Showing 3001 words to 6000 words out of 36565 words

Chapter 2 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt

27 Nov 2024

2106

manyan fararen oily eyes ɗin shi mai cike da kwarjini, inda fuskar sa ta ƙara yalwatuwa da siririn dogon hanci da madaidaicin baki.


Saida yaja iska ya fesar kafin ya fita, dan yasan halin kayar tashi sarai, tunda ta juya masa ƙeya fa bazata shiga ba.


Haba my love, fushin ya isa haka, ya kikeso nayi? Nayi iya bakin ƙoƙari na na fahimtar dake babu abinda ke tsakani na da Amreesh wlh, yarinyar yayan Mummy (mahaifiyar shi) ne kinji na rantse miki.
Hutu tazo gidan mu, shine tace jiya na ɗan fita da ita taga gari, wannan shine dalili.


Uhm! Naji, sai kuma me? Khansa'u ta faɗa cikin ƙunar zuciya kamar ta fashe da kuka.


Ajiyar zuciya matashin ya sauke yace ''Khansa'u''!
Cike da mamaki ta kalleshi, dan bai taɓa kiran sunan ta haka ba cikin kakkausar murya.


Baki yarda da Zayd ɗinki bane?
Juyawa tayi ta kuma cewa ''uhm''.


Murmushi yayi dan idan da sabo ya saba da shan wahala wajen rarrashin masoyiyar tashi, yanzun ma hakan ne ta kasance saida suka share kusan 40mins suna abu ɗaya, kafin ya samu ya shawo kanta. Ɗaukar ta yayi suka fita, basu tsaya ko ina ba sai munjibir park, dan ya santa da ƙaunar park, sosai taji daɗi kuwa yana ta yi mata hotuna tana dariya wanda ke ƙara bayyana kyawun fuskar tata.


Saida suka biya ta gidan sister ɗinshi dake zoo road kafin suka kamo hanyar gida, akan hanyar su ne aka soma wani faɗa tsakanin wasu samari dake unguwa daban-daban, sosai ake faɗa ana zubda jini ana kisa tamkar rai ba'a hannun kowa yake ba, ganin haka yasa Zayd ƙoƙarin yin reverse saidai kafin yakai gayi sun far musu.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa ita kuma tana kuka tana ƙoƙarin kiran Abban ta.... Ji kake tassssss ƙarar fashewar glass, glass ɗin dake gefen driver aka fasa inda yayi tsalle ya caki goshin Zayd ya shige ciki, ko shurawa baiyi ba, su kuma suka ci gaba da tarwatsa mota tare da tsiyaya mata fetur, saidai ashanar su taƙi kamawa hakan yasa sukayi gama abinsu... Faɗi kawai suke ''sai mun rama, baza'a dakemu da daki banza ba, sai mun ɗau fansa akan al'umma''.


Inda a ɓangaren Khansa'u kuwa girgiza Zayd kawai takeyi tana wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraron ta, sosai take kuka ta ɗauki kusan awa ɗaya tana abu ɗaya kafin ta fito daga motar zuwa lokacin abubuwan sun lafa, dan har al'ummar Annabi sun ɗan soma fitowa.


Kallon motar kawai tayi ta kuma rushewa da kuka ganin yadda ta tarwatse, wayar ta ta fiddo ta kira Abban ta har kira uku bai ɗagaba, nan ta maida akalar wayar kan lambar Mummy itama bata ɗaga ba, hakan yasa ta kira Aliyu ƙanin Zayd ta sanar masa halin da ake ciki tare da faɗa masa inda suke.


Hankali tashe ta tabbatar mata da gashi nan kuma kada subar wajen. Ba ɓata lokaci kuwa ya iso, kallo ɗaya zaka masa ka hango tsantsagwaron tashin hankali a fuskar sa, da ƙyar suka iya buɗe ƙofar mazaunin direban shida wasu matasa biyu.


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu ya furta har sau uku, kafin wani zazzafan hawaye ya biyo kuncin sa, ya ƙurawa Zayd da fuskar sa ke ɗauke da murmushi ido, kamar ka kirasa ya amsa.


Lee (daman haka take kiran shi) mu kaishi asibiti mana.. ta faɗa cike da tashin hankali.


Girgiza kai kawai Aliyu yayi, dan kallo ɗaya yayiwa ɗan uwan nashi ya gano babu sauran numfashi a tare dashi....


Lee dan Allah ka ɗauko shi mu tafi, ta ƙara faɗa a karo na biyu cikin kuka mai ban tausayi.


