Showing 1 words to 3000 words out of 44401 words
[14/11 à 12:10] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
01
‘ Lokacin da muna yara,da zarar an ce MAFIYA kawai abu guda kwanyata ke bani ƙungiyar shan jini ce mai sa a yi kuɗi.Amma yanzu da na girma,na kuma tsinci kaina a ciki sai na fahimci cewa MAFIYA na nufin cikar muradi.
Sunana HAROON matashi ne ni ɗan kimanin shekara talatin da takwas a duniya,maraya na uba ,shalelen mahaifiyata.Na taso cikin matsin rayuwa ta talauci kafin kuma na tsinci kaina cikin daula...... '
“Haroon sakatariyarka ta ce yau ba za ka fita ba ko zan san dalili?” muryar Ammy ta katse mini ɗan taƙaitaccen tunanin zucina wanda kusan lokuta da dama nake zama haka kawai ina bai wa kaina labarin kaina.
Na saki murmushi ina kallon sanyin idaniyata abar alfaharina,“ ban jin daɗi ne Ammy shi yasa,amma kar ki damu ciwon kai ne kawai”
“Kamar ya kar na damu ? Ciwon kan ne kake faɗa ƙaramin abu? Jira ni ina zuwa” ta faɗa tare da yin gaba.
Na bi ta da kallon ƙauna,Ammyna kenan uwa ta gari wacce a idonta sam ba na girma kullum tamkar ƙaramin yaro haka take ɗauka ta.Ina nan zaune ta dawo hannunta riƙe da wata tasa da kuma ƙaramin towel,na lumshe ido lokacin da ta soma tsoma towel ɗin a ruwa tana matse shi sai kuma ta dinga dadanna shi a kaina.Cikin ikon Allah na ji ciwon kan yayi sauƙi,“Ammy ya isa haka je ki huta mana ban san yaushe za ki daina ɗawainiya da ni ba,kamar wani ƙaramin yaro dai sai ririta ni kike” na faɗa ina mai riƙe hannunta mai ɗauke da towel ɗin.
Ta dungure mini goshi cikin faɗanta da ta saba yi min ta ce “ sai ranar da ka kawo matar aurenka a gidan nan.Wai HAROON yaushe za ka yi aure ?”
Da sauri na miƙe ina mai cewa “ aure! Aure dai kullum shine zancenki Ammy,duka nawa nake?”
“Yanzu na haife ka” ta bani amsar da ta saka ni dariya,sai kuma na ce “ kar ki damu zan nemo miki suruka kafin ƙarshen shekarar nan in sha Allah!” na furta ina mamakin furucina na ƙarshe da na ambaci sunan maƙagina,wanda a ƙalla zan kai shekaru biyar da muka yi hannun riga ni da umarninsa.Yanzu haka ambaton sunansa sai da na ji maƙogorona yayi min wani zafi,halshena kuwa tamkar an saka reza ne an tsaga shi.
“Allah ya nuna mini wannan babbar rana, Ubangiji yasa ina da rai albarkacin Manzon Rahama Ya Rabb ka dubi Harunana ka basa mata ƴar aljanna mai haska duk wani duhun gidansa” ita ce addu'ar Ammy gare ni,ban ko amsa ba na yi gaba abina.
Ina fitowa harabar tsakar gida direbana yayi saurin tashi tare da nufar motar da a yau ita ce zan shiga.Da kansa ya buɗe mini gidan baya na zauna,sannan ya ja motar. Hanyar babban ofis ɗina ya ɗauka amma na yi saurin dakatar da shi.“ Ka ga kai ni wurin da zan ɗan shaƙi iska yau ban ra'ayin aiki ko kaɗan ” na faɗa don haka kawai nake jin yau raina a dagule babu daɗi ga wani irin bugawa da zuciyata take.
Gudu yake da ni amma hankalina ba ya ga hanya na lula sosai cikin tunani,ƙiiiii ya ja wani uban burki sai a lokacin na dubi gabana.Wata kyakkyawar budurwa na hango tana tsallakar da yara ƴan makaranta,yayin da duk ababen hawa suka tsaya suna jiran sai yaran sun gama wucewa.
