Showing 30001 words to 33000 words out of 52381 words

Chapter 11 - AUREN FANSA Book Complete Document by NIMCY.txt

04 Dec 2024

4315

faÉ—in
"Dan darajar Annabi kayi hqr wlh suɓutul kalam nayi, dan Allah kada kai min komai dan son da kakewa Ummi"
A hankali ya shiga buÉ—e nauyayyen idanunsa wanda sukai jajirr.
Ya sauke a kanta tsanar da yaywa Yarinyar yasa yake ganin fuskarta nada munu a idanunsa.
ÆŠauke idanunsa yay hakan yasa ganinsa ya sauka akan wayar hannunta zare ido yay.
A hankali kuma ya miƙa hannunsa da sauri tai baya zata sauka yay saurin cafke Hannunta ya shiga kallon wayar hannunta kafin ya kalleta fuskarsa kamar hadari babu walwala.
Kallon da yake mata yasa tace "Wlh ba ruwana Ya Omer yaban wai nai karatun littafi.
Baice mata komai ba ya kama hannunta tare da sauka daga saman bed ɗin jikinsa duk rawa yake, Moha kam gaba ɗaya ta firgita da Ganin Ya Heemu bata taɓa ganinsa a haka ba.
A waje ya samu Ya Omer da Ya Areef suna Mgnar gidan gonar Ya Heemu, tun daga nesa Ya Areef yaja baya domin shima ya tsorata duk da cewa shi ne gaba da Ya Heemu gaba ɗaya Ya Heemu shi ne ƙarami a cikinsu.
Shima Ya Omer gyara tsaiwa yay domin yasan kwanan zan can tunda yaga wayarsa a hannunsa ga Moha daya riƙe kamar zai ɓalla ta.
Idanun Ya Heemu har ruwa yake sbd zallar bala'i yana zuwa bai tsaya jiran komai ba yasa ya zabgawa Ya Omer mari zafi da ƙarfin marin yasa Ya Omer yin baya yana dafe kunci abinka da mai Zcy shima ya nufi Ya Heemu zai mara Moha na ganin haka tai saurin ƙanƙame Ya Heemu tana sakin kuka tsayawa Yay cak yana kallon Mmki.
Baffa da Baba Haroon da Kawo Shuriem (Mahaifin Shoona da Areef) suka tsaya cak suna kallon ikon Allah domin basu taɓa sanin akwai saɓani a tsakanin Yaran nasu ba.
Baffa kam Murmushi Yay sbd abinda Moha tayi ga wanda ta saba dashi ta shaƙo dashi an maresa batai komai ba amma wanda ta tsana anzo marinsa ta hana.
Ya Omer yace
"ka maran?"
Ya Heemu ta huci yana son zare Moha daga jikinsa amma tai masa mahaukacin riƙo yana fesar da iska yace "Sai na mallaka yanzun nan, ashe girman banza gareka ashe baka da hankali yarinyar da an zuba mata ido wacce Allah ya kaya bare ka ɗauki waya ka bata, abin takaicin bama karatu makaranta zatai ma wai Hausa novels ka bata ta karanta, what the fuck? Heeee!! What's this answers my questions OMER ALIYU AL'AMEEN?" Murmushi Baffa yay yace "AL'AMEEN sunana ke nan"
Bai ko kalli inda Baffa yake ba yace "Baka da amsa ko? Sbd kana son ka gina soyayyyar ka a zcyrta shi ne baka son komai ka bata waya tai karatu may be she understands very well ko? Well-done Omer Aliyu Al'ameen"
Ya faɗin hakan yana buga wayar a ƙasa ta watse nan take.
Baffa ne ya samu damar faÉ—in "Malam Ibrahimul Khalel meya faru kai da waye jikalle?"
Hucie kawai yake ganin hakan yasa Kawo Shuriem ya ƙara so wajan tare dasa hannayensa ya riƙe hannun Moha kuka tasa tace "Kawo dukansa Ya Omer zai yi haka kwanaki ya dakesa a ƙirji"
Kallon juna sukai wato faÉ—an bana yanzu bane kenan.
Ya Omer kam duk ihun da Ya Heemu yake baya fahimta fargaba da tsoro suka kamsa, ganin yadda Moha take nuna kariya ga Ya Heemu.
Da sauri ya zube gaban Baffa yana riƙe ƙafafuwansa yace "Baffa dan Allah dan Annabi kayi min rai ka aura min Aysherh idan duk akanta yake wannan abun zan kawo ƙarshen abun yazo, dan Allah Baffa nai maka al'ƙawarin duk abinda za kace amma ka fara aura min ita wlh zan iya rasa rai na idan ban sameta ba"
Baba Haroon ne yace "Omaru baka da hankali amma dai ko, wannan yarinyar zaka aura gaba É—aya nawa take?"
Baffa ne yace "Haruna kira min Aliyu yanzun nan, sannan ka kira min Al'mustapha yanzu shima"
Da mmki Baba Haroon yace "Amma Baffa kiran na mene?"
Baffa yace "Bana son mgn" yana faɗin haka ya kama hannun Khalel da jikinsa ke rawa kana ya riƙe na Ya Omer yace "Kawo min matar nan" ya faɗi hakan yana nufar cikin ɗakinsa.


