Showing 9001 words to 12000 words out of 36565 words
Chapter 4 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
(The famous arabic poetess
By
Babylorh🌹❤️
*(Shalelen Women Writers)*😎
Marubuciyar;
1. *Rushdah*
2. *Maraici na*
Loading.......
3. *KHANSA'U*
_(The famous arabic poetess)_
13 & 14.....
__________ _Bayan faruwar al'amarin kam sosai harkar kasuwancin mal.Shehu ya ƙara haɓaka, sosai yake ganin haske cikin al'amuran sa ga kuma ƴan yaransa maza suna ta wayau abin su abin sai godiya. A ɓangaren Sa'ade kuwa ta uzirawa malam ta hanasa rawar gaban hantsi, ganin bazai iya ba yasa ya sauwaƙe mata, murna wajen ta kam ba'a magana._
_Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu har girman su, su Daddy nada shekara 18 Malam Shehu ya soma wata cuta wadda aka rasa gane kanta, yayi jinya ba kaɗan ba kafin Allah ya karɓi rayuwar sa a safiyar juma'a. Nan sabon babin rayuwa ya buɗe musu, kasancewar dukkanin su dashi suka dogara, dan a lokacin yaran duk sun kammala secondary amma babu halin cigab. Da wuya da zufa suke iya buga-buga su nemo abinda za'a saka a bakin salati, haka rayuwar su tayi ta tafiya, Abba bai taɓa sanin su mal Shehu ba sune iyayen sa ba sai lokacin da inna ta tashi rasuwa bayan shekara 1 da mutuwar mal. Shehu, daren ranar da zata rasu ne duk ta sanar dasu labarin Abba, tana gama faɗa kuwa ta cika da kalmar shahada, sosai Abba yayi kuka ba kaɗan ba, kuka masu tarin dalilai ciki har da rashin sanin iyayen sa da baiyi ba haɗi da rasuwar wa'innan bayin Allah da suka riƙe shi da zuciya ɗaya._
_Sosai suke fuskantar rayuwa da halin rashi da suke fama har suka soma ƴar sana'ar su, su nami na yau su samu na gobe, Allah cikin ikon sa kuwa ya cigaba da buɗa musu har shekaru yaja musu, cikin ƙanƙanin lokaci sukayi suna suka zaga arewacin Najeriya, a lokacin suka soma tunanin aure. Nan Abba da Daddy suka firgita da mata har aka sanya ranar aure, a ranar ashirin da biyu ga watan Agusta shekara ta dubu biyu da ashirin da biyar 2015 da misalin ƙarfe ɗaya na rana aka ɗaura auren *Daddy da matar sa Rabi'atu* sai kuma *Abba da matar sa Maria*_.
_Bayan zuri'a da kowannen su ya tara ne babban ɗan Daddy wato Zayd da ɗiyar Abba Khansa'u suka jone, a lokacin Khansa'u na aji biyu a Babban sakandare wato SS 2, yayin da Zayd ke ajin ƙarshe a jami'a, babu wanda baiyi na'am da wagga lamari ba, tun suna jin kunyar bayyana soyayyar su har suka daina. Khansa'u ta kasance mace mai kishi ta yadda ko yaya taga Zayd da wata mace da bata santa ba ta ringa kishi tana kumbure-kumbure, wannan yasa Zayd kiyaye duk wani abu dazai ɓata mata rai, domin sonta a halittar sa yake, bai taɓa ganin ko wacce mace yadda yake ganin Khansa'u ba. Wannan dalili ne yasa Khansa'u kasa ɗaukar mutuwar Zayd a zahiri, duk duniya bayan iyayen ta babu wanda ke nuna mata ƙauna da gudun ɓacin ranta sama da Zayd, duk da kuwa suma su Zayyad ba daga baya ba wajen bata kulawa, sabida yarinya ce ita mai shiga rai lokaci ƙalilan._
_~WANNAN KENAN~_
*BACK TO STORY*
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin ahalin biyu, burin ko wannen su ya farantawa Khans, burin ko wanne ya kiyaye wajen ɓata mata rai, ita kanta tasan duk inda wani maiji da dangi maiji da kanshi cikin shalelen dangi ta wuce nan, a ko da yaushe takan yi iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta cire abin a ranta amma ta kasa, bata taɓa zaton haka takeson Zayd ba, tayi danasani iya danasani na fitar da sukayi a ranar, amma har yanzu bata daina addu'a ba kullum tanayi, sannan iyayen tama na taya ta.