Shi da ƴan samarin ne suka cicciɓeshi tare zuwa motar Aliyu, kowa na wajen fuskar shi cike da alhini, yayin da ƙwalla ta gangaro kan fuskar Aliyu, tunanin sa ɗaya idan har Zayd ya rasu tayaya zasu fara gayawa Daddy, daddy nada hawan jini faɗa mai irin wannan tashin hankalin akwai matsala, daidai sun ƙaraso hospital ɗin...


Nurses ne suka fito da gadon da za'a ɗaurashi a gurguje, cikin ƙanƙanin lokaci aka shiga dashi Emergency room....


_____________________________________✍️
Babylor ce😘


More comments,,, more typing.....
Sai najiku a jam'iyar comments, dan shi kaɗai zai ƙaramin ƙarfin gwiwar sakin muku sabon update😇
[9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍
*{The famous arabic poetess}*




By
Babylorh






Marubuciyar;
*Rushdah*
*Maraici Na*
and now....
*KHANSA'U*
_(The famous arabic poetess)_






5 & 6.....


________Kiciɓis sukayi da Daddy daidai ƙofar ɗakin shi shima yana shirin fitowa.
Alhaji, dama wajen ka zanzo, meya faru da Zayd ne, yanzu aka kirani anayimin ya haƙuri, dan Allah idan wani abu ya faru ne ka sanar dani dan Allah Alhaji, sosai ta bashi tausayi yadda tayi maganar, daya rasa yadda zaiyi kawai saiya kama hannun ta yaja ta suka bar part din. Khansa'u da fitowar ta kenan taga sun fita itama ta mara musu gaba gaban ta na tsananta faɗuwa.


Daddy bai tsaya ko ina ba sai sashin su Zayd, har ɗakin sa ya kaita sannan ya saki hannun ta ya tsaya daga bakin ƙofar, a hankali Mummy ke takawa harta isa bakin gadon, hannun ta har rawa yakeyi wajen ƙoƙarin buɗe mayafin da aka rufe Zayd dashi. Da sauri tayi baya jikin ta na ƙara tsananta wajen karkarwa, wata ƙara mai sauti aka saki daga bayan su koda suka juya wa zasu gani? Khansa'u ce kwance a ƙasa sumammiya, hawaye ne suka zubowa Mummy kana ta ɗaga hannu sama tana yiwa ɗan nata, tanayi tana kuka har takai inda kukan ya ƙwace mata, daidai su Aliyu da Ma'eesha da sukaji ihu sun shigo a sittin, girgiza ta Aliyu ya somayi amma ko alamar motsi ba tayi, nan ya ɗauke ta suka nufi part ɗin su Mum bayan yayi kiran Zayyad ya tabbatar masa da gashi nan zuwa.


Sai kusan bayan 20mins sannan Zayyad ya shigo, dubata ya somayi tare da bata taimako amma abin yaci tura, ganin abin bana gida bane yasa ya ɗauke ta zuwa mota, Mummy da Daddy sunso su bisu amma Zayyad yace suyi zaman su, da Ma'eesha kawai suka tafi incase Khansa'u ta farka ya zamana akwai wani kusa da ita, cikin daƙiƙu goma suka isa asibitin Zayyad take Sharaɗa phase 1, cikin ƙanƙanin lokaci aka kawo gadon suka shiga da ita emerge, har kusan awanni biyu amma shiru kakeji, wai malam yaci shurwa, sai kusan awa biyu da rabi sannan Zayyad ya fito yana sharce zufa kana yayi wa Aliyu alama daya biyo sa office.


Ba musu yabi bayan shi zuwa office, zama sukayi kafin Zayyad ya yace masa ''ammm Aliyu ina ganin ku tafi gida kawai dan a gaskiya bana saka ran farfaɗowar yanzu, zuciyar ta ta harba da alama taga wani abin daya mugun firgita ta, so a lokacin da mukazo ko numfashi ma batayi, sai yanzu mukayi nasarar daidaita numfashin ta, so yanzu ka ɗauka motana kuje gida, amma karka sanarwa kowa halin da ake ciki plss'', ya ƙarasa tare da miƙa masa key ɗin motar tasa. Amsa Aliyu yayi cike da tausayin Khansa'un, kallon Zayyad yayi da niyyar aika masa tambaya, amma inaa tuni ya faɗa toilet ɗin office din nasa, gudun tambayar.


