Showing 3001 words to 6000 words out of 44401 words
wannan mamakin ba na ji na yi sama cikin iska kafin kuma in ji ni gammm,bayana ya bugu da bango yayin da hannuwana kuma aka banƙare su tare da ɗaure su da kacar tsafi.
“Babu soyayya a tsarin ƙungiyarmu,amma kai ka karya doka! Zaɓi biyu zan baka ko dai ka sadaukar da budurwar da kake so,ko kuma na aika ka ɓoyayyar duniya yanzu nan tun kafin wa'adin shekarunka su cika”
Ido na rumtse gam,a cikin zaɓin biyu babu mai sauƙi a gare ni.Shekara biyar ta rage mini a doron duniya kamar yadda muka yi yarjejeniya a ranar da zan sayar da ruhina,an bani shekaru goma na rayuwa a wannan duniya kafin na isa ɗayar,a cikin goman kuma na yi biyar saura biyar suka rage mini.‘Wane zaɓi zan ɗauka?’ na tambayi kaina a zuci.......
[16/11 à 09:04] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
04
“Wato soyayyar da kake yi mata har ta kai ka kasa sadaukar da ita kai tsaye shi ne ka tsaya shawara? Hahaha! Ōgāfōr̃!” Oga yayi lafazin ƙarshe cikin Yaren matsafa a nan take kuma na ga tile ɗin ɗakin na darewa wata jar turɓaya na bayyana kuma sai girrrr kake shi tamkar ƙatuwar tirelar ɗan danƙarau mai yin gina.
A inda nake can sama ɗaure a jikin bango nake kallon duk abin da ke faru,gidan ƙasa ne ya bayyana sai a lokacin kuma kacocin hannuna suka kwance kansu yayin da na soma yawo cikin iska ina kaɗawa kamar wata leda.
Wasu ɗalasiman tsafi Oga ya soma kafin ya ce “ je ka ɓoyayyar duniya ka yi ziyara na tsawon kwana uku,in ka fito daga ciki sai ka bani zaɓin ka” rufe bakinsa ke da wuya na soma ji na ina yin ƙasa har na shiga dogon ramen mai ɗauke da wata daular .
Ina shiga ciki komai ya soma komawa normal ya ɗinke,sai da na ja wani numfashi sa'ilin da na ji ƙafafuna sun dogane da ƙasa.
Baƙar ƙofar na kalla ta gabana wacce nake da tabbacin ita ce za ta sada ni da ainahin abin da ake kira da ɓoyayyar duniyar.Na shagala sosai ina kallon ƙofar tare da tunanin da na san ba zai fishe ni dare ba,kawai sai na ji ƙiiiiii ƙofar ta buɗe da kanta.
Ido na tsura ina jiran ganin wanda zai fito,amma sai na ji wata murya na cewa “ Barka da zuwa duniyar Ruhaniya ” ban amsa ba haka ban gusa daga inda nake ba .
Sai na ji an kamo dukkan hannuwana biyu ana jana amma ban ganin masu jan nawa,a dole na soma taka ƙafata har muka bi ta ƙofar nan a take kuma ta rufe ji kake gammm.Duhu ne ya turniƙe wurin,sai a lokacin kuma na ga inuwar masu jaye da ni saboda wani jan haske da goshinsu ke fitar wa kamar wuta.
Ci gaba suka yi da ja na izuwa ciki,matakala muka soma takawa muna daɗa yin can ƙasa.Har muka ainahin duniyar,nan ɗin ko ina da haske tamkar goshin azahar haka.
Duk masu bi suna wuce wa na soma duba,dayansu siffar mutane ce da su yayin da sauran kuma suke ɗauke da sifofin dabbobi iri-iri.
Irin inuwar nan gani ta waɗanda suka yi min iso,a zuci na ce ‘ ko su waye su?’
“Dōr̃ānī! Masu kula da shige da ficen duk al'ummar nahiyar nan.Ko da wasa wani ya tsaya hutawa dangane da aikin da yake yi za su hukunta shi ne” na ji muryar ɗazu ta faɗa wacce ta tarbo ni tun a bakin ƙofa.
