Showing 33001 words to 36000 words out of 36565 words
Chapter 12 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/22, 8:31 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*
🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚
The writer of:
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_
41 & 42....
📖____________Yana dawo wa gida direct ɗakin sa ya faɗa tare da nufar toilet, wanka yayi haɗi da alwala sannan ya fito. T-shirt da three-quarter ya sanya kana ya soma nafila, ba shi ya kwanta ba sai kusan ƙarfe 12:30, ji yayi gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idanun sa, lokaci ɗaya yaji yana tsananin begen matar sa, lokaci ɗaya yaji wani matsanancin kewar ta ta kamashi, juyi kawai yake akan gadon badon yanajin daɗin kwanciyar ba, ji yake tamkar wanda yayi shekara dubu babu ita. Wayar sa ya janyo tare da danna kiran Khans, amma a kashe! Tsaki yayi gami da jefar da wayar gefe haka har bacci ɓarawo ya sace shi.
Toh a ɓangaren Khansa'u ma hakan take, ji take kamar tayi tsuntsu ta koma wajen mijin ta, dan tayi kewar shi sosai, ji take baccin ma ba lallai ya mata daɗi babu Zayyad ɗin ta kusa da ita ba. Duk wani motsi nata Mummy na lura dashi, kuma tuni ta harbo tsuntsun ta, dan tasan kewar mijin ta ke damun ta, "wai Khansa'u baza ki kwanta bane? Sai faman juyi kike kamar ana tsikarin ki." Mummy data gaji ta tanbayi Khans.
Murmushin yaƙe Khans tayi kana tace "Mummy baccin ne kawai bai zo ba."
"Be zo ba ko baki kira shi ba?"
Ita dai batace komai ba ta ƙara juyawa kamar wadda tayi shirin bacci. Miƙewa Mummy tayi ta kashe mata wutar ɗakin ta fita. Ai kamar jira take Mummy ta fita, ta miƙe tare da ɗaukar wayar ta, number Zayyad tayi dialing harya katse ba'a ɗaga ba, ƙara dialing tayi still ba'a ɗaga ba. Kamar a cikin bacci Zayyad kejin wayar sa na vibrating, koda ya ɗakko wayar matar sa yaga ta kira har sau biyu yasa shi saurin dialing, ai kam bugu biyu ta ɗaga tare da sakar masa kukan shagwaɓa, jugum yayi na ɗan wani lokaci kana yace "baby ni ya kamata nayi kuka ai ba ke ba, ni da Mummy ta jamin kwanan kaɗaici ba tare dana shirya ba, kinji gidan kuwa? Tamkar prison, babu daɗi wlh, nayi kewar ki to the essence that no words can express it."
Ajiyar zuciya Khans ta sauke tare da tausayin mijin nata kana tace "ya Zayyad nima anan ɗin haka yake, wlh bacci babu kai kwata-kwata babu daɗi, nayi kewar ka nima matuƙa." Sosai suka taɓa hira ba laifi cike da ƙauna da kewar junan su, sai kusan 1:30am suka kashe wayar.
Washe gari da sassafe saiga Zayyad a gidan Mummy, baki buɗe Mummy ke bin sa da ido harya ƙaraso, gaida ta yake amma inaa bata ma sani ba, tsabar mamakin daya cika ta. "Zayyad" ta furta cikin tabbatar wa. Ƙasa yayi da kansa kafin ya ƙara cewa "ina kwana Mummy?"
"Hmm Zayyad ni kam kafi ƙarfi na, sai dai na zuba muku ido kuma."
Shi dai kunya ce ta lulluɓe shi sosai kamar ƙasa ta tsage ya shige. "Oyoyo babban yaya" Ameesha data fito cikin shirin makaranta ta faɗa, murmushi ya mata kawai suka gaisa ita kuma ta nufi dinning dan tayi breakfast. Mummy kam miƙewa tayi ta kama hannun Zayyad ɗin, bata tsaya ko ina dashi ba sai ɗakin Khans da har lokacin bacci takeyi, "ku gaku tantabaru koh? Toh ku cinye juna ƙarewar soyayya" tana gama faɗi tayi waje tare da ja musu ƙofar. Daɗi kamar zai sheƙe Zayyad ya ƙarasa har inda take kwance cikin blanket, shafar sumar kanta yayi yana lumshe ido, a hankali take buɗe idon ta har ta sauke su kan Zayyad, ihu ta saki haɗi da dariya yayi saurin toshe mata baki kafin mom ta leƙo tace wani abu ya mata. Zare ta a jikin sa yana "maintain mana, kar kisa Mummy tazo ta katse min jin daɗi."
