Showing 30001 words to 33000 words out of 44401 words

Chapter 11 - MAFIYA Part 1 By MRS SADAUKI .txt

03 Dec 2024

3201

in ta jinkirta ajiye kurwarsa Habibah za ta iya fahimtar haka.Tsawon lokaci ta ɗauka cikin siffar mugunta kafin ta dawo normal,zuciyarta ta ji fayau babu ƙunci.Tana nan zaune sai ga Munira wacce rabon ta da gidan tun lokacin da aka ce ta fita.Kusa da mahaifiyarta ta zauna ta soma bata labarin yadda yaron maƙwabciyarsu ya faɗi suna tsaka da wasa,“ je ki nemo min Munir ya dawo gida ” shi ne kawai abin da ta ce tana jin wani daɗi a ranta ba don komai ba sai don ta yi mugunta.








Habibah na shiga ta miƙa wa Sakeenatu gorar ruwa mai sanyi haka ta shanye su tasss tana sauke ajiyar zuciya.“Ki dinga kula da kan ki mana,ko barin kai a buɗe ai yana sa maƙiya su yi galaba kanka”


“To in sha Allah ” Sakeenatu ta faɗa tana mai ɗan satar kallon jaririyar ƙawarta,ido ɗaya babyn ta buɗe ita ma tana kallonta babu shiri Sakeenatu ta miƙe tsaye tana cewa “ Feenat zan tafi sai kuma gobe in sha Allah zan zo da safe tun da babu aiki”
“Na gode sosai Keenat wai ina Ma'idah?”
“Tana wurin Mama tun wancan satin na kai ta kin san Komandan ta zo”




Safeenat ta waro ido ta ce “ ki ce dai a takure kuke yanzu,kai tsohuwar nan an yi ƴar masifa mine ne na zuwa hutu ke ba ƴar makaranta ba”


Sakeenatu ta tuntsire da dariya ta ce “ kar a yi babu ita mana,duk gani take wasu kuɗi ne da shi ba ta san rabin hidimar gidan ni ke yi ba a haka kuma za ta dinga tsiro da abubuwa tana saka sharaɗin abin da take so”




Safeenatu ta ce “ ah lalle ta ci sunan Komandan ɗin” nan dai suka yi sallama Sakeenatu ta fito.Kafin ta isa gida sai da ta saya wa Mamuh kifi don ta san tana son shi,da sallama ta shiga amma ta ƙi amsa mata sai ma tambaya da ta jefo mata “ daga gidan uban wa kike? Wato kin matsu na koma ƙauye shi ne kika je gidan malamai da bokaye a yi min asiri na tafi ban shirya ba”




Jikin Sakeenatu banda rawa babu abin da yake yi,kanta ƙasa ta soma rantse-rantse tare da sanar da ita inda ta je.
“Ita ƙawar taki ce ta baki magani kika yi wanka da shi ta yadda zan ji tsoron ki? Sakeena lalacewar taki har takai ki dinga faɗawa ƙawarki ƙarya da gaskiya akan ta baki magani? In maganin za ki nema mi yasa ba ki ce a baki na haihuwa ba sai na korar maƙiyiyarki”




“Wallahi Mamuh babu wani magani da aka bani,na faɗa miki barka kawai na je” Keenat ta faɗa cikin muryar kuka.




Mamuh ta tsure ta da ido,sam babu tabon duk muguntar da ta ajiye a jikin Sakeenatun komai ya rushe ta koma normal.Sannan a baccinta aka nuna mata ta yi wanka da ruwan magani duk mugun nufinta ya fita daga jikinta,jin shiru yasa Sakeenatu ta ɗago ido da zumar kallon Mamuh mugun ganin da ta yi ne yasa zuciyarta kusan faso allon ƙirjinta ta faɗo.




