Showing 24001 words to 27000 words out of 36565 words

Chapter 9 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt

27 Nov 2024

2108

rabu da ita gara ya mutu shahidi. Sosai zai baka tausayi a wannan lokacin. "Ina sonki ƙwarai Khans, kuma na tabbata koba yanzu kema wataran zaki so ni, amma maganar saki kam bazan iya ba ko kaɗan."


"Shikenan Zayyad, wallahi kayi sallama da bala'i da masifa kala-kala harsai ka gaji da kanka ka sake ni, zaka gani."


Jin hawaye na ƙoƙarin zubo masa yasa ya miƙe ta sauri yayi waje, da fitar sa kam wani zazzafan hawaye mai raɗaɗi ya zubo masa, ya daɗe tsaye yana tunanin ta yadda zai ɓullowa Khans amma ya kasa, cikin sanyin jiki ya ƙarasa zuwa ɗakin sa.



Kamar kuwa yadda Khans tayi alƙawarin ƙuntatawa Zayyad bata fasa ba, na yau daban na gobe daban, na yanzu daban na anjima daban. Ko da wasa hakan bai taɓa sa Zayyad ƙoƙarin sakin ta ko ramawa ba, dan yasan kowa da irin tasa ƙaddarar, ta yiwu shi irin tasa kenan. Ganin abin yaƙi ci yaƙi cinyewa bashi da niyyar sakin ta yasa ta kiran aminiyar ta Nasreen, saidai cikin rashin sa'a Nasreen bata ƙasar, sakamakon strike ɗin da makarantar su ta tafi yasa baban ta fita da ita ta ƙarasa karatun acan. Khans tayi baƙin cikin rashin ƙawar tata a ƙasar, dan bata san ma ta tafi ba, kasancewar kashe wayar ta da tayi na kusan satuttuka, tasan kuwa Nasreen ɗin ta nemeta. Toh a ɓangaren Nasreen itama bata ji daɗin tafiyar ta ba, dan kuwa tasan Khans bata fasa ƙuntatawa Zayyad ba.




*3 WEEKS LATER*
Kamar yadda ya saba zuwa ya duba lafiyar ta kafin da bayan ya dawo asibiti, yau ɗin ma hakan take, duk da hakan bai hanata yi masa rashin kunya da wulaƙanci. Yadda ya saba shiga ya ganta yau akasin haka ya tarar, dan bai taɓa shiga dap da Isha'i ya same ta kwance ba, da ɗan sassarfa ya ƙarasa inda take kwance ya yaye duvet ɗin data rufa ya tallafo ta, zafi rauu yaji jikin ta ya ɗauka, ba shiri ya ajiye ta ya fita, bayan ƴan daƙiƙu ya dawo ɗauke da box, allura ya haɗa ya ƙara ɗago ta. Cikin rashin tsammani Khans taji saukar allura, aikam ba shiri ta saki wani wahalallen ƙara, bai bi ta ihun ta ba, ya sake ɗakko wani syringe ɗin, cikin dabara ya ɗauka jinin ta ya fice ya barta ta ba tare da ya ce komai ba. Ya fita da kusan daƙiƙu arba'in da biyar sannan ya dawo. Ɗaya daga ledojin daya shigo da ita ya buɗe ya fiddo magungunan ciki kafin ya buɗe ɗayar ya fito da farfesun kazar daya taho mata dashi. A hankali ya ɗago ta daga kwancen da take gaba ɗaya jikin ta ya saki, feeding ɗin ta ya somayi a hankali har ta ƙoshi, wajen shan magani ne dai saida ta bashi wuya, bayan mintina 30 haka ya miƙe ya shiga toilet ɗin ta, sosai yabi ilahirin ko ina da kallo ganin shi a tsaftace kamar ba'a shiga. Ruwan wanka ya haɗa mata ya taimaka mata ya kaita bayin, kasancewar yasan bazata bari ya mata wankan ba yasa shi ficewa. Saida ya gyara wajen sannan ya dawo ya zauna, tagumi ya zabga tare da tunanin ta inda zai fara gayawa Khans ciki ne da ita, domin yasan zata iya yin komai ta zubar dashi. Yana nan zaune harta fito, da alama ma ta samu ƙarfin jikin ta, ko kallon inda Zayyad yake batayi ba ta shige dressing room, ba daɗewa ta fito sanye da doguwar riga ta bacci mai kauri, wardrobe ta buɗe ta ɗauki hijabin ta ta nufi inda prayer mat yake tayi Sallah, tana idar Zayyad ya miƙe tare da damƙa mata maganin ta a hannu, ya kuma yi mata bayanin yadda zata sha sannan ya fice.