Kamar yadda ta saba ƙulewa cikin ɗaki ta zauna tasha kukan ta sa'ilin data tuna da Zayd, yau ɗin ma hakan ne ya kasance, zaune take bisa lallausan katifar data mamaye ƙaton gadon ta hannun ta riƙe da album na zallar hoton Zayd tana kallo, sautin kukan tane naga ya ƙari yayin da tazo kan wani hoto da suke tare, tana sanye da baƙar Abaya shi kuma ya sanya farar jallabiya da baƙin takalmi sau ciki haɗi da rawani, sakk suka fito larabawa, musamman data ƙawata fuskar ta da murmushi suna kallon junan su, ban ankara ba naga ɗiyar ruwa akan hoton, koda na duba sai naga hawayen Khans ne ya zuba akai, a hankali tasa hannu ta share ta cigaba da buɗe album ɗin. Zaman da taji anyi kusa da ita ne yasa tayi saurin ɗagowa, Ummi ce ke zaune fuskar ta cike da tausayin ɗiyar tata, "haba Khans, meya sanya kike son shiga damuwa ne? Which is very very risk to ur life, shin mune bama faranta miki? Ko kuwa salon kula dake da mukeyi ne bakyajin daɗi?"
Kukan daya ƙwace mata ne ya hanata magana yayin da take girgiza wa Ummi kai alamar a'a kafin tace "Ummi na duk ta dalilina wannan abin ya faru da ya Zayd, da ban biye masa mun fita ba da duk haka ta faru ba, naso ace ni suka kashe suka barshi a raye, nasan zai fini jure rayuwa babu ni." Ta ƙarasa tana faɗawa jikin Ummi tare da sakin wani kukan.
A hankali Umma ke bubbuga bayanta haɗi da rarrashin ta har kukan ya lafa, cikin dibara Ummi ta zameta a jikin ta ta shiga bathroom, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta fito, badan Khans taso ba haka ta tashi ta shiga, dan a halin da take ciki ma wanka ba ƙaramin wuya yake mata ba. Aikam bata wani daɗe ba ta fito, Ummi taso ta mata magana, amma gudun matsala yasa ta ƙyale ta tare da bata wuri ta shirya.
Cikin combination na paper lace pink da purple ɗin atamta ɗinkin doguwar riga ta shirya, ba tare data shafa koda mai ba ta fito, dan hatta gashin kanta ma bata gyara ba, tamkar dai wacce ta tashi daga bacci. Parlor taje inda su Haseena ke zaune itama ta zauna, nan suka soma sakata cikin hirar su kuma ba laifi ta sake anyi hirar da ita, dan su har sunyi mamaki ma matuƙa.
***********
Yammaci ne mai ɗauke da sassanyar iska inda bishiyo ke kaɗawa suna bada ni'imtacciyar iska mai ratsa jiki, tsaye take a garden ta harɗe hannayen ta ta ƙurawa ɗan matsakaicin pool ɗin dake gefe ido kamar mai nazari, ta ɗauki lokaci sosai kamin fuskar ta ta fidda wani ƙayataccen murmushi da rabon da tayi irin shi tun kafin rasuwar Zaid.
Mahfouz dake tahowa a hankali cikin sanɗa hannun sa riƙe da feather 🪶 ya goga mata a wuya, da wata razananniyar ƙara ta juyo dan ganin meye, lokaci guda kuwa ta tamke fuska tace "ya Mahfouz ba kyau firgita mutum." Ƴar dariya yayi yace yace "Congratulations sis."
Da mamaki ta kalle sa kafin cikin rashin sani ta furta "for?"
"Ohh, baki ma sani ba kenan?," ya faɗa yana zaro wayar sa ƙirar iPhone daga aljihu, ƴan latse-latse yayi kafin ya ya miƙa mata wayar.
