Showing 27001 words to 30000 words out of 44401 words
ta shiga ta soma yin wanka sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita .Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata”
Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai dace mace mai takaba ta fita ba”
Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani abu ne da ya haifar miki da hakan”
“Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?”
“Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su yi sallama.
Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta.
Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?”
Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci haihuwar ce ta zo bilhaƙi.
Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ”
“Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta fara wani gurnani mai haɗe da nishi.
“Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa.
Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana Goggo cire mata kayan ba.
Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara juya ido tare da soma kai wa kurwar jinjirin hari sai dai ba ta ida cin galaba ba nishin Safeenat haɗi da kukan wata babyn ya dawo da ita hayyacinta.
Ƙirjin Goggo Hajara ne ya kusan ɓallewa zuciyarta ta faɗo tsabar firgici,jaririyar da faɗo cibinta a yanke yake sannan kuma babu marakiya saɓanin shi namijin da har yanzu take masa reto.
Sai a lokacin ne ma ta samu zarrar yanke mahaifar,ba tare da kuma ta san dalilin kawar mata da mugun nufinta ba ta soma kimtsa Safeenat wacce babu laifi ta dawo hayyacinta.
Goggo Hajara ta wanke kayan da kuma gyara ɗakin ta saka turaren wuta,ita ce kuma ta zaɓo wa Safeenat riga da zane.Har da haɗo mata tea mai zafi ta sha,gefe ta koma bayan ta gama komai tana tunanin zuci ‘ mi ya shiga kaina ni Hajara? Kamar ni kamar ba ni ce ba’ kukan jariran ne ya katse mata tunani ,ta ce “ ki ɗora su ga abincinsu” sai kuma miƙe ta soma nuna mata yadda za ta yi.Namijin kawai ya sha ita kuwa macen baya ga kuka babu abin da take,Goggo Hajara na ɗaukar ta sai kuma ta yi shiru kamar ba ita ce ke kukan ba.Muƙut ta haɗiye wasu yawu hango wani baƙin kallo daga cikin ƙwayar jaririyar da ko minti talatin ba a yi ba da haihuwarta......
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
22/09/24
3
Sannu a hankali Gwaggo Hajara ta soma jin wani sanyi na ratsa ɓargo da tsokarta,kamar wacce aka yi wa doli kuma ta ƙi kawar da dubanta daga cikin idon Babyn.Idonta suka soma kafewa saboda wata irin shaƙa da ta ji an yi wa wuyanta,babu shiri ta buɗe bakinta na maita kurwar jaririn da ta soma cin galaba kansa ta fara fitowa daga can cikin hanjinta tana fitowa ta bakinta .Wani koren hayaƙi ne ya soma shiga cikin jaririn wanda daga bakin Gwaggo Hajarar yake fitowa,wata irin atishewa ya soma yi kafin ya tsala kuka.
Da mugun sauri ta yi baya ta zauna kan kujera,idonta na kan babyn wacce tuni ta soma bacci.
“Gwaggo ya ƙi yin shiru ko cikinsa ke ciwo?” Safeenat ta faɗa kamar za ta yi kuka tana ririga yaron,ran Gwaggo Hajara ne yayi mugun ɓaci sai yanzu tunaninta ya dawo a tunzure ta ce “ uban mi zan yi masa to? Lokacin da na yi haihuwata uban wa ya kama min wurin rainon ? Ki riƙe abin ki” ta faɗa tare da ajiye mata babyn kusa da ita,jikin Safeenat sai yayi sanyi dakyar ta samu yayi shiru bacci ya ɗauke shi.Ta shimfiɗe shi kusa da Baby girl ɗin kafin ta je ɗakinta don ɗauko wayarta,tana dawowa sai ta hangi maciji kan jaririyar duk ya naɗe jikinta da shi ba ta san lokacin da ta saki wata ƙara ba wacce ta yi daidai da ɓacewar macijin.Safeenat ta zo da mugun sauri ta ɗauki yaranta ta mayar da su ɗakinta,sai da aka ɗauki lokaci kafin nutsuwarta ta dawo ta soma kiran mutane tana shaida musu zancen haihuwar.Hatta Daddy sai da ta kira shi ta sanar da shi,babu jimawa kuwa sai ga ƙanwarsa Habiba ta zo gidan sosai Safeenat ta ji daɗin ganinta musamman da ta ga har da ƙullin kayanta ta zo da alamu za ta jima.
