Showing 21001 words to 24000 words out of 36565 words
Chapter 8 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
sa dariya suka shiga ciki, fira suka ɗan soma taɓawa na yaushe gamo kamin kuma suka shiga ɗaki, saida Khansa'u ta dawo ta ɗauka dukkan kayan abincin ta shiga dasu, nan suka ci suka sha sannan suka soma serious talk. Saida Nasreen ta tsaya ta ƙarewa Khans kallo sannan tace "wai ke Khans sai yaushe zaki amshi Zayyad a matsayin miji ne? Kada ki cutar da ɗan mutane fa, dan shima yana da gata kamar yadda kike dashi."
Tsaki Khansa'u tayi tace "Nasreen kinfi kowa sanin koda akayi auren mu ba sonshi nakeyi ba, toh me zaisa in amshe shi a matsayin miji?"
"Hmm, Khans kenan. Amma kinsan yana da haƙƙi a kanki kamar yadda kema kike da haƙƙi akan shi ko?"
Cikin rashin fahimta Khans tace "me kike nufi?"
"Ina nufin kamar yadda yake baki haƙƙin ki kema its your responsibility ki biya masa dukkan haƙƙin sa, wlh nayi tunanin zuwa yanzu kin aje dukkan wasu makaman yaƙi kun zauna lafiya, Khansa'u sati biyu ba, kwana goma sha huɗu amma baku taɓa fahimtar juna ba, ko ince baki bashi haɗin kai ba, dan nasan Zayyad na iya bakin ƙoƙarin sa, ki sani Khans wlh sai Allah ya tambaye ki, dan wannan cutarwa ce, idan dashi yake miki haka za kuji daɗi?"
"Ke da Allah ki ƙyale ni, zaki fara cikani da surutun naki, ni idan bazaki bani shawarar yadda zan rabu dashi ba toh ki ƙyale ni."
Waro idanu Nasreen tayi kana tace "lallai abin babba ne," a ranta kuma tace in kinsan wata bakisan wata ba.
Tashi duk sukayi sukayi alwala kasancewar la'asar ta gabato, da ƙyar Khans ta yarda suka shiga kitchen dan saamawa mijin nata abinda zaici in ya dawo, tuwon shinkafa sukayi masa miyar egusi taci kifi da nama, pineapple juice suka haɗa masa dashi, bayan fitar Khans, Nasreen ta leƙa ta tabbata da ta tafi, saita ciro wani tablet daga aljihun doguwar rigar ta, guda biyu ta ɓallo ta sanya cikin wannan pineapple juice ɗin da sukayi ta maida fridge. Koda khansa'u ta dawo wani juice ɗin suka ƙara haɗawa a karo na biyu, saidai a wannan karon watermelon and cucumbers juice sukayi, saida suka gama komai Nasreen taja Khans zuwa ɗaki ta zaunar da ita, ta soma mata magana kamar haka "idan har da gaske so kike ki rabu da Zayyad cikin sauƙi, toh ta wannan hanyar zaki ɓullo masa, kada ki riqa hora sa da yunwa dan wlh bazai rabu dake ba, kullum dare safe rana ki masa abinci, amma bance ki riƙa sake masa fuska kuna hira ba, kodan kada ya raina ki, so a hankali a hankali ni kuma zan riƙa daura ki kan abinda zakiyi step-by-step, Amma fa ki tabbatar duk abinda ake ciki kin sanar dani. Yanzu wannan drink din da mukayi guda biyu, kada kisha pineapple juice ɗin ki bar masa, nasan zai kashe masa jiki ta yadda duk abinda kikace yayi zaiyi, ni zan wuce yanzu, ki tabbatar kin sanar dani halin da ake ciki, sannan kije kiyi wanka, kada kuci abincin sai bayan Isha'i, kada kasala ta hanashi yin sallah." Ta ƙarasa tana miƙewa.
Itama Khans miƙewan tayi tana mai matuƙar jin daɗin shawarar ƙawar tata, dan a jikin ta takejin aikin su zaiyi kyau.
Hakan kuwa akayi, Zayyad ya shiga gida dap da maghriba sabida patients da suka masa yawa, sannan ya dawo a matuƙar gajiye tayadda har ya manta bai yi musu takeaway ba, Khans da taji shigowar sa tayi murmushin mugunta a ranta ta furta 'ka shigo hannu Zayyad'. Tana jin shigar sa ɗaki yana waya, da alama abokin sa ne, batayi yunƙurin bin sa ba, illa fitowa da tayi ta shirya komai kan dinning ta nemi waje ta zauna tana jiran fitowar sa. Ta ɗauki kimanin mintina talatin, dan har ta cire tsammanin fitowar sa ma, kawai taji ya murɗa handle, nan ta gyara zaman tare da zaman sexy night gown ɗin dake jikin ta. Karap sukayi ido huɗu da Zayyad dake ganin abin tamkar mafarki.....
