Showing 6001 words to 9000 words out of 44401 words
ne ya furta ba ni ba.Amma sai na yi saurin cewa Ammy “ saboda ina mugun ƙaunarta shi yasa a duk in tana kusa da ni ina jin sautin zuciyata na canza wa”
Ammy ta shiga yi min dariya kafin ta kama hannuna kamar wani ƙaramin yaro muka fito.
Ina taka step ina kallon Malama Zainab wacce ke zaune tana duba wani littafi,yanayin nutsuwarta da cikar kamalarta sun fi komai burge ni a tattare da ita.
Ammy ce ta yi sallama,da sauri ta ɗago tana amsawa tare da gaishe ta.
“Lafiya lau Malama ya gida ina kuma iyayenki fatan duk kuna lafiya?”
“Alhamdullah suna gaishe ki ma” ta faɗa cikin rawar murya tana sunne kai,cikin ƙwaƙwalwata na ji muryar nan na ce mini “ kar ka cika kallonta hakan fa zai sa ta fasa son ka”
Ammy ta ɗan zungure ni,na dube ta sai ta yi min alamu kan na yi wa malamar magana.Na yi gyaran murya na ce “ uhum! Hajiya ko na ce Malama na gode sosai da kika karɓi wannan aiki na koyar da Mamana karatu muna godiya...” sai kuma na yi shiru, Ammy ta gusa ta bar falon tana harare na tare da yi min alama kan na zauna kan kujera .Abin da Ammy ba ta sani ba iya wannan tsayuwar ji na nake a takure,tamkar wanda ya shiga wurin da babu iskan shaƙa na san kuma hakan bai rasa nasaba da ƙarfin imaninta.
Ɗan nesa da ita na yi,sai na ji abin yayi dama .Na sauke ajiyar zuciya kafin na ce “ Malama Zainaaab?” a hankali ta ɗago ta dube ni muka haɗa ido,sai na ji wani ƙuna tamkar ta watso min barkono wannan karon ni ne na sauke idona ina rayawa a zuci ‘ tabbas da matsala! Yarinyar da na kasa haɗa ido da ita ta yaya kenan za mu yi aure har mu haihu? Ko dai duk abubuwan da na gani cikin madubi ƙarya ne? ’
Ɗayar muryar mai min magana cikin kwanya ta ce “ sam wannan ba ƙarya ba ce,tabbas za ka aure ta sannan ku samu yara sai dai saurin yiyuwar haka na tattare da kai akwai abubuwan da ake buƙata ka yi kafin har ka cimma ƙudirinka in ka ji kana iya wa tun yau za ka soma”
Tun da na soma jin maganar na yi shiru har aka ida kafin na sake tambayar muryar ‘ ta yaya kenan? ’
“Ta hanyar sato farin tauraro daga jikin wani bil'adama mai sakaci,tabbas da tauraronsa za ka yi amfani domin biyan buƙatarka” ina gama jin amsa na saki murmushi ,ina ɗago kai sai na kama Malama Zainab na satar kallona.
Na sakar mata murmushi yayin da ta yi saurin miƙe wa tana cewa “ zan koma ina da ɗalibai da zan yi wa karatu”
“Ok jira na kira Ammy ” na faɗa tare da zuwa ɗakin Ammy,tana gani na ta miƙe tana cewa “ komai ya tafi daidai? Ka furta mata ɗin kana son ta?”
Na yi murmushi mai sauti na ce “ A'a Ammy amma mun samu kusanci sosai ina ga ita ma tana sona ”
“Wato ba ka furta mata ba? Mtsww !” ta ja tsuki tana harare na tare da ficewa,duk sai na ji babu daɗi na take mata baya.
Da murmushinta mai tsadar nan take sanar da Ammy uzurinta,“ HAROON ka sauke Malama a makaranta”
“To Ammy ” na furta ba tare da na san yin haka babban kuskure ne a rayuwata ba.Har kusa motata Ammy ta yi mana rakiya,ita ce da kanta ta buɗe wa Malama Zainab gidan gaba.Dakyar na shiga na zauna na yi wa motar key,numfashina sai barazanar tsaya wa yake ba don komai ba sai don na yi kusa da farin ruhinta.