“Yi haƙuri yalaɓai bari na canza hanya” cewar direba ,da sauri na ce “no ! Jira” ido kawai na tsura mata yadda take ta zulumniya cikin ƙaton hijabinta ,yayin da hannunta kuma wanda ya sha jan lalle ke faman kamo na yara.
Ido na lumshe sa'ilin da ta game dukkan hannuwanta alamun godiya ,ban san mun bar wurin ba sai da na ji direba yana cewa “ba don Malam Zainab ba ce da ƙila mutanen nan ba su tsaya ba sai an samu waɗanda za su ce sai sun wuce”
“Ka san ta ne dama?” na samu kaina da tambayarsa.
Yayi ƴar dariya ya ce “to wane ne zai ce bai san Malama Zainab ba,yarinyar da duk shekara ita ce ke cin gasar musabaƙa ta duniya.Makarantar can ma gwamnati ne ya buɗa mata ita da sunanta,yalaɓai in ka ji yadda ɗalibanta ke yin larabci kai kace ƙyanƙyasar Saudiya ce uwa uba ita in tana yi.Zaƙin muryar.....”
“Ya isa haka juya ka mayar da ni gida” na yi saurin katse shi saboda bugun zuciyata da na ji sai ƙara hauhawa yake.Muna isa gida ko wani burki mai kyau bai yi ba na yi saurin fita daga motar ba tare da na jira ya buɗe min ba.
Ammy na falo ta ga na shigo a hargitse,ta yo kaina tana tambayar lafiya amma ban bata amsa ba na haye step ina taka shi bibiyu yayin da ita kuma ta mara min baya tana faman kiran sunana.Ina isa ɗaki kuma na rufe shi gam da key,ga ƙofar na jingina ina sauke numfashi kafin dakyar na ƙarasa na je na zauna kan kujera ina kallon kaina cikin baƙin madubin da shine silar canza rayuwata daga jiya zuwa yau.A zahiri ni mutum ne complet,amma a cikin madubi ba komai ne ba face ƙwarangwal ba tsoka saboda da kaina na sayar da ruhina ga MAFIYA.........
[14/11 à 15:44] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*
02
Karon farko kenan da na yi da na sanin shiga MAFIYA,a tsawon shekarun da na yi a ciki na yi su ne cikin farin ciki.Hawayen takaici nake yi yayin da ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ke ƙyartata dariya,ita ƙwarangwal ɗin nan ba kowa ba ne face Ni,inuwata ce ko kuma na ce ruɓaɓen ruhina.Daga can bakin ƙofa ina jin Ammy na buga wa tare da kiran sunana amma na kasa tashi ,zuciyata ta yi rauni ba zan iya tsayuwa gabanta ba na shaida mata alƙawarin da na yi mata na samo matar aure ne ya cika sai dai kuma baƙin ruhina da farin ruhin kyakkyawar budurwar nan sam ba za su iya zama a inuwa ɗaya ba saboda rayuwar da ta rage min ƙalilan ce.
Wayata ce ta ɗauki ruri,ina dubawa na ga sunan Oga.A dole na ɗaga,“ ka zo muna da meeting ɗin gaggawa” shine abin da ya faɗa kafin ya kashe.
Jiki babu ƙwari na miƙe na shiga toilet na wanke fuskata na goge ta da towel sannan na fito.A bakin ƙofa na ga Ammy idonta sun yi jawur,na sakar mata murmushi na ce “ kar fa ki damu kan ki zan nemo wata tun da wannan ɗin ta fi ƙarfina”
“Wa kenan?”
“Budurwar da na gani yanzu da muka fita,kin ga Ammy kar ki damu zan cika miki alƙawarin da na ɗauka” ina gama faɗa na soma tafiya,ta biyo bayana har muka sauko ƙasa sannan ta ce “ ƴar wace ce ita da har ta fi ƙarfin ka?”
“Ba kowa ba ce kawai malamar makaranta ce” na bata amsa,“ mi sunanta?”