__________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/12, 7:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*
The writer of
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_
29 & 30...
________Wani tsinkakken yawu Zayyad ya haɗiye yanajin jikin sa na masa wani irin chanji da bazai iya fassara shi, da ƙyar ya iya ƙarasowa dinning area ɗin ya zauna ɗaya bisa kujerun dinning ɗin, har lokacin bai ɗauke idanun sa kan Khans ba. Inda-inda ta shiga yi na tunanin yadda zata fara, dan tun daga kallon farko da Zayyad ya mata wani bala'in kwarjinin sa ya mamaye ta, da ƙyar ta miƙe cikin jarumta ta soma serving ɗinshi tana murmushin yaƙe kafin kuma murmushin ya koma na mugunta, sai da ta gama serving nashi tsaff, itama tayi wa kanta ta zuwa nata watermelon juice ɗin sannan ta zauna, shidai Zayyad baki buɗe yake bin Khans da ido yana tunanin anya ita ce?
"Bismillah koh?" Tace tana sakar masa wani murmushi mai tsuma jiki, tamkar wani robot (mutum mutumi) haka ya koma, a hankali ya soma cin abincin yana jin daɗin abincin har tsakiyar ƙwaƙwalwar sa, akai-akai sukan saci kallon junan su kuma saisu cigaba, har dai suka gama. Bayan kammalawar su da kusan minti 5-10 Zayyad ya soma jin kanshi na juyawa, ga azababbiyar sha'awa take bijiro masa kamar zaiyi hauka, idanun sa sun kaɗa sunyi jajir tamkar garwashin dake ruruwa, tun yana dannewa har cikin sa ya soma murɗawa, a daddafe haka ya miƙe ya shiga ɗaki, Khans da dawowar ta kenan taga shigar sa ɗaki, wata uwar dariya ta sheƙe da ita harda riƙe ciki, kukan da wayar Zayyad ta somayi ce tasa ta maida hankalin ta wajen, (Daddy) shine abinda ta gani yana yawo kan screen ɗin wayar, kamar zata ɗaga sai kuma ta miƙe ta shiga ɗakin Zayyad ɗin, 'wow' ta furta cikin ranta, domin ɗakin Zayyad ɗin ƙarshe ne wajen haɗuwa da ƙayatuwa, komai na ɗakin milk and coffee ne kama daga furnitures zuwa curtains har center carpet ɗin, wata ƙofa data gani ta nufa tana mai ƙarewa ɗakin kallo har ta isa ga ƙofar, a hankali ta tura ƙofar tana leƙawa kamar wadda tazo sata, dressing room ne wanda ya taka nata kyau, taɓe baki tayi taja ɗan siririn tsaki ta janyo ƙofar. Ƙara ta saki tana runtse idanun ta jikin ta na kyarma, Zayyad daya daɗe wajen yana kallon duk abinda takeyi yayi murmushin gefen baki, a hankali ya ƙarasa dap da ita, yasa hannun sa ya zare wayar ya ajiye, har lokacin jikin ta bai bar kyarma ba kuma bata buɗe ido ba. Rungumo ta yayi jikin sa yana shafa bayan ta a hankali, yanajin yadda take jan numfashi, nan take ya soma romancing ɗin ta cikin fitar hayyaci, ganin abin nasa na neman wuce gona da iri yasa Khansa'u yunƙurin dakatar dashi, amma inaa? Zayyad tuni yayi nisa bayajin kira (Hhh su Khans next Idan aka tashi gina ramin mugunta a gina shi gajere). Yarap suna faɗa kan gado, Khansa'u na kuka da magiya amma Zayyad kamar mara imani, duk yadda takai ga ƙwatar kanta ta kasa, yabi ya tokare da dukkan sassan jikin sa, tsoron ta bai ƙaru ba saida ya raba ta da dukkan kayan jikin ta, shi kam dama towel ne a jikin sa, dan daga wanka ya fito, da lalube ya nemi switch ɗin wutar ya kashe musu. Addu'ar saduwa ya karanto cikin disashewar murya, lokaci guda Khans ta saki wata wahalalliyar ƙara ta cigaba dayi masa magiya, bai ko bi ta kanta ba, sukuwar sa kawai yakeyi tamkar wani doki, nidai ina zaune harna wani lokaci inajin yadda kukan Khans ke fita a wahale.
