Showing 6001 words to 9000 words out of 36565 words
Chapter 3 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
sai da yayi kusan 30mins sannan ya fito.
Office ya koma ya zauna tare da dafe kansa yana mai mamakin wani irin so ne yayi wa Khansa'u mummunan kamu haka har yayi causing mata ```Heart Attack```. Yana wannan tunanin ne su Abba suka shigo, dukan su zama sukayi tare da ƙurawa Zayyad ɗin ido cikin son ƙarin bayani game da Khansa'u. Saida ya fuzgi iska ya fesar sannan ya soma magana kamar haka ''amm Abba bisa yadda bincike ya nuna min, ta kamu da heart attack, wanda in har ba'ayi takatsantsan wajen ɓacin ranta da damuwar taba, it can lead to her death. Moreover, brain ɗin ta yayi sanyi shima, so dole za'a chanza mata asibiti, coz ba fanni na bane, ni a nawa shawaran ina ganin a fitar da ita outside kawai, su zasu fi bata irin kulawar data dace'', ya ƙarasa maganar yana mai kallon Daddy.
Sunkuyar da kansa Abba yayi da yakejin wani hawaye na ƙoƙarin zubo masa, yana matuƙar ƙaunar ɗiyar sa, addu'ar sa ɗaya Allah ya raya masa ita cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali. Daddy ne yayi ta maza yace ''yanzu wani asibiti ne kake ganin suna da kula sosai ta wannan fannin''?
Eh toh, kamar London, ko Dubai ina ganin zaifi gaskiya, ko India ma, cewar Zayyad.
Daga haka Daddy bai ƙara cewa komai ba illa kama Abba da yayi suka fita......
__________________________________✍️
Babylorh ce💖❤🔥
07069929131
[9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍
*(The famous arabic poetess)*
By
Babylorh🌹
Marubuciyar;
*RUSHDAH*
*MARAICI NA*
loading...... *_KHANSA'U_*
{The famous Arabic Poetess}
Wannan page sadaukarwa ne kacokam gareku masoya littafin Khansa'u, ina alfahari daku😍🌹💝❣️
Page 7 & 8.....
___________sun gama daidaita shi zasu sakashi ciki kenan jikin Daddy ya soma wata irin rawa yana karkarwa, da sauri Aliyu da Mahfouz suka nufesa suka riƙe shi tare da barin wajen dashi. Mota suka koma suka sanya shi ciki suna masu tashefa da addu'a, ganin kamar zai shiɗe yasa Aliyu komawa mazaunin driver suka yaja motar, yayin da Mahfooz ke ci gaba dayi masa addu'o'i har suka isa asibitin Zayyad, cikin gaggawa aka karɓe sa akayi ciki dashi, basu tsaya dashi ko ina ba sai Emergency room, abinka da asibitin kuɗi da nuna kulawa wa patients, nan doctors suka rufu akan sa, moreover kuma sunsan Family ɗin su Daddy da nasu Khansa'u, sai zuwa kusan 45mins sannan likitocin suka fito, ɗayan cikin su yayiwa su Aliyu alamar su biyo sa office. Ba musu sukabi bayan shi zuwa ofishin nasa suka zauna, likitan ne ya soma magana kamar haka ''a gaskiya a halin da ake ciki akwai matsala, is like Alhaji ya sanyawa kanshi damuwa ne zance ko tunani, har takai ga jinin sa ya hau sosai, yanzu akwai buƙatar sauyin magunguna da za'ayi masa, kuma insha Allah zai samu lafiya''.
Rinannun idanun sa Aliyu ya ɗago tare da sauke su kan doctor ɗin na ɗan wani lokaci kafin ya maida su kan Mahfouz dake faɗin ''toh shikenan doctor, mun gode sosai, amma yanzu zamu iya ganin shi?''
Nope, sabida har yanzu yana emerg sannan mun masa allurar bacci dan yasamu ya rage tunanin nan, cewar doctor.
Nan Mahfooz ya ƙara da ''okay doctor toh sistern mu fa, ita zamu samu damar ganin ta?'', ya faɗa cike da damuwa shimfiɗe kan fuskar sa. Murmushi likitan ya masa kana ya zagayo tare da dafa kafaɗun sa yace ''calm down my bros, suna cikin ƙoshin lafiya insha Allah, bt file ɗin kula da ita baya waje na, yana tare da Zayyad, so idan yazo zakuji komai daga gareshi''.