Ruwan zafi ta je ta ɗora cikin ƙatuwar tukunya kafin ta dawo,“ Safeenat ya zama doli ki kula da yaran nan musamman namijin don na ga shi ne mai rauni” Habiba ta faɗa tana shafar twins ɗin.
“In sha Allah Gwaggo Habibah zan yi,da alamu ma ya fi kuka dakyar na samu yayi baccin nan” cewar Feenat.
“Hum! Baccin wahala ne,ah to ai doli ma yayi Allah dai ya kyauta”
“Amen!" Feenat ɗin ta amsa ba tare da ta san dalilin Gwaggo Habibah na faɗar haka ba.Bayan ruwan sun tafasa ta juye su ta yi wa yaran wankan,namijin ana saka shi a ruwa ya farka tare da canyara kuka amma ita hajiya babba har aka gama wankan tana bacci tamkar wacce ba ta rai.Gwaggo Habibah kuwa sai murmushi take tana jin wani farin ciki ƙasan ranta,dama ita Allah bai taɓa bata haihuwa ba .
Safeenat ma sai da ta yi wanka da ruwan zafin ta gasa kanta da kyau ta fito ɗaure da towel,sai kuma yanzu ne Gwaggo Habibah ta lura da yadda fatar Safeenat ta yi ja.Da wani mugun sauri ta tashi ta cabke hannunta da ke ƙoƙarin ɗaukar kwalbar mai,“ jira na duba na gani” ta faɗa tana mai duba man ba tare da ta ce komai ba sai kuma ta fita direct ɗakin Gwaggo Hajara ta wuce ko sallama ba ta yi mata ba kuwa ta yi tsaye kai gare ta tana mai cewa “ an gaishe da uwar mugaye ta duniya,wato baƙar zuciyarki na nan daram babu canji .To asirinki ya tonu na ga bala'in da kika zuba cikin man shafawar Safeenatu,sai dai ki sani sai dai ki ci kanki amma Twins sun fi ƙarfinki ”
Da wani mugun sauri Gwaggo Hajara ta tashi zaune,dama tun bayan da ta shigo ɗaki take jin duk jikinta babu daɗi dalilin kwancin da ta yi kenan sai kuma yanzu da ƙanwar mijinta ke feso mata kalaman rashin mutumci.Wani makirin murmushi ta yi kafin ta ce “ da alamu dai kin manta wace ce ni ko Habibah? Amma za ki gani”
“Babu abin da zan gani sai alkhairi...”
“Eh lalle wuyanki ya isa yanka” Gwaggo ta faɗa tana juya ido,Habibah ta tuntsire da dariya ta ce “au kin zata guntun tsafinki zai iya yin tasiri a kaina? To ki canza shawara tun wuri bai ƙure miki ba don yanzu daidai nake da ke”
Ganin alamun tabbas ba Habibar da ce ke tsaye a gabanta ba yasa Gwaggo Hajara haƙura da surkullen,idonta masu cike da mugunta ta tsura mata ta ce “ mi ya kawo ki ɗakina?”
“Ina so ki fita sabgar Safeenat da ƴaƴanta,in kuma ba haka ba....” sai kuma ta yi shiru tana cije baki haɗi da jinjina kai.
“Ki tona min asiri? A tunaninki akwai wanda zai yarda? Hahaha! Yaro man kaza,Habibah kar ki manta hatta gyatumarki a tafin hannuna take....” ta yi saurin katse ta da “sai dai shi wanda kike tutiyar da shi mugun tsafinki bai yi tasiri kansa ba ,na san kin san haka”
Ran Gwaggo Hajara ne ya ƙara yin baƙi,duk duniyar nan Habibah ce kawai ta zame mata ciwon ido duk yadda take son gudanar da lammuranta to muddin tana ga wuri sai ta roga su.
Ƙarar buga ƙofa ce ta maido ta daga guntun tunanin da take,ta bi bayan Habibar da mugun kallo tana jin baƙin cikin da ba ta da MAITAR IDO (MRS SADAUKI,duk mai son complete book ɗin nan zai iya tuntuɓa ta kai tsaye ta lambar da na rubuta a can sama) da tabbas ta jefa wa Habibah ƙwayar cutar da za ta zama ajalinta.
SAKEENATU
Tana tashi daga aiki ta fito don samun adaidaitar da za ta kai ta can gidansu Safeenat kwatsam sai ga kiran wayar mijinta Abbas .