Ina tuƙi ina haƙi kamar wanda yayi tseren doki,zuciyata ji nake tana matse wa tana takurewa wuri guda .Hancina kuwa tamkar wanda aka matse sam babu daɗi ,iya ta baki kawai nake samu ina sheɗawa.Tun ina daurewa har na kasa,ina ƙoƙarin tsayar da motar kuma wayar Malama Zainab ta hau ruri ƙira'ar Sheikh Aliyu Jabeer ce inda yake karanta suratul yaseen.
“Yiiii!” na soma kyarma yayin da na kusa sakin sitiyarin motar ina,idona kuwa wani baƙin abu kawai nake gani da alamun lantarkin nasu ne yake dab da tsayawa.Hannunta na ji kan nawa on daidaita tsayuwar motar sai dai kafin wannan zuciyata ce ta tsaya cak da bugawa ........
Ga masu son fara yin payment ga detail nan ,500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 .Ki tura kawo sai ki turo min evidence sai na saka ki group.
Talla! Talla! Talla!!!
Set d'in gyaran gashinmu na dauke da
* Shampoing don wanke gashi
* Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi
* Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules
* Garin ambunu da zai hana karyewar gashi
* Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i
* Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi
* Man coco na asali don gyaran fata
+22780416252
[21/11 à 15:01] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
07
Cikin ikon Allah Malama Zainab ta yi nasarar tsayar da motar wuri guda,sama-sama nake jin sautin muryarta tana kiran sunana haɗi da girgiza ni “ HAROON ! HAROON ! Please ka tashi ! Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! ” ta furta kafin ta fita ƙila don neman taimako.
Fitarta yayi daidai da dawowar bugun zuciyata,na buɗe murfin motar na soma kelaya amai kamar raina zai fita.Ta zagayo tare da yin tsaye tana kallona,sai kuma ta je za ta tsallaka titi tana mai tsayar da mai sayar da ruwa .Manta wa na yi da halin da nake ciki na yi wani uban tsalle na jawo ta baya don kauce ta daga motar da saura ƙiris ta kaɗe ta.
Tamkar yadda in boom ta fashe take ɗaga mutum sama ta cilla shi gefe haka ce ta faru da na jawo Malama Zainab,sai da muka yi sama ni da ita kafin mu faɗa can gefe kaina ya bugu da dutse yayin da ita kuma ta faɗo kan ƙirjina gaba ɗayanta.A wannan karon babu wani jinkiri ruhina yayi nisan zango daga wannan duniyar na fita daga hayyacina ban ƙara sanin abin da ya faru ba.
A ruɗe Malama Zainab ta tashi daga jikin HAROON idonta na kawo ruwa,mutanen da ke bakin hanya ne suka matso.Ita ɗin ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai wannan yasa cike da girmamawa suka fara tambayarta ba'asi.
“Yayana ne ya faɗi ne kansa ya bugu” ta faɗa cikin kuka ganin kan HAROON sai jini yake zubarwa,wasu samari suka taimaka mata suka saka shi a gidan baya yayin da ita kuma ta hau mazaunin direba ta tuƙa shi zuwa wata asibiti ta kuɗi.
Da isar su aka karɓe shi,duk da kuwa ba tada kuɗi a hannunta amma sai ta nuna musu katin ɗan ƙasarta cikin ikon Allah ma wasu sun santa.Abu na farko da aka soma yi wa HAROON shine tsayar da jinin kansa aka naɗe da bandeji,cikin ikon Allah kuma numfashin nasa ya dawo normal sai dai yana buƙatar hutu.