Idon Mamuh sak irin na maciji yanayin fuskarta ma ya canza duk ta yi baƙi,“ in kin gama gulmar sai ki wuce ki ɗora min wake da shinkafa” Mamuh ta faɗa tare da yin gaba,Sakeenatu ta ce “ akwai sauran na ɗazu bari na zubo miki ”
Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ban so wani nake so ki dafa min”


Jakarta ta ajiye ta shiga kitchen ta ɗora girkin,wannan karon ko waken ba ta wanke ba kamar yadda tsarin dafa shi ya zo mata daga Mamuh ɗin ,dama ita shinkafar ba irin wacce ake wankewa ce ba.Cikin plate ta zuba bayan ta tsalala mai dayawa,sai ta fito ta nufi ɗakin Mamuh da sallama ta shiga duk da ta san ba za ta amsa ba.




Cike da ladabi ta duƙa har ƙasa ta miƙawa Mamuh plate ɗin wake da shinkafar amma ta ƙi karɓa sai ido da tsura mata.Tuni gaban Sakeenatu ya fara dukan uku-uku,“ ba zan ci ba!”
“Amma ke kika ce na girka miki ” ta faɗa murya na rawa.
“Tun zuwana gidan nan na faɗa miki sai an dirje wake an waken shi da hannu sannan ake girka min mi yasa yanzu ba ki yi ba?”




“ Na zata kina jin yunwa ne sosai shi yasa na yi haka don na yi sauri”


“To sai ki je ki sake dafa wani” Mamuh ta faɗa tana mai miƙe wa tsaye,cikin dakiyar zuciya Sakeenatu ta ajiye plate ɗin ta ce “ ki yi haƙuri Mamuh akwai aikin da nake son yi yanzu,ki ci wannan ɗin gobe in Allah ya kai mu sai na yi miki irin wanda kike so ɗin”




Sam ko kaɗan Mamuh ba ta yi mamakin furucinta ba ,don dama da tsafi ne ta ci galaba har Sakeenatun ke mugun tsoronta yanzu kuma komai ya karye.Ita kuma tana gama faɗar haka ta fice,da ta fito har sai da ta ja ajiyar zuciya tana mamakin yadda yau ta cire tsoron Mamuh.
Tana shiga wanka sai ta ga period ɗinta ya zo,wanda kuma ba komai ya haifar da haka ba sai gwagwarmayar fitar da sihirin jikinta.Cikin ƙananan kaya ta shirya sannan ta haye bed tare da kiran Abbas,cike da nishaɗi suka yi hirar soyayya nan ne kuma ya shaida mata gobe zai zo sannan a karɓo Ma'idah don ita yake son fara cin karo.Har ƙasan ranta ta ji daɗin furucinsa , wannan yasa suna gamawa ta kira can gidansu ta ce a kawo mata Ma'idar.


Washegari
Kuwa tun safe Sakeenatu ta soma gyaran gida ita da ƴar aikinta wacce ba za ta wuce shekara ashirin ba mai suna Fa'iza.Mamuh dai na ta kallonsu ba ta ce komai ba don fushi take da Sakeenatu,da kanta ta yi girki Fa'iza na kama mata.


“Shi kuma waken nawa sai yaushe za a girka?” Mamuh ta leƙo kitchen ɗin tana mai faɗar haka.
Sakeenatu ta ce “ yanzu zan yi” ba ta ƙara cewa komai ba ta tafi.


“Fa'iza wanke min waken nan da kyau sai ki girka wa Komandan ban son ta kawo min cikas ina cikin farin ciki”


Ƴar dariya Fa'iza ta yi kafin ta soma wanke waken kamar mai wankin kaya,ita ce ta girka shi kuma.Sakeenatu ta zuba a plate da kanta ta kai wa Mamuh jikinta har rawa yake ta soma ci tana lumshe idonta waɗanda tuni suka soma yin hasken nan.Ita dai Sakeenatu Allah na gani tsoron yanayin nan take ,da sauri ta wuce ɗakinta ta yi wanka ta shirya cikin wani rantsatsen less tana tsaka da fesa turare Ma'idah ta shigo da gudunta ta na kiran Ammyna.Ita ma sosai ta yi kewar yarinyar sai ta rungume abarta tana cewa “ ke da wa ne?”
“Anty” ta bata amsa.
A ɗan firgice Nafisa ta shigo tana cewa “ anty Sakeena wace ce waccan a kitchen? Zo ki ga abin da take”
“Ƴar aikina ce lafiya?”
“Zo dai ki gani” cewar Nafisar tana mai yin gaba Sakeenatu na take mata baya har suka shiga kitchen ɗin.
Fa'iza suka tarar duk ta cire suturar jikinta tana fitar da wani nishi idonta a rufe suna tsiyayar da hawaye.......
[03/12 à 16:30] MRS SADAUKI 💫: *ZAWARCI*



LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️


*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)


*Lambar waya:* +22795045822


*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.