Saitin inda murya ta fito na duba,sai na ga yanzu ana ganinsa da kyau sai dai muninsa ma ba zai bari ka ci gaba da kallonsa ba.
“Amma kuma ƴan Adam ne?” na tambaya.
“Duk faɗin nan babu mai ruhin bil'adama sai kai ,duk waɗanda ka gani da irin siffarka to mutum ne da rigar aljan.Bima'ana gangar jikin ce ta mutum amma ruhin aljani ne a ciki”
“To ya ake hakan tana faruwa?” na sake jefo masa tambayar.
“Mutanen da suka sayar da ruhinsu ga MAFIYA ,bayan wa'adin shekarun da aka ɗibar musu ya cika za a aiko da su izuwa nan.Ruhikansu za su dinga yin bauta ,yayin da gangar jikinsu kuma aljanai za su ɗauke ta su dinga amfani da ita.” yana kawo wa nan sai yayi shiru yayin da ɗaya abokin aikin nasa ya ɗora da cewa “ dayawan jinnu na son ganin kansu a duniyar bil'adama sai dai babu damar yin haka don ba za su iya bayyana da siffarsu ba,wannan ya sa suka ƙulla yarjejeniya da manyan masu ƙungiyoyin asiri da su dinga sayar musa da gangar jiki”
“To mi za su yi da ita?” na yi tambayar cikin zaƙuwa zuciyata na bugawa jin ni ma abin da ke shirin faruwa da ni kenan nan da wasu shekaru.Sai da suka ƙyalƙyace da dariya kafin su yi haɗin baki wurin cewa “ duk wanda ya sayi gangar jikinka in yana so zai iya shiga duniya yayi yawo,wasu ma har auren bil'adama suke yi ”
Tsoro ne ya kama ni,sai nake ganin tamkar in na dawo da zama a duniyar nan aljanin da ya sayi gangar jikina zai iya zuwa ya cutar da Ammyna.
“Amma wanda ya sayar da ruhinsa ga MAFIYA shin zai iya karɓe shi kuwa? Ina nufin akwai wata hanya da mutum zai bi ya rushe waccan yarjejeniyar ta farko sai a kafa masa ta biyu?” duk shiru suka yi suna kallona,na gyara tsayuwa tare da matsawa can gaba ta yadda za mu yi facing juna na ce “please ku sanar da ni”
“Eh to ba za a rasa ba,sai dai sharuɗan suna da tsauri sosai”
Duk da ban ji su ba haka na ji raina ya ɗan sanyaya har sai da na sauke ajiyar zuciya da kuma ɗan guntun murmushi ko ba komai zan samu damar da zan yi rayuwa da abar ƙaunata.
Muna nan tsaye wata rundunar wasu inuwoyi ta zo wuce wa,inuwar siffar mutum ce da ita amma babu gangar jiki.
“Ka ga wannan shine ruhi! ” ya faɗa.
“Amma suna jin magana?” na tambaya,babu wanda ya bani amsa sai yin gaba suka yi har na soma take musu baya suka ce “ kar ka biyo mu,tuni mun gama aikinmu yi maka iso da kuma amsa tambayoyinka”
“To amma ina zan je?” na yi tambayar cikin ɗaga murya,ko juyo wa ba su yi ba ballantana su bani amsa a haka suka ɓacewa ganina.Sai a yanzu ma ne na ji mugun tsoro ya shige ni fiye da na farko,haka na soma bulaye a ƙatuwar duniyar ina kallon abubuwan ban mamaki har na isa wani wuri inda ake yi wa wani aski.Duk suka ɗago suna dubana kafin su fara ƴar kallon-kallon,ɗaya daga cikinsu ya ce “ wane ne kai?”
Ba tare da wani tunani ba na basa amsa da “ Ni bil'adama ne!” ko ida rufe baki ban yi ba suka yi min caaaa kowa na faɗar ra'ayinsa“ a'a ni zan ɗauka! ” “A'a wannan fa gangar jikin tawa ce! ” “ kai kana da wajen biyu fa ka bar min kawai”
Ido kawai na rumtse ina rawar jiki,jin ana rigima akan gangar jikina wacce Allah ne ya halitta min ita amma saboda wata buƙatata na butulce wa rahamarsa na sayar.Ina cikin haka ne sai na soma jin canjin yanayi,ina ware idona sai na koma fanko wato ruhi babu gangar jiki.Da ido nake kallon yadda ake faɗan shiga gangar jikina wacce ta zama tamkar riga mai haɗe da wando............