Na juyo muna facing juna sannan na bata amsa da “ zan fita yanzu in na dawo za mu yi maganar”
“Allah tsare ka ya maido mini kai lafiya”
Dakyar na amsa da “Amen ” .Ina fita na karɓi key ɗin mota,don in magana ta shafi Oga ban bari a yi draving ɗina.Tuƙi nake amma idona ita suke hasko min,dakyar na samu na kai kaina can inda muka saba meeting ɗin.
Tuni mutane sun fara taruwa,na samu wuri na zauna muka ɗan soma cacabke wa da sauran members.Sai da kowa ya hallara sannan wurin yayi tsit,Oganmu sai a lokacin ya miƙe ya soma jawabi.“ Kamar yadda kuka sani wannan Association ɗin namu yana da tsari,ba a shiga kudin sirrin kowa hakan ne yasa wasu informations ɗin ba mu samunsu kai tsaye ta yadda za mu fahimci daga ina suka fito.Sai dai sosai dakarun bayar da kariya suke iya ƙoƙarinsu wurin ganin babu wata ƙungiya ko baƙin haure da za su kawo mana hari.To yau ma ɗin mun samu labarin cewa wani mummunan al'amari na tunkaro ƙungiyarmu ,kune ƴaƴanta kune kuka san yadda kuke gudanar da rayuwarku don haka ku nutsu ku yi nazari a cikinku babu wanda ya tsokano faɗa ko kuma yayi wani kuskure wanda bai dace da tsarin ƙungiya ba?” Oga na kawowa nan da zancensa sai duk ya soma bin mu da ido ɗaya bayan ɗaya.
Ko kaɗan ban kawo a raina cewa malam Zainab da na soma jin ƙaunarta ita ce matsalar da Oga ke magana a kai ba wannan yasa sam ban ma nuna damuwa ba.Har aka gama meeting babu wanda ya ce ga wata matsala sai Oga ya sallami kowa.Har zan fita ya tsayar da ni,sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya ce “ HAROON ka shekara biyar a cikinmu”
“Ai na sani Oga” na faɗa don ban ga amfanin sanar da ni ɗin ba.
“Eh tuni ne na yi ma don kar ka shagala” ya faɗa yana ƙara yi min kallon nan da ke sa mutum ya tsargu,shiru kawai na yi masa.Can ya ce “ kana iya tafiya” na jinjina kai.
Bayan na fito daga can direct wani gidan shaƙatawa na tsaya Park,wuri ne da iyaye suke kawo yaransu don shan iska da kuma buɗe ido.Karon farko da na ji sha'awar ajiye yara,yadda suke wasa gwanin ban sha'awa sai ya sake tuna min da Malama Zainab.Hoton fuskarta nake gani a kan fuskar duk iyayen da ke wurin,sai nake ganin tamkar ma a nan ita ce ke kula da su.Na ɓata lokaci sosai kafin na bar wurin,ina draving ina tunaninta har na isa gida.Cak na tsaya bakin ƙofa ganin Malama Zainab ɗin tare da Ammy a zaune.Na girgiza kai tare da dariyar kaina a zuci na ce ‘ HAROON ka haukace tun da har a cikin gidanku Malama Zainab kake gani ’ sai na yi gaba har na hau step ɗin farko sai na tsinkayo muryar Ammy na cewa “ HAROON zo ku gaisa da malamar da za ta dinga koyar da ni karatu”
Da sauri na juyo sai muka haɗa ido da ita amma ta yi saurin kawar da kai,tamkar wani gumki haka na tsaya ina kallon ta .Sanye take cikin pink ɗin hijabi,tafin hannunwata a waje suke ta riƙe litattafai da su.Kamar wani sakarai haka jan lallen yatsunta ya ja ra'ayina har ban san lokacin da na taka can inda suke a zaune kan salon ba,“ mu ga littafin da za ku soma” na faɗa tare da kai hannuna zan karɓa amma wani azababen suraci da ban san na mene ne ba ya daki hannuna da bala'in sauri na yi baya har ina shirin faɗuwa.
“Yi sannu mana,Malama miƙo min na basa” cewar Ammy ta karɓo littafan ta miƙo min sai dai sam na kasa amsa saboda wani irin haske da nake ganin yayi min katanga da littafafan.Na girgiza kai na ce “ a'a Ammy ba sai na gani ba” sai kuma na nufi step da mugun sauri na haye can sama,ina shiga ɗaki na ƙargame shi da key ina jin wani tsohon ilimina na baya na dawo min.A nan take a inda nake na fahimci wani abu,ina cikin fushin Allah mai tsanani ta yadda har har littafai masu kalmomin saninsa suka yi min tawaye suka haramta gare ni........
