Showing 30001 words to 33000 words out of 36565 words
Chapter 11 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
na takura mata yasa ta zumbula doguwar rigar ta ta Abaya golden color mai matuƙar kyau, ta riga sa shiryawa hakan yasa ta nufi turakar sa dan dubawa ko ya gama, "fatabarakallahu ahsanul khaliƙeen" ta furta sa'ilin da sukayi ido huɗu dashi, a kowace daƙiƙa ganin kyawun sa take yana ƙaruwa tamkar ba jinin Nigeria ba, cikin baƙin yadi mai santsi, hular kansa zanna bukar ce mai kwalliyar baki da fari, takalmi baƙi yasa kana ya kwasa wayoyin sa yana "muje koh?"
Inaaa! Ai bata ma san da ita yake ba, dan ta daɗe da shagala da kallon sa, har ya matso dap da ita bata sani ba saida ya hura mata iska sannan ta dawo hayyacin ta, murmushi tayi tana mai sada kanta da ƙasa dan sosai taji kunyar sa, shima murmushin ya mata yaja hannun ta suka fita har harabar gidan. Brown ɗin Lexus RX 2018 suka shiga suka ɗau hanya. Sunyi tafiyar kusan mintina 30 kafin yayi parking a wani babban shopping mall ƙayatacce kuma haɗaɗɗe, fita yayi ya zagaya ya buɗe mata itama ta fito kana ya sawa motar lock suka shiga. Sassanyan ƙamshi ne kawai ke bugar hancin mutum tun taga ƙofar shiga, sun yi kusan tafiyar minti biyar sannan suka isa wani sashi na zallar kayan yara jarirai da dama sama dasu. Sosai Zayyad ya jida kaya kala-kala dan har saida Khans ta tausaya masa, tana tunanin fitar kuɗin, tayi-tayi dashi ya bari su riƙayi a hankali amma yaƙi, a cewar sa bayaso suna yawan zuwa siyayya, babu yadda ta iya haka ta ƙyale shi har suka gama, suka nufi inda zasu biya kuɗin, suna tsaye ana yi musu calculating yayin da Zayyad ke danne-danne a wayar sa.
"Dr. Zayyad?" Wata ƴar matashiya da zata iya girmewa Khans ko kuma suyi sa'anni ta faɗa.
Ɗagowa yayi dan ganin wanda ya kira shi ɗin, da mamaki ya amsa dan shi bai santa ba, balle yasan nata sunan.
Ƙara washe baki tayi tace "sannu ya gida? Been a while."
"Alhamdulillah" ya bata amsa a taƙaice.
"Uhm baka gane ni ba ko? Sunana Zeenat Ibrahim Ɗangaske also knwn as Nina, nasan kasan Alh. Ibrahim ɗan gaske ko?"
"Eh na sanshi."
"Mahaifi na ne then, zaka iya tuna lokacin da kazo kayi treating ɗina da bani da lafi...?"
Kafin ta ƙarasa Khans ta buga wani uban tsaki tayi waje, da ido Zayyad ya bita dan yasan kishi take. Tana nan tsaye wajen mota har Zayyad ya fito wanda saida ya kwasa mintina goma aciki kafin ya fito ɗin, har ya fito ya sanya kayan a booth ya buɗe motar bata kalla inda yake ba, saida yayi yayiwa motar key, suka bar harabar asibitin kamin yace "ranki ya daɗe, fushi kuma akeyi dani ne?"
