Showing 42001 words to 44401 words out of 44401 words
azababen sanyi na game duk illahirin jikinta tamkar wacce aka jefa a frigini.Haƙoranta ne suka fara dantsewa suna fitar da wani ƙasƙas,sai a wannan lokacin Gwaggo Habibah ta miƙe ta cire Babyn tare da lumshe ido tana mai bata haƙuri “ku yi haƙuri uwa-uwza ce ta yi kuskure ba za ta sake ba” tana maganar ne tana jimƙe da hannun hagun Baseerat wanda ke fitar da haske,Gwaggo Habibah ba ta buɗe idonta ba sai da ta ji Sakeenatu na sauke numfashin wahala ta yi mata wani kallo ta ce “yanzu kin fahimci abin da nake son yi miki nuni?” kai ta gyaɗa,Baseerat ta soma yin kuka.
“Zo ki bata ta sha”
Safeenatu ta maƙe kafaɗata ta ce “wallahi tsoronta nake”
“Sun tafi yanzu ita kaɗai ce ,zo ki bata yunwa take ji” tana ji tana gani haka ta shayar da jaririyar.
Ana kiran sallar magrib Murjanatu ta dira a gidan da ɗirkeken cikinta,cike da murna suka rungume juna ita da Gwaggo Hajara.“Na yi kewarki sosai Mama ” cewar Murjanatu tana matsar ƙwalla,shiru Gwaggo Hajara ta yi jin ƙaton cikin ƴarta na tokare ta yayin da kuma yawunta suka soma tsinkewa tsabar maita......
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛
💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)*
💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏♀️🧏♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰
💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin
💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁
💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍
💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢
💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️
💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba
💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko
💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan.
Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
01/10/24
*Last free page 13-14*
Wani irin mugun ƙishi ne ya wanzu a maƙoshin Gwaggo Hajara saboda Maitar shan jini ta motsa.Dakyar ta iya sakin Murjanatu ta koma gefe tana kallon ta,sai kuma ta kasa haƙuri sai da ta shafi ƙaton cikin da mugun sauri Murjanatu ta kai hannunta ita ma kan cikin saboda mugun juyawa da yayi.
“Washhh! ” ta furta a wahalce kafin kuma ta dafe ƙugu jin kamar ta soma naƙuda ne,“ sannu Murjanatu ki zauna mana” Gwaggo Hajara ta faɗa tana haɗiyar yawu don tsaf take kallon jaririn wanda sai juyi yake a ciki.
Kan gwiwanta ta zube tana mai ci gaba da yin gumurzu,tuni ita Hajara ta san da yau in ba wani iko na Allah ba sai ƴarta ta haihu.Da sauri ta shiga cikin ɗaki ta fito kafin ta ce “tashi mu je asibiti” a wahalce ta ɗago ta dubi mahaifiyarta ta ce “ wallahi Mama ban iya tashi”
“To haka za ki zauna? Sai nake ganin kamar haihuwar ce”
Ba ta rufe bakinta ba Murjanatu ta fasa wani uban ihu wanda ya jawo hankalin Gwaggo Habibah da saurinta kuwa ta fito tana tambayar lafiya sai kuma ta yi tozali da Murjanatu a cikin mawuyacin hali.Da taimakonta suka samu suka Murjanatu ta miƙe tsaye,Munir ne ya je ya nemo musu mai ɗan sahu.Kayan robar Safeenatu aka yi aro aka kai ta asibiti,sai uban ihu take tana kururuwa tana faɗin za ta mutu.
Daga nan waje kuma inda mutane ke zauna wa,ran Gwoggo Habibah ya ɓace sosai tun tana ɓoyen abin har ta kasa ta ce “ yanzu ke hatta ƴarki ba ki bari ba? Wannan mugun hali naki bai yi ba.Wato babu babban makunyaci a duniya irin maye,tun da har jininsa bai bari ba”
Gwaggo Hajara ta ƙanƙance idonta da suka kaɗa suka yi ja kafin ta ce “ ina ruwanki da ni ? Ke kika haifa min Murjanatun? Ƙanwar uwa ko ta uba?”