*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman




_____________________
24/09/24




6-7




Tamkar wacce ke wata mu'amala da namiji haka Fa'iza ke yi ,hankalin Sakeenatu in yayi dubu to ya watse.Ta kalli ƙanwarta ta ce “ Nafisa ko iskokai ne? Dubi abin da take yi”
Nafisa ta ce “ anty Sakeena tun da nake ban taɓa ganin mai kalar iskokan nan ba,hatta masu aljanin soyayya ai sai in suna bacci ne suke zuwar musu dubi ita wannan fa tamkar idonta biyu fa”


“Yanzu dai don Allah ki taimaka mata tun da ke Malama ce kin ga Ma'idah har ta soma kuka” cewar Sakeenatu tana mai jan ƴarta zuwa waje.Nafisa ta cika kofi da ruwa ta tofa ayatul ƙursiyu da amanar rasulu sannan ta shiga watsa ma Fa'iza ruwan,a sannu a hankali ta soma barin abin da take daga ƙarshe ta buɗe idonta waɗanda suka kaɗa suka yi ja.Nafisa ta shiga yi mata sannu kafin ta taimaka mata ta mayar da kayan jikinta,“ dama kina da aljanu?” Sakeenatu ta tambaya wacce ta dawo.


Fa'iza ta girgiza kai,“ to tashi ki yi wanka sai ki zo ki zuba abinci ki ci”
Da “ toh” ta amsa kafin ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida kamar yadda Sakeenatu ta shaida mata da ita za ta dinga amfani.
Wanka ta soma sai da ta saɓa jikinta har sau biyu sannan ta fito,wasu kayan Sakeenatu ta bata ta saka abincin ma da ta zuba gidansu ta wuce da shi.
Su kuwa a falo suka zauna suna hira Nafisa na bai wa Ma'idah abinci a baki,Abbas yayi sallama da gudu ta nufe shi tana “ Daddyyy” ya caɓe ta tare da cira ta sama yana yi mata wasa haɗi da kai mata sumba.
Cike da farin ciki ya ƙarasa ya zauna,Nafisa ta gaishe shi yayin da suke aikawa juna wani kallon so shi da Sakeenatu mai cike da kewa.
“ Mu je ka fara yin wanka ko?”
“A bani abinci tukuna don Allah ” ya faɗa yana wani murmushi,Ma'idah ta ce “ Daddy ni ma ina ci” sai aka zuba musu ya dinga bata a baki ita kuma sai surutu take yi masa.Suna tsaka da nishaɗinsu sai ga Mamuh ta fito,fuskar nan kicin-kicin,“ ita kuma wannan farar tinkiyar?” ta yi tambayar tana zunɗen Ma'idah wacce ta tsorata da ganin Mamuhn.
“Ina wuni Mamuh? Fatan na same ku lafiya?” Abbas ya faɗa cike da ladabi.
“Ka bani amsa ta”
“Ma'idah ce fa ƴar wurin Keenat” ya bata amsa a sanyayye.


“Shegiya za ka ce wacce ba a san taƙamaimai wane ne ubanta ba,kai da ka iya kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk ƙwayaƙwayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan nan ba” Mamuh ke faɗa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh.


Abbas ya sunne kai ya ce “ a dai yi haƙuri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita yarinya ce ba ta san komai ba”