Wani abune ya kawo mata kuya yaƙi gaba yaƙi baya ya tsaya cak, tsabar baƙin ciki. Kamar ta fasa ihu haka takeji amma tayi shiru batace dashi komai ba, maganar duniyar nan Zayyad yayi amma ko uffan bata ce ba, bata ma san yanayi ba har suka isa gida. Bata jira ya gama daidaita parking ɗin bama ta ɓalle marfin motar ta fice, tanajin yana ƙwala mata kira amma tayi kunnen uwar shegu dashi tayi gaba, shima baiyi ƙasa a gwiwa ba ya mara mata baya, har takai bakin ƙofar ɗakin ta zata buɗe Zayyad ya cin mata tare da shan gaban ta, "haba babyna, kina ji tun daga waje nake kiran ki amma kiyi banza dani? At least u should have listen to my explanation first, before kiyi fushi haka, ita fa wannan yarinyar da kika gani mahaifin ta mutumi na ne, muna mutunci dashi sosai, sannan yakan kira ni in duba yaran shi in basu da lafiya, har dashi kanshi ba, so i once treated her lokacin da tayi wani ciwo, shine data ganni tayi min magana fa. Ni banma gane ta ba, dan kamar ma ba'a ƙasar take ba, coz tunda na duba ta lokacin ban kara ganin ta ba ko naje gidan, ki yarda dani habibty nothing more."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "amma kasan da bakayi kyau haka ba da baza ta maka magana ba, kaga fa yadda nake ta wani washe maka baki kamar wani mijin ta, sai fari take maka kai kuma kana biye ta, yadda kayi kyau wadanda suka fita ma ai zasu tare ka."
Sosai maganar taba Zayyad dariya matuƙa, dan saida yayi da gaske sannan ya danne dariyar shi, yasan halin kayar ki sarai idan har dariyar ta kufce masa akwai ƙura matuƙa, ƙara narke fuska yayi alamar rarrashi yace "extremely sorry bibty, kinsan so na hana ganin muni, maybe ma ke kadai kike ganin kyawu na. Yanzu ma ki rasa dawo zakiyi kishi sai wannan? Haba bibty karki bani kunya mana, ni Ina dake a doron ƙasa wace ce ta isa tace zata shiga tsakanin mu, ai tayi kaɗan, so kwantar da hankalin ki, Zayyad naki ne ke kaɗai."
Murmushi ta sakar masa kana mai lafewa a jikin sa, dan sosai take samun natsuwa duk lokacin da take jikin sa, sun ɗauki kusan 2mins a haka, kafin a hankali ya zame ta a jikin sa yace "bari in shigo da kayan." Da toh ta amsa masa tana shiga ɗaki. Mayafin kan ta ta zare tana mai ƙure fanka dan sosai takejin zafi kamar ta kama da wuta, kayan jikin ta ta cire da zunmar shiga wanka, dai dai Zayyad ya shigo da kayayyakin, ganin haka yasa shi saurin cire nashi kayan a cewar sa tare zasuyi, dariya Khans tayi ta faɗa toilet ɗin ba tare da tace dashi komai ba, ganin haka nikam nace bari nayi musu sallama nikam...
_____________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929231
[10/19, 8:28 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*
🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚
The writer of:
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_
39 & 40....
📖____________Haka rayuwar auren su ta cigaba da wakana cikin farin ciki, kwanciyar hankali da ƙaunar juna, Inda cikin Khans keta ƙara girma yana fitowa. Kamar yadda ya saba janta su fita da safe da kuma yamma, yau ma hakan ce ta kasance, tafe suke da yammacin ranar asabar suna tafe suna labari, Khans kam duk tafiyar minti ɗaya sai ta tsaya ta huta da haka har suka iso gida, kan kujera ta faɗa tana sauke numfashin gajiya, kafin ta miƙe ta shiga tayi wanka. A kusa tare suka fito, dan shima yana shiga ɗakin wankan ya faɗa, cikin skyblue jallabiya mai kyau da santsi ya fito, ta matuƙar amsar jikin sa inda ya sanya farin silipar ɗinsa ya fita, ba daɗewa sosai ya dawo ɗauke da takeaway, dan yanzu Khans ta dena girki, sakamakon duk abinda ta girka in ƙamshin ya buge ta saitayi amai, wani lokacin ma tana tsaka da girki zata kwara amai, hakan yasa Zayyad dakatar da ita har zuwa ta haihu. Babu jimawa sosai ya dawo, bai tadda ta a parlor ba, kitchen ya shiga ya ɗaukar masu plate kana ya shiga ɗakin ta. Zaune ya tadda ta kan sallaya ta mimmiƙe ƙafafu, murmushi yayi yace "mummyn babies duk gajiyar ce haka?"