Godiya Mahfouz ya masa kana yaja hannu abokin nasa dake zaune kamar an dasa shi suka fita, ganin suna nufi parking lot yana Aliyu cewa ''Malam wai ina zaka kaini sai wani jana kakeyi''? ya faɗa tare da fizge hannun sa. Mahfouz dake jingine jikin mota ne yayi folding hannaye sa yana mai faɗin ''Aliyu zuwa yanzu nasan su Abba (baban shi) sun dawo daga maƙabarta, ya kamata kazo mu koma mu sanar dasu halin da ake ciki, kada hankalin su ya tashi''.
Babu inda zanje Mahfouz, kaidai kawai ka tafi kaje duk yadda ake ciki na kira ka, idan na tafi waye zai kula da Daddy in ya farka? Ina tare dashi har inga yadda ta Allah zata kasance, Aliyu ya faɗa cikin tsantsar damuwa.
Aliyu, Daddy yana ƙarƙashin kulawar Ubangiji dana doctors, nothing will happen insha Allah kuma zai farka very soon, kazo muje gida dan Allah.
Wallahi Mahfouz babu inda zanje, kaji na rantse, ya ƙarasa tare da komawa cikin asibitin ba tare daya jira cewar Mahfouz ba. Da kallo kawai Mahfooz ya rakasa harya ɓacewa ganin sa, sannan ya shiga mota yayi mata key ya fice, kusan tare ya dawo da ƴan maƙabarta dan a lokaci ɗaya suka isa. Jira yayi har su Abba suka ƙaraso, Abbane ya soma tanbayar sa ina suka kai Alhajin? Yana asibiti Abba, wai hawan jinin sa ya tashi sosai, shine nace bari in dawo in sanar daku halin da ake ciki.
Toh yanzu wa kuka bari a wajen sa? Cewar Abba.
Eh Aliyu na can, Ni kaɗai nazo dama. Muje ka kaini asibitin, daddy ya faɗa tare da shiga motar Aliyu da Mahfouz ya taho da ita.
Zayyad kam bai bisu ba, illa ma shiga cikin gidan da yayi wajen Mummy. Zakuyi mamakin yadda ya shiga cikin gida wasu zasuce cikin mata, so a ƙa'idar al'adar su basa zaman makoki zaman gulma, a cewar su babu abinda akeyi sai gulma da munafinci uwa uba gutsiri tsoma, hakan yasa saidai kawai azo ayi musu gaisuwa a wuce. Zayyad bai daɗe ba ya fito shima ya shiga tashi motar zuwa asibiti, yana isa bai wani ɗauki lokaci ba yaje ya shirya cikin kayan likitoci sannan ya fito tare da bada umarnin a chanzawa Daddy ɗaki zuwa special emerg, hakan kuwa akayi cikin lokaci ƙalilan aka fito dashi akan gadon su na turawa, da sauri Aliyu ya miƙe cikin tashin hankali ganin yadda Daddyn nashi yake, sanye yake cikin rigar asibiti blue ɗinnan ta patients da hula, sai hancin sa dake ɗauke da Oxygen yana fuzgar numfashi, da sauri Aliyu ya taka zaije wajen, Mahfouz yayi saurin riƙe shi tare da girgiza mai kai alamar yayi haƙuri mana, baiyi musu ba ya koma ya zauna wasu hawaye na bin fuskar sa, tsoro yakeyi kada ya rasa Daddyn sa da yayi masa saura, addu'a ma ƙauracewa bakin sa tayi sai daga baya ya samu ya iya aikawa mahaifin nasa addu'a.
Sosai kuwa Daddy ya samu sauyin kulawa a special emerg, dan harsun samu nasarar ƙara daidaita numfashin sa a karo na biyu, wanda suke tsoron zuwan karo na uku dan komai zai iya faruwa.
Yana zaune cikin wannan halin na mutuwar ɗan uwan sa da kuma rashin lafiyar mahaifin sane wayar sa ta hau kuka tana neman ɗauki, koda ya duba 'Role model' ya gani yana yawo kan screen ɗin wayar, da sauri ya ɗaga tare da karawa a kunnen sa yana mai furta ''Mummy''.