MRS SADAUKI ce 💫✍️
[15/11 à 15:32] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
03
Duk yadda na so nuna wa zuciyata ruwa ba a sa'an kwando ba ne amma sam sai ta yi min bore ta ƙi aminta akan muradinta.Soyayyar Malama Zainab ɗin dai ta zaɓa ,duk da tunanina ya ƙi bata haɗin kai wannan bai canza zane ba.Dakyar na cira ƙafafuna zuwa toilet,kayana na cire kafin na shiga ƙarƙashin shower na buɗe pampon duka.Ruwa suka soma jiƙa ni,sanyinsu na rantsa sumar kaina ina jin wata ƴar nutsuwa na sauko min.Rabon da na ji yanayin buƙatar mace har na manta,zan iya kai wata biyu haka ban yi lalata da ƴar kowa ba amma yau soyayyar Malama Zainab ta motso mini da tsimin.
Pampon na kashe ba tare da na yi wankan sabulu ba,towel na ɗaura a ƙugu kafin na fito ina tsane gashina da ɗan ƙarami.Bayan na gama na saka ƙananun kaya na fashe jikina da turare kafin na sauko ƙasa ,sai na tarar tuni ta tafi sai Ammy kaɗai zaune a falo tana duba littafi.
Na ƙaƙalo murmushin dole na ce “ Barka da yamma uwa ta gari”
Ta ɗago ta ɗan dube ni na wani lokaci kafin ta ce,“ meke damunka HAROON ? Ina ce ganin Malama Zainab zai sa ka nutsu amma sai na ga saɓanin haka”
Kusa da ita na zauna kafin na ce “ wai aka yi kika nemo ta? Ko dama kin san ta ne?”
“To wane ne bai san Malama Zainab ba duk Yamai? Na san ta mana har gidan marayun da take kula da shi ina zuwa duk ƙarshen wata”
Na ɗan saki murmushi,taimakon al'umma yana ɗaya daga cikin halin kirki na Ammy.Duk wata ƙungiya mai kula da marayu sun san ta sannan ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai don kusan duk wani abu da ya shafi Islam sai an kawo mata takardar gayyata irin taron ci gaban addini da sauransu,amma ko kaɗan ban yi tunanin ta san Malama Zainab ɗin ba.
“Bayan fitarka ne na tambayi direba sai yake sanar da ni,shine fa muka je har can inda take na nemi alfarmar ta dinga zuwa tana min karatu a gida ” Ammy ta faɗa murmushi kan fuskarta.
Ita ɗin tana da son Addini sai dai ba tada yawan karatu,kuma samun ilimi na ɗaya daga cikin burinta sai dai ta karaya ne tana ganin ai shekarunta sun ja.
“To Ammy sai ku yi ta karatun,yaushe da yaushe za ta zo?”
“Duk bayan sallar magrib in sha Allah,zan dinga aika direba ya ɗauko ta in kuma ta gama sai ya mayar da ita”
“Amma iyayenta sun bari?”
“Eh sosai,ai a gabansu na nemi alfarmar shi fa mahaifinta gani yayi ma kamar zunubi ne ƙin yarda da abin da na roƙe su ɗin.Iyayenta ƴan mutumci ne kamar dai ita” ta ƙarashe zancen fuskarta na canzawa,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “ mene ne kuma Ammy? Don Allah kar ki tuna shi,kar fa ki manta kin yi mini alƙawarin haka”
Kai ta jinjina mini kafin ta ce “ zan shiga ciki sallar magrib ta gabato zan yi wanka” sai kuma ta miƙe,na bi bayanta da kallo kawai.Ina nan zaune mai aiki ta kawo min abubuwan motsa baki,ko kallon ta ban yi ba na soma ci ina tunanin abar ƙauna.Na kurɓi lemun zoɓo kafin na miƙe na fita harabar gidan,mota na shiga na ƙara ficewa.