Washegari gari ya kama saturday, da wuri Zayyad fita sabida yana da theater da zaiyi karfe 8, saida yaje ya duba jikin Khans tare da tabbatar da tasha magani, ya kuma jaddada mata shan na rana, sannan ya fita, dan baya da tabbacin dawowa da wuri.
Bashi ya dawo ba kuwa sai 4pm, ɗakin ta ya fara shiga dan duba lafiyar ta, ya samu ta fito wanka. Harara ta watsa masa tana wucewa gaban mirror, babu wanda ya furta ƙala har ta gama shafe-shafen ta kafin ta juyo ga Zayyad dake zaune riƙe da wayar sa da tata tace "wai kai Zayyad me kake nufi ne? Daga kawai bani da lafiya sai kazo ka taremin a ɗaki kai a dole kana ban kulawa ko? Toh idan ma tunanin ka ciki gareni toh ka cire wannan tunanin, dan bazan taɓa haihuwa dakai ba, ba kaƙi saki na ba, indai wulaƙanci ne ka ringa gani kenan."


Murmushi kawai Zayyad yayi a rashi, a zahiri kuma yace "your excellency, nazo dubawa inga ko kinsha magani ne."


"Toh idan bansha ba lafiyar ka ko tawa? Banson shisshiga cikin lamarin da bai shafi mutum ba."