Bata rai itama tayi kafin tace "ai wlh ya Zayyad duk kai kaja min wannan gajiyar, ni babu inda zanje gobe gaskiya, wanda nayi a baya ma Allah yayi albarka, amma gaskiya na gaji, kullum mutum yayi ta yawo kan hanya, haba."
Dariya ya kwashe da ita kafin yace "baby ke nake samawa sauƙi fa, kinsan Allah yanzu ma aka fara, daga nan har ki haifemin ajiyar dana baki, kinga daganan saiki daina, amma yanzu kam inaa.." ya ƙarasa yana buɗe musu abubuwan daya shigo dasu.
Takeaway uku ne, ko wanne ɗauke da lafiyayyen abinci, ɗaya shinkafa da miya ne sai nama a sama, ɗaya kuma ɗauke da farfesun kaji yayin da ɗayan ke ɗauke da lafiyayyar waina da miyar egusi. Wainar dake ta tiriri tana fidda daddaɗan ƙamshi ran Khansa'u ya biya, sosai taji tana so taci, dan tana tunanin zai zauna acikin ta. Nan taja plate ɗin ta soma ci, kamar abin arziki har taci ɗaya da rabi taji ta fitar mata a rai ko ƙamshin ma batason ji, ture plate ɗin tayi tare da kawar da kai, Zayyad dake cin shinkafa ne ya ɗago yana "lafiya?"
"Banason jin warin wainar, ka ɗauke plate di..." Ai bata ƙarasa ba ta soma amayar da abinda taci tamkar zata amayar da hanjin cikin ta, da ƙyar Zayyad ya samu Aman ya tsaya yana mai matuƙar tausaya wa matar tasa. Sosai cikin ke matuƙar wahalar da ita tunda ya shiga wata biyar, abin da batayi ba farkon cikin, da kanshi ya gyara wajen tare da taimaka mata wajen gyara jikin ta. Zama yayi kusa da ita na ɗan wani lokaci kana yace "yanzu me kikeson ci?"
"Zogale" ta faɗa a marairaice tare da kwantar da kanta saman kafaɗar sa.
Agogon hannun sa Zayyad ya kalla, ƙarfe 7:30pm ya gani, tunanin inda zai samu dafaffen zogale ya somayi, gashi shi ba iya dafawa yayi ba, dan samun zogale ba abune mai wahala ba, dan akwai shi a lambu, samun wanda zai dafa ne matsalar. *Mummy* ita ce ta faɗo masa a rai, nan ya miƙe tare da sanar da ita bari ya yaje ya dawo. "Toh" tace masa tana gyara zaman ta saman gadon.
Tuƙi yake cikin ƙaguwa da son ya isa wajen Mummy kafin dare yayi, cikin lokaci ƙalilan kuwa ya isa, sosai Mummy tayi mamakin ganin sa yanzu daya kamata ace yana masallaci, dan Isha'i ake kira. Saida suka gaisa sannan ta tanbaye shi lafiya? Ƙeya ya sosa kafin ya sanar da ita abinda ke tafe dashi cikin kunya. Dariya sosai Mummy tayi kafin tace "su Zayyad sarakan kunya, toh sunkuyar da kan me kake kuma, ni kakejin kunya kome?"
Shi dai Zayyad bai ce komai ba sai murmushin kunya da yake ta yi yana sosa kai. "Toh maza yanzu tashi ka tafi masallaci dan Aliyu bai daɗe da fita ba shima, nayi mamaki ma da baku haɗu ba, zan san yadda za'ayi ka kai mata zogale a daren nan, harda rama ma."
Dariya yayi yace "yauwaaa Mummy na, shiyasa nake sanki, sai na dawo," ya faɗa yana mai ficewa.