Sai a lokacin kuma ta kira mahaifiyarsa ta shaida mata ,babu jimawa kuwa sai ga Ammy.Ita ma kukan ta soma sai ya zamana babu mai rarrashin wani,ita sai faman faɗin “ HAROON kar ka mutu ka bar ni,kai kaɗai ne farin cikina a duniyar nan”
Ita kuma Malama Zainab cewa take “ duk laifina ne,da ace ban yarda ya sauke ni ba da ƙila hakan bai faru ba,saboda son kasancewa da shi yasa na aminta oh ni Zainabu na ga ikon Allah! ” sai kuma ta fashe da kuka.
Bacci nake mai kamar mutuwa, sama-sama nake jin sautin kukansu a hankali na ware idona ba tare da na buɗe su tarau ba.Ta ƙasan gashin ido nake hango yadda masoyana biyun ke kuka,sai na shagala yadda manyan idon Malama ke tsiyayar da ruwa ,pink leɓenta kuma duk ya jiƙe da yawunta yana rawa.Yatsun nan nata masu ɗaukar hankalina sai shafar hawaye suke,na dafe gefen kaina da ke sara min kafin na kira sunan Ammy.Da sauri ta matso kusa da ni tana cewa “ ka tashi? Mi kake ji? Ina yake ma ciwo?”
Murmushi na sakar mata tare da nuna mata saitin zuciyata da kuma yi mata alama da Malama Zainab,wacce ta yi tsaye tana kallona hawaye na bin kumatunta yayin da fuskarta ke ɗauke da ɗan murmushi.
Ammy ta ce “ za ka same ta in sha Allah kar ka wani damu” sai kawai na lumshe ido ina tuna abin da ya faru da ni, a daidai lokacin da mugun iskan nan mai ƙarfi yayi cilli da ni kaina ya bugu da dutse ɗigon jinina na farko ya ɗiga ga ƙasa Oganmu na gani a can gefe a tsaye yana kallona,bai samu damar ƙaraso wa inda nake ba sai da Malama Zainab ta ɗan yi nesa da ni,abin da na fahimta shi kansa yana shakkarta.Hakan kuma sai yasa na ƙara jin mugun sonta da ƙaunarta sun ƙaru a Wani farin abu ya saka min a inda kaina ya fashe kafin ya ɓace wa ganina.
Dakyar ta iya cewa “ ya jikin naka?”
Ammy ta ce “ bari na kira likita” sai ta fice.
Sai a lokacin na amsa mata “Da sauƙi! Na gode sosai”
Ta ɗan dube ni cikin ido kafin ta ce “ babu komai!” sai kuma duk muka yi shiru ,ni na ƙure ta da ido yayin da ita kuma take satar kallona lokaci-lokaci .A haka Ammy ta shigo ita da wata nurse,awon tension ta yi min kafin ta ce “ ka gyara zan yi ma allura ga cinya”
“Ga cinyaaa ?” Malama Zainab ta faɗa da sauri duk muka kalle dukkan mu ukun sai ta yi saurin wayancewa ta ce “ ina nufin wace irin allura ce za a yi ga cinya? A yi ga hannu ai zai fi”
Nurse ɗin ta ce “ saboda cinya ta fi tsoka,in ga hannu ne za ta iya yi masa zafi”
“Bai komai ai shi namiji ne,ki yi masa ga hannun kawai tun da dai ana yi” ta faɗa cike da kishin da ita kanta ba ta san ya fito ba,Ammy dai sai murmushi take.
Hannun rigar na cire sannan nurse ɗin ta yi min allura ga damtse,ni aka caka da allurar amma Malama Zainab ce ta yi ƙara har da rumtse ido.
Nurse ɗin ta yi dariya tana mai cewa “ ah Madam irin wannan tattali haka ? Ko duk don kar a yi miki kishiya ne?”
“Wace irin kishiya kuma ? Ai ...ai ba mij...” sai kuma ta yi shiru ƙila yadda muka haɗa ido da ita ne yasa ta kasa idawa.