_Hello Son wai Ina kuka shiga ne kaida Alhaji? Koda kuka dawo maƙabarta Zayyad ne kawai ya shigo._
Amm Mummy muna asibiti, daddy ne ya faɗi a maƙabarta, sunce hawan jinin sane ya tashi shiyasa, bakiga yanda aka fito dashi ba Mummy zattausayi, Ina tsoron...... A fusace Mahfouz ya kwace wayar daga hannun sa yana mai auna masa harara kana ya kara wayar a kunnen ya soma magana ''Mummy kinaji, ba wani abu bane kawai hawan jinin sane ya tashi, so yanzu an fito dashi zuwa inda za'a chanza masa magunguna ne ba wani abu ba, karki damu, ai bazai wuce 30mins ba zai farka insha Allah''.
Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kana tace _shikenan son duk yadda ake ciki ka kirani dan Allah. Ya batun Khans kuma?_
Eh muna jiran fitowar Zayyad ne tukun, tunda sunce file ɗin ta na wajen shi.
_Okay Allah ya basu lafiya, sai naji ka_
Ameen Mummy sai anjima, ya katse wayar tare da fuskantar Aliyu ya soma magana cikin faɗa kamar haka ''wani irin raunin zuciya gareka ne wai Aliyu, sai kace mace, gaba ɗaya ka kasa sawa kanka natsuwa duk kabi ka tada hankalin ka kuma kana ƙoƙarin tadawa Mummy nata, dame zataji ? Mutuwar Zayd ko halin da Daddy ke ciki, instead ka kwantar mata da hankali amma kanata wani ƙoƙarin sanya ta cikin ruɗani, ya ƙara sa tare da jan tsaki.
Aliyu dai baice komai ba, dan ba ƙaramin ɓata masa rai Mahfouz yayi ba, idan yace zaiyi magana zasu iya samun matsala, danshi mutum ne mai shegiyar zuciya hakan yasa kawai yayi shiru ya ƙyale shi.
A ɓangaren Khansa'u kuwa abin saidai godiyar rabbi kawai, dan yadda aka kawo ta haka take, wataran numfashin ta ya tsaya cak, wataran kuma yayi daidai, hakan yasa Zayyad yanke shawarar shiga da ita Intensive Care Unit (ICU) Wanda kanawa suke masa laƙabi da (ɗakin duhu)😜.
Hakan kuwa akayi washe gari da safe around 8am aka shiga da ita ICU, gaba ɗaya ahalin biyu sun hallara a asibiti gashi sun gaza samun sukuni daga masu hawaye sai masu kukan zuci, dan kowa ya shaida daga ICU babu kuma wani ɗakin gaba, ko rai ko mutuwa. Sosai Zayyad yake nuna bajintar sa wajen ganin ya ceto ran ƴar uwar tasa kuma mafi soyuwa a gare sa, dan yadda yakeji da ita daban ne. Akai-akai Ummi (mummyn Khans) takan duba agogo sannan ta kalli ƙofar ɗakin ko zataga sun fito amma shiru kakeji har kusan 1hr, hakanan suka cigaba da haƙuri har suga abinda Allah zaiyi. Fitowar Zayyad yasa dukkanin su miƙewa suka nufe sa tare da tanbayar sa an samu nasara, share zufar sa yayi yace ''calm down all of u, har yanzu dai bata farka ba, amma zamu jira zuwa gobe mu gani idan har bata farka ba dole saidai a fita da ita outside''. Abba ne yaja wani dogon numfashi, dan shi inda za'abi ta shawarar shima yanzu bai ƙi su fitar da ita ba, amma zaiyi haƙurin su jira zuwan goben.
Kamar yadda Zayd yake shalelen parents ɗinsa, haka itama Khansa'u, Zayyad da Mahfouz ba ƙaramin ji suke da ita ba balle kuma uwa uba Ummi da Abba, kowa ya shaida yanda Khansa'u keda babban matsayi a zuƙatan su, domin kyawawan ɗabi'un ta kaɗai sun isa susa mutum ya sota saidai kuma in kana hassada, hakan yasa duk hankalin su ya gaza kwanciya, babban burin su bai wuce ace musu ta farka ba, amma abu yaci tura.........