Da murmushi kawai Mummy ta raka shi tana mai jin ƙaunar sa a ranta.
Yana fita itama Mummy ta miƙe ta fito tana ƙwalawa Tanimu mai gadi kira, da hanzari ya ƙaraso tare da ɗan duƙawa yana "ranki ya daɗe gani."
"Yauwaa Tanimu, dan Allah zogale zaka samo min a lambu yanzu kaji, zanyi anfani dashi ne da gaggawa.
"Ah haba hajiya, ai bama sai kin roƙa ba, yanzu za'a kawo." Ya karasa tare da miƙewa ya nufi lambu da sassarfa, ba daɗewa ya dawo ɗauke da zogale mai yawa kuwa, sosai Mummy taji daɗi, dan tanason aikin Tanimu bashi da wasa ko kaɗan.
Cikin lokaci ƙalilan suka gama tsinke zogalen da gyarawa ita da Laure da Kubra masu aikin ta. Har ta dafa Zayyad da Aliyu basu dawo ba, hakan yasa ta danna kiran Zayyad, amsawa yayi tare da furta "muna hanya Mummy," daga haka ya katse.
"Yaya daga zuwa masallaci kuma sai kuje ku zauna kamar masu gadin masallacin."
Dariya duka su biyun sukayi kafin Aliyu yace "Mummy munje gidan mune fa, ba wani waje muka je ba."
"Ku kuka sani, kai kuma ga zogalen nan ka ɗauka maza ka kama hanya ka koma gida, sannan ka dawo da yarinyar nan gida da zarar cikin ta ya shiga wata na takwas ta haihu a gaban mu, kar kace zaka karɓa haihuwar ta."
Turƙashi, anya zan iya kuwa Mummy? ya faɗa a ransa, a zahiri kuma yace "toh Mummy na gode." Ya ɗauka yana fice wa.
Ba shi ya isa gida ba sai kusan ƙarfe 9 na dare, a parlor ya tadda ta tana zaman jiran sa, riƙe da ayaba a hannun ta taci kwatar ayaban. "Madam, ga zogalen."
A gajiye ta ɗago taja warmer ɗin zogalen gaban ta, buɗewa tayi tana yatsine fuska, lafiyayyen haɗi Mummy tayi mata, harda ƙarin lettucce (latas) a akai, da yankakkiyar albasa haɗi da tumatir da sweet papper da sauran su, tururi kawai yake fitar wa mai daɗin ƙamshi. "Spoon" ta faɗa tana mai da kanta kan kujerar, a hanzarce Zayyad ya miƙe ya nufi kitchen, ba daɗewa ya dawo ɗauke da cokali ya miƙa mata. Ci biyu uku tayi ta ture, dan ji take idan ta cigaba daci zata iya yin amai. "Yadai bibty, mai ya faru?"
"Ba naci" ta furta a taƙaice.
"Baki ci kuma? Haba Khans, yanzu Mummy ta dage ta dafa miki sannan kice ba kici! Bayan kuma ke kikace kina so!"
"Ni nace ina so dear, amma yanzu banaso, dan Allah ka ɗauke, wlh ko warin shi banson ji. Ni kaga banason yawan hayaniya ma, dan Allah kayi shiru.
Da ido kawai Zayyad ya bita, dan ta soma bashi mamaki ma, ace mutum yana buƙatar abu, kuma a kawo masa yace bayaso?
_Haba Zayyad sai kace ba likita ba, kasan ko wani ciki da irin nasa laulayin ai, sai kayi mata uziri_, wata zuciyar ta bashi amsa.
Jan warmer din yayi gaban sa ya ɗibi spoon ɗaya yakai bakin sa, tsabar daɗi ma ya hanashi magana saida yayi spoon uku kafin yace "bibty yanzu wannan kike cewa baza kici ba, lallai anyi babu ke, ashe haka yake da daɗi dama, anya ba gidan Mummy zan koma da zama ba kuwa? Kullum ta riƙa dafamin....