Talla! Talla! Talla!!!!
Set d'in gyaran gashinmu na dauke da
* Shampoing don wanke gashi
* Man ganshi da zai taimakawa gashin wajen k'ara tsayi
* Man gashi wanda zai cire miki kwarkwashi/dandruff/Pellicules
* Garin ambunu da zai hana karyewar gashi
* Man karkar da zai taimakawa gashi wajen k'ara bak'i
* Garim amrfit don sakawa a hamata ta kasance cikin kamshi
* Man coco na asali don gyaran fata
+22780416252
[17/11 à 15:36] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
05
Ni da gangar jikina amma banda iko da ita wannan lokaci,ban ma san taƙamaimai ya zan yi na mayar da ruhina a cikinta ba ko kuwa sun maido min ita.A yanzu da nake gantali cikin iskan ɓoyayyar duniya sai na fahimci a cikin MAFIYA ni ba kowa ne ba fa ce ɗan ƙaramin jinjiri ashe ban san komai a kanta ba.
Dōr̃ānī kamar yadda aka sanar da ni sunansu tun shigowa ta nan,irinsu ne su biyu suka zo suka ƙwace gangar jikina daga hannun aljanan kafin su miƙo min .
“Ka shiga gangar jikinka sannan ka koma duniyarku tun da wa'adin da aka ɗebar ma ya cika,ka yi kwana uku cicif ”
Tsakanin furucinsa na cewa na yi kwana uku alhalin ni dai a lissafina ba zai wuce na yi minti talatin ba,da kuma tunanin yadda zan mayar da gangar jikin nawa a ciki sai na rasa wane zan yi.
“Ka mayar mana za mu mayar da kai” ya ƙara faɗa .
“Ban san ya zan yi na mayar da ruhina a ciki ba” na basa amsa.
Suka kalli juna kafin kuma su haɗin baki wurin cewa “ kai ɗin ba ahalin MAFIYA ba ne?”
Na jinjina kai na ce “sosai ni ɗin ɗana ga Mafiya amma ban san ya ake yin duk abubuwan nan ba” ban rufe bakina ba na ji sun soma karanta wasu ɗalasima wanda na yi imani na tsafi ne.Wani girrrr na soma ji,gangar jikina na haɗe wa da ruhina ban san ta yaya hakan ta faru ba amma tabbas yanzu na dawo HAROON ɗina.
Na ja ajiyar zuciya lokacin da suka ja ni izuwa can wajen ƙofar fita,na kasa haƙuri na ce “ amma ɗazu kamar na ji ka ce wai har na yi kwana uku a nan,sai nake ganin kamar minti talatin ne ko zuwa da biyar haka”
“Lokacin nan ba iri ɗaya ba ne da na duniyarku,duk minti goma ɗin ku matsayin kwana ɗaya yake a nan” ban kai ga ƙara yi masa wata tambayar ba suka cillo ni waje.
Ta hanyar da na bi na shigo nan ta haka na koma,a gaban idona yanzu ma can saman ya tsage kamar wata leda marar nauyi haka na tashi cikin iska na fito har tsakar fadar Oga ,tile ɗin ya koma ya ɗinke kansa.
Ɗaya bayan ɗaya nake kallon members ɗin ƙungiyar tamu,da dukkan alamu sun shirya wa fitowar tawa kamar yadda nake tsammanin Oga ya sanar da su komai.
A cikin abin da bai fi minti biyu ba na ga wani sabon abu wanda can farko ban taɓa ganinsa ba,ba komai ne bai sai shatin Cross a goshin kowa na member ƙungiyar sannan a ƙasan Cross ɗin kowanne daga cikinsu yana da alamun lamba,wasu 9,wasu 18 da dai sauransu.Ban yi nauyin baki ba wurin cewa “ Oga lambobin mene ne nake gani a goshi mutane?”
