ga jini na zuba a jikin jelar ta ta.
Ya Heemu kasa motsa wa yay sbd yadda magen take wani kalar kuka tana buɗe bakinta tare da saita fiƙoƙinta tana shirin kai cizo.
Ya Heemu Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai buÉ—e manyan idanunsa tare da cije bakinsa, a hankali yakai dubansa ga magen dake Shirin kaiwa Mannal cizo wacce dalilin hakan ya sanya ta fara ficewa a hankalinta.
Fesar da iska ya shigayi yana kallon yadda magen take buɗe baki tana miƙar da gashin jikinta tare da fito da fiƙoƙinta.
Gaba ɗaya faracen ƙafarta sun fito, ga mmkinsa sai yaga ta fara maida hankalin ta kan Moha dake maƙale a bayansa.
Hannunsa yake cike da jarumta da kuma zafin nama yana mai ƙara riƙe Mannal wacce numfashinta ya ɗan fara tsayawa.
Kafin yakai hannunsa ta daka wani tsalle ta sauka a bayan Moha wata gigitacciyyar ƙara Moha ta sanya tare dayin Ajjiyar zuciya jikinta ya saki.
A kuma za bure Ya Heemu daya gama fusata da iskancin magen ya juya da sauri yana mai fisge magen daga wuyanta wanda ya harta fara kartar mata fatar wuyanta.
Wurgi yay da ita jikinsa na rawa tare da tsuma idanunsa yay jajir, itama magen fusata tayi sbd yadda yay cilli da ita ga zafin ciwon da yake gusar mata da hankalinta hakan yasa ta fara wani kuka tare da jijjiga ta shiga miƙar da ƙafa.
Gane nufinta da ya yi ne yasa ya ɗan zame Mannal daga jikinsa amma duk da haka maƙalesa tai jikinta duk rawa yake, sosai take tsoron mage kamar yadda take tsoran ganin abinda baƙan tawa Arman ɗinta rai.
Da sauri Ya Heemu ya sunkuci Moha tare da goyata a bayansa, jinta a faffaɗan bayansa yasa ta sauke wahalalliyar ajjiyar zuciya tare dasa dukkan hannunta ta riƙo ƙirjinsa.
Kana ta runtsa idanunsa sbd wani abu dake mata yawo akai abun shekaru masu yawan gaske ya shiga dawowa cikin tunaninta, manna kanta tayi a bayansa tana sauke tagwayen ajjiyar zuciya.
Yana goyata a bayansa magen na sakkowa ta nufi inda yake kafin tazo yasa hannu ya sunkuci Mannal wacce tai suman tsaye da wani irin zafin nama yasa ƙafa yay ball da magen tare da jifa da ita.
Ƙara tasa sbd yadda kanta ya daki wani glass nan take kuma ta baje a wajan matacciya.
Harabar gidan ya nufa yadda yake tafiya cike da kuzari da kuma jarumta kaÉ—ai ya isa ya tabbatar da cewa Ya Heemu jarumin namiji wanda baya barin ko ta kwana.
Musamman yanzu da ransa yake babu daɗi hakan yasa ya ƙara saurin tafiyarsa kamar mai yin gudu, yana ɗauke da mata har biyu amma sam ba za kaga alamar gajiya a tare da shi ba.
Yana zuwa wajan motar ya saki Mannal ta faɗi ƙasa, ƴar ƙara ta saki tana mai ɗan cije bakinta haɗe da jan numfashi, sosai ta kejin zafi a ƙirjinta musamman yanzu da zcyrta take mata bala'in raɗaɗi, ƙunci haɗi da takaicin abinda akai mata.
Ƙara rufe idanunta tayi sbd yadda fitinan nan ƙamshin sa ke dokan hancinta yana kaiwa Dukkan wata ƙofa ta hancinta farmaki.
Ya Heemu kota kanta bai bi ba ya nufin bangaren driver, yana jin yadda Moha ke fisgar numfashi da ƙyar tana ƙara manne masa a baya.