Amsa tayi ta soma dubawa, 'Admission later' ne dake nuna ta samu admission kuma akan course ɗin da duk duniya take muraɗi wato (Lawyer). Wani tsalle ta buga tare da rungume yayan nata tsabar murna, da sauri ya ture ta yana ɓata rai kamin yace "ke bakisan kin girma bane, meye kuma na wani faɗomin kamar sa'anki."
Ɗan ɓata rai tayi tana turo baki tace "toh kai ɗin ba yayana bane."
"Uhm bani waya ta nidai, saiki fara shiri," ya faɗa yana miƙa mata hannu.
Itama miƙa masa tayi tana murmushi sannan tayi cikin gida da ƴar murnar ta harda tsalle, sosai Mahfouz yaji daɗi ganin ƴar ƙanwar tasa cikin farin ciki, shima juyawa yayi tare da nufar sashin su...
_______________________________________✍️
*BABYLORH*🤞❣️
~*(Shalelen Women Writers)*~
07069929131✍️
Next page loading........
[9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(Shalelen Women Writers)*🌹💓
Marubuciyar:
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.......
3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_
15 & 16....
_________Nan fa su Khans aka soma shirye-shiryen shiga jami'a, domin nan da wata ɗaya zasu soma karatu. Saida suka kammala komai daya ƙunshi makarantar da kuma tabbatar data mallaki dukkanin abin buƙata kafin ranar karatu.
Yau take Monday, wato ranar dasu Khansa'u zasu fara karatu, Zayyad shine ya ɗauke ta zuwa makaranta ya kuma nuna mata department ɗin su, saida ya tabbatar da bata buƙatar komai sannan ya tafi.
*1st day at school*
Duk wata murna dajin daɗin da take tayi suna zuwa taji sun tafi, tunanin ta ɗaya yadda zata fara rayuwa cikin makarantar da babu wanda ta sani balle kuma a santa, waje ta nema ta zauna a kujerar dake ɗan nesa da department ɗin nasu ta cigaba da kallon yadda al'umma ke kai komo.
"Assalamu alaikum baiwar Allah," wata kyakkyawar budurwa ta faɗa wadda alamu suka nuna itama sabuwar zuwa ce.
"Wa'alaikis Salam," Khans ta amsa mata cikin sakewar fuska.
"Sannu baiwar Allah, dan Allah department of law nake nema."
"Ga shi can," Khans ta faɗa tana nuna mata da yatsa.
"Okay na gode sosai, sunana Nasreen Ahmad Sulaiman, kefa?"
"Khansa'u Muhammad," ta furta a taƙaice.
"Wow, nice name. Da alama kema sabuwar zuwa ce koh?"
"Eh," khans ta bata amsa cike da ciƙe da ƙosawa da shegen tambayoyi da surutun Nasreen din.
"Wow, amma ko wuri baki bani ba, kuma kinsan ance baƙon ka annabin ka."
Cikin murmushin yaƙe Khans tace "bismillah zauna mana."
Zama Nasreen ɗin tayi ta cigaba da jan Khans da surutu, duk da sai tayi magana kusan biyar kafin Khans ta bata amsar biyu, tun dai bata sake ba har ta saki jiki suka ɗan taɓa hira, duk da kusan gaba ɗaya hirar akan karatu ne. Basu wani jima a wajen ba suka shiga class aka soma lectures, sai kusan 2 suka fito, a gajiye Khans ta fito ga kuma yunwa da takeji, wayar ta ta ɗaga ta daddanna kamin ta kara a kunnen ta na ɗan wasu lokuta sannan tace "Hello ya Mahfouz, dan Allah kazo ka ɗauke ni kaji?"
Banji me akacedai ba daga ɗaya ɓangaren, naji ta amsa da zan jira ka kusa da department ɗinmu toh.
Inda ta zauna ɗazun nan ta koma ta zauna ta soma game da wayar ta, kwatsam saiga Nasreen, ita harga Allah tama manta da wata Nasreen wallahi, nan dai ta murmusa mata kana tace "sai yanzu kika fito?"