Bai bani amsa ba sai jin shuuu na yi,wani ɗan madaidaicin madubi ne ya zo yayi tsaye a gabana,ba wai wani ya riƙe shi ba a'a shi ke riƙe da kansa.A ta cikin madubin na hango hoton fuskata,wannan karon da tsokarta irin ta ƴan adam ba ƙwarangwal ce ba.Lamba ɗaya(01) na gani a tsakiyar goshina kuma ni ma ina da zanen Cross ɗin,ina gama gani madubin ya ɓace daga gabana.
Sai a lokacin Oga ya soma magana,“ Barka da shigowa wani level daga cikin MAFIYA! A can farko ba kowa ne kai ba face costumer mu,amma a yanzu kana level 1 sannan kamar yadda ka nemi alfarmar janye yarjejeniyar mu ta farko domin kawo wata sabuwa,mun karɓi kokenka.Sai dai kamar tun can farko yanzu ma zan sake jaddada maka cewa kowanne tasiri yana da farashi,ina nufin yanzu shekaru biyar ɗin da suka rage maka a duniya za ka iya ƙara su domin yin doguwar rayuwa” yana kawo wa nan sai yayi shiru tare da nuna mini kujera na je na zauna kamar sauran.
Zamana kan kujerar sai na ji tamkar ba normal kujera ba ce amma na dai yi shiru kawai ina jiran ƙarin bayani.
“ HAROON ?” Oga ya kira sunana,na ɗaga kai na kalle shi sai kuma na je zan mayar da shi ƙasa amma ya hana ni ta hanyar ce mini “ tsakiyar ido za ka kalle ni sannan ka sanar da ni ka gani a ciki”
Har sai da na ɗan ƙanƙance idona don ƙara samun tabbacin abin da nake gani shin gaskiya ne ko kuwa?
“Mi kake gani?” ya jefo mini tambayar.
“ Maƙabarta!” na basa amsa.
“Ka san me ake yi a can?”
“Eh na sani Oga!”
“Yawwa madallah da kai HAROON tabbas alamu sun nuna kana yunwar ƙara tsawon rai” cewar Oga kafin ya nufi allon da yake yi mana rubutu ko nace darasi.Wani suna ne ya rubuta mai harafi bakwai wanda tuni na soma tambayar kaina ‘ mene ne kuma alaƙarmu da sunan?’ ashe kuwa amsar na kusa.
“ HAROON ko tashi ka karanta mana abin da ke rubuce a nan” Oga ya umarce ni.
Na tashi tsaye kamar yadda ya buƙata kafin na karanta “ likafani ”
“Ƙwarai kuwa likafani ne kamar yadda ka karanta ɗin,ka yi daidai ina fatan kuma aikin da za ka yi da shi shi ma ɗin ya zama daidai”
“Aiki kuma Oga?” na tambaya cike da tsoro,duk kowa ya kwashe da dariya sai da suka yi son ransu kafin Oga ya umarci kowa yayi shiru.Fuskarsa babu alamun wasa ya dube ni yana cewa “daga lokacin da wa'adin shekaru biyar ɗinka ya cika to za ka dinga farautar likafanin sabuwar gawa domin luluɓa shi a jikinka ka kwana da shi,ta wannan hanyar ce kawai za ka ci gaba da rayuwa a wannan duniyar akasin haka kuma za ka koma inda ka fito yanzu.Na sanar da kai ne tun yanzu don ka zamana cikin shiri,abu na biyu kuma da ƙungiya ke buƙata a wurinka shine tsofin takalmi na yara ƙanana.Kowa zai iya tafiya meeting ya ida” yana gama faɗa ya bi wata hanya ya shige yayin da kowa ya watse ya bar ni cikin zullumi.
Dole dangin na ƙi ce ta saka ni fitowa ni ma,sai yanzu na tuna inda na bar motata wato can tsohon gidana.Taxi na shiga aka kai ni can amma abun mamaki babu motar a nan,a dole na ƙara shiga wata taxi ɗin na nufi gida.
Tun a bakin ƙofa na ga kallon da direbana ke yi mini,kamar zai yi shiru sai kuma ya kasa ya ce “yalaɓai yanzu ko minti ɗaya ba a yi ba na ganka da baƙaƙen suite fa kuma ga shi har ka canza kaya”
Na haɗe rai na ce “wato sa ido kake yi min?”