A ɓangaren su Mummy kuwa kuka kawai takeyi kamar yarinya, zuciyar ta cike da tunani da jimamin rasuwar ɗan nata, babu abinda take tunawa illa yadda Zayd ke kula da ita, ta yadda yake nuna tsantsar biyayyar sa gare su, domin kuwa Zayd namiji ne mai tarbiyya da daraja na gaba dashi, bashi da ɗagawa sannan bashi da nuna yana dashi balle kuma girman kai, ga haƙuri ya kauda kai akan abu, dan kafin kaga fushin sa abune mai matuƙar wuya, da ire-iren tunanin nan har su Aliyu suka shigo. Ganin jikin sa a mace yasa hankalin ta ƙara tashi, dan Aliyu mutum ne dake kasa ɓoye damuwar sa.
Son, lafiya yana ganka haka, Ina Khansa'un da Zayyad? Murmushi Aliyu ya ƙaƙalo sannan yace ''relax Mummy na, mun barsu chan asibitin, so bazasu iya sallamar ta yanzu ba, shiyasa muka taho, amma Bro yace duk yadda ake ciki zai kirani''. Wata ajiyar zuciya Mummy ta sauke kana ta zabga uban tagumi ta cigaba da aikin tunanin ta, duk yadda akayi da ita da taje ta kwanta taƙi, saida Daddy yayi da gaske sannan ta tashi ta shiga ɗaki ita da Ma'eesha bawai dan zasuyi bacci ba, ganin zaman bazai ƙaresu da komai ba yasa Mummy ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta soma gabatar da nafila, yayin da Ma'eesha ke zaune tana karatun Alkur'ani a haka har aka yi kiran assalatu, saida suka gabatar da Sallah sannan suka fito, zuwa lokacin gari harya fara haske daidai lokacin Daddy da Aliyu sun shigo suma.


Nan fa aka fara shirye-shiryen tafiya da gawar Zayd gidan ta gaskiya har kusan ƙarfe 7:30, daidai sistern su (Jumayna/anty Jumayna) ta iso itama cikin kuka da tashin hankali, jikin Mummy ta faɗa ba tare da la'akari da abinda zai samu cikin dake jikin taba, da sauri Mummy ta gyara ta tare da daidaita ta ganin bata ma damu da cikin nata ba. Sosai take kuka Mummy kam tana da rarrashi, dan zuwa lokacin damuwar ta sun ragu cikin 100 kusan 75 sun ragu sakamakon kukan ta da takai wajen mahalicci, ganin Jumaynan bata da niyyar tsayawa yasa ta ɗago ta ta soma magana cikin faɗa tana mai faɗin ''haba Jumayna meye haka ne wai? Kinzo kin tasa ni a gaba sai kuka kike kamar wadda iyayen ta suka rasu, haba sai kace baki san ƙaddara ko jarabawa ba, yadda na rungumi ƙaddarar rashin Zayd da dukkan ku kunsan nayi rashi ba kaɗan ba, kuma haka zaku rungumi taku ƙaddarar, Allah ya bamu ikon cin jarabawar mu kawai, amma a halin yanzu ba kuka Zayd ke buƙata ba, dan ina masa kyakkyawan zato da kuma addu'ar Allah ya dube shi da idon rahma sannan kuma halayen sa na gari su bishi''.


Daga Ma'eesha har Jumaynan saida jikin su yayi sanyi matuƙa, wani mummunan faɗuwa gaban Jumayna yayi tunawa da hawan jinin Daddy da tayi, wanda idan ya tashi Allah kaɗai yasan mai zai faru, nan hawayen ta suka cigaba da ambaliya aranta kuma ta kwararawa Zayd da Daddy addu'a. Mummy ko sai faman faɗa take mata dan a zaton ta mutuwar takeyi wa kuka, daidai lokacin an fito da gawar Zayd za'a kaishi gidan shi na gaskiya, daidai gaban Mummy suka ijiye gawar kana suka ce mata ta masa addu'a.


Jiki a sanyaye Mummy ta matsa kusa dashi ta soma yi masa addu'a harta gama, sannan suka daukeshi suka fita dashi, hawayen da Mummy keta riƙe wa be suka zubo ganin wai yau Zayd ne aka ɗauke shi aka fita dashi a kafaɗa da sunan ya rasu, Allah sarki rayuwa kenan, yau kaine gobe wanin ka, mutuwa mai yanke ƙauna, toh mukam saidai muce Zayd Allah yaji ƙanka, Ameen.
Sosai nayi mamakin dubban jama'an da Zayd ya tara kamar babban mutum, gaba ɗaya tun daga farko har ƙarshen layin nasu baya biyuwa, a haka aka yi mota mota manya-manya sama da guda talatin, banda masu mashina da sauran su, aka ɗunguma zuwa maƙabarta, cikin lokaci ƙalilan aka gama haƙa kabarin sa, da Daddy da Abba (Daddyn Khansa'u) da Aliyu da Mahfouz da kuma Zayyad ɗin aka kama Zayd wajen saka shi a gidan nasa, sun gama saitawa kenan zasu sakashi aciki.....