Driving daya ɗauko Mannal nayin parking ta fito daga cikin motar a nutse take tafiya amma hankalinta gaba ɗaya baya jikinta tana shiga cikin babban parlo Dad ɗinta na fitowa da sauri ta nufi inda yake yana ganinta yasan akwai matsala, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana sakin kuka tana riƙe tana faɗin "Dad!! Dad!! Dad Abban Arman" sai kuma ta ƙara saka wani kukan, janta yau zuwa wajan kujerar ya shiga rarrashinta sai da tayi Shiru tana manne jikinsa tana sakin ajjiyar zcy kamar wata yarinya Dad yace "Ƙara zuwa kikai ko? Ashe kin girma ba zaki hankali Ba Daughter na? Kinfi son ki zauna da wanda zaici mutuncin ki yaci mutuncin mahaifin ki? Ke kika hanani kaishi Court da al'ƙawarin ba zaki sake mgn dashi ba yanzu shine kika karya al'ƙawarin ko?" Waya ya ɗauka ba tare daya janyeta daga jikinta ba ya kira yace "Kamal kazo kai da Jamil" yana faɗin hakan ya da ɗa kiran wata number yace "Yace Sufyan har yanzu kana sha'awar Auran Daughter?" Kai ya jinjina kana yace "Ok meet me right now" gaban Mannal ya bada sauti rasss rasss dam! Miƙewa tayi tace "Dad?" Hannu ya ɗaga mata yace "Kinyi abinda ki kaga dama yanzu nima zanyi abinda naga dama a matsayi na mahaifinki"
Wayarsa tayi ƙara bayan sun gaisa ya tsaya yana jin abinda ake cewa shiru yay sai kuma yace "Ikon Allah"


Baffa ya kalli yaransa, Baba Haroon da kawo Shuriem sai kuma Uncle Aliyu, da kuma Al'mustapha mahaifin Moha wanda dawowarsa daga ƙasar kenan, Baffa ya kalli Ya Heemu dake gefen damarsa wanda har yanzu jikinsa rawa yake, kana ya kalli Ya Omer sai kuma ya kalli Moha yace "Aysuhtul humaira wa kike son Aura tsakanin Yayanki Ibrahimul Khalel da Omaru?".
Narkakkun idanunsa Ya Heemu ya ɗaga ya sauke akanta yaci Sa'a suka haɗa ido tsuro tayi tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta a lokaci na farko da tasan cewa shi ɗan uwanta ne kuma jininta domin Moha ƴar wajan Al'mustapha shi kuma Al'mustapha ɗan uwan Ummi ne, Anut Meera kuma ƴar ce wajan Baffa, sai yanzu take ganin kamar su sosai da Ya Heemu hatta dimples teeths gave da tusar jakinsu duk iri guda ce, kallonsa take kamar yadda yake kallonta hawaye ya sakko mata bata taɓa sanin kalmar aure ba sai a bakin Ya Omer dan haka ta juya ta kalli Ya Omer kana ta kalli mahaifinta mutum mai karamci da kuma alkunya muryarta na rawa tana son sakin kuka tace "Baffa Ya Omer na keson ya auran"
Da sauri Ya Heemu ya miƙe yana haɗa hanya ya bar ɗakin yana ɗan sakin gajeran tari.