Murmushi ta kuma yi kafin tace "kamar kasan mafarkin ka nakeyi."
"Wow! Bani labari."
"Ba wannan ba dai, kazo ɗauka na ne?"
(Ni kam nace kuji marasa kunyan mutane🙈🙈)
"Hmm, kinsan ko me zai faru Mummy bazata bari in tafi dake ba, dama dai Ummi ce da sauƙi."
Marairaicewa tayi tare da langwabar da kanta kan kafaɗar sa tace "toh sai yaushe zamu koma gida kenan?"
"Sai kin haife wannan inji Mummy" ya faɗa yana shafa ƙaton cikin ta.
Hira suka ɗan taɓa zuwa ƙarfe 8 sannan ya fito tana biye dashi, sauri-sauri yake domin yana da patients sosai a asibiti, da kallo kawai mom ta bisu dan su suke abin amma ita kejin kunya, har dai Khansa'u ta dawo Mummy ta galla mata harara, dariya Khans ta kwashe dashi tana shigewa ɗaki, dan baccin ba sakin ta yayi ba. Gida ya nufa direct, yana shiga wanka yayi ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya ya fita, zuwa 9:20 ya isa asibitin ya soma gudanar da abin da ya kaishi.
*THREE WEEKS LATER*
Tafe yake kan hanyar sa ta zuwa duba lafiyar matar sa kamar yadda ya saba kullum safe da yanma, yau ya kama Friday, kasancewar baya komawa asibiti duk ran Friday. Da isar sa gidan da Khans ya fara tozali, ta shirya tsaff cikin maroon Abaya da ratsin baƙi mai matuƙar kyau, yayin da ta ƙawata fuskar ta da murmushi mai susutu mijin nata. Tsaye yayi yana bin ta da kallo har ya sauke duban sa kan cikin ta da yake haihuwa yau ko gobe, "oya u knw we don't have time, tashi mu tafi" Zayyad ya faɗa yana miƙa mata hannu.
Kamawa tayi ta miƙe suka nufi fita yana riƙe da ita har suka isa parking lot, gidan gaba ya buɗe mata ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga mazaunin direba yaja suka fice. Bai tsaya ko ina da ita ba sai gidan su, suna shiga suka yada zango a parlor, kallon gidan Khans ta somayi tana mamakin yadda ya gyaru tsaff tamkar da mace a ciki, bata ankara ba taji Zayyad ya rungumo ta ta baya, wani zazzafan nishi ya soma sauke mata akan wuyan ta kafin ya furta "i miss u so much bibty" ya ƙarasa yana ɗaukar ta cak zuwa ɗakin sa, ji yayi ta ƙara wani nauyi sosai da ƙyar ya iya ƙarasawa da ita kan gado, saida ya sauke numfashi kafin ya soma romancing ɗin ta zuwa wani lokaci da akalar tasu ta sauya salo.
A gurguje ya taimaka wajen yin wanka shima yayi kana suka fito, gida ya maida ta har zuwa lokacin kuwa su Mummy basu dawo ba, nan ya zauna suna ɗan taɓa hira, duk da rabin hirar duk shi yakeyi, lura da yadda take cijan leɓe ne yasa shi matsawa kusa da ita yana tanbayar ta ko lafiya?
"Babu komai" ta bashi da murmushi kan fuskar ta.
Shigowar Mummy ce ta sashi saurin sakin ta tare da matsawa kusa da ita, yana mai sada kanshi da ƙasa kafin kuma ya zame daga kujerar yana gaida ta. Cikin fara'a ta amsa masa tana mai faɗawa kan kujera, dan ajiye take, miƙewa Zayyad yayi yayiwa Mummy da Khans sallama ya tafi.
Tun Khans na iya daurewa da ciwon da marar ta keyi har ta gagara saida ta bayyana, Mummy bata kawo komai ba, dan a zaton ta normal ciwo ne, ruwan wanka ta haɗa mata na magunguna da kuma nasha tasha tayi tsarki da wanka dashi. Bai wani tafi ba, amma ya rage babu laifi.
