Showing 36001 words to 39000 words out of 44401 words
waken ni ma na ci yunwa nake ji”
Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“ uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?”
Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita .
Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido
My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
28/09/24
10
A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan zuciyarta.
A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta.
“Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi.
Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“ wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice.
Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi.
Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki’
“Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?”
“Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?”
“Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo”
Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna.
Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’
“Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?”
“Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa.
Hajiya ta ce “ karɓar ta” tana mai miƙo Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce “ Hajiya don Allah ki riƙe t...” ba ta kai ƙarshe ba Hajiya ta miƙe ta je ta shimfiɗe Baseerat a shimfiɗa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ƙirjin Hajiya saura ƙiris ta faɗi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya ɗebe ta.
Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ƙatuwar gora.
“Habibah bani pilow bacci nake ji” cewar Hajiya ,da sauri ta ɗauko ta miƙa mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta .
Safeenatu ta ce “ Gwaggo Habibah ni fa na fara jin tsoron lamarin Baseerat kina dai ganin abin da ya faru, wannan ai ba zan fita da ita unguwa ba gudun ta jawo min masifa ace mayya ce ma”
Da mugun sauri Habibah ta katse ta “ kar na sake jin kin faɗi haka,saboda ƴarki ba mayya ce ba ƴar baiwa ce”
“To amma ai wasu ba za su ganin haka ba ko? Tun yanzu tana jaririya tana haka ina ga ta girma?”
Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ Safeenatu bari dai na soma ɗan guntsira miki labaran duniyar ɓoye, kowane mutum da kike gani a duniyar nan yana da matriculation na sama.Ko kuma lambar sirri ta samaniya,da wannan ne in aka sayar da ruhin mutum daga lokacin matriculation ɗinsa ta saminiya sai ta canza.Duk wani ɗan Adam kasance yana da taurari iri-iri waɗanda suke taimakawa wurin gudanar da al'ammuran duniyarsa.Ya zama doli kowa ya kare taurarinsa ya basu tsaro,muddin ka yi sakaci da su kuma to wannan mutumin zai iya zama cikkaken maƙasudi wurin tallafawa masu sayar da taurari su ƙwace masa su.”
Safeenatu ta katse ta da cewa “ ta ya za a ƙwacewa mutum taurarinsa alhalin mallakinsa ne?”
Gwaggo Habibah ta bata amsa da “ ba ki taɓa jin labarin wata ma'aikaciyar saloon ba mai gyaran gashi? Ki nemi littafin Mrs Sadauki na MAITAR IDO a nan duk za ki samu cikakken labarin.Ki sani cewa matsafa don su kama ruhinka ma abu ne mai sauƙi,abin da suke buƙata shi ne kawai keɓaɓen abu na gaskiya ta atomatik da ke fitowa daga mutumin da ake son cutarwar,kamar gashinsa,sunansa,date ɗin ranar haihuwarsa,zufar jikinsa wato tufafin da ya saka ba a wanke ba,ko kuma jinin jikinsa.Daga lokacin da matsafi ya riƙe ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya buɗe katinka na samaniya kuma ya karɓe ƙarfin ikonka wato power daga nan sai yayi abin da yake so”
A sanyayye Safeenatu ta ce “ duk Baseerat za ta iya yin wannan? Gaskiya ni dai ban so in kin san hanyar da za a toshe wannan baiwar tata ni dai ki taimaka min don ina ji a jikina muddin aka bar ta da ita a gaba za ta zame mana masifa”
Gwaggo Habibah ta yi mata wani irin kallo irin na ba ki da hankali kafin ta je ta ɗauki safar hannun ta saka ma jaririyar wacce ta buɗe ido sai kalle-kalle take kamar mai wayo,kafin kuma ta kafe idonta ga madubi Gwaggo Habibah ta yi kasaƙe tana kallon Baseerat a sannu a hankali ta ga idon yarinyar na sauya kala har suka zama farare tasss babu ɗigon baƙi,wani abu kuma ya soma fita daga bakinta yana bin direction ɗin madubi.Habibah ta ja wani dogon numfashi don kuwa ta fahimci Baseerat za ta yi tafiya ne ko kuma yawon buɗa ido wanda dayawan mutane na yinsa ba tare da sun san mine ne ba.Sai ka ji tamkar jikinka ya zama gawa kana son tashi daga bacci amma ka kasa tamkar an danne ka da dutse,har kwatanta buɗe ido ake amma baka iyawa saboda ruhinka da yayi balaguro ya bar gangar jikinka a kwance.