Shidai baice da ita komai ba harya shiga dressing room ta fito sanye da wata milk ɗin swiss atampa mai ɗankaran kyau ɗinkin riga da skirt sun ɗame ta sosai, dan ita kanta saida taji kamar ta ƙara ƙiba, ga boobs ɗinta da suka cicciko kamar mai shayarwa. "Kayi sallah ne da kazo ka zauna kana ƙaremin kallo?" Ta ƙarasa cikin sigar faɗa. Ba tare da Zayyad yace da ita komai ba ya fice (domin kunsan Zayyad ba mai son magana bane). Tunda Zayyad ya fita bai sake dawo wa gidan ba sai bayan sallahr Isha'i ɗauke da takeaway ɗin daya saba yi musu, dan ko zasu shekara ba abinci Khans baza ta dafa ba, tun wanda tayi kwanaki, bata ƙarayi ba. Kwance ya sameta tana chatting da Nasreen mutanen ƙasar waje, fuskar ta ɗauke da murmushi wanda ya matuƙar ƙara mata kyau, sosai Zayyad ya shagala da kallon ta dan kuwa rabon da da yaga murmushin ta tun kafin auren su, balle kuma dariya. Tafin da tayi ne yasashi firgigit ya dawo hayyacin sa, ƙeyar sa ya sosa kamin ya soma ƙoƙarin magana wayar sa ta soma ƙara, "Abba kuma." Ya furta a bayyane cike da mamaki, ɗagawa yayi tare da sanya speaker bakin sa ɗauke da sallama. Cikin wata iriyar murya Abba ya amsa, ba tare daya amsa gaisuwar da Zayyad ke masa ba yace _"dakai da matar ka kuzo gobe Inason ganin ku, kada ku wuce ƙarfe goma."_ daga haka ya katse wayar ba tare daya jira me Zayyad ɗin zai ce ba, kallon juna duka sukayi, fuskar Zayyad cike da fargaba yayin da Khans ko ɗarr batayi ba. Har Khans taci abinci ya bata magunguna dai jikin sa a sanyaye, babu walwala ko kaɗan, dan yana tunanin abinda zasuje su tarar goben, har bacci bai iya yi ba sai daƙyar baccin ya sace shi, yayin da Khans ta shari nata baccin hankali kwance....












```Toh danjin ya zata kaya tsakanin Abba dasu Zayyad, ku cigaba da bibiya ta danjin cigaban labari.```
~A madadin ni Babylorh dana rubuta kuma na tsara nake cewa *Assalamu alaikum*~








____________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/14, 12:12 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_






By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚




The writer of:


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_






33 & 34....








📖____________Washe gari dukkanin su suka shirya suka tafi amsa kiran da Abba yayi musu da misalin 9:30 na safe. Tun a hanya jikin Zayyad ke basa akwai wani abu a ƙasa har suka ƙarasa gidan, sosai Khans keta farin ciki da murnar zataga ƴan uwan ta da Ummin ta yau.
Saidai, mamaki ne ya cika su dukan su biyun lokacin da suka shiga suka tadda duka familyn na wajen har su Mummy, alamu kuma ya nuna su kaɗai ake jira. Wani mahaukacin mari Abba ya saukewa Khans a fuskar ta, fuskar sa ta nuna tsantsar ɓacin rai a tare dashi. Dafe da kuncin ta Khans ta ɗago idanun ta sun kawo ruwa suna shirin sauka ta furta "Abb...." Ai bata ƙarasa ba Abba ya kuma wanke ta da wani marin da bayan hannun sa, wanda saida yasa Khans kusan kifa wa badan Zayyad ya taro ta ba, sosai takejin zafin marin na ratsa can cikin tsakiyar ƙwaƙwalwar ta, ba shiri kuka ya kufce mata kamar zata shiɗe. Hankalin Zayyad kuwa yakai ƙololuwa wajen tashi, musamman yadda shatin yatsun Abba suka bayyana tangaran akan kuncin ta, ta take kuwa fuskar tayi jajir tamkar tumatir, abinka da farar fata, ga gefen bakin ta da shima yake fidda jini kaɗan-kaɗan. "Calm down pls, nasan abin da tayi bata kyau ta, amma irin wannan marin zai iya yi mata illa, ko ya kashe mata kunne ko ya mata illa a ido, control your temper pls, faɗa da nasiha ya kamata a musu gaba ɗaya." Daddy da dake riƙe da kafaɗun Abba ya faɗa yana mai ƙoƙarin zaunar da Abba bisa kujera.