Gwaggo Habibah ta miƙe ta ce “ kina fa da gaskiya,amma ki yi haƙuri farar zuciyata ta taimakon jama'a tasa na zo na tsoma hannnuna inda ba a gayyace ni ba.Tabbas Murjanatu ƴarki ce in kina so ki haɗa har da ita duk ki cinye” tana gama faɗa ta yi tafiyarta ta bar Hajara a zaune babu jimawa kuwa Murjanatu ta haifo ɗanta namiji.
Ɗakin hutu aka kai ta,murya na ɗan rawa Gwaggo Hajara ta ce “ yo ina jaririn?”
“Nurse na duba shi ne don tabbatar da lafiyarsa” ta bata amsa.
Tsawon lokaci kafin a kawo shi jikinta har rawa yake ta karɓe shi,nurse ta ce “ a basa abincinsa ya sha da alamu yunwa yake ji”
“Toh! Toh” cewar Hajara tana wani kafe yaron da idon mugunta,ya soma kuka Murjanatu ta tashi zaune babu kunya ta ce “ Mama kawo shi” ba don ta so ba ta miƙa mata shi ta koma gefe cike da ƙwarewa ta damƙe kurwar yaron .Da ta fita wankin kayan da suka ɓace ta samu wuri ta haƙa rame ta binne ,duk da zuciyarta babu daɗi amma ji take ya zama doli ta cinye jikanta na farko ko yawunta sun koma.
Daren nan dai ba su yi bacci ba jariri nata yin kuka hatta likitocin sai da suka shigo suka duba shi,sai asubahi ya rumtsa wuraren ƙarfe tara na safe aka basu takardar sallama bayan sun biya.Hajara ce ta je ta taro ɗan sahu,bayan ta saka kayansu Murjanatu ta shiga sannan ita ma ta shige tana kallon wurin da ta binne kurwar jariri can ƙasan zuciyarta ta furta ‘ zuwa dare zan zo na tone’ haka suka isa gida.
Ta kuwa ci sa'a Daddy bai fita ba,Murjanatu ta gaishe shi ya amsa tare da yi mata barka kafin ya maida dubansa ga Hajara wacce sai raba ido take kana gani ka san ba ta da gaskiya.
“ Hakan da kika yi daidai ne? Don dai ba ni ne na haifi Murjanatu ba shine kika koro Habibah daga asibiti? ”
“Ka yi haƙuri ba koro ta na yi ba,na dai ce ta dawo gida tun da ba za a barin mai jego ita ɗaya ba a gida”
“Mi yasa ba ki kira ni kin shaida min zancen haihuwar ba? Ban cancanta ba ne ko me?”
“Ka yi haƙuri Daddyn yara,yanzu dai ka kira shi mijin nata ka shaida masa zancen haihuwar ”
Bai amsa mata ba ya fice,sai a lokacin Habibah ta fito idonta kan jaririn wanda ke baccin wahala.Cike da tausayinsa ta ƙarasa ta ce “ barka Murjanatu Allah raya shi kan sunnah”
“Amen na gode” ta amsa tare da miƙa mata jaririn,Habibah ta karɓe shi tana mai zaunawa kan kujera ta shafi sumar gashinsa tana kallonsa da kyau ta tabbata kurwarsa na gidan yari ba a cinye ba sai dai ba ta san a ina aka binne ta ba.Haka ta gaji da binciken ta miƙa shi ga uwarsa ta miƙe suna ƴar kallon-kallon ita da Hajara wacce idon nan nata suke wiƙi-wiƙi na maras gaskiya.
A sanyayye Habibah ta koma ɗakin Safeenatu,“ ya dai Gwaggo Habibah lafiya na gan ki duk kin yi wani iri?” Feenat ta tambaya.
“ Babu komai Safeena,bacci Baseerat take?”