#SAKEENATU
Gefen da Nafisa ke ta sharar bacci ta duba kafin ta ɗaga kanta sama tana kallon yadda rufin ɗakinta ke wani lomaƙawa tsabar yadda ake tafiya a guje.Kukan jaki da na kare ga kuma na mage duk a lokaci guda,gefe guda kuma wata siririyar murya take ji tana kiran sunanta.Idonta ya ciko da hawaye,fitsari take ji amma tsoro ya hana ta tashi.Nafisa ta soma tayar wa,ita kuwa dakyar ta buɗe ido ta ce “ mine ne ?”
“Fitsari nake ji” ta bata amsa kamar wata ƙaramar yarinya,cikin magagin bacci Nafisa ta ce “ ki je ki yi mana” sai ta koma baccinta.A hankali Sakeenatu ta zuro ƙafafunta ƙasa a tsorace ta shiga toilet ko Bismillah ba ta yi ba ballantana karanto addu'a,a tsorace ta je ta haye WC ɗin ta soma fitsari sai kuma jikin ya soma kyarma ganin ruwa na ta ɓulɓulowa ta ƙasan tile suna cika toilet ɗin ko kafin ta ƙyafta ido sun kawo mata a wuya ta yunƙura za ta tashi amma sai ta ji tamkar an saka super glue an manna ta a jikin WC ɗin ta ƙurma wani uban ihu wanda dama su mugayen shine suke jira ai kuwa suka tsaga rufin ɗakin ji kake ƙiiiiii kamar suna yaga zane.Idon Sakeenatu duk a waje take kallon yadda bindi mage,na kare da kuma idon wata baƙar mujiya a daidai wurin da suka tsaka.Cike da mugunta suka diro toilet ɗin wanda yayi daidai da tsinkewar numfashin Sakeenatu.....
My book is only 500 via 6042551755 Hassana Ibrahim Keystone bank DM +22795045822
💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛
💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)*
💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏♀️🧏♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰
💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin
💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁
💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍
💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢
💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️
💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba
💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko
💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan.
Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman
_____________________
29/09/24
11
💛💛💛GHT B-CLEAR,FEMALE CARE AND GANODERMA💛💛💛
💛💛*BACK TO VIRGIN KIT* *(SABON BUDURCI)*
💛💛Assalam alaikum Mata albishirin ku🧏♀️🧏♀️ga abin da kuka Dade Kuna mafarkin samu ya samu💃🥰
💛💛Abin nema ya samu ,Kowacce mace aduniya tana mafarkin sake kasancewa virgin
💛💛Ina manyan Mata da suka hayayyafa😁
💛💛ina zawarawa masu shirin aure😍
💛💛Ina budurwa da iftila'i ya fadawa a yayin tsallaka rame 😢
💛💛Ina Mai jego da keso ta dinke ta game tsaf ciki da waje❤️💛💛Duk ku marmatso kusa ga GHT back to virgin set na kawo muku ,magunguna ne namu na gargajiya bana bature ba💛💛Kuma Sha akeyi ,insha Allahu muddin kikayi amfani da wannan Kayan Zaki dawo da martabar ki ta farko 💛💛Sai kin gwada za ki tabbatar da hakan.
