Showing 12001 words to 15000 words out of 44401 words
masu son sanin sirrin wani.
“Yalaɓai na faɗa ma zan yi duk abin da ka ce,ka yarda da ni ” ya faɗa cikin tsoro,na shafi sajena kafin na ce “in ma ba ka yi ba ai ka san meke jiran ka! Sannan duk faɗin duniyar nan ba za ka taɓa ɓoye min zan lalubo ka” ina gama faɗa na wuce ciki.
Yau Ammy ba ta falo ban kuma nemi na san inda take ba kawai na shige ɗakina,wanka na soma yi kafin na fito ɗaure da towel.Kai tsaye kusan madubina na je na tsaya,ina son sanin abubuwa da dama game da MAFIYA wacce a yanzu garɗinta nake ji.Kamar wanda zai shiga ɗaki haka na yi na ratsa ta cikin madubin na shiga ciki,yau ɗin ma kamar waccan lokacin yanayin duniyar hazo-hazo ce sai dai hakan bai hana ni ganin abin cikinta ba.Wani aji na gani inda aka rubuta “TSAFI DA MATSAFI” babu wani tunani ai kuwa na je na tsaya sai na ga wata malama a tsaye tana koyawa wasu karatu,ba tare da neman izini ba na je na zauna ina kallon darasin . Tana gamawa kuma sai ga wani shi ma malamin ya bayyana kamar daga sama,kamar wani rediyo kuma ya soma yin magana.
“Sannu Matsafana da kuma Mayuna!A yau za mu gano abokiyar sufi da muka fi so wato: cat da turanci,wacce a Hausa za mu kirata da mage ko kuma ƙuliya.Wannan halitta ko da yaushe tana da alaƙa da sihiri da mayu.Za ku ga a gidajen Mayu,matsafa ko malaman tsibo suna ƙawata shi da mage ko kuma ƙuliyoyi wanda normal mutum zai ɗauka iya soyayya ce kawai amma yanzu zan muku gwanjon sirrikan.Bari mu fara da labarin da zai burge ku!” sai ya tsaya da magana tare da soma yin rubuta a ƙaton allon da ke cikin ajin.
# Cat da Bokaye: Tsohuwar ajiya a cikin kundin Labari na ƙarni biyu.
Shine abin da ya rubuta kafin ya soma yi mana bayani dalla-dalla.
“Tsawon ƙarnoni, ƙuliyoyi sun kasance abokan bokaye. Masarawa sun bauta musu a matsayin alloli. Indonesiya sun yi imanin cewa ƙuliyoyi na iya gani fiye da mayafi. A takaice, abokanmu na sirri sun fi dabbobi kawai.
Abu na gaba shine :
# Ikon Sufanci na Mage
A naku hange me yasa mayu suke son kyanwa sosai? ” Mr Zulu na kawowa nan sai ya tsaya yana tambayar mu,wato ya bamu damar tsoma baki a ciki kamar yadda malaman makaranta ke yi.
“ HAROON ko za ka faɗa mana dalili?” ya jefo min tambayar,duk sai hankalin kowa ya dawo kaina.
Na ce “Domin suna da ƙarfin ikon sihiri”
Yayi alama da babban yatsansa irin na jinjina kafin ya ce “ba shakka! HAROON yayi gaskiya a cikin halittun da duniyar Ruhaniya ta aminta da su mage nada kaso casa'in na ƙarfin tsafi yayin da sauran halittun kuma nada ƙarancin rinjayen.Daga cikin quality ɗin mage akwai:
* Hankali, Cats suna jin kuzari da ruhohi mara kyau. Mafi dacewa don kiyaye gidanku.Ma'ana a duk lokacin da wani mummunan abu zai faru cikin gida mage tana sani kuma za ta iya kare mamallakinta daga wata cutar wa ita abin ya same ta.
* Kariya :suna tunkuɗe mugayen ruhohi da munanan kuzari.Daga lokacin da mugu ya shigo gida zai ji ya kasa zama a ciki saboda wanzuwar ƙuliyar.