"Ya salaam" ta faɗa tana dafe kanta, daga bisani kuma ta miƙe tayi hanyar ɗaki ta barshi a wajen. "Ohh tafiya ma zakiyi ki barni?"
Bata bi takan tanbayar shi ba tayi shigewar ta ɗaki, dan ko kaɗan batason furta wani harafi balle kuma kalma. Kan gado ta haye bayan ta sauya kaya izuwa na bacci, ta kuma kashe bulb ta bar side lamp kawai, lallausan duvet ɗin gadon taja ta kima shi a kanta. Bayan wasu ƴan daƙiƙu da shigowar ta ɗakin Zayyad ya biyo bayan ta, _"toh fah_" ya furta a ransa kafin kuma a zahiri yace "abin babba ne, shi ne zaki kwanta amma baza kice min inzo mu kwanta ba?"
"Khans kuwa tuni bacci yayi gaba da ita, bata ma san yanayi ba."
Ganin tayi shiru ne yasa shi ƙarasowa inda take kwance, fuskar ta ya leƙa yayin da ya sauke idanun sa kan luntsuma-luntsuman nata idanun masu ɗauke da zara-zaran eyelashes mai cika da baƙi, a hankali take sauke numfashi tana jan wani. Miƙewa yayi tare da cire jallabiyar jikin sa ya faɗa toilet, wanka yayi ya fito kana ya shirya cikin singlet da boxer ya haye gadon shima. Kamar a mafarki Khans ke jin ana shafa mata jiki har ta farka, ganin Zayyad manne da ita ne yasa ta haɗe rai tace "ya Zayyad dan Allah ka barni inyi bacci."
"Toh ni me na miki kuma? Kar ki damu, yi baccin ki ƴar flower ta" ya faɗa yana shafa goshin ta zuwa lallausan gashin kanta, a haka ta koma baccin, ganin haka nima na tattara alƙamina ina maiyi musu fatan asuba ta gari.
★★★★★★★★★★★★
*2 MONTHS LATER*
Da ƙyar take takawa har ta iso kan three-seater ɗin da Zayyad ke zaune, a hankali ya taimaka mata ta zauna ya jingino da ita jikin sa, sai sauke numfashi take tamkar wadda tayi gudu, cikin tausayawa Zayyad yace "yaya jikin naki?"
Murmushi tayi tana mai ƙara lafewa jikin sa tace "da sauƙi hubbee, amma ba ya jiki ake cewa ba, ya nauyin jiki ake cewa." Dukkan su dariya sukayi kafin Zayyad yace "toh ya ƙarfin jiki?"
"Yauwa ko kai fa, Alhamdulillah...."
Wayar Zayyad dake ƙara ce ta kashe ta, lovely mom ne ke yawo kan screen ɗin, kamar bazai ɗaga ba, dan baya so tace ya kawo Khans gida wallahi, sai kuma ya ɗaga bakin sa ɗauke da sallama, amma mishi tayi da "wa'alaikumus salam." Saida suka gama gaisawa kafin Mummy tace "Zayyad yaushe ka zama mai kunnen ƙashi ne?"
Kallon Khans yayi suka haɗa ido, ko wannen su fuskar sa ɗauke da mamaki, "Mummy me nayi kuma?"
"Oh me kayi ma kake tanbaya na? Toh ka dawomin da ɗiya ta gida yanzun nan, kaji na gaya maka." Daga haka ta kashe wayar ba tare data jira amsar Zayyad ba.
Samm Zayyad baiji daɗi ba ko kaɗan, haka ya haɗawa Khans kayan ta, da kuma na baby haɗi da wanda zasu kai asibiti lokacin haihuwa, tamm ya cika booth ɗin da kaya suka tafi, bashi ya baro gidan ba sai ƙarfe 10:30 na dare, shima saida Mummy ta kore shi, haka yana ji yana gani ya tafi ya bar Khans sai ɗacin rai yakeyi, ita kuwa Khans me zatayi in ba dariya ba.....
_____________________________________________✍️
Daga alƙalamin