_____________________________________✍️
Babylorh❤‍🔥💞
07069929131
[9/24, 2:34 PM] Babylor: 💍💍💍💍KHANSA'U💍💍💍💍
*{The famous Arabic Poetess}*




By
Babylorh🌹💞






Marubuciyar;
*Rushdah*
*Maraici na*
loading.........
*KHANSA'U*
_(The famous arabic poetess)_




9 & 10.....


_________Washegari da misalin ƙarfe 8 su Mummy dasu Ummi harda anty Jumayna duk suka ɗunguma zuwa asibitin, inda suka saba zama nan suka nufa, wato corridor ɗin ɗakin da Khans ke ciki, yadda dai suka barta jiya haka suka tadda ta yanzu ma, zama Jumayna da Mummy da Ummi da duk damuwa sun bayyana ƙarara kan fuskar ta sukayi, yayin da Ayeesh da Ma'eesha ke tsaye jikin window ɗin glass ɗin da suke iya hango Khansa'un kwance. Wata iriyar zabura Ayeesh tayi tare da damƙe hannun Ma'eesha tare da murmushi kan fuskar ta da tayi jagab da hawaye, faɗi take ''sis Ma'eesha kinga hannun ta na motsi ko, wallahi ta motsa, bari inje in kira ya Zayyad'', tayi hanyar barin wajen da gudu. Da sauri su Mummy suma suka miƙe dan ganewa idanun su, daidai lokacin ta ƙara motsa hannun ta, nan Ummi ta ɗaga hannayen ta ta soma godiya ga Allah tana mai hawaye. Suna cikin hakane saiga Zayyad da Ayeesh da kuma wasu likitoci guda uku cikin shigar likitanci cikin sassarfa, da sauri suka buɗe ɗakin tare da faɗawa ciki kana suka rufo ƙofar.


Wajen da suke iya hangota Ayeesh ta nufa tana mai share hawayen daya ɓata mata fuska bawai dan sun dena zubowa ba.
Zayyad ganin motsin takeyi da gaske yasa yazo ya sauke curtain ɗin wajen da ake hangowa tare da komawa suka soma gudanar da aikin su cikin ƙwarewa. A hankali ta soma buɗe idanun ta da sukayi nauyi da duhu, tana buɗewa tana lumshe wa harta daidaita tare da sauke su kan yayan nata dake tsaye, a hankali a hankali abubuwan da suka faru suke dawo mata kamar sabo, wani zabura tayi tunawa da cewa ta rasa Zayd ɗin ta, nan su Zayyad suka rirriƙe ta tana cigaba da ƙwace wa kamar sabuwar kamu. ''Ku sake ni, ni ku sakeni, ya Zayyad ka sakeni nace, ina Zayd ɗina yake? Ni nasan bai mutu ba, kuma bazai taɓa tafiya ya barni ba....'' haka dai ta ringa sambatu tana ƙwace kanta ita ƙarfin nan, ganin haka yasa Zayyad sakin ta tare da nufar inda ya ajiye allurar daya shigo da ita, da sauri-sauri yake haɗawa harya gama yazo yayi mata, cikin minti ɗaya jikin ta ya saki gaba ɗaya kamar lagwani ta tafi luuuuu, maidata kan gadon sukayi sannan sukayi abubuwan da zasuyi suka fito bayan sun bar nurses guda a wajen koda ta farka. Koda suka fito saurin barin wajen Zayyad yayi gudun kada suyi ta tambayar sa dan yasan sunji ihun data rinƙayi, suma basuyi yunƙurin dawo dashi ba dan sunsan babu labari mai daɗi, Ummi kam tunda ta fara jin ihun Khansa'u hawaye ke zirya a fuskar ta, dukda tasan manta Zayd a tarihin Khansa'u abu ne mai matuƙar wuya, amma basu taɓa tunanin abun yakai haka ba.