```Toh wai waɗannan ahalin biyu meye alaƙar su ne? Ƴan uwan juna ne ko kuwa maƙwafta ne ko abokai?```
Nasan readers kuna ta wannan tunanin, toh karku damu, kasance tare da Babylorh danjin jikakkun tarihin wannan family
____________________________________✍️
Bebilo ce❤🔥💝
07069929131
[9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍
*{The famous arabic poetess}*
__________________________________
By
Babylorh♥️❤🔥
Marubuciyar;
*Rushdah*
*Maraici na*
loading..........
*KHANSA'U*
_(The famous arabic poetess)_
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
_(Domin Marubuta Mata)_
✨(W.W.A)✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
___________________________________
11 & 12......
*INDIA*
Hakan kuwa akayi, washegari da safe jirgin su ya ɗaga zuwa ƙasar India, inda suka tafi da Daddy, Abba, Ummi, Aliyu sai kuma Mahfouz, a wani *City Psychiatric Hospital* dake babban birnin Mumbai akayi admitting ɗin ta, tare da fara aiki kan matsalar ta. Abinka da ƙasar waje, basu da matsala fannin kayan aiki nan danan kuwa suka gano matsalar tata tare da yi mata dukkan abinda ya dace. Doctor Karan wanda ke kula da sashin Khans ne ya fito tare da cewa su Daddy su sameshi a office.
Office ɗin nashi suka shiga tare da zama inda aka tanadar musu, doctor ɗinne ya soma magana kamar haka ''Sir, yarinyar ku ta kamu da matsalar zuciya da ƙwaƙwalwa, duk da ƙwaƙwalwar tara bawai ta samu matsala bane, saidai koda ta farka she would become a psychiatrist, a yanayin binciken mu hakan ta faru ne due to heart attack data samu shiyasa ya taɓa ƙwaƙwalwar ta, amma karku damu, she would be fine and become healthy as before, saidai zuciyar ta ba zata dawo daidai ba, saidai kuma wani iko na ubangiji'', duk cikin harshen turanci yake maganar harya gama.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yanajin wani irin yanayi na ziyartar shi, ganin haka yasa Daddy tanbayar ''shin zata ɗauki tsawon wani lokaci a haka''?
Zatakai kamar 6 months with us here, shima dan kun kawo ta da wuri ne kafin abin yayi worst, so we would try our best akan ta muga ta samu lafiya, kada ku damu ku cigaba dayi mata addu'a, she will soon recovered by the grace of Almighty, daga haka bai ƙara cewa komai ba, nan suma su Abba suka bar ofishin.
Kwanan su Mahfouz uku suka dawo 9ja inda aka bar Ummi da Abba suna jinyar ta, badan Mahfouz yaso ba haka ya dawo saidan kawai aikin shi, amma yakan je ya duba ta musamman weekend. Shima Zayyad ba'a barshi a baya ba, dukkanin su sukan zo su duba ta a haka har suka kwashi watanni uku, amma babu abinda ya canza, ba Ummi ba hatta Abba kanshi ya riga ya sallama Khans bazata rayu ba, duba da yadda ta lalace ta rame tayi baƙi bata Um bare um um, in kaga tayi magana toh abu yakai ya kawo, amma komai ta gwammaci tayi shi da gaɓoɓin ta.
Yauma zaune suke ita da Ummi da kuma su Haseena da Ayeesh da Mahfouz da suka zo, a wanan karon ma harda Zayyad, sosai tayi farin cikin ganin su saidai ta kasa nuna hakan, sosai sukejan ta ta hira amma ba wani fiye amsa su takeyi ba, amma babu yadda suka iya, ko hakan da suka samu ma sunji daɗi.
Washegari da safe bayan Dr. Karan ya shigo sashin su Abba ya bishi Office, da gaisuwa suka fara kafin Abba ya nemi sallama daga asibitin a cewar sa gara ya koma suyi mata da Islamic. Duk yadda Dr. Karan yaso ga tausasa Abba kan a bari zuwa ko nan da wata ɗaya amma Abba yaƙi sam, tunda ta samu lafiya me zai zauna kuma yayi? Abin daya rage kaɗan ne dan haka tafiya kawai zaiyi. Badan yaso ba haka yayi discharging nasu tare da musayar number da sukayi dan wata matsalar. A ranar Abba yayi musu booking jirgin dazai tashi washe gari, cikin sa'a kuwa ya samu wanda zai tashi da ƙarfe 7 na safe.