“Mamuh ta ce yau ba ki bar mata abin da za ta ci ba ina son sanin dalili?” shi ne abin da ya fara cewa ko sallama babu,ran Sakeenatu ya ɓace amma ta haɗiye shi ta ce “ na samu ƴar aiki fa kuma kafin na fito na shaida mata kan ta girka mata abin da za ta ci”
“Ƴar aiki za ta kula da uwata? Keenat mi ya shiga kan ki ne? Yanzu dai na baki minti goma ki tabbatar kin yi mata girkin abin da take so” yana gama faɗa ya yanke kiran.
Tamkar za ta fashe haka take ji,mai ɗan sawu ma dakyar ta faɗa masa inda zai kaita.Tana shiga gidan ta tarar da Mamuh zaune kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani yamutsa fuska,gaban Sakeenatu ya faɗi kamar kullum muddin dai za su haɗa inuwa ɗaya da surukarta ta.
“Barka da yamma Mamuh” ta faɗa murya na rawa,Mamuhn ta ce “ in kin gama yawon tanbaɗar sai ki shiga kitchen ki girka min wake da shinkafa”
Idonta tab ƙwalla ta shiga kitchen ɗin ta ɗora tukunya ko kayan ba ta cire ba haka ta tsaya sai da ta tabbatar ta gama sannan ta zuba a plate ta kai wa Mamuh.
Da zafi da komai ta saka hannunta tana ci mai na bin hannunta sai wani lumshe ido take alamun yana yi mata daɗi, Sakeenatu wacce ta tsaya don ganin ko yau ma Mamuh za ta yi irin yanayin nan sai kuwa ta ga ta yi.Idon Mamuh sai wani haske-haske suke fitar wa kamar kullum muddin dai wake da shinkafa ta girka mata.
A tsorace ta nufi ɗakinta ,kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet.Shower ta sakar wa kanta,kamar abun almara haka ta soma jin yanayin jikinta na canzawa tana jin feeling wanda kuma abu ne mai wuyar faruwa da ita muddin dai ba Abbas ke a wurin ba.
Abu kamar wasa amma sai yin gaba-gaba yake,kafin Sakeenatu ta farga tuni ta hankalinta ya soma gushewa ta dumulmiya duniyar son kasancewa da mijinta.Tamkar a mafarki ta soma jin kamar ana wasa da sassan jikinta,sai dai idonta sun yi nauyin da ba za ta iya buɗe su ba ballantana har ta ga shin zahiri ne ko kuwa? Sama da minti goma tana cikin wannan yanayi kafin ta dawo hayyacinta,a doli ta tsarkake jikinta ta fito tana mamakin al'amarin.Bayan ta shirya tsab cikin riga da zane sai ta fito falo,Mamuh ta gani sai sharar bacci take kamar matatta .Dining ta je ta zauna ta buɗe kulolin da ƴar aikinta ta yi girki,shinkafa ce da miyar kaji haka ta zuba ta soma ci tana mamakin yadda aka yi Mamuh ta zaɓi cin wake da shinkafa akan lafiyayen abincin nan .Bayan ta gama ta ɗauki waya ta kira Safeenat ta shaida mata za ta zo yanzu ,sai kuma ta koma ɗaki ta saka hijabinta ta ɗauko jaka ta fito.Tana fita ba ta wani wuya ba ta samu ɗan sawu ya kaita,da sallama ta shiga gidan har ta wuce can ɗakin da Safeenatu take wanda ya cika da mutane kusan dangin Bashir ne.
A mutumce take gaishe da kowa amma yanayin jikinta na bata ana kallonta,tana juyawa suka haɗa ido da Habibah wacce ta kasa ɗauke idonta kan Sakeenatu har sai da ta ji ta tsargu.Ta zauna kusan Safeenat tana mai cewa “waccan wace ce sai kallona take?”
“Ƙanwar Daddy ce fa ba ki gane ta ba?” Feenat ta faɗa tana mai miƙa mata boy bayan ta shafi kansa sai kuma ta ajiye shi aka miƙa mata girl ɗin.Wani irin shock ne ya ratsa Sakeenatu har sai da ta zabura,yayin da gabanta yayi mummunar faɗuwa ganin Babyn ta buɗe idonta tana kallon ta alhalin lokacin da aka miƙo mata ita tana bacci.Sakeenatu ba ta ida shiga tashin hankali ba sai da ta ga tamkar Babyn na yi mata murmushi......