Sisters no 08142506271 mmn Khadeejah sai najiku
Duk da Sakeenatu ta suma hakan bai sa mugayen nan sun ƙyale ta ba,haka suka ajiye mata cutar a jikinta kafin su bar ta nan yashe a toilet.Cike da murna suka koma asibiti suka dinga bai wa Mamuh labarin abin da ya faru,cike da mugunta ta ce “ gobe da safe da hannunta za ta dafo wake ta kawo min ,daga nan kuma zan datse alaƙar farin cikinsu ita da Abbas zan maye mata gurbinsa ” duk suka sa dariya suna ƙara tsara mata wani salon muguntar.
Washegari
Kiran sallar asuba ya tashe da Nafisa,ta sauka daga bed ta shiga toilet nan ta ci karo da Sakeenatu a yashe babu numfashi.Hankalinta a tashe ta cika bokiti da ruwa ta zuba mata,ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta soma kuka cikin firgici.Nafisa ta kamo ta tare da fiddo ta haɗi da tambayar ta,duk a tsorace take wannan yasa ta kasa yi wa ƙanwarta bayani.Ganin haka yasa ita kuma ta je ta yo alwala ta yi sallah,bayan haka ne ta matsa wa Sakeenatu ta je ita ma ta yi sallar.Ko wanka ba su yi ba ta ce “ Nafisa tashi mu je gida wallahi tsoro nake ji” haka suka runguɗa suka je can gidan Mama wacce ke ta ƙoƙarin hura wuta domin ta ɗora ɗumame,tana ganinsu ta san ba ƙalau ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta je ta rungume mahaifiyarta tana wani sabon kukan,“ Subahanallahi! Nafisa mike faruwa?”
“Wallahi Mama ban sani ba ni ma na yi ta tambayar ta amma ta ƙi faɗa min,alamu dai sun nuna tsorata ta ake yi a can gidan nata” Nafisa ta bata amsa.
Mama ta ce “ to Allah ya sawwaƙa,ku wuce ciki bari na kira malam na shaida masa ”
Can cikin mitsitsin ɗakinsu suka shiga,Ma'idah na kwance sai bacci take ba ta farka ba.Sakeenatu ta ɗauki abarta ta rungume ƙam kamar an ce za a raba su,mugun mafarkin da ta yi kan Ma'idar ya dawo mata a kai.Ta lumshe ido ruwan hawaye na kwaranya a kumatunta,ta yi tunanin kakarta ta yanke saƙa,ba ta taɓa tunanin za ta sake yin ƙunci a rayuwa bayan wanda ta yi a baya ba tun lokacin da Abbas ya shigo rayuwarta komai ya dawo mata normal ashe da sauran kallo a sama.Tsohuwar shuɗaɗiyar rayuwarta ce kwanyarta ta soma yi mata tariya,cikakken sunanta shi ne Sakeenatu Abubakar,ƴar gwagwarmayar rayuwa mai zuciya cike da burin zama wata aba a duniya.Karatun boko shi ne abokin da ta riƙa sannan kuma tubali don gina rayuwa mai inganci,sai dai ƴan magana na cewa rashin sanin ya fi dare duhu.Sakeenatu ba ta taɓa sanin cewa ba sanadin boko ne za ta zubar da mutuncinta ba,zuwanta jami'a shi ya ƙara buɗe mata ido sosai ta waye ta zama ƴar gayu,ƙwazonta a wurin karatu shi yasa ta ciri tuta a wurin malaman makaranta kusan duk maganarta suke suna yabon baiwar da Allah yayi mata banda malam Agali wanda tun ranar da ya ɗora idonsa kanta yake jin mugun sha'awarta saboda ta haɗu ta kowanne fanni.A wata rana Laraba ce wacce ta kasance ranar farko da ya fara ɗana mata tarko da kuɗi,“ki hau taxi” ya faɗa cikin taushin murya a gaban ɗalibai ba