Showing 24001 words to 27000 words out of 44401 words

Chapter 9 - MAFIYA Part 1 By MRS SADAUKI .txt

03 Dec 2024

3198

ke kwance suna hutawa a daidai wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda suke kwaɗayin ɗanɗanon jini.
Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe ƙaton cikinta tana sharara bacci.
Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani sabon shirin.

“Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon, ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka.

Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi wani baccin kirki ba.

Washegari
Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba.
Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin abinci.
“Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau Feenat ya ƙarfin jikinki?”
“Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?”
Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba”

Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir.

“A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata.
Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki”

Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina”

Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya.

“Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi.
“ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba”

Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba”

“Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure”

“To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana so ta dawo gida ta haihu ”

Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za ta zo?”

Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa.
Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito.
Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet ta shiga ta soma yin wanka sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita .Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata”

Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai dace mace mai takaba ta fita ba”
Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani abu ne da ya haifar miki da hakan”
“Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?”
“Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su yi sallama.
Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta.

Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?”
Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci haihuwar ce ta zo bilhaƙi.

Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ”
“Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta fara wani gurnani mai haɗe da nishi.
“Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa.
Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana Goggo cire mata kayan ba.

Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara juya ido tare da soma kai wa kurwar jinjirin hari sai dai ba ta ida cin galaba ba nishin Safeenat haɗi da kukan wata babyn ya dawo da ita hayyacinta.

Ƙirjin Goggo Hajara ne ya kusan ɓallewa zuciyarta ta faɗo tsabar firgici,jaririyar da faɗo cibinta a yanke yake sannan kuma babu marakiya saɓanin shi namijin da har yanzu take masa reto.
Sai a lokacin ne ma ta samu zarrar yanke mahaifar,ba tare da kuma ta san dalilin kawar mata da mugun nufinta ba ta soma kimtsa Safeenat wacce babu laifi ta dawo hayyacinta.

Goggo Hajara ta wanke kayan da kuma gyara ɗakin ta saka turaren wuta,ita ce kuma ta zaɓo wa Safeenat riga da zane.Har da haɗo mata tea mai zafi ta sha,gefe ta koma bayan ta gama komai tana tunanin zuci ‘ mi ya shiga kaina ni Hajara? Kamar ni kamar ba ni ce ba’ kukan jariran ne ya katse mata tunani ,ta ce “ ki ɗora su ga abincinsu” sai kuma miƙe ta soma nuna mata yadda za ta yi.Namijin kawai ya sha ita kuwa macen baya ga kuka babu abin da take,Goggo Hajara na ɗaukar ta sai kuma ta yi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba.Muƙut ta haɗiye wasu yawu hango wani baƙin kallo daga cikin ƙwayar jaririyar da ko minti talatin ba a yi ba da haihuwarta......
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*

LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman.

_____________________
21/09/24

1-2

#Damagaram

Ƙarfe uku na dare agogon ɗakin ya nuna,a sa'ilin da mutane ke kwance suna hutawa a daidai wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda suke kwaɗayin ɗanɗanon jini.
Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe ƙaton cikinta tana sharara bacci.
Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani sabon shirin.

“Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon, ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka.

Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi wani baccin kirki ba.

Washegari
Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba.
Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin abinci.
“Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau Feenat ya ƙarfin jikinki?”
“Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?”
Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba”

Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir.

“A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata.
Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki”

Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina”

Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya.

“Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi.
“ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba”

Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba”

“Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure”

“To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana so ta dawo gida ta haihu ”

Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za ta zo?”

Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa.
Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito.
Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login