MASOYA NA MASOYA LITTAFAI NA, NESA TAZO KUSA, ABINDA KUKE ZAMAN JIRA YA KUSA ZUWA GAREKU, SOYAYYAR KU KAWAI YA JIRA, LITTAFIN *ABU_MALEEK* KADA KU SAKE A BAKU LABARI, DOMIN DUK WANDA YACE ZAI BAKU LABARI TO TABBAS YAY MAKU ƘARYA, DOMIN LABARIN *ABU_MALEEK* YA HUCE TUNANIN MAI TUNANI, DA HARSHASHEN MAI NAZARI, DUK YADDA KA KAI DA FAHIMTA LABARIN *ABU_MALEEK* ZAI MAKA WAHALAR GANEWA, SOYAYYA CE MAI ƊAUKE DA SARƘAƘIYYAR ƘIYAYYA DA KUMA ZALLAR MULKI DA IKO TA *MASARAUTAR KANZAF* KU NUNA MIN SOYAYYA KO FARANTA MIN KAMAR YADDA NAKE FARANTA MAKU KUZO KUYI PAYMENT NA ABU MALEEK AKAN #500 KACAL ZAKU SAMU BOOK 1 2 3, KUN KARANTA MOON, UNCLE NE, THE NEW EMIR, JIDDAH, JUYAYI DUK KUNJI UWA UBA SIRRIN MU TO ABU MALEEK YA HUCE DUK SANINKU, BAZAN FARA POSTING BA SAI AN GAMA PAYMENT KUMA ZAN FARA POSTING NE BAYAN NA KAMMALA BOOK 1 KA SANCE MUTUM NA FARKO WAJAN BIYI HAKAN ZAI BAKA DAMAR SHIGA VIP POSTING SAMA DA ƊAYA KULLUM TARE DA KYUATAR LITTAFIN *SAI NA AURETA* VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 GA ƳAN NIGER ZA SUYI MGN TA NAN 84506476 KADA KO MANTA NAIRA 500 NE.








SARAUTA
11/30/21, 9:05 AM - Ummi Tandama😇: 🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈🌈
*AURAN FANSA*
NA'IMA SULAIMAN SARAUTA
Nimcyluv