_Wato abinda bata sani ba shine, lokacin da Khans ta koma ɗaki, Nasreen ta zuba ƙwayar tada sha'awa cikin pineapple juice ɗin da sukayi, hakan yasa tayi duk abinda zatayi ta hana Khans shan juice ɗin, Nasreen tana da manufar ta nayin hakan, dan yana ɗaya daga cikin abin da takeson ya gyara zamantakewar auren nasu._
Bayan wani ɗan lokaci Zayyad ya kunna wutar ɗakin, innalillahi wa inna ilaihi raji'un na furta a zuciya ta ganin Khans kamar sumammiya, koda na lura da kyau naga ashe ba suma tayi ba, wasu siraran hawaye kawai ke gangara kan kunnen ta tana daga kwance, tayi Allah ya isa wa Zayyad yafi a ƙirga, tayi dana sanin shigowa turakar Zayyad yafi sau shurin masaki, gashi ya karɓe budurcin ta wanda batayi niyyar basa ba a banza ya barta da wahala da gajiya. Wani kukan ta sake saki amma a wannan karon mai sauti ne. Zayyad baice da ita komai ba ya miƙe a hankali ya nufi toilet, saida yayi wanka sannan ya fito ya cicciɓi Khans, tayi ƙoƙarin zillewa amma taga ita zata sha wuya, dan wani raɗaɗi kawai kasan ta keyi, hakanan ta haƙura har ya kaita toilet ɗin. Duk yadda yaso ta bari ya mata wanka amma taƙi, babu yadda ya iya hakanan ya fita ya zauna jiran ta a ɗakin. Khans kuwa duk yadda ta motsa taji zafi sai ta sakawa Zayyad Allah ya isa, a halin da take ciki ma in akace ta rufe Zayyad ɗin da duka, tsaff zatayi. Cikin ƴan dabarun ta tayi jiƙa-jiƙan ta ta fito, (dan banace wanka ba). Daga yanayin tafiyar ta ma zaka tabbatar da ba wankan Allah da Annabi tayi ba, sosai tafiyar taba Zayyad matuƙar dariya wanda saida ya kasa riƙe dariyar ya ɗan murmusa, haushi ne ya mamaye Khans ta ɗanyi magana ciki-ciki wanda banji mai tace ba. Bata ko damu da kallon da Zayyad ɗin ke mata ba, tayi hanyar ƙofa abinta, da sauri Zayyad ya miƙe yasha gaban ta tare da furta "ina kuma zaki?"
Harara ta watsa masa tace "inda ka aikeni." (Nikam nace su Khans baki baya mutuwa).
Murmushi yayi ransa cike da farin ciki abin sa baiko damu da baƙar maganar taba ya ƙara da cewa "sorry dear, ki zauna pls, bari in kawo miki kaya."
"Bana buƙata Zayyad, ka bani hanya in wuce," ta faɗa cikin tsawa. Ba tare da Zayyad ya shirya ba ya matsa, gudun kada ya jawa kansa, wucewar ta tayi ba tare data ƙara kallon inda Zayyad yake ba.
Koda ta koma ɗaki wani marayan kuka ta saki tana latse-latse a wayar ta kamin ta kara a kunne, bugu biyu kuwa aka ɗaga tare da furta _"kawas ya ake ciki?_"
Kuka Khans ta ƙara saki tana mai cewa "na shiga uku Nasreen, shikenan Zayyad ya gama dani a duniya, ya cuceni wlh, na shiga uku ni Khansa'u," ta kuma rushewa da wani kukan.
_"subhanallahi, ke meke faruwa ne, me Zayyad ɗin ya miki kike wani kin shiga uku?"_
Tiryan-tiryan ta zayyanewa Nasreen kaff abinda ya faru, ta kuma ƙara da faɗin "dan Allah Nasreen ki samomin flusher gobe ki kawo min, wlh na tsani Zayyad, bazan iya haɗa jini dashi ba wlh, na roƙe ki Nasreen."
Sosai ƙawar tata ta bata tausayi amma kuma taci dariya, cikin salon yaudara ta soma rarrashin ta har ta samu tayi shiru ta kuma tabbatar mata da zatazo goben insha Allah, nan sukayi sallama ta kashe wayar. A hankali ta kwanta ba tare data cire towel ɗin jikin ta ba taja bargo.
Dukkan abinda Khans ta faɗi a kunnen Zayyad ta faɗe su, sosai yaji babu daɗi jin yadda ƙanwar tasa ta tsane shi, ya daɗe nan tsaye yana tunani barkatai gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi, cikin jarumta yaja ƙafar sa da yakejin ta masa nauyi ya tafi ɗaki. Alwala ya shiga yayi ya fito ya tada sallah harya idar, ya daɗe kan sallayar yana roƙon Allah yasa yayi ajiya a cikin Khans tare da neman kariyar Allah ga duk wani hari da Khans zata kaiwa cikin, akan sallayar ma bacci yayi gaba dashi.......
____________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/13, 1:01 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*
🪶_*WOMEN WRITERS ASSO...*_📚📚
The writer of:
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_
31 & 32....