Wasa-wasa har kwana uku Khans na fama da matsanancin ciwon mara, sai da ta soma naƙudar da bata shirya ba a kwana na ukun. Zayyad Mummy ta kira cikin kiɗima ta sanar dashi, babu jimawa kuwa sai gashi, dan yana asibiti lokacin, sosai ya tausaya mata ganin yadda ta fita hayyacin ta gaba ɗaya. Asibiti suka nufa tare dasu Mummy, gwaje-gwaje ya somayi mata, nan take ya gano da ciwon yakai kusan kwana uku tare da ita, tunani ya somayi tun ranar da sukaje gida, "ya salaam* ya furta a ransa suna mai cigaba da bata taimakon gaggawa. Sosai take shan baƙar wahala ga kuma sakamako daya nuna ba haihuwa bace, nan take Zayyad ya soma jin raɗaɗin zafin ciwon ya jikin sa, domin yama rasa ta yadda zai soma ceto ranta dana abinda ke cikin ta cikin gaggawa gudun samun matsala.
Shirya ta yayi tare da umartar Nurses su shiga da ita theater room kafin ya dawo, yana gama faɗi ya fice tare da nufar office ɗin sa....
_____________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/27, 8:23 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*
🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚
Marubuciyar:
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_
43 & 44....
📖____________A gurguje nurses suka fito da ita suka nufi ɗakin theater, ba jimawa shima ya dawo tare da wata doctor suka shiga, wahala iya wahala Khans tasha, a gurguje nurses ɗin suka fito da ita zuwa theater room, ko ina daga sassan jikin ta zufa ne ke fita. Babu jimawa shima Zayyad ya dawo tare da wata doctor mace cikin shirin yin theater. Sosai Doctor Na'eema da Zayyad ke nuna bajintar su wajen ciro babyn, amma inaa abu na nema ya zarce tunanin su, da ƙyar suka sami damar zaro kan yaron har suka ciro shi. Sun daɗe sosai matuƙa, kafin komai ya kammala, Zayyad da kanshi ya gyara ta tsaff sannan aka wuce rest room da ita. Ba ita ta farka ba sai bayan kusan awa biyu bayan Cs ɗin, zuwa lokacin kuwa dangi duk sun hallara, su anty Jumayna, Ummi da yaran ta su Haseena da auta Ayeesh da Ameesha, kai mazan ma ba'a barsu a baya ba, dukkanin su sunyi jugum suna jiran farkawar ta. A hankali ta soma buɗe idanun ta sai kuma ta rufe har dai ta Idasa buɗe su, duk da bawai sosai ta buɗe idanun nata ba, sabida hasken daya gauraye wajen ya kuma yiwa idanun ta nauyi, hannun ta ta ɗaga ta sauke shi akan cikin ta a hankali, jin babu cikin yasa ta kai kallon ta kan cikin dan tabbatar wa idanun ta. Ummi dake gefen gadon zaune ta kalla da idanun ta da suka kumbura sukai jajir, sai kuma ta maida duban ta ga Mummy dake kan kujera hannun ta riƙe da jariri, sai da tabi dukkan mutanen wajen da kallo kana tayi ƙarfin halin furta "Ummi ya Zayyad fah?" ta faɗa cikin disasshiyar murya mai cike da rauni da tausayi. Kafin ta rufe bakin ta sukaji sallamar Zayyad ya shigo, hakan yasa kowa yayi ba tare daya bata amsa ba, tunda ga amsar tambayar tata ta gani. Ƙarasawa yayi har inda take kwance, tare da kama hannun ta wanda ke riƙe da carnular, a sannu ya zare mata kasancewar ruwan da aka sa mata ya ƙare, sai da ya faki idanun Ummi da Mummy sannan ya kashe mata ido ɗaya tare da sakar mata murmushi. Kanta kawai ta iya kawar wa gefe, dan magana, dariya ko murmushi bashi da hali a halin yanzu.
Kwanan su takwas a asibiti suka dawo gida, zuwa lokacin Khans ta ɗanji sauki babu laifi, nan aka soma shirye-shiryen yiwa baby (Muhammad Al-ameen) taron suna. Sosai kuwa Daddy da Abba haɗi da shi Zayyad ɗin kansa suka nuna one love wa jikan su jinin Zayyad. Washe gari aka shirya liyafar gudanar da taron, kuma Alhamdulillah komai ya tafi yadda ya kamata kuma yadda aka tsara, inda yaro yaci sunan mahaifin Zayyad kuma mahaifin Khans, amma suna kiran shi (Areef).
Bayan suna da sati biyu bikin Haseena da Ameesha ya iso, anyi shagali kamar yadda suka saba gudanarwa a familyn, wato ɗaurin aure da walima kawai, (sauran Ayeesh, Allah nuna mana naki😌) Ameen.