“Wallahi sai ta bar gidan nan” Mamuh ta faɗa cikin ƙaraji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu abin da take yi .
Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo.
Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa “wayyo idona! Ƴar daba ta kashe ni” jikin Abbas na rawa ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti.
Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce “ Nafisa ki ɗauke ta ku wuce gida don Allah”
“Ke kuma a nan za ki zauna? ”
“To ina zan je Nafisa? Haƙuri zan yi dama aure ya gaji haka sanin kan ki ne a can gidan ba wani jituwa muke ba ni da Mama ta ɗauki ƙiyayyar ɗan farin ta ɗora min”
“To amma dai ki kula da kan ki,in kin ga abin ya yi yawa kawai ki tawo gida”
Kuɗi ta basu sannan suka bar gidan,ita kuma ta ɗauki waya ta kira Abbas don jin asibitin da suke shi da Mamuh yana shaida mata ita ma ta fita ta je.Tuni Mamuhn ma ta yi bacci an naɗe idon nata da bandeji ga kuma ƙarin ruwa an saka mata.
Jikinta a sanyayye ta ce “ ka yi haƙuri” Abbas ya kamo hannunta ya ce “ dama haka Allah ya tsara,ina Ma'idah?”
“Nafisa ta koma da ita can gida”
“Don me? Zan rarrashi Mamuh na san za ta amince ta zauna da mu”


Ta sakar masa murmushi ta ce “ na gode sosai da kawaicinka gare ni” wani kallo yake aika mata yana mirza tafin hannunta,da ido ɗayan mai lafiya Mamuh ke kallonsu tana jin wani irin haushi da takaici.




“Mine ne haka? A asibiti fa muke ka bari har mu koma gida” Sakeenatu ta faɗa tana janye jikinta daga nasa ganin abin zai wuce gona da iri.
“Mu je gidan to tun da kin ga Mamuh ta samu bacci ,sai mu dawo daga baya” Abbas ya faɗa yana langwaɓar da kai saboda ba ƙaramar kewar ta yayi ba.




“To ai na farka” cewar Mamuh tana mai tashi zaune haɗi da hararen Sakeenatu,da ɗan sauri ya miƙe yana tabayarta jiki.“ Ka kira likita ya cire min ƙarin ruwan nan sai mu wuce gidan tun da uwarka ba za ta barin ka cikin salama ba” cewar Mamuh a zafafe,Abbas ya fita don kiran likita.




“Duk tsiyarki dai ba za ki iya canza ma tuwo suna ba,Abbasi ɗana ne ba naki ba don haka ni ke da iko da shi ba ke ba.Kuma wannan shegiyar taki sai ta san ni ta caka da cokali sai na shayar da ke mamaki”




Da wani mugun sauri Sakeenatu ta je gaban Mamuh ta tsuguna ta ce “ don girman Allah Mamuh ki yi haƙuri , Ma'idah yarinya ce ba ta da wayo ko me za ki yi to ki yi min amma kar ki taɓa ƴata” ta ƙarashe maganar hawaye na zubo mata saboda zuwa yanzu ta yarda Mamuh muguwa ce.




Kafin ta kai ga bata amsa Abbas ya shigo shi da likita,ya ce “ sai kin yi kwana uku sannan za mu sallamar ki”
“To ka sanar da uwarmu wacce ta matsa mu je gida” Mamuh ta faɗa a zuciye tana hararen Sakeenatu.
Likitan yayi murmushi ya ce “ yanzu yadda za a yi sai ka nemo wacce za ta zauna da Mama,amma gaskiya ba za mu sallame ta ba yau” sai yayi wa Mamuh allurar bacci,duk yadda masifa ke cin ta haka ta haƙura saboda ƙarfin allurar.




Shi kuwa Abbas Gwaggonsa ya kira wacce ke nan Damagaram ita ke bi ma Mamuh,babu jimawa kuwa ta zo .Ya ja matarsa zuwa gida,cike da zallar soyayya suka gamsar da junansu.










SAFEENATU




Tun bayan da kowa ya watse aka bar su ita da Gwaggo Habibah sai ta nutsu sosai kafin ta ce “ Gwoggo ni kam ɗazu wani abin ban mamaki ya faru,maciji na gani ya naɗe Baby girl ɗin nan ina yin ihu ya ɓace kamar aljani ”


Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ kar ki wani ji tsoro,sannan ina so ki kwantar da hankalinki duk wani abu da za ki gani ki yi shiru da bakinki.Duk kusan ƴan biyu suna da wannan baiwar,to ke macen ce ke da shi don haka ki shirya ganin abubuwa iri-iri wasu na tsoro wasu kuma na almara”