Babu abinda Abba keyi sai huci, jin zuciyar sa yakeyi tamkar ta fito ya tsoma ta a ruwa sabida zafin da take masa, hannu yasa ya karɓi ruwan sanyin da Mahfouz ke miƙa masa, saida yasha da kamar mintina biyar sannan ya soma magana, "kin bani kunya Khansa'u, haƙiƙa kin bani kunya, nayi zaton na haifi ƴaƴan da zasu rufamin asiri, nayi zaton na haifi ƴaƴan da zasu karɓi zaɓin da nayi musu hannu bibbiyu, nayi zaton na haifi ɗiyar da zance tayi kuma tayi koda hakan bazai mata daɗi ba, ashe duk haukan banza na nakeyi, in miki gata amma kina ƙoƙarin kwance min zani a kasuwa, kinason tozarta ni Khansa'u, ni Khansa'u!!!"


Cikin rashin fahimtar inda zancen Abba ya dosa Zayyad yace "amm Abba wani abu ne ya faru?"


"Rufemin baki Zayyad, ko kaɗan kaima banji daɗin abinda kayi ba, na ɗauka ni mai share maka damuwa ne, nayi tunanin ni mai sama maka mafita ne a kan rayuwar ka gaba ɗaya, ashe samm ba haka kuka ɗauke ni ba. Kasan haka rayuwar auren ku ke tafiya, amma baka sanar dani ba Zayyad, kayimin adalci kenan?"


Gaban Zayyad ne ya faɗi jin zancen zaman auren su da Khans, sai da ya saci kallon Khans da har lokacin hannun ta bai bar kuncin ta ba, sannan ya maida kallon sa a Abba cikin in'ina kuma yace "A'a Abb......Abba, b...ba..babu abinda k..ke faruwa, wani yace bama zaman lafiya?"


Wayar Abba dake kan table Abba ya ɗauka cikin ƙufula ya kunna wani record da ake magana kamar haka (```toh idan ma tunanin ka ciki gareni toh ka cire wannan tunanin, dan bazan taɓa haihuwa dakai ba, ba kaƙi saki na ba, Indai wulaƙanci ne ka ringa ganin sa kenan....```)


Ba Khansa'u dake rusar kuka ba kaɗai, hatta Zayyad saida gaban sa yayi wani mummunan faɗuwa, dan baisan sanda ya cire hular kansa ya soma fifita ba. Abu kamar a mafarki, shi dai yasan ba shine yayi recording abin nan ya kawo musu ba, toh a ina suka samu? Ko aljanu ne suka kawo musu! Ha'a, toh kodai wani yaje gidan ne jiya? Toh amma basuji motsin kowa ba balle shigowar su, toh ko Bala mai gadi ne? Toh amma ai ko parlon su baya shiga balle yayi gigin zuwa ƙofar ɗakin dayan su, tunani barkatai haka ya riƙa zuwa ma Zayyad, yayin da har lokacin zufar bata bar keto masa ba.
Khansa'u data daskare a wajen na ɗan wani lokaci a ranta tace "lallai ma Zayyad, wato har kayi isar da zaka haɗani da mahaifi na, muyi magana dakai jiya ashe recording kakeyi, har ka iya kawowa su Abba? Lallai ka ɗibo ruwan dafa kanka, tunda ba kashe ni za'ayi ba zakaga abinda zai biyo baya, wlh dani kake zancen..."


Sai bayan da recording ɗin ya gama ne Abba ya ɗago ya kalli Zayyad dake ta faman fifita yace "zaka cemin wannan ba muryar ka bace, ko kuwa ba muryar Khansa'u bace? Ko zaka cemin ba kaine kake cewa kazo ka duba ko tasha magani ba? hmm!" Ya ƙarasa yana bubbuga ƙafar sa a ƙasa na ɗan wani lokaci.


Shiru parlorn ya ɗauka na ƴan daƙiƙu kafin Daddy yayi gyaran murya yace "zo nan ƴa ta." Cikin shessheƙar kuka ta miƙe a hankali tana taku tamkar wadda ƙwai ya fashe mawa aciki, ta lura da uban hararar da Abba da Ummi suka mata, wanda ya matuƙar sanya jin wasu sabbin hawayen na antayi wa. Har kusa da ƙafar Daddy taje ta zauna sannan Daddy ya ƙara da faɗin "ƴa ta banyi tunanin zaki ɗibi ƙasa ki watsa mana a ido ba, Zayyad ko ba ɗan uwan ki bane shi a ƴan uwan taka, shi ɗin ɗan uwan ki ne a musulunci, shin abin da kikeyi ya dace kenan? Ce maki akayi bashi da gata ko me? Kiji tsoron Allah Khansa'u, mijin ki yana da haƙƙi akan ki, ko babu igiyar aure tsakanin ku, kiyi masa magana mai daɗi ma jin daɗi ne, kuma sadaƙa ne, yanzu idan Allah ya ɗauki ranki a haka kina tunanin kina da hujjar