Toh a ɓangaren daddy kuwa abin sai godiya, dan basu Aliyu kaɗai ba, hatta likitocin sunyi matuƙar mamakin yadda Daddy ya farka kamar bashi ne yake cikin wannan yanayin ba, nan kuwa akayi discharging ɗinsu bayan magungunan da aka basa wanda aka chanza masa, saida yaci abinci yasha maganin sa sannan suka nufi gida shida Aliyu suka bar Abba da Mahfouz. Wanka kawai Daddy yayi suka dawo asibitin, sai a lokacin sukejin labarin abinda ya faru, sosai hankalin Abba ya tashi amma yayita ƙoƙarin danne damuwar shi gudun kada a gane, Daddy ma addu'a kawai yakeyi ɗiyar aboki kuma ɗan uwan nashi.
Suna nan zaune har kusan ƙarfe 3 sannan Khansa'u ta farka, ɗaya daga cikin nurses ɗin da aka bari ne suka ta fito tana mai nufar office ɗin Dr. Zayyad, nan ta sanar masa data farka, da sauri ya miƙe ya fita office ɗin nurse ɗin ta mara masa baya, bai tsaya ko ina ba sai ICU room 2 inda Khansa'u take, kwance ya sameta idanuwan ta na kallon sama suna tsiyayar iska wanda a baɗini ba saman take ba. Da gudu ta miƙe ta nufeshi tare da faɗawa jikin sa ta saki wani marayan kuka kamar zata sheƙe, da kallon tausayi kawai nurses ɗin suka bita suna masu tausayi ga halin data shiga. Da ƙyar Zayyad ya iya raba ta da jikin sa kana ya zaunar da ita kan gadon shima ya zauna, hawayen ta ya fara sharewa kafin ya sakar mata murmushi tare da tanbayar ta ya jikin nata, ko akwai inda ke mata ciwo?
Kanta kawai ta girgiza masa tana cigaba da hawaye kamar famfo. Ɗagowa tayi ta kalle sa tana faɗin ''yaya ina Zayd ɗin?''. Sunkuyar da kansa yayi ƙasa yana mai girgiza kan kafin kuma yace ''Khans ɗina kiyi haƙuri, Zayd ya amsa kiran da bazai taɓa dawowa ba''.


Wani kukan ta kuma saki daidai lokacin dasu Mummy suke shigowa, da sauri Mummy ta ƙarasa inda take zaune shi kuma Zayyad ya miƙe tare da ficewa. Kuka sosai Khansa'u takeyi tana kwance jikin Mummy, rarrashin duniyar nan anyi amma Khansa'u taƙi shiru har sun gaji, kuka kawai take tana faɗin ''Mai yasa Zayd zai tafi ya barni Mummy, Maiyasa sai a lokacin da rayuwa ta zata shiga gagari a dalilin rashin sa zai tafi ya barni, mai yasa zai barni in this horrible life Mummy, na tabbata nima bazanyi lasting ba, dan banga amfanin zamana da duniyar nan..... Da saurin Mummy ta toshe mata baki tana mai girgiza mata kai, Ummi dake zaune kan kujera kuwa kasa cewa komai tayi banda hawayen dake ambaliya kan fuskar ta, Mummy ne kawai tayi ƙarfin halin faɗin ''ki dena faɗar haka Khans, a duniya ko wani bawa yana da tasa ƙaddarar, toh ke irin taki ƙaddarar kenan ko ince irin tamu ƙaddarar kenan, mai yasa baza kiyi imani da ƙaddara ki kuma roƙi Allah ya baki ikon cinye jarabawar ki ba? Allah ne ya baki yanzu kuma ya amsa abinsa, duk son da kike masa yakai kwatankwacin wanda Allah ke masa ne? Dan kawai ya karba abinsa shine zakiyi masa butulci Khansa'u? Har kina iƙirarin kema kin kusa mutuwa, kashe kanki zakayi ko me? Kada in ƙarajin makamanciyar irin wannan maganar a bakin ki, ki zama mai godiya ga Allah aduk halin da kika samu kanki Khans, kinji''.


Ba Khansa'u kaɗai ba duk wanda ke wajen saida jikin sa yayi sanyi, babu abinda kakeji sai shessheƙar kukan Khansa'u, can kuma sai idanuwan ta suka ƙafe duk jikin ta ya rirriƙe, dukkan su sunji tsoron ganin ta haka, Jumayna data tashi domin kiran likita ne sukayi kiciɓis da Zayyad a bakin ƙofa, da sauri shima ya ƙaraso dan duba maike faruwa. Nan yaba su Mummy umarnin su fita, basuyi gardama ba suka miƙe suka