Ba Ummi kaɗai ba hatta ita Khansa'un ba ƙaramin daɗi taji ba na komawar su 9ja, dan dama ta gaji da zaman asibitin ainun, a daren ranar duk suka wuce *Jalwa Guest Palace* da suka kama da zunmar shirya kayan su, babu wanda yayi bacci saida suka tabbatar da duk sun kimtsa. Washegari da misalin ƙarfe 7 daidai jirgin su ya ɗaga zuwa Nigeria....
*NIGERIA*
_____Alhmdlh sun isa lafiya kuma cikin ƙoshin lafiya, manyan motoci na alfarma ne har guda uku suka zo ɗaukar su, da Abba, Mahfouz da Zayyad motar su ɗaya, Haseena da Ayeesh suma motar su ɗaya, sai Ummi da Khansa'u suma mota ɗaya, tafiyar sa'a guda ta kaisu gida. Nan fa al'ummar annabi suka soma shigowa jajanta musu da kuma gaida maras lafiya, ranar gidan gaba ɗaya hargitsewa yayi kamar ana sha'ani, hatta Mummy da tawagar ta duk saida suka hallara a gidan, basubar gidan ba sai misalin ƙarfe 11 na dare.......
*Masu iya magana kan ce _WAIWAYE ADON TAFIYA_, toh! A wannan gaɓar nake mai muku albishir da muma zamu waiwaya danjin cikakken tarihin wannan Family.*
_Alh. Muhammad Shehu wato (Abba) da kuma Alh. Safwan Shehu wato Daddy sun taso tare inda sukayi komai tare, suka zauna tare kana sukayi aure tare a rana ɗaya._
_Alh. Muhammad (Abba) ya kasance ɗan riƙo ne a gidan su Alh. Safwan (Daddy), ya kasance maraya wanda tun tasowar sa bai taɓa tozali da iyayen sa ba. Ya kasance tsintacce ne wanda ba'a san iyayen sa ba, Mahaifin Daddy (Malam. Shehu, Allah ya masa rahma🙏) ya tsincesa ne a wani hatsari daya faru a KOFA dake ƙaramar hukumar BEBEJI dake garin Kano, hatsarin ya auku ne daidai express ɗin shiga KOFA, da misalin ƙarfe 6:30 na yanma inda burki ya ƙwacewa motar dake bayan su harta cin masu, da musu wani irin duka da bazaka so ka ƙara ƙallo ba, yadda motar ta tarwatse kaɗai ya isa ya tabbatar maka da bbu mai rai. ba'a iya ganin wanda ke tuƙin bama balle wa'inda ke ciki, unfortunately aka jiyo kukan jariri na tashi, daƙyar da wuya aka iya ɓamɓare ƙarafunan jikin motar aka binciko inda jaririn yake, zattausayi ganin a lokacin yazo duniya dan gaba ɗaya jikin sa jinin haihuwa ne, rasa wanda zai ɗauki jaririn da akayi yasa malam Shehu yin jahadi da ƙarfin halin ɗauka tare da tunanin rayuwar da jaririn zai shiga na halin rashi domin shi ɗin ya kasance talaka ne iyayen sa talakawa, wanda bai ajiye ba kuma bai bada ajiya ba, mutum na shi mai zuciyar nema kuma bashi da son abin duniya, wannan yasa Allah ke basa damar samun abu aduk lokacin da yayi ƙoƙarin nema. A lokacin daya dawo gida da wannan jariri ya fuskanci tashin hankali da barazana iri-iri wajen matar sa Sa'ade (kishiyar mamar Daddy), daga baya ma cewa tayi ya fitar mata da ɗan shege daga gida, wai yaje yayi cikin shege an haife masa. Kasancewar malam Shehu mutum mai haƙuri yasa ya tafi gidan ɗaya matar sa Habiba, saida ta fara tambayar sa inda ya samo shi dan kada zargin ta ya tabbata, bai ɓoye mata komai ba ya sanar da ita, sosai ta tausaya masa matuƙa gaya kana ta amsheshi ta cigaba da shayar dashi, dan dama batayi arba'in da haihuwa bama_...........
___________________________________✍️
Daga alƙamin babylor💓🌹
07069929131
[9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