“Yi haƙuri yalaɓai” ya faɗa yana rusunawa.
Ina shiga cikin falo na ci karo da Ammy ita ma idon ta waro tana cewa “ HAROON canje-canjen kayan na mene ne? Ko don ka burge Malama Zainab ne? Hahaha! Wannan kayan fa kamar ma sun yi datti,waɗancan ɗin dai sun fi yi maka kyau”
Murmushi kawai na sakar mata ina cewa “ina zuwa” sai kuma na haye can sama,ina buɗe ɗakina na hangi irina sak yana ƙoƙarin shiga madubina.
“Dakata!” na faɗa da sauri,ya juyo muka haɗa ido amma bai saurare ni ba yayi wata suka cikin madubin tamkar wanda ya shiga ruwa haka ya nitse ciki tun ina ganin inuwarsa har madubin ya dawo normal........
Assalamu alaikum,mata da ƴan matan garin Agadas.CHAFA'ATU MAKE-UP fitacciyar kuma jajirtaciya mai koyar da kwalliya iri-iri.Ta yi tattaki tun daga Nigeria ta zo nan Nijar a garin Agadas domin horar da masu buƙatar koyon kwalliya,ɗaurin kallabi.Wannan horar wa da za a yi za ta kwashi kimanin sati biyu ,kuɗin koyo jika ashirin ne (20.000f).Ga masu buƙatar ƙarin bayanin za su iya kiranmu kai tsaye ta wannan lambar 88584336 ,ko kuma ku tuntuɓe mu lambarmu ta WhatsApp 09041604348 .
[19/11 à 07:55] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
06
Gaban madubin na je na soma shafa shi tamkar wasu ruwan Teku haka na ji hannuna ya nitse a ciki.A kullum cikin ganin sabbin abubuwa nake tare da madubin da ni ne da kaina na saye shi,maimakon da na saka hannuna na ga ya nitse na fiddo shi a'a sai na gwada shigar da dukkan gangar jikina.
Hazo-hazo na soma gani a cikin sabuwar duniyar da na tsunduma kaina,ban ganin komai sai wani abu da ke zuba kamar dusar ƙanƙara .Idona na soma ƙanƙancewa nan na hango gobena,ga ni tare da Malama Zainab har da yarinyarmu.Wani daɗi ya wanzu a zuciyata,ina son ƙara samun wani bayanin amma daga can waccan duniyar nake jin muryar Ammyna a kunnena raɗau.Da sauri na fito ina mamakin ‘ dama ana iya shiga cikin madubi ? ’ Sai kuma na watsar da tambayar na nufi ƙofa na buɗe murmushi kan fuskata.
“ HAROON ka fito mana ko ka manta yau rana ce ta musamman a gare mu?” Ammy ta faɗa tana murmushi tare da gyara min zaman rigata ta sama.
Sai yanzu na lura,kayan jikina sun sauya daga waɗanda na shigo da su zuwa irin mai kama da ni da ya ɓuya cikin madubi.
‘ Wane abu ne zai faru mai muhimmanci haka?’ na yi wa kaina tambayar a zuci,yayin da kuma na samu amsar tambayar kuma a cikin kwanyata “ yau za ka sanar da Malama Zainab kana son ta,shine alƙawarin da ka yi wa Ammy ”
Shiru na yi ina tunanin ‘ ta ya aka yi nake jin muryar mutum na yi min magana cikin ƙwaƙwalwa? ’
Nan ɗin ma wata amsar aka bani “ saboda yanzu ka fita daga matsayin 0 ka koma level 01 ,kana da buƙatar ɗan kariya mai baka rahoto akan abubuwa da dama, waɗanda suka faru da kuma shawara wurin yanke hukunci”
Ajiyar zuciya kawai na sauke ina kallon Ammy tsakiyar ido,“ ya dai? Kar ka ce min dai tsoro kake ji?” Ammy ta faɗa ,na girgiza kai na ce “ mu tafi ga ta can har ta iso”
Da mamaki Ammy ta ce “ ta ya aka yi ka san ta iso?” sai ta ja kumatuna.
Abin da na fahimta wannan ɗin sam ba furcin tunanina da niyyata ba ne, mataimakina