“Eh ba ta jima da rufe idon ba”
“Mu gan ta” Habibah ta faɗa tare da yin zama, Safeenatu ta ɗora mata jaririyar kan cinya.Hannunta mai safa ta kamo ta cire sannan ta soma shafa shi ,zuciya cike da rauni ta soma yin magana “ ki tausaya ki ceto jaririn da bai san komai ba,ki sani shi ma tamkar Basheer yake mai rauni ne.In kuma har yanzu kuna cikin fushi ne shi yasa kuka hana ta ɗauki mataki ku yi haƙuri,amma dai a duba lamarin” tana gama faɗa Baseerat ta buɗe idonta taram cikin na Habibah,ita kuwa ta shiga kallon abubuwan da suka faru bayan ta bar asibitin a cikin ƙwayar idon jaririyar ta ga komai har inda Hajara ta binne kurwar.Tana gama gani Baseerat ta maida idonta ta rufe, Safeenatu dai na gefe a yanzu ma kallonsu take ba tare da ta ce komai ba.
Habibah ta ja ajiyar zuciya ta sakar mata murmushi ita kuwa kai ta ɗauke,tana mai jawo wayarta ta kunna data so take ta yi bincike don gano shin abubuwan da suke faruwa zai iya kasancewa ko kuwa ƴarta ce kawai ke da shi.
Tunanin ta watsar ta shiga WhatsApp ta fara duba saƙonnin mutane masu yi mata barka kafin kwatsam ta ganta cikin wani group.A hankali ta soma biyayar abubuwan da ke faruwa sai ta ga amsoshin tambayoyinta kan wani posting.
```“M” CIKIN TAFIN HANNU,MAUME HAND/PAUME DE MAIN
Chiromancy wata daɗaɗiyar hanya ce ta hango makomar mutum da kuma fassarar halayyar mutum daga dalilin layukan hannu. Wani lokaci waɗannan layuka na iya samar da lambobi da haruffa. Ɗaya daga cikin waɗannan wasiƙun na iya zama wasiƙar M, ma'anar wacce mystics da dama suka yi nazari a kanta.
Kamar yadda mutane da yawa suka yi imani, layukan da ke kan tafin hannunmu suna bayyana halinmu da ƙaddararmu. La lettre M est attribuée à des personnes vraiment spéciales(The letter M is assigned to truly special people). An ba su kyakkyawar fahimta kuma suna wakiltar abokan haɗin gwiwa akan dukkan wasu kasuwanci.
Idan mutanen da kake so suna da wasiƙa ta musamman M a cikin tafin hannu ya kamata ka sani cewa ba za ka iya raina masa hankali ba kuma ta wata hanyar ba za ka iya yin ƙarya ko yaudarar wannan mutumin ba. Kasancewar shi mai dubara da hankali da tsantsar lura sosai, mutamin da ke da harafin M a tafin hannu cikin sauƙi zai fahimci cewa ana yi masa ƙarya ne ko yaudara.
``Matan da suke da harafin M a tafin hannunsu suna da zurfin tunani fiye da maza, har ma da waɗanda suke da wannan wasiƙar. Ana yi musu baiwa da ikon sarrafawa da shawo kan duk wani cikas a rayuwa, kuma sun san yadda ake amfani da albarkatu da damar da ake da su.
Harafin "M" a kan tafin hannu ma na iya nufin:
• Ƙwarewar shugabanci
• Iko wato power/pouvoir```
Zuciyar Safeenatu banda bugawa babu abin da take yi har sai da ta ajiye wayar ta je ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha .Ta dawo ta zauna don ƙara duba saƙon sai dai hatta shi kansa group ɗin ya ɓata a wayarta babu shi sam .Kamar mahaukaciya haka ta miƙe ta je ta yi wani gurwanau a gaban net ɗin da aka saka Baseerat,ta zuge zip ɗin ta kalli ƙofar toilet inda motsin ruwa ke ta zuba da alamu Habibah wanka ta shiga ba tare da ita ta san yaushe ta shiga ba .
Murya a ɗan kasalance ta ce “ Baseerat ni ce mahaifiyarki,ni na haife ki.Duk wani wanda bai son ganin kin cutu to tabbas sai dai ya biyo bayana,don haka kar ki ga kamar ban son ki a'a wallahi zuciyata raunk ne da ita.Magana nake son yi miki game da abin da na gani cikin wayata,shin kina da masaniya? In dai tabbas ke ƴar baiwa ce kamar yadda saƙon nan ya bayyana to ki buɗe idonki ki kalle ni” ko rufe baki ba ta yi ba kuwa Baseerat ta buɗe idon sai da Safeenatu ta dafe ƙirji saboda tsoro.