“Zuwa an jima za a sallame ku in Dr ya hau aiki,sannan akwai gwaje-gwajen da aka yi ana jiran result” nurse ɗin ta faɗa kafin ta fice.
“Ni ma zan tafi Mama,am...ina nufin Hajiya Allah ya bada lafiya” shine abin da ta faɗa kafin Mama ta yi mata rakiya.
Suna fita Oga ya bayyana a cikin ɗakin fuskar nan tasa kicin-kicin,kamar zai fashewa da kuka ya ce “ ina mai yi maka gargaɗi akan ka bar sheɗaniyar yarinyar can.Sam tarayyarku babu alkhairi a tattare da ita,sannan ina so ka yi gaggawar barin asibitin nan kafin ta kwaso zugar ɗalibanta su zo duba ka”
Sam ban yi mamakin ganin nasa ba,amma na fi mamakin yadda yake so na bar asibiti alhalin banda lafiya.“ Amma Oga me yasa zan tafi? ”
“Za ka iya jurar addu'o'in da za su yi ita da zugar ɗalibanta? Kai ka rasa wacce za ka so sai babbar maƙiyiyarmu? Ko ba ka san manyan sheɗanu sun yi tirrr da halinta ba? In banda karatun littafinsu babu abin da ta iya,a haka ne kake tunanin haɗa wuta da ruwa wuri guda?”
“Ina son ta!” na furta kai tsaye ba tare da shakka ba,“ dole ka rabu da ita”
“Zan zauna da ita Oga,kai dai kawai ka zuba min ido” bai kai ga bani amsa ba Ammy ta shigo.
“ Da wa kake magana HAROON ?” ta tambaye ni.
“A'a ban yi magana ba Ammy ”
“Yanzun nan kafin na shigo na ji kana magana fa”
“To ƙila ko dai a ɗaya ɗakin ne”
“Ok to .Ka ga Malama Zainab na son ka ko? In sha Allah zan je can gidansu ni da Kawunka ” sam ban ɗauki maganar da wani muhimmanci ba na miƙe na shiga toilet saboda yadda na ji marata ta ƙulle,kamar jira ake ina shiga toilet ɗin na ga an zagaye ni na zamana a tsakiyarsu.Duka mutanen na gane su ahalin ƙungiyarmu ne,ban san da wane Siddabaru suka yi amfani wurin ɓatar da ni ba sai kawai na tsinci kaina a wani gun daban.
Cikin faɗa Oga ke faɗa “tun da ka ji za ka iya sai ka zo a ƙaddamar da kai ta yadda za ka samu power da yawa,sannan waccan abar ka sani lokaci guda ne kawai za ka iya kusantarta wato in tana period”
Cike da mamaki nake kallonsa kafin na ce “wannan ai ƙazanta ce! Ta ya zan kusanci matata da jinin al'ada?”
“Ba kada zaɓi” Oga ya faɗa yana matsowa kusa da ni hannunsa riƙe da wata ƴar tasa ,yatsana manuniyar ya kama ya sa reza ya tsaga shi nan jinina ya soma zuba cikin tasar nan har sai da ta cika duka.Ya ajiye tasar sannan ya saka wani abu ya rufe wurin da ya tsaga sai jinin ya tsaya.
Daga nan wani ɗakin sirri dukkanmu muka shiga ,ni dai ban san da zamansa ba amma su sauran da alamu sun saba shigowa.Komai na cikin ɗakin baƙi ƙirin yake sannan an yi masa adon zanen Cross da jan penti,gaban wata aba mai kamar halittar duniyar sama Oga ya je ya tsaya jinina da ke cikin tasa ya dangwala a yatsa ya shafa daidai bakin halittar ,wani irin girrrr na ji a yatsan nawa kafin kuma a sannu wani abu ya game dukkan gangar jikina.A gabana dukkan members ɗin suka dinga dangwalar jinina da yatsa suna lasa da alamu ma kamar daɗinsa suke ji saboda yadda kowa ke ta ƙoƙarin ganin ya fi ɗan uwansa sha.Bayan nan sai Oga ya ja mu izuwa wani katafafen capet duk kowa ya zauna amma ni ya hana ni,na buɗe baki da niyyar tambayarsa don me banda ni,kawai na ga abokan ƙungiyarmu sun shiga yin aman kuɗi sabbi dal da su wani irin tsoro ya kama ni har ban san lokacin da na saki ihu ba.