* Warkarwa : Tsaftace su yana da tasirin warkewa, cikakke don rage damuwa.In mutum na cikin wata damuwa ta dalilin yadda yake mu'amulantar magensa zai iya samun sauƙi daga abin da ya shige masa.
Sannan ku sani bayan wannan ɗin akwai wani ɓoyayyen sirri a tattare da kowacce mage.Abu na gaba da nake son ku sani shine TASIRIN LAUNI,kowacce mage da kuke gani da nata tasirin sannan ba haka kawai ake mallarkarsu ba sai an cika sharuɗa.Amma kafin nan bari na sanar da ku tasirin kowacce daga cikinsu.
Kowane launin yana da ma'anarsa ta sihiri da tsafi.
_Baƙar fata: Yana nuna kariya da sihiri. Saɓanin camfi suna kawo sa'a.
_Fara: Yana wakiltar tsarki da waraka.
_Grey: Yana jawo hikima da hankali.
_Ja: Yana jan hankalin sa'a da kuzari.
_Tiger: Yana wakiltar sassauci da daidaitawa, cikakke don lokutan canji.
Zan tsaya a nan sai wani lokaci ” Mr Zulu ya faɗa tare da yin ɓaton dabo.Ina zaune dai cikin mamakin wannan lamari sai ga kuma wani tsoho shi ma ya shigo ajin tare da rakiyar dog.Na gyara zama don jin wane darasi ya zo mana da shi kawai na tsinkayo murya Ammy na faman kiran sunana,a dole na tashi na fito abun mamaki har yanzu jikina na ɗigar da ruwa kamar yanzu ne na fito daga toilet.
Ƙofar na buɗe ina ƙirƙiro murmushi na ce “ Barka da maraice Ammy!”
Ta dube ni da kyau kafin ta ce “ HAROON wai meke damunka ne? Ka dawo daga aiki amma ba za ka zo ka gaishe ni ba? ”
“Yi haƙuri Ammy na gaji ne sosai,kaina kamar zai tsage haka nake ji shi yasa na soma yin wanka.Amma kina zuciyata ” na yi ƙaryar ciwon kai saboda shi ne abin da ke sa hankalin Ammy gusashe wa a duk lokacin da ta kama ni da wani laifi ni kuma ina gudun ta yi min faɗa .
“Tun yaushe ka fara jin ciwon kan?” ta faɗa hankali tashe,na ce “ bai wuce minti goma” ba ta ce komai ba da sauri ta fita sai kuma ta dawo da ruwan ƙanƙara da towel,kamar ƙaramin yaro haka ta zaunar da ni ta soma yi min tausar kai har sai da na ce mata ya daina na bar ji.Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta sauke wacce har sai da na ɗora ayar zargi da tambaya na ce “ Ammy me yasa hankalinki ke tashi in nace kaina na yi min ciwo?”
Ɗan daburcewa ta yi kafin ta ce “ ka saka kaya ka sauko ƙasa na yi maka girki mai daɗi” tana gama faɗa ta fice,na bi ta da kallo ina cewa “ tabbas akwai wani ɓoyayyen sirri da Ammy take ɓoye min” haka na miƙe na kimtsa sannan na sauka zuwa ƙasa.
Ammy ta zuba min abinci amma na kasa ci,ta zauna kusa da ni tare da soma bani a baki tana mai cewa “ zama da yunwa bai da kyau yana haifar da cutar olser,ka yi niyya ka yi aure HAROON ko hankalina zai kwanta na san matarka za ta kula da kai” ban ce mata komai ba sai murmushi.
Da sauri na juya bayana jin kukan mage yau a gidanmu ,magen fara ce sol ko tabo ɗaya ba tada kuma dumul-dumul da ita kana gani ka san ba ta da yunwa.
“Ammy ina kika samu mage?” na yi tambayar ina kallon magen sam na kasa ɗauke idona a kanta .