“Mine ne wai?” daga bayanta Habibah ta tambaya ,zip ɗin net ɗin ta mayar tana mai cewa “ babu komai Gwaggo Habibah,na yarda na aminta da lamarin nan gaske ne ana samun ƴan baiwa to Allah bata ikon yin amfani da ita ta hanyar ƙwarai” ruwan sama ne suka fara sauka a daidai lokacin da Safeenatu ta rufe bakinta.
Gwaggo Habibah ta yi wani ɗan ihun murna tare da rungume Safeenatu ta ce “ kin ga ko? Ƴarki ta musamman ce ancestor/ ancêtre suna tare da ita”
A wannan daren cike da zullumi da tunani Safeenatu ta yi shi,da ta samu bacci ya ɗauke ta mafarkai ta yi barkatai akan goben Baseerat.
Washegari tun da safe kukan jaririn Murjanatu ya cika gidan kamar wanda ake cirewa rai.
“Jaririn can ba dai kuka ba” Safeenatu ta faɗa .
Habibah ta ja baki ta yi shiru tana tuna jiya irin gumurzun da suka yi ita da Hajara akan kurwar yaron.Dakyar ta yi nasara ta tone ta tare da saka Hajara don doli ta mayar masa abarsa wacce tuni ita kanta kurwar ta yi rauni,kukan da yake yi kuma saboda ciwon jiki ne.
★A kwana a tashi babu wuya wurin Allah yau ne sunan Twins ɗin Safeenatu waɗanda dangin Bashir suka yi bajinta sosai wurin yankan manyan raguna uku biyu na BASHEER ɗaya kuma na BASEERAT .A wannan rana ta farin ciki Safeenatu ta rakuɓe wuri guda tana ta yin kuka,ga shi dai ta sha ƙunshi da kitso ga kuma gizner ta gani ta faɗa amma rashin masoyinta ya dawo mata daram musamman yadda ake ta faɗar an yi masa madadi da kuma addu'o'in da mutane ke yi.
Da wannan damar Gwaggo Hajara ta shirya mugunta wacce take kambacin fansar da ta yi niyyar ɗauka akan Habibah da hana ta rawar gaban hantsi.Sai da ta bari duk hankalin mutane ya ɗauku,sannan jarirai duk an fitar da su can tsakar gida saboda zafin da ɗakin ya ɗauka sannan ta nufi ɗakin Safeenatu.Duk da akwai mutane hakan bai hana ta gwada sa'arta ba,“ ungo Safeena Gwaggonki Habibah ta ce ki ci abincin nan kafin ta zo ta yi miki ta ƙarfi tun da dai ke ba ki jin magana kina jego amma kin ƙi cin abinci ” Hajara ta faɗa tare da miƙa mata plate mai cike da nama ya sha jar miya,ta karɓa tana turo baki tare da soma ci don ita duk a tunaninta gaske dai Habibar ta bata.Cike da murna Hajara ta bar ɗakin ta je ta kasa kunne tana jiran sakamako.
Da rana mutanen arziki sun cika gida, Safeenatu ta shiga Toilet ta yi wanka da canza kaya daga shadda zuwa less.Kamar wacce aka yi wa wankin ido haka take ganin ƴan biki tsirara tamkar babu kaya jikinsu,zuciyarta ta yi wani mugun bugawa ganin ta soma ganin hanjin cikin mutane yayin da kuma take jin wani abu a bakinta da ba ta san mine ne ba.A daidai nan free page ya ida,duk mai son ci gaba za ta biya kuɗi domin shiga PAID GROUP.
*FREE PAGE/ PAGE NA KYAUTA YA IDA*
Detail 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
In kin san ba ki shirya saya ba kar ki min magana,ga detail nan kawai ki tura kuɗin ki turo min evidence ta WhatsApp.
*NB:* daga lokacin da ya kammala ya zama complete zai koma 1000.
01 octoba 2024
#CHAMSIYA LAOUALI RABO
MRS SADAUKI 💫