Wallahi kuwa Khans, ki taso muke muci abinci mana, yunwa nakeji sosai.
Laaaa, nikam har na kira yaya nama, yanzu zaizo ya ɗauke ni.
Okay, nima bari insa azo a ɗauke ni kawai, ta faɗa tana fiddo wayar ta, kira tayi itama kan azo a ɗauke ta, kamin suka cigaba da hira.
A wannan karon kam babu laifi Khans ta saki jiki da Nasreen, sunyi hira sosai kamin Mahfouz yazo. Nan sukayi sallama cike da kewa, musamman ma Nasreen da lokaci ɗaya taji son Khans da ƙawa.
Da sallama ta shiga ɗauke a bakin ta, Mahfouz dake motar ya amsa mata.
Washh, ta furta yayin da take zama.
Dariya Mahfouz yayi sosai sannan yace "yau fa manya an banbance secondary school da jami'a."
Baki ta turo tana ɓata rai yayin da take faɗin "kaiii yaya bazaka gane bane wallahi, akwai gajiya sosai."
Haha, lallai fa bazan gane ba, tunda ni banje jami'a ba.
Dariya duk suka sa kamin ta soma duba jakar ta, ganin bataga abinda take nema ba yasa ta ɗaga wayar ta tayi dialing number Nasreen.
Bugu biyu kuwa ta ɗaga tana faɗin "ba sai kin tambaye ni ba, yana waje na, saida kika tafi nima na gani."
Dariya duk sukayi kana sukayi sallama ta cigaba da sauraron ƙira'ar *Al'afasy* da Mahfouz ɗin ya kunna, har suka ƙarasa gida.
Cikin tangaɗi ta shiga parlor tamkar wacce bata taɓa zuwa makaranta ba, kan kace me dukkan wajen ya kaure da dariya, harda autar su Ayeesh ta dake cire socks ɗin ƙafar ta, wanda k nuni da itama yanzu ta dawo gidan.
Sosai ta ɓata rai ta nufi inda Ummi ke zaune itama ta zauna yayin da take faɗin "kinga Ummi wallahi ki jawa yaran ki kunne, musamman waccan mai ƙaramin hancin su fita a idona," ta ƙarasa tana nuna Ayeesh.
Nan ma dariyar aka ƙarayi kamin Ummi tace "toh ɗiyar albarka za'a ja musu kunne, maza tashi kije kiyi wanka kizo muci abinci."
"Tabdi, ƙyale wankan nan Ummi, bari in fara cika tumbin na tukun, kinji yadda kayan cikina ke kuka kamar zasu faɗo kasa," ta faɗa tana miƙewa tare da nufar dinning. Da dariya ƴan uwan nata suka bita, yayin da Ummi ta raka ta da murmushi haɗi da kallon ƙaunar ƴar tata, tare da fatan Allah yasa farin ciki ya ɗore har ƙarshen rayuwar ta.
Washegari ma haka Zayyad ne ya sauke ta a makaranta shi kuma ya wuce, nan suka ƙara jonewa da Nasreen, yau kam sosai Khans ta sake sukayi hira, cikik ƙanƙanin lokaci kuwa sabo mai tsanani ya shiga tsakanin su kasancewar tasu tazo ɗaya, abu ɗaya ke ɓatawa Khans rai da Nasreen shine yawan surutun ta, amma da sauƙi abun tunda bata sakin baki, surutun ta mai ma'ana ne. A haka har suka kammala level 1 suka shiga 2, ba ƙaramin ƙara maida hankali suka yi ba, duk da cewar ƴan matan biyu ba daga nan ba....
Kamar yadda suka tsarawa kansu shiga library bayan kammala lecture ta ƙarshe, yauma hakan ce ta kasance, basa bari wani uziri ya shigo musu a lokacin, a ƙalla kusanyi karatun 40mins kafin ko wacce ta kira azo a ɗauke su.