“Ka jira yanzu mai ita ta shigo ” cewar Ammy tana dariya,babu jimawa kuwa sai ga wata kyakkyawar budurwa fara tas da ita har da wani ƙaton baƙi a goshinta na sallah .Sallama ɗauke da bakinta sannan kuma ta gaishe da Ammy,kafin ta soma kiran sunan magen “ Mira! Mira! Zo mana” kamar uwa da ƴa haka magen ta je da gudu wurinta,ita kuma ta duƙa ta ɗauke ta kafin ta zo ta miƙawa Ammy key ta ce “ ga shi in Mama ta zo ki bata ni zan koma makaranta” Ammy ta karɓa ita kuma ta fita,da sauri na yi jarumtar tattara nutsuwata na share zancen magen na ci abinci.
Kiran sallar magrib aka soma,“ HAROON je ka yi alwala ka wuce masjid ni zan shiga daga ciki” cewar Ammy,a dole na amsa mata da “ toh” sai kuma na fita can harabar gidan.
Da hannu na yi wa Illiya alama da ya zo,da sauri ya ajiye butar da yake alwala ya zo jikinsa na rawa .“ Ga ni yalaɓai”
“Yarinyar nan da ta fita yanzu Mai mage wace ce ? Ka san ta ne?” na tambaye shi .
Ya ce “ Eh yalaɓai Salima ce ƴar gidan Yakubu soja tana karatu a babbar jami'a ne”
“Ina son ta ne,ka san yadda za ka yi ta yarda da hakan” na faɗa kai tsaye.
“Amma yalaɓai Malama Zainab fa?”
Har sai da ƙarar rawar zuciyata ta motsa jin an ambaci sunanta,na saki wani murmushi na farin ciki kafin na ce “ ita wannan ta musamman ce” sai kuma na bar shi nan na koma ciki.
ILLIYA POV
Bin bayan HAROON kawai yayi da kallo yana mamakin wane irin rikitacen mutum ne shi,a haka ya koma yayi alwala ya je masallaci.Har aka yi sallar isha'i yana ta tunanin hanyoyin da zai bi ɗin ya sanar da Salima,da kuma ya tuna zancen Yalaɓai na ya kai masa matarsa gobe sai hankalinsa ya ƙara tashi.Haka dai ya samu ya fito daga masjid ɗin ya je bakin hanya ya samu taxi ta kai shi can gidansa,yau ko motar bai tafi da ita gida ba kamar yadda ya saba.
Yana shiga kuwa ɗansa Abdul ya rugo yana tara masa hannu,sam ya manta bai shigo da komai ba kamar yadda ya saba musu ba.”Yi haƙuri Abdul na manta ban sayo ba ka bari har zuwa gobe” yana gama faɗa yaron ya fashe da kuka,hakan ya jawo hankalin matarsa Mariya ta fito tana kallon mijinta ta fahimci ba ƙalau ba,gaisuwar da ta yi masa ma dakyar ya amsa.
Ruwan wanka ta kai masa,haka ya je yayi ya fito ya zo ya shige can uwar ɗaka ya rabka uban tagumi.
“Baban Abdul” ta faɗa cikin Hausarta da ba ta dafu ba.
Ya zabura ya ɗago ya dube ta,sai kuma ya haɗe rai ya ce “ lafiya kike wani kirana haka?”
“Kai dai zan tambaya lafiya duk ka bi ka sauya haka?”
“Mariya haka ya dace a tarbi miji in yana cikin damuwa? Ko abinci fa ba ki bani ba” ya faɗa wannan karon ya sassauta murya.Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ ka yi haƙuri bari na kawo ma” sai ta fita ta je ta kawo masa.Ya ce “ ina Abdul?”
“Ya gaji da kuka har yayi bacci ” ta basa amsa tare da zuba masa abinci a plate ya karɓa ya soma ci yana ƙare mata kallo,bafulatana ce ita kyakkyawa ba ta da ƙiba hakan yasa ƙirjinta har yanzu a cike suke kuma tsaye daram .
“Lafiya kake ta ƙare min kallo kamar yau ka fara gani na?”