23-24




Baffa ne yabi bayan Grandson É—in nasa da kallo yana mmki hali irin na Ibrahimul Khalel.
Not too long Ya Heemu ya dawo cikin É—akin É—auke da gorar ruwa yana kafawa a bakinsa tare kwankwaÉ—ar ruwan da sauri da sauri kamar zai janye gorar ruwan zuwa cikinsa.
Yana gama sha yaja ya zauna dab da Baffa kansa a ƙasa amma jikinsa har yanzu was vibrate amma ko a fuska baza ka taɓa gane ai nayin abinda yake cikinsa a zcy ba.
Huci kawai yake yana fesar da iska hatta gashin kansa wanda suke a murmurÉ—e kamar anyi masa (Dada)
Sai da suka miƙe tsaye.
Baffa ya gyara zama yana É—an daidaita nutsuwarsa cike da kamala da kuma haiba irinta kamilallun maza Baffa ya kalli Al'mustapha yace.
"Al'mustapha ina neman amincewar ka akan ka bawa jikana auran Æ´ar kuma jikata idan babu damuwa"
Wanda aka kira da Al'mustapha yaja gajeran numfashi tunanin halayyar Moha yake.
Yarinyar tana da wahalar sha'ani mai gane mata sai ya shirya.
Bata da tsoro sam ga tsaurin ido haɗi da zallar ƙuruciya, bata sanin dai-dai da abinda yake ba dai-dai ba, sai dai ita ɗin abin tausayi ce sosai.
Musamman idan ciwonta ya tashi ko da yake duk zafin ciwonta bai kama ƙafar na (Hawwa'u Jidderh, kulu kuma Julde ƴar makauniyar Abu Maleek ba).
Tana da rauni sosai amma shi kansa bai san mene rauninta ba, har gobe kuma abu guda yake sawa ta saduda shi kansa baya gane wannan lamari nata domin abun yana masa kama da JUYAYI.
rawar kai yay mata yawa over nutsuwarta É—aya Ya Heemu gashi wani dalili na sawa ya cire dukkan wani hope nasa akan É—an Æ´ar uwar tasa.
Idan Khalel baya kusa mgnar wa Mamansa za taji? Wazai mata tsawa É—aya ta samu nutsuwa?
Baffa ne yay gyaran murya yace
"Alhj Al'mustapha kai muke saurare"
Numfasawa Alhj Al'mustapha yay kafin ya ɗaga kai ya kalli Aysuhtul humaira yaga taiwa Ya Heemu ƙuri da idanu kana ya mayar da kallonsa ga Ya Heemu yaga hankalinsa kwance kamar ba shi ya shiga tension ɗin daya shiga yanzu ba.
Kansa a ƙasa yana latsa Wayarsa mai ƙirar Iphone 12 max pro.
Cikin sanyin nutsuwa haÉ—i da kamala da kuma kamewa irinta mazan jiya masu sanin darajar na gaba dasu yace.
"Baffa Nima kamar É—a nake gareka to bana da haufi akan dukkan wani shawara daka yanke akan wannan sabon al'amarin, yadda Jikar ka Aysuhtul humaira zata amince da sharaÉ—in ka haka nima zan amince da sharaÉ—in ka Baffa, ka amince É—ari bisa É—ari Allah yasa Albarka ya kaÉ—e fitina"
Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa yana mai tausayin yarinyar tasa, wacce har yanzu bata san abinda yake mata ciwo ba, girman jiki ne kawai da Ubangiji ya bata.
Jinjina kai Baffa yay cike da gamsuwa da kuma girmama girman karamcin da Al'mustapha yay masa.
Kullum yana buƙatar kasancewar da yarinyar sa, amma baya samun damar haka.
Domin dashi da Baffa ba'a san wanda yafi son Moha ba, ƙarfin soyayyar da Baffa ya kewa Moha yasa gaba ɗaya ya dawo da zamanta wajansa, ganin haka yasa sauran jikokinsa dawowa wajansa baki ɗaya, Shoona, Hannah Sai kuma Sunaina ita wannan tana karatu waje sbd tana ɗan gaba dasu, Murgayiya Safa kam ƙulafucin uwa gareta kamar dai SARAUTA haka take, sometimes shike ɗaukan ƙafa yaje wajanta yana cewa yaje biko.
Tuna wannan karamcin na Al'mustapha yasa Baffa faÉ—in.
"duk da cewa ina da iko akan abinda zan aiwatar amma dole dai na nemi amincewar ka domin kai ka haifi Aysuhtul humaira, Ina gdy ƙwarai da wannan karamcin ka nuna min nima mahaifi nake gareka kamar yadda nake mahaifi a wajan Matarka (Aunty Meera)".
Casbahar hannunsa ya ajjiye tsohun yasan me yake duk da cewa ya tsufa ainun amma sosai yake da himma da kuma saurin fahimtar abubuwa masu muhimmanci.
Yaransa ya kalla sannan ya kalli jikokin nasa a nutse yace.
"Haruna fito min da dukkan abinda yake aljihun ka"