Yauma tafe ƴan matan biyu suke suna labari har suka isa wajen wani cin abinci dake cikin makarantar, sosai Khans ke bin wajen da kallo, dan a iya shekara ɗaya da ƴan ɗoriya data ɗauka a makarantar bata taɓa shiga cafeteria ba. Nan dai suka ci abinci su suka fito, inda suka saba zama nan suka koma yayin da Khans ta kira Zayyad kan yazo ya ɗauke ta, itama Nasreen drivern su ta kira, hirar su suka cigaba dayi har akazo ɗaukar Nasreen ɗin, sallama sukayi sannan sannan ta wuce yayin da Khans ta cigaba da jiran Zayyad. Wayar ta ta fiddo waje ta soma game kwatsam ta jiyo sallama daga tsakiyar kanta. Da sauri ta ɗago dan ganin waye, wani matashi fari mai kyau ke tsaye gaban ta fuskar sa ta ƙawatu da sassanyan murmushi. A hankali ta amsa masa tana tanbayar lafiya?
Zama yayi a kujerar dake gefen ta yace "lafiya lau ma kuwa, idan bazaki damu ba zanso ki bani aron lokacin ki domin in zayyane maki abin da ke tafe dani."
"Saidai kayi sauri, domin kuwa dap nake da tafiya."
"Babu komai na gode, ko zan iya sanin sunan ki?"
"Magana kace zakayi koko sanin sunana ne ya kawo ka."
"Afwan ranki ya daɗe, da farko ni sunana Zaid Ibrahim , ina ajin ƙarshe a ɓangaren karatun likitanci a wannan jami'a, ni ɗan asalin jihar Kaduna ne, karatu ne ya kawo ni garin Kano, dan Allah kema zanso insan sunan......."
"Bai ankara ba ya lura da runtse idanun da tayi, domin tun a lokacin daya ambato sunan shi zuciyar ta tayi wata mugun bugawa. Zayyad da ƙarasowar shi kenan ya hangi Khans dafe da gefen zuciyar ta ya fito da sauri, cikin sassarfa ya ƙaraso gare ta tare da kama ta yana tanbayar Zaid (part 2) abinda ke faruwa. Iya abinda ya sani kawai ya faɗa, shi kanshi Zayyad saida ya ƙara ƙare masa kallo sannan ya jata suka wuce, baya kama da asalin Zayd ɗin Khansa'u ta fuska, amma yanayin sak iri ɗaya hatta da yanayin askin sumar kansu iri ɗaya ce, sai dai masu iya magana sunce *kama da wane bata wane*, Zaid ɗin daya riga ya daɗe da rasuwa. Gidan gaba ya sanya ta tare da sauke mata kujerar, shi kuma ya zagaya ya shiga mazaunin sa, a natse yake nuƙi yana kallon ƴar uwar tasa akai-akai, jin ta soma magana yasa shi tattara dukkan hankalin sa wajen ta "Yaya kace min abin daya faru mafarki ne, ni Zayd ɗina ba haka yake ba, ba kunce ya rasu ba yaya...?" Ta ƙarasa tana fashewa da kuka jin wata irin suka da zuciyar ta tayi, Zayyad dai baice da ita komai ba har suka ƙarasa asibitin nashi, dan dama shi ba ma'abocin magana bane, shi da kanshi ya shigar da ita tare dayi mata allurar da aka tadana na masu irin ciwon idan ya tashi. Ta samu bacci na kusan awa ɗaya da rabi sannan ta farka bakin ta ɗauke da addu'a, bin wajen tayi da kallo sosai sannan ta gano asibiti ne, sai a lokacin abin da ya faru ya dawo mata, bata wani tsaya dogon tunani ba ta miƙe ta shiga toilet, alwala tayi ta fito kana da tada sallah, tana tsaka da sallah ne Zayyad ya shigo, zama yayi a ɗaya daga kujerun room ɗin harya jira ta idar, "muje in maida ki gida." Ya faɗa a taƙaice. Da ido kawai ta bishi tana mai tausayawa ɗiyar da Zayyad ɗin zai auro, dan ba ƙaramin fama za'a sha ba musamman idan bata da haƙuri, ace mutum magana ma wuya take yi masa.... daidai ta gama ɗaukar kayan ta tayi waje, a parking lot