“Kin san ke ɗin ce kullum kyau kike ƙarawa” ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya yana murmushi,ita ma dai ta ɗan saki ranta ta soma yi masa surutunta da wannan ta ɗan sassauta zuciyar Illiya har suka yi bacci,amma tsakar dare ya tashi a firgice saboda mummunan mafarkin da yayi.Sam kasa komawa yayi sai yayi zaune yana ta saƙa da warwara har garin Allah ya waye,suna tsaka da cin abinci kiran HAROON ya shigo wayarsa,gabansa ya faɗi rasss haka yayi ta kallon kiran har ya yanke wani ya sake shigowa amma shi ma ya ƙi ɗauka sai ana uku ne yayi ƙarfin halin tashi ya fita can tsakar gida sannan ya ɗaga idonsa na kawo ruwa ya ce “ yalaɓai ina zuwa yanzu nan zan kawo ta” yana gama faɗa kuma aka kashe kiran daga can ɓangaren.Illiya ya goge ƙwalla kafin ya dawo ɗaki,Mariya ta kafe shi da ido sai dai bai bata damar yin magana ba ya ce “ Ogana ne bai da lafiya yanzu nan aka kira ni,tashi ki saka hijabinki mu wuce”
Ganin yadda mijin nata ya shiga tashin hankali yasa ta bi umaninsa kawai,Abdul ta kimtsa ta goya shi sannan suka fito bakin titi ya tsayar musu da taxi ya faɗa masa sunan babban kamfanin da za su je.
HAROON
Da abu uku na kwana daren jiya,na farko soyayya da ƙaunar Malama Zainab,na biyu kuma son mallakar magen Salima,na uku kuwa shine son ganin matar Illiya . Wannan yasa gari na wayewa na yi wanka na shirya,shayin Ammy kawai na sha kafin na fito sai kuma na tarar Illiya bai zo ba na yi tunanin don kar ya cika umarnina ne ya ƙi zuwa wannan yasa na soma jera masa kira domin yi masa gargaɗi sai kuma ga shi ya bani tabbacin zai kai ta.
Ɗaki na koma na ɗauko key na mota,da kaina na yi draving na isa can kamfanina.Ko sauraren gaisuwar mutane ban tsaya ba na shige ciki,babu jimawa kuwa sai ga Illiya ya shigo shi da matarsa wacce idonta ƙurrr a kaina masu cike da mamaki da tambayoyi.
Kujeru na nuna musu ,ta kwance goyonta kafin ta zauna shi kuwa Illiya ya ma kasa zama da alamu jira yake ya ji dalilin zuwan nasu.
Rigar rashin mutumci na sake yaɓawa kaina kafin na ce “ Illiya karɓi yaron nan ku fita waje ina son yin magana da ita” jikinsa na rawa ya ɗauki yaron da tun da muka haɗa ido da shi ya soma kuka,Illiya ya je bakin ƙofa ya waiwayo yana kallona na banka masa harara da sauri ya fice ina mai ganin ƙwalla na zubo masa.
Daga inda nake zaune na baiwa ƙofar umarnin rufewa,da sauri ita matar Illiyan ta juya tana kallon yadda key ke murɗa kansa handle kuma na motsi.Tana juyowa ta gan ni a zaune kan table gabanta har ƙafafuwanmu na gugar na juna,cikin ido na dube ta na ce “ ki cire hijabinki”
Idonta ya kawo ruwa amma na san tabbas ba za ta iya musa min ba,haka ta cire shi nan na yi arba da siffarta mai ɗaukar hankali.Rabon da na yi mu'amala da mace har na manta, wannan yasa jikina ya ɗau rawa har ban san lokacin da na kai hannuna na zuge zip ɗin rigarta ba.Nan na yi arba da ainahin surarta,hawayenta da suke ɗiga sam ba su dame ni ba haka na yi mata sintiri ina shafar dukkan sassan jikinta.Daf da zan cimma burina na ƙarshe na ji sautin muryarta mai kamar tafasasshen ruwa,cak na tsaya ina sauraren amon muryarta wanda kuka ya gurɓata shi “ ka sani ni ma mace ce mai daraja kamar uwar da ta haife ka! Yadda baka son wani ya keta mutumcinta haka ni ma yarona da ke can waje yana kuka bai son a keta nawa” da sauri na yi baya ina dafe zuciyata ina kallonta ta soma mayar da kayan jikinta.Daidai nan na gama page na kyauta mai so sai ya biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Kawai ki tura in na zo zan saka ki group,wacce ta san ba biya za ta yi ba ta yi wa girman Allah kar ki yi min magana.