Baba Haroon ya sanya hannunsa ya É—auko harfar kuÉ—i ta 500 wanda ya kasance 50k ne, kuÉ—in ya ajjiye gaban Baffa da sauri kuma yasa hannu ya É—auki zoben daya faÉ—a daga cikin kuÉ—in.
Zoben Ya Heemu yabi da kallo sai kuma ya janye idanunsa yana maida kallonsa ga Wayarsa.
Baffan yace
"A bisa abinda yake faruwa ga yaran nan ni kuma na yanke nawa hukuncin da nake ganin shine dai-dai da abinda nai nazari, dan haka na bawa Omaru auran Aysuhtul humaira, bisa sadaki dubu hamsin Allah ya sawa Auran albarka"
Gaba É—aya suka amsa da Ameen.
Nan Baba Haroon ya zama waliyin Ango Ya Omer sai Kawo Shuriem ya zama waliyin amarya.
Ya Omer wani hawayen farin ciki ne ya sakko daga cikin idanunsa ya rungome Baffa yana masa gdy.
Moha kam shiru tai sai zare fararan Idanunta masu sheƙi wanda kamarsu ya ƙara fita sak dana Ya Heemu.
Ji tayi abu mai girma da kuma nauyin gske ya danne mata kai.
Yayinda bugun zcyarta ya tsananta, ƙarfi da harbawar ko wacce ƙofa da take jikin zcyrta ya ƙaro fiye da ko wanne lokaci.
Cikin rashin makamar abinyi da kuma rashin gane ainahin abinda yake faruwa idanunta ya fara fidda wasu zafaffun hawaye mai fidda zafi da kuma kala, yadda hawayen suke gudu a saman farar ƙyakkyawar fuskarta zai sanya ka tabbatar hawayen bana jin daɗi bane sam-sam ko kaɗan.
Duk wannan abinda ake idanunta yana kan Ya Heemu ita kanta ba tace ga kallon da take masa ba.
Wasu abubuwa na shekarun baya suka fara dawowa gareta da tunanin, Shadow'n photon abin ya fara yawo cikin ƙwayar idanunta masu fidda ƙyallin zaiba.
Ya Heemu ya ajjiye wayarsa ba tare daya kalli kowa na wajan ba ya mayar da ganinsa kan Baffa yace
"Baffa ina da buƙata"
Shafa kansa Baffa yay yana mai jin so da kuma ƙaunar Ya Heemu na ƙara huda ƙofar jijiyoyin zcyarsa.
Cike da kulawa yace
"Haba zakina, faɗi ko mene indai maifi ƙarfina ba Tabbas zan maka"
Lumshe idanunsa Ya Heemu yay yana tsotsar laɓɓansa wanda suka gama yin jaaa sbd azabar da yake gana masu wajan cijesu.
Numfashinsa na fita ɗai ɗai yana samun daidaito a tsakiyar ƙahon zcyarsa wacce take wassafa masa dukkan abinda yake yana fesar da kuntun numfashi mai zafin gaske tare matsawa sosai wajan Baffa nasa cikin ƙasaitacciyar muryarsa wacce ya gama dai-dai ta yace.
"Aure na keso ka nema min, Nima yau na keson Auran ya kasance"
Jinjina kai Baffa Yay domin daman abinda yake jira kenan bashi da Burin daya huce ya ɗauki baƙaƙen yaran Ya Heemu wanda yake fatan su ɗauki baƙar fatarsa sbd jar fatar ta ishi idanunsa da gani.
Yana Murmushi yace
"Kada ka damu gaya min Wacece wacce kake so, kuma Æ´ar ina ce waye mahaifinta"
Idanunsa ya lumshe yana kokawa da Numfashinsa wanda ya ke son fallasa a sirin zcyarsa yace.
"Baffa Mumyn Arman na keso"
Ba Baffa ba hatta Moha da take ƙarama sai data ɗaga kai ta kalli Ya Heemu haka Ya Omer da sauran mutanan cikin ɗakin.
Sam Baffa bai mmki ba sbd Uncle É—in Mannal ya jima da faÉ—a masa, kuma ya amince da haka sbd babu haramci ciki, fiyayyan halitta ma ya auri wacce ta girmesa so dukkan abinda za'ai koyi dashi bai huce nasa ba, kuma daman shekaru ai lamba ce kawai.
Kawo Shuriem yace "Khalel mariƙiyyar taka? Mahaifiyar Arman best friend ɗin Hjy Ruma fa?"
Ko kallan inda yake Ya Heemu bai kalla ba Baba Haroon yace
"ikon Allah kenan"
Uncle Aliyu kam Shiru kawai yay dan ba komai kake jin yay mgna ba, sai abu mai muhimmanci yanzu ma har yay Shiru sai kuma yace.
"Son a shekarunka? Baka son mure ƙuruciyar ka ne? Mannal fa, this is difficult dear age mate ɗin Mahaifiyar ka"
Alhj Al'mustapha yace
"Ai age is just a number ba dai shi yaji ya amince ba to Allahamdulillah ai, kawai ku saka albarka is better than talk"
Baffa yace "Aliyu kiramin Mahaifin Mannal"
Ba musu ya kira ya bawa Baffa suka gaisa Suna jin sanda mahaifin Mannal yace "ikon Allah"
Ya Heemu kam jikinsa yaja zuwa na Baffa yana yanayinsa na sauyawa ya shiga tasbihi a ransa yana ƙara kwantar da kansa jikin Baffa.