📖____________Haka rayuwar auren su ta cigaba da wakana, tun bayan faruwar wannan al'amari Zayyad bai ƙara sa Khansa'u a idanun sa ba, bata taɓa fitowa sai ya bar gidan, sannan kafin ya dawo ta koma ɗaki, duk yadda yakai ga ritsa ta a gida ya kasa, ga abu har ana neman sati 5, harya soma jin haushin kansa ma. Idan kuma ya zauna yayi tunani, sai yaga ba laifin sa bane, lokaci ɗaya sha'awar da bai taɓa zaton akwai ta a duniya ba ta taso masa, baiga wani aibu aciki dan ya sadu da matar sa ta sunna ba da har zata ƙaurace masa.
Yau ya kama Friday, tun bayan da aka sakko sallahr juma'a ya nufi gida, dan bayajin zai iya zuwa asibiti balle kuma ya duba patient, koda ya shiga gida a tunanin sa zaiga Khans a parlor amma sai yaga akasin hakan. Yanke shawarar zuwa ɗakin ta yayi bayan yaje ya ɗakko extra key ɗin ƙofar, cikin sa'a kuwa ya buɗe tare da faɗawa ɗakin, zaune ya same ta tana shan oat milk, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallon TV, koda taga shigowar shi batayi mamaki ba, dan tasan bazai rasa spare key ba. Cikin takun nan nasa mai kama dana isa yake nufar inda take, kallo ɗaya zaka masa ka gano yana cikin damuwa, amma baiyi ƙasa a gwiwa ba ya zauna gefen ƙafafuwan ta ya kafe ta da ido. Tun da ya shigo harya ƙaraso, bai samu arziƙin kallon mutunci daga Khans ba, duk da ma tunda ta kalle shi sau ɗaya bata ƙara mararin kallon wajen ba harya zauna.
"Ina mai haɗaki da girman Allah daki juyo ki saurare ni muyi magana," Zayyad ya faɗa cikin sigar tausayi.
Ba tare data kalle sa ba tace "ina ce kunne keji? Dan haka ka faɗi abinda ke tafe dakai, idan kuma babu ka bar min ɗaki dan banason ganin ka."
Wani abu ne yazowa Zayyad wuya, ya tokare yaƙi gaba yaƙi baya, amma bai bari ta lura ba, cikin jarumtar su ta maza ya ƙara da cewa "kunne ji kawai yakeyi Khans, hankali ke auna maganar ita kuma ƙwaƙwalwa ta bada amsa, dan Allah ki saurare ni."
"Ina jinka," ta faɗa tana kafe sa da mayun idanun ta masu sanya dukkan wani lafiyayyen namiji cikin halin ha'ula'i.
"Wata biyu ake nema da bikin mu Khans, amma dukkanin mu bamu san meye daɗin aure ba, ta sani cewa baki sona, amma ban ɗauka tsanar da kika min yakai har kiji bakison haɗa jini dani ba. Yau ko bani da asali mahaifin ki ya zaɓa miki ni ya kamata ki karɓa da hannu bibbiyu, tunda kin shaida bazai zaɓa miki wanda za'a zo ana dana sani daga baya ba. Tun tasowar ki kika ganni gidan ku, wanda kikayi tsammanin ciki ɗaya muka fito, ban taɓa ɓata miki ba kema kuma haka, hasalima bayan Mahfouz babu wanda kuka shaƙu dashi kamar ni, duk da kuwa nasan ni ɗin bamai son shiga jama'a bane. Amma meyasa daga haɗa auren mu dake kika ɗauki tsanar duniya kika ɗora min? Alhalin kinsan bani nace Abba yayi haka ba, banaso in zama macuci a gareki, haka zalika banso kema ki riƙa cuta ta a zaman auren mu. Banso maganar nan tayi girma takai bakin manya, domin nasan bazamu kwashi ta daɗi dasu ba, ina roƙon ki daki sassauta ƙiyayyar ki a gare ni, ki riƙe ni mijin ki kamar yadda Allah ya zaɓa miki ni a matsayin miji."
"Zayyad kenan, kana tunanin zuciyar da aka cuta zatazo taso wanda ya cuce ta ne? Ka rabani da farin ciki na Zayyad, a dalilin ka Zaid ya barni yana kuka, wanda bansan halin da yake ciki ba yanzu. Da ace kana sona kamar yadda ka faɗa da bazaka zo ganina a irin wannan halin ba, da tun lokacin da akeson haɗamu zaka cewa Abba bakaso, dan nasan maganar ka kaɗai zaiji, bazamu taɓa iya dawowa kamar yadda muke dakai ada ba Zayyad har sai ranar daka miƙamin takardar saki na," ta ƙarashe hawaye na biyo kuncin ta.
Wata uwar razana Zayyad yayi, jin Khans na musu fatan saki, abinda ko a mafarki bai taɓa zato ba, yana son Khans iya son da daya