Littafin MAFIYA labari ne ya cakuɗe da true life da kuma wanda na ƙirƙirar,sannan wannan duk shimfida ce ba mu ma shiga cikin zallar labarin ba.
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[28/11 à 08:15] MRS SADAUKI 💫: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
11
Tun da nake babu wata ƴa mace da na taɓa rabawa da kayanta kuma ban kusance ta ba sai wannan.Har ta kai bakin ƙofa na dakatar da ita “ keee!” ta wani juyo a firgice jikinta na rawa,idona na kafe ta da su ina son sanin ko tana ɗauke da wani sirri ne na daban amma ban gansa ba.Na dafe goshina cike da takaici kafin na kwashi kayana na shige Toilet,gaban shower na je na tsaya na buɗe shi duka ruwan na soma sauka a kaina tsohuwar rayuwata ta baya ta fara zuwar min kamar wanda aka kunna wa video.
Wannan labari yana ɗaya daga cikin mafi ruɗani da na samu. Yana da gami da madubi. Ba wai kawai kowane madubi ba, amma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ake ganin suna ɗaukar wani abu fiye da kawai tunaninsu.
A ƴan shekarun da suka gabata, na ci karo da wata kasuwar kayan gargajiya a wani gari da nake wucewa.Kasancewar ni ɗin direban babbar mota ne,ina son yawo a cikin waɗannan wuraren koyaushe suna samun abubuwa masu ban sha'awa tare da labari. Ina zagawa wani tsohon madubi ya kama idona tamkar mayen ƙarfe. Yana da ban sha'awa, tare da firam ɗin katako da aka sassaƙa, an ƙawata shi da ƙira. Wani katon madubi ne, kusan girmansa kamar ƙofa, ga fuska kamar ya ɗan dusashe da shekaru.
Dillalin kayan tarihi ya gaya mani cewa wannan madubin ya fito ne daga wani tsohon gidan da aka yi watsi da shi kuma ya kasance a wurin shekaru da yawa, ba tare da wani ya so ya saya ba. Ya ce wasu mutane in sun ga wannan madubin suna cewa “yana tattare da damuwa” ba tare da sun iya bayyana dalilin da ya sa ba.
Tabbas, a matsayina na mai son abubuwan bazata da na ban mamaki sai na yanke shawarar saya. Na kai shi gida da tunanin zai dace da duniyata.
Tun daga ranar farko da na rataye shi, na ji wani abu mai ban mamaki. A duk lokacin da na wuce nakan ji kamar tunanina yana kallona ta wata hanya mai ban mamaki. Ba kamar wani tunani mai sauƙi ba, amma kamar wani sigar ni a cikin madubi yana kallona ta baya, ko da kuwa bayan na kawar da kaina.
Da farko na ɗauke shi a matsayin gajiya ce da na yi, tunanina kawai hankalina ne ke wasa da ni. Amma da yawan kwanakin da suka wuce, wannan jin yana ƙara tsanantawa. Abin da ya fara damuna da gaske shine lokacin da na lura cewa tunanina yana motsawa.
Wata rana da yamma, ina wucewa gaban madubin , sai na ga tunanina ya ɗan juya kaina kafin in yi haka. Tsawon daƙiƙa ne kawai, amma a fili yake. Har na yi gwaji, ta wurin tsayawa a gaban madubi ina motsi a