Kano state/Nassarawa G.r.a
Mannal na cikin É—akin ta ta sauya kaya zuwa sleeping dress Black Silk short robe
Companyn La Perla.
Sai Aquaholic Slippers bedroom slippers kenan, ta rufe kanta da wata tattausar red hula mai gashi.
Tana zaune saman kujera tana operating system É—inta sbd duba oder da tayi daga Dubai zuwa 9ja.
Cikin nutsuwa take danna keyboard ɗin system ɗin tana ƙara zaɓar wasu sabbin kaya wanda zata zuba Mall ɗinta.
Yadda take É—an sauke ajjiyar Zcy da sauri da sauri kaÉ—ai zai tabbatar maka cewa bata cikin hankalinta.
Amma a zahiri ka kalleta cewa zakai babu abinda yake damunta jan da idanunta yay ta É—iga masa wani abu ya washe ta wanke fuskarta tass.
Amma har yanzu tsoro da kuma fargabar abinda zaizo ya dawo take domin tunda Dad ɗinta ya fita mgnar aurenta bai dawo gida ba shiyasa tsoro da fargaba shigeta sai dai bata bari yay tasiri a zcyarta ba bare abin ya taɓa rauninta.
Hamdala kawai take ga Allah domin da ace Ya Heemu ya samu nasara a kanta gwamma ko É—an garuwa ne Dad É—inta ya bata bare kuma É—an uwanta Sufyan.
Turo ƙofar bedroom ɗin nata akai aka shigo tare dayin sallama.
Ba tare data ɗago kanta ba ta gyara zaman farin siririn glass ɗin idanunta wanda suke ɗan ƙara mata ƙarfin gani.
Kafin a hankali ta miƙa hannu ta ɗauki mug ɗin gabanta wanda yake ɗauke da haɗin fruits wanda yasha fresh milk.
Zame mug É—in tayi cikin nutsuwa da É—an dakewa tace "Wasalamu alaiki"
Kallonta Anuty Lubna tayi kafin tace.
"Dad É—inki na son magana dake"
Jinjina kai kawai tayi tare da rufe system É—in ta É—auki hijab ta sanya saman kayan baccin tabi bayan Anuty Lubna.
Downstairs ta sakko ta samu Dad É—inta zaune yana sanye da Jallabiya yana kallon tafsir É—in Sheikh Imam Deedat Balarabe.
Sai coffee dake gabansa da kuma gashasshen naman zabo.
Zamewa tayi gefen ƙafafuwansa ta zauna tana ƙasa da kanta zcyrta na ɗan bugawa.
Gyara zama yay sosai ya bata dukkan nutsuwarsa yace "Khadijertou matsayin wa nake gareki?"
Kanta a ƙasa tace "You're my father Dad!"
Jinjina kai yay yace
"Good"
Kallonta ya ƙarayi yace
"A matsayina na Mahaifinki kamar yadda kikace a karo na biyu na aurar dake, daman na farko bawai dan ina so bane, na rabu dake ne sbd

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login