da zaki gaya wa Ubangiji ne? (Bakison shi) hujjar da zata kare ki a wajen Allah ne? Kiji tsoron Allah, ki guji ranar da Allah zai kama ki da wannan abin, yau ga iyayen ki na fushi dake akan wanda kike iƙirarin bakiso, hakan bai isa ya nuna miki irin soyuwar da yayi a zuƙatan su ba, idan ke mai hankali ce daga yanzu da muke maganar nan bazaki ƙara gigin muzguna masa ba, balle kuma ki riƙa furta baƙaƙen magana akan sa." Sosai Daddy yayi mata nasiha mai matuƙar ratsa jiki sannan ya ƙara da faɗin "ki tashi yanzu ki nemi yafiyar iyayen ki akan abinda kika musu."


Jiki a matuƙar sanyaye ta miƙe ta isa gaban Abba da tunda Daddy ke magana kansa ke a ƙasa harya gama bai ɗago ba, durƙusawa tayi tare da kama hannun sa yayi saurin ƙwace wa, "kayi haƙuri Abba na, ina roƙon ka daka yafemin laifin dana maka, insha Allah bazan ƙara ba, zaka same ni mai biyayya ga mijina in Allah ya yarda."
Cikin jin daɗin maganar ƴar tasa ya ɗaura hannun daman sa a kanta tare da sanya mata albarka, kowa ya amsa da Ameen. A sannu ta kuma miƙewa ta isa gaban Ummi, nan ma yafiyar ta nema tare da alƙawarin zata yiwa mijin ta biyayya. Hatta Mummy da Daddy bata barsu a baya ba, suma ta roƙi yafiyar su, a taƙaice dai basu bar wajen nan ba saida iyayen nasu suka sanya wa rayuwar auren nasu albarka.
Daga Zayyad har Khans babu wanda zaka kalla baka tausaya masa ba, Zayyad ne mai jarumtar rarrashin dama, toh a halin yanzu shima rarrashin yake buƙata, har suka fito zasu tafi Khans bataga Mahfouz ba, hakan yasa ta tanbayi Zayyad cikin sanyin murya. Waya ya ɗaga ya kira Mahfouz ɗin, babu daɗewa kuwa sai gashi, amma abin mamakin Zayyad kawai ya yiwa magana ya soma ƙoƙarin juyawa. "ya Mahfouz." Khans ta faɗa hawaye na cika idanun ta, cak ya tsaya ba tare daya juyo ba. Ƙarasa tayi ta tsaya a gaban sa tana faɗin "ya Mahfouz baka ganni bane?"


"Na ganki Khans, sai akayi ya?"


Batayi mamakin maganar ba, amma bata mata daɗi ba ainun, cikin danne kukan dake taso mata tace "ba komai, dama naga ban ganka bane shine ya Zayyad ya kira ka. Ya Mahfouz idan na maka laifi ne dan Allah kayi haƙuri, idan kuma akan abinda ya faru ne na maka alƙawarin daga yanzu haka bazan ƙara ba."


Sosai yaji daɗi a ransa, amma bai nuna mata alama ba, saima ƙara tamke fuska da yayi yace "Allah yasa." Daga haka yabi gefen ta ya wuce ba tare daya jira mai zata ce ba. Hannu tasa ta share hawayen daya gangaro mata, sannan ta nufi motar da Zayyad keyi mata horn, alamar ita yake jira. Tana shiga yaja motar suka nufi hanyar gidan su, har suka isa babu wanda yace da wani ƙala, hasalima banda shessheƙar kukan Khansa'u babu abinda ke tashi a motar. Shi kanshi Zayyad kasa rarrashin ta yayi, sabida tuna masa da wani memory da akayi a wannan taron, amma har ƙasan ruhin sa yakejin zafin zubar hawayen nata.






_Wato abinda basu sani ba bayan dowowar Zayyad gida da shigar sa ɗakin Khans, su Haseena da Ameesha suka zo, suna ta sallama amma shiru ba'a amsa ba, sai suka yanke shawarar duba ɗakin Khans, Haseena dake a gaba ta kama handle ɗin ƙofar zata buɗe kenan ta jiyo muryar Khansa'u na gawasa Zayyad magana, Ayeesh da wayar ta ke hannun ta ita ke recording komai, sannan suka yanke shawarar komawa gida ba tare da sun shiga ba. Koda suka koma gida direct sashin Mahfouz suka shiga tare da sanar dashi abin da ya faru haɗi da audio ɗin da sukayi recording, sosai ran Mahfouz yakai ƙololuwa wajen ɓaci, ya amsa wayar tare dayin forwarding zuwa wayar shi sannan ya goge wanda ke wayar tasu, bashi ya samu ya sanar da Abba ba sai bayan Isha'i, shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login