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
23/09/24
4-5
Wani irin abu ne marar misaltawa ke ratsa Sakeenatu tun daga kan babban yatsan ƙafarta har zuwa kwanyarta da ta soma toshe wa .Lamarin da take ji a al'aurarta kuwa kusan girme wa hankalinta ya yi,tamkar wacce ake fitar wa da wani dafi haka take jin ana yi mata motsi gami kuma da samun sassauci a doli ta lumshe ido ba ta shirya ba.Ita kuwa Gwaggo Habibah da ke can gefe sai murmushi take tare da yin zancen zuci don duk tana ankare da abin da ke faruwa.‘ Tabbas a duk inda ke da mugunta da cutar wa Allah sai ya kawo mai ceto mai magani,na zo kenan a gidan nan mutuwa kawai za ta fitar da ni zan saka ido sosai akan jaririyar nan zan raine ta da hannuna ta yadda zan taimaka mata wurin fahimtar baiwar da Allah ya yi mata da yadda za ta sarrafa ta’ sai kuma ta miƙe tana yin wani murmushin nasara.Babyn ta ɗauke daga cinyar Sakeenatu wacce gumi ya jiƙa ta har goshinta na ɗiga,babu kuma wanda hankalinsa ke wurin hatta ita Safeenat sai hira take da dangin mijinta waɗanda suke cewa shi namijin a saka masa suna Bashir a yi madadi.
Sakeenatu ta ware idonta jikinta na ɗan rawa kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki.Idonsu ya sarƙe cikin na juna,Gwaggo Habibah ta ce “ sannu! Bari na nemo miki ruwa masu sanyi” sai kuma ta shimfiɗe babyn wacce tuni ta koma baccinta.
Kitchen ta nufa don samo ruwa masu sanyi,sai suka yi kiciɓis da Gwaggo Hajara ƴar kallon-kallon suka yi kowacce na hararen ƴar uwarta.
“In tusa za ta iya hura wuta a yi mu gani mana,sai shegen kinibibi da nuna isa kan an san ɓoyayyar duniya nan kuma ba asss ” Gwaggo Hajara ta faɗa don kuwa a goshin Habibah ta fahimci sun karya wata muguntar tsafi.
Ita kuwa Habibar murmushi ta yi don ta fahimci mi take nufi wato in ta isa ta yi wa kanta maganin damuwarta.“ Nan gishirinki zai ƙare a dafuwar ƙaho,yadda bacci ya bar ido haka za ki gaji ki bar Habibah saboda kabewar kan kabari nake baƙin cikin masu taushe”
“Aikin banza sai aukin cika baki ,a hakan kuma na yi sanadin hana ki baccin kullum cikin kukan kin ƙi haihu ba”
“Haihuwa ai ta Allah ce,kuma alhamdullah yanzu na samu irina wacce tsoron samun ta yasa kika jefo min mugun nufinki ” Habibah ta faɗa tana wani murmushi,Gwaggo Hajara ta kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ ko ba ki gane abin da nake nufi ba? To Safeenatu ta haifi wata Habibar sak irina ce ko na ce ma ta fi ni don ita murucin kan dutse ce ba ta fito ba sai da ta shirya” muƙut! Gwaggo Hajara ta haɗiye wasu yawun tsoro don kuwa ta fi kowa sanin babyn Safeenatu ba normal jaririya ce ba tun da ta ga zahiri.
Ta ja wani irin numfashi jin saukar ruwan sanyi kan fuskarta,dakyar ta ware ido tana kallon Habibah wacce tuni ta juya ta yi tafiyarta tamkar ba ita ce ta gama zuba mata ruwan a fuska ba.Cike da baƙin ciki ta koma ɗakinta,a yadda take jin jininta ya hau in ba jini ta sha ba ƙila zuciyarta sai ta buga.Tukunyar tsafinta ta ɗauko ta yi ƴan surkullenta kafin ta ɗauki mayafi ta fita waje,yara ta gani suna wasa daga inda take a tsaye ta soma kiran kurwar wani yaro cike da ƙwarewa wurin maita tsafi.Yaron ya dafe gefen wuyansa inda ya ji kamar an tsikare shi da allura amma bai bar wasar ba haka yake ci gaba da gudun yana son kamo wani,idonsa ne suka soma rufe wa kafin bugun zuciyarsa ya tsaya cak kawai sai ya faɗi ga ƙasa.Ita kuwa Gwaggo Hajara da wani mugun sauri ta rufe ƙofa,tuni yara sun fara ihu suna faman kiran sunansa.
Ɗakinta ta koma ta ci gaba da tsotse jinin yaron ko jira ba ta yi ba,don ta san sarai