Ban yi nisa ba kuwa aka soma kiran sallah,amma ban wani damu ba na ci gaba da tuƙina har na isa inda nake tunanin zan samu macen da za ta sama min nutsuwa.
Daidai wurin bada hannu na tsaya,almajiran suka fara miƙo min robobinsu duk da kuwa gilashin motata a rufe yake ruf.Dayawansu ba za su wuce shekara ashirin zuwa da uku ba,ganin ban buɗe ba yasa duk suka tafi sai ɗaya ce ƴar jaraba ta tsaya .Sai a lokacin kuma na yi ƙasa da madubin motar,cikin daƙiƙa biyar na ƙare mata kallo fara ce ita amma dauɗa ta saka ya disashe sannan irin kamar Fulanin nan na daji.
“Alhaji ka taimaka mini ina son kai Mamana asibiti ne” ta faɗa cikin marairaice murya.
“Nawa ne farashinki? ” na samu kaina da furta wa,ido kawai ta zuba min da alamu ita sabuwar zuwa ce ba ta san tabi'ar nan ta ban manda na baka gishiri ba.
“Za ki bi ni mu je in kina son na baki kuɗi” na faɗa a karo na biyu,sai na ga tsoro ya bayyana a fuskarta.A hankali na soma mayar da madubin motar amma ta yi saurin dakatar da ni ta hanyar saka hannunta daga sama ,sai na ƙara yin ƙasa da shi.
“In mun je da gaske za ka bani kuɗin?” ta jefo mini tambayar cike da yarinta.
Kai kawai na jinjina mata,sai na ga fuskarta ta faɗaɗa da murmushi.Gaban mota na buɗe mata kafin na yi mata key,tuni gari ya ɗauki duhu sai hasken fitilun kan hanya.Gudu nake sosai ta yadda ta soma yi min magana cikin tsoro “ don Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka sayar da ni ”
Na ja tsuki ban tanka ta ba,sai dai na rage gudun motar sai ta saki ajiyar zuciya.Gidana na kai ta wanda babu kowa a cikinsa hatta mai gadi ban sa ba,a waje na yi parking duk muka fito.Na buɗe gidan na shiga sai na ga ita ta tsaya bakin ƙofa,“ki shigo”
“A'a ba sai na shiga ba ka ɗauko kuɗin ka bani” tsabar takaici ban san lokacin da na wani jawo hannunta da ƙarfi ba na shigo da ita ciki tare da rufe gidan.
“In kika ce ihu ko kuka za ki yi min zan sayar da ke ɗin tun da haka kike so” na faɗa tare da yin gaba,a dole ta take min baya har cikin falo.Na kunna wutar ko ina sannan na haɗe rai tare da nuna mata toilet na ce “ ki shiga ki yi wanka” jikinta na kyarma ta shiga ɗin,sama da minti goma amma ta ƙi fitowa sai na mara mata baya ina shiga na ja wani uban burki zuciyata ta soma bugawa fat! Fat! Fat! Sakamakon ganin Oga cikin shigar kayan yarinyar da na ɗauko a mota.
Waige-waige na fara sai dai babu ita sai shi ɗin dai,kamar ƙyaftawar ido yarinyar ta dawo normal ta soma magana amma muryar oga ce ke fita.
“ Tun da na soma meeting ɗin yau hankalina yake kanka,wato a fuskar kowa na lura da damuwa saɓanin kai.HAROON ka fara soyayya faɗa mini wace ce ita?” yana gama faɗa sai ya ɗauki siffarsa ta namijin kayan yarinyar nan suka zube a ƙasa sai nasa kayan jajaye masu kamar jini.
Kasa furta komai na yi,don in na ce in yi magana ƙarya ce zan faɗa kuma tsaf zai gane.To mene ne ma abin yi wa mutumen da yake da ƙarfin power ɗaukar siffar mace? Shirun dai ne ya fi alkhairi a gare ni.
Kafaɗata ya dafa sai na ji wani zuuut,sai muka ɓace daga cikin toilet zuwa daularsa wacce kusan a can muke taro masu muhimmancin sosai ko kuma in wani sabon members ya shigo.Ban fita daga