*7 MONTHS LATER*
Zaune suke a dinning suna dinner cikin so da ƙaunar juna, Areef keta tsala ihu dole sai ya hau kan table ɗin, Daddy Zayyad🙈 ne ya miƙe tare da miƙa masa hannu, ai da da kuwa ya tafi yana dariya wanda ya bayyana haƙwaran sa guda takwas. Ciki suka shiga, kasancewar Zayyad dama ya gama cin nashi, Khans ce dai sai yanzu take ci, tana gamawa itama ta mara musu baya, koda ta shiga wasa ta taddasu sunayi, Areef sai ƙyaƙyata dariya yakeyi, kamar me!!
Washe gari ya kama Sunday.
*3:00 PM*
Cikin wata maroon shadda Khans ta shirya ita da rabin ranta kuma zuciyar ta gaba ɗaya wato Zayyad, sunyi kyau matuƙa, dan sosai kayan ya karbi jikin su, Areef kam cikin riga da wando ƴan kanti ta shirya sa, sakar baki nayi ina kallon Areef ganin yadda ya mugun yiwa kayan kyau, ga tsantsar kamannin sa data bayyana da Zayyad, sai kuma farin Khans daya ɗakko ya sirka da kalan hasken baban sa, ya bada wani kala na daban mai matuƙar kyau, inda suka bambanta da Zayyad, shi yana da san wasa da magana, shi kuma Zayyad shiru-shiru ne.
Tare suka fito Zayyad riƙe da Areef a hannu, ita kuma tana riƙe da side bag ɗin ta, mota suka shiga Zayyad yaja su, basu tsaya ko ina ba sai Ado Bayero mall. A 360 Zayyad ya figi motar zuwa inda zai daidai ta parking ɗin sa, sosai hankalin jama'a ya dawo kansu, suna jiran fitowar mai motar ganin yadda yake driving kamar zai tashi sama, kasancewar glass ɗin tint ne shiyasa basuga wanda ke ciki ba. Zayyad ne ya fara fitowa cikin salo da ɗaukar ido, yana takun sa na ƙasaita har ya ƙaraso mazaunin gaba ya buɗe tare da karɓar Areef daga hannun ta, bayan kamar minti 1 itama ta fito nan suka sakarwa junan su murmushi mai cike da saƙonni, kaii abin sai wanda ya gani. A tare suke ɗaga ƙafa su sauke, tafiyar su kaɗai ya isa ya yaja hankalin ka wajen kan su, fuskar mutanen wajen kaɗai ya isa ya bayyanar maka da yadda suka birge kowa sannan suka dace da juna. Ɓangaren play ground suka nufa first, nan Areef ya soma zillo kamar zai ƙwace kanshi, wajen wasa da mota suka nufa tare da sanya shi a ciki, shikam banda jin daɗi babu abinda yakeyi, dan Allah ya zuba masa wayau kamar wanda ya shekara, sosai kuwa yayi wasa, camerar Zayyad kamar zata fashe tsabar hotuna. Kasancewar Zayyad nason wasan tsere yasa suka nufi inda ake hawa doki, daidai wasu suma da bazasu wuce sa'annin Zayyad ba suma sunzo kan karawa dashi a harkar tseren, nan kuwa suka shirya ko wanne yahau dokin sa, ɗaya zuwa uku aka ƙirga ai kam dawakai suka soma gudu, wani kuka da dokin Zayyad yayi haɗi da miƙewa yasa ilahirin wajen ɗaukar ihu da tafi, yadda dokin Zayyad ke gudu kaɗai ya isa ya tabbatar maka da ƙwarewar sa a harkar, dan duk wani ja da yake yiwa dokin yasan inda ya dosa. Zayyad shine yazo first, inda wa'incan sukayi bracket (2). Banda murmushi babu abinda ke bayyana a fuskar Khans harya ƙaraso inda suke, hannu yasa ya karɓi Areef suka nufi wajen sallah. Suna yin sallah suka nufi wajen cin abinci, basu suka baro wajen ba sai kusan 6 tare da shopping ɗin da Zayyad yayi musu.
★★★★★★★
A kwana a tashi ba wuya wajen rabbussamawati wal ardi, yau Areef ya cika shekara ɗaya a duniya, ya ƙara wayau yayi haske yayi ɓul-ɓul abunsa zassha'awa. Tafe suke kan hanyar su ta dawowa daga gidan anty Jumayna, hold up daya cunkushe hanyar yasa Zayyad bai bi ba, yabi ta