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[23/11 à 07:44] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
08
Tun da uwar da ta haife ni ban taɓa ganin inda mutum ɗan Adam yayi aman kuɗi ba sai yanzu,tamkar wasu ruwa haka takardun kuɗin ke fito wa daga bakin kowanne members har sai da suka kusan cika ƙaton capet ɗin.Ni kuwa banda kyarma babu abin da jikina ke yi,a nan take a inda nake tsaye kuma na ƙaryata fassarar da na yi wa sunan MAFIYA daga “cikar muradi ” zuwa “tsafi da shan jini”.
Ashe ban kai maƙura wurin mamakina ba sai da na ga kuɗin na ware kansu suna yin dunƙule-dunƙule na 100k ,kamar ƙyaftawar ido suka jeri rasss a hakan kuma kowace takardar kuɗi ta san wanda ya amayar da ita .
“ HAROON wannan ɗin duk kuɗinka ne!” Oga ya faɗa yana murmushi haɗi da bubuga gefen kafaɗata.
Na ce “ duk me zan yi da uban kuɗin nan?”
Sai duk suka hau yi min dariya,can suka tsagaita Oga ya ce “ ka manta akwai aiki jajur a gabanka? Ko da kanka za ka dinga bin maƙabartu kana ciro likafanin?”
“Wane irin likafani kuma?” na tambaya cikin tsoro.
Oga ya haɗe rai ya ce “ wanda zai taimaka ma ka yi tsawon rai nan gaba,ko ka manta ne?”
Murya na rawa na ce “ ban manta ba amma Oga ai sai nan da shekara biyar ko?”
“Bayan wannan akwai wasu sharuɗan! Kowanne ƙarshen wata za ka samo mana jinin period na budurwa,kar ka tambaye ni ta yaya .Ka fara tunanin hanyar da za ka bi ka kawo na wannan watan don yau muna ashirin da uku ga wata”
Wasu irin yawu na haɗiye masu mugun ɗaci,ido kawai na tsura musu da alamu ko a jikinsu sai harakar gabansu suke suna saka min uban tulin kuɗin a jakakuna.
“Amma Oga ina zan ajiye kuɗin nan? ”
“Bisa kaina”
“Ka yi haƙuri in na je da su gida Ammy za ta zarge ni ”
Ran Oga ya ƙara ɓace wa ya ce “ HAROON ka fita idona,kana yawan matsa min da zancen Ammynka in ba ka yi sa'a ba kai ne za ka yi silar mutuwarta ”
Gabana ya bada rasss jin wata lukutar masifa,amma na kawar da tsoron gefe na ce “ wannan shine babban kuskuren da za ka yi kuwa a duniya shine taɓa Ammyna,duk duniyar nan banda tamkar ta.Kar ka manta silar ta ne a yau nake cikin wannan ƙazamar rayuwar,Ammyna ita ce komai nawa in babu ita ban ma ga tsiyar da zan yi a duniya ba” duk wurin tsit yayi suna kallona shaye da mamaki,na sani sarai yadda duk ake tsoron Oga ni ma ina tsoronsa amma ba zan juri a taɓa Ammyna ba ko kaɗan ai gwara ya yanki fatar jikina ya fi yi min sauƙi.
Ban taɓa ganin Oga cikin fushi irin haka ba sai yanzu,tako ɗaya yayi ya isa inda nake idonsa sun kaɗa sun yi ja sosai.
“Ōgāfōr̃!” furucinsa kusan tsinke igiyar da ke saita mini numfashi yayi,na riƙe