Showing 36001 words to 36565 words out of 36565 words
Chapter 13 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
cikin layika kawai, karap idanun sa suka sauka kan wasu mata almajirai da suke bara a bakin hanya, samun kansa yayi dason taimaka musu, hakan yasa yayi parking ya kuma fita a motar, su su biyar ne a wajen kuma saida yabi ko wannen su da 2k, ya juya da niyyar tafiya kenan yaji an ambata sunan shi. *"Zayyad"*
Cak ya tsaya na ɗan wani lokaci sannan ya juya da niyyar son ganin mai kiran nasa, wata baiwar Allah ce matso daga inda take zaune tana hawaye, "Zayyad kai ne!" Ta kuma furtawa a karo na biyu.
Tsugunnawa yayi daidai tsawon ta, kasancewar a keken guragu take yace "baiwar Allah kin sanni ne?"
Kukan da yaci ƙarfin tane ya hana ta magana, Zayyad baiyi yunƙurin hana ta ba, a cewar sa kukan zai iya sama mata relief. Ganin lokaci na tafiya yasa Zayyad faɗin "baiwar Allah baki ce komai ba."
"Darl lafiya kuwa?" Khansa'u da isowarta kenan ta faɗi. Ɗaga mata hannu yayi, alamar shima bai sani ba.
Ɗagowa matar tayi tana faɗin "haƙiƙa sakayya ba sai anje lahira mutum ke gani ba, ni shaida ce tun a gidan duniya mutum ke ganin sakayyar shi, haƙiƙa wanda yaɗau duniya gidan zama tabbas zata koya masa darasi. Na cutar dakai Zayyad, na azabtar dakai, dan Allah ina mai haɗa ka da Allah kayi min afuwa ka yafe min ko Allah zai dube ni da idon rahama." Ta ƙarasa tare da rushewa da wani kukan.
Tunda ta soma magana Zayyad ya sunkuyar da kai, dan sai a lokacin ya lura da Karima ce matar baban sa, hannu yasa ya share zazzafan hawayen da suka biyo kuncin sa tamkar zasu ƙona fuskar sa. "Ban taɓa riƙe ki a rai ba, kuma na ɗauke ki tamkar mahaifiya ta data haife ni, na daɗe da yafe miki duniya da lahira, Ubangiji Allah ya yafe mana baki daya kuma ya gafarta mana." Daga haka ya miƙe tare da kama hannun Khans suka nufi mota, yana jin kukan ta dake ɗauke da tsantsagwaron nadama amma bai tsaya ba yaja motar sa zuwa gida, har suka isa babu abinda ya shiga tsakanin su na magana. Khans da kanta ta kira Ummi ta sanar da ita komai, Ummi dai batace komai ba, illa fatan shiriya da tayiwa masu hali irin nata, da kuma fatan Allah ya yafe mata, hatta su Daddy da aka gaya mawa suma addu'a da sukayi kenan. Nan kan familyn ya ƙara haɗuwa, gefe guda kuwa sai ƙara haɓɓaka sukeyi, dan Haseena da Ameesha dukkanin su su sauke ribar so suma, inda Haseena ta samu mace Ameesha ta samu twins duka maza. Abin sai godiyar rabbi.
*ƘURUNGUS*
Anan na kawo ƙarshen wannan littafi nawa mai suna *KHANSA'U*
Ina mai bawa readers haƙuri, da rashin typing da banyi ba kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon wani uziri mai girma.
Ina ƙara bawa readers haƙuri da yayyanke musu labari da nayi, hakan ya faru ne sabida gujewar yawan pages, Dan ba kowa ke jurar karanta littafi mai yawa ba.
A ƙarshe ina mai roƙon Allah daya yafemin kan kurakuren da nayi acikin wannan littafi, tare da fatan zaku kasance tare dani a littafai na na gaba masu suna:
*HALIN ƘADDARA* da kuma *ƳAR LESBIAN CE*🙏
Fatan alkhairi ako da yaushe fans, Ina ƙaunar ku.
*BABYLORH* CE😎
07069929131