Safeenat ta ja wani numfashi kafin ta ce “ to Allah cire min tsoron” ba ta ida rufe bakinta ba hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya turnuƙe shi kai ka ce dare ya tsala.Duk tsit suka yi babu wanda ya ce wani abu,sai kukan jaririyar da ya soma tashi sannu a hankali tsawon minti biyu kafin ta yi shiru.Hasken ɗakin na dawowa Safeenatu da Gwoggo Habibah suka yi ƴar rige-rigen ɗaukar babyn duk suka yi tsaye suna kallon yadda goshinta ke fitar da wani haske yana ƙyalli a gaban idonsu ya ɗauke sai ga shatun haƙoran maciji ya bayyana raɗau .Safeenat ta kai hannu ta shafi wurin sai kuma ya ɓace,ta ja ajiyar zuciya tana mai ɗaukar jaririyar ta soma shayar da ita.


Daddy ya yi sallama ya shigo,duk suka gaishe shi kafin a basa babys ɗin ya gani.Sosai yayi musu addu'a sannan ya fita,haka suka ci gaba da yin hirarsu har dare ya tsala.Duk sun yi shirin bacci za su kwanta amma ita Baby kamar ɗiyar aljanu ta ƙi baccin sai ma wani kuka-kuka da take yi.


“Safeenat ki bata abincinta mana” Gwaggo Habibah ta faɗa tana shirin tashi ta kunna wuta.
“Ina ta ƙoƙarin bata ta ƙi karɓa” cewar Safeenar.
Kusa da ita ta zauna tana shirin ɗaukar babyn sai ta lura da yadda hannunta na hagu ke fitar da wani zane mai hasken wuta kamar ta murhu.Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Gwaggo Habibah ba tare da ta shirya ba cike da murna ta jawo hannun jaririyar ta riƙe sannu a hankali har zanen ya fito raɗam letter M ta fito sai a lokacin kuma jaririyar ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa.
A ɗan ruɗe Safeenatu ta ce “Gwaggo mine ne kuma wannan?”


Sam Gwoggo Habibah ba ta bata amsa ba sai safar hannu da ta je ta binciko cikin kayansu ta saka wa hannun mai zane.“Daga yau kar ki ƙara barin hannunta a buɗe ki dinga saka mata safar hannu ”


“Gwaggo ina tambayar ki mine ne ba ki bani amsa ba”


“Alama ce ta prophétie/prophecy,da yawan ƴan baiwa tana soma aiki ne in sun kai shekara sha takwas amma ke yarinyarki tun farkon dirowar ta duniya tata baiwar ta fara aiki.Ta ceci ɗan uwan tawaicinta sannan kuma ta ceci ƙawarki Sakeenatu ”


Ba don ta fahimci zancen da kyau ba ta ce” mi ya samu Keenat ɗin?”
“An yi mata ajiya cikin ruhinta ta yadda esprit zai samu damar yin yanda ya so da gangar jikinta har ya cutar da ita”
“Ya aka yi kika sani to?”
“Safeenatu yi bacci in lokacin fahimtarki yayi babu buƙatar ki yi tambaya”


Da wannan duk suka yi bacci, Safeenatu na tsaka da yin mafarki akan goben ƴarta Gwaggo Habibah ta tashe ta daga bacci.“Ruwan wankan ki na can toilet ta tsakar gida,ki je yi wankan sabulu kafin na zo na gasa miki jikinki da towel”
Ta yi miƙa ta tashi a gajiye saboda kwana dare ta yi tana shayarwa,sai da ta ɗauki wani zane da hijabi sannan ta fita ta bar Gwaggo Habibah za ta yi wa Twins wanka.




Sakeenatu na fitowa suka yi kiciɓis da Gwoggo Hajara ta gaishe ta sannan ta wuce toilet.Ita kuwa tsabar mugunta yasa ta koma ɗakinta ta yo shirin mugunta yau ma siffar tsakaka ta ɗauka ta yi tsinke can toilet inda Safeenatu ke wanka tun tuni.Da ga can saman katanga Gwaggo Hajara ke ƙarewa surar Safeenat kallo,cikin salon mugunta ta mayar da harshenta dogo sannan ta zuro shi tun daga can sama har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login