Murfin motar ya buÉ—e a hankali kamar mai tsoran wani abu yasa tattausan hannunsa wanda yake fidda gumi kaÉ—an kaÉ—an ya sakko da ita daga bayansa.
Back seat yay niyar kwantar da ita amma yadda yaga ta fice a hayyacinta tana shirin rasa numfashinta yasa ya zauna tare da ita a mazaunin driver yana lumshe idanunsa masu kaifi da kuma É—aukar hankali ya shiga fesar da numfashi.
Mannal yadda take a durƙoshe nan kasa tashi tayi sbd wani bala'in ƙuncin da ta keji a ranta, musamman daya kasance kayan bacci ne a jikinta, baza ta taɓa tashi ba bare ya kalli jikinta, idan ma dalilin hakan yasa ya aureta to tabbatas zata shayar dashi mmki.
Zata nuna masa ta fi ɗan isa sanin tasha, ban dama tsaurin ido irin na yau har ita Ya Heemu zai kalla yace yana so kuma zai aureta? To Yay mata me? Me zata ɗauka jikinsa itafa duk duniya idan ba Abban Arman ba, bata jin akwai wani ɗa namiji da zai gamsar da ita tasan cewa ita ɗin mai Lfy ce kamar kowa, idan ba Abban Arman ba babu wani ɗa namijin da zataiwa surutu akan gadon aure bare kuma ƙaramin yaro ɗan talili like Ibrahimul Khalel.
Wani ƙaramin tsaki Ya Heemu yaja yana mai fesar da iska daga cikin bakinsa haɗe da tura dukkan hannayensa cikin sumar kansa yana hargitsa wa, domin samawa kansa nutsuwa.
Domin idan yace zai mgn Tabbas zai faÉ—i abinda bai dace ba, amma ya lura sam bata gama fahimtar waye Ibrahimul Khalel ba.
Yaga alamar su take yay tai mata ihu a aka tana bashi ciwon kai.
Buɗe narkakkun idanunsa yay wanda suka ɗan sauya launi zuwa jaa, ganinsa ya mayar kan Moha wacce ta maƙale sa wanda yana da tabbacin da a hayyacinta take ba zatai hakan ba.
Shima bazai taɓa hakan ba, yana tausayinta ne kawai yanzu sbd ciwon dake damunta wanda ta samesa wajan Mahaifiyar ta.
Numfashi taja da ƙarfi tana danna kanta cikin ƙirjinsa sbd Numfashin da taji ya tsaya mata.
Ba tare daya kalleta ba ya ɗura tattausan hannunsa saman ƙirjinta yana ɗan danna mata domin samun sauƙi.
Lumshe idanunta tayi sbd daÉ—in da yaji kafin ta buÉ—e idanunta tare da sauke su akan kayakkyawar fuskarsa mai kyau.
Hawayen da bata san na menene ba suka shiga sakko mata, kafin ta kama hannunsa ta riƙe sosai muryarta na rawa sosai tace.
"Ya...Ya Heemu!!!"
Sai kuma tayi shiru tana ƙara riƙe hannunsa, firgitattun idanunsa masu sanyi da kuma daɗin kallo ya sanya saman fuskarta yana kallon yadda fuskarta tai wani haske na abun mmki ga wani kyau data ƙara, har wani yellow take.
Kallonta kawai yay bai ce komai ba, sai ɗan gajeran tsaki daya saka yana mai taune leɓansa yana huce takaicinsa a kansu.
Kamar daga sama yaji tace "Meyesa ka tsaneni Ya Heemu? Me nai maka? Meyesa baka sona kamar yadda kake son Æ´an uwa na?"
Lumshe idanunsa yay yana dafe kansa ƙoƙarin zame ta yay jikinsa sai kuma ya fasa sbd tarin da yaji ta nayi tana Miƙewa sbd azabar da ta keji a ranta.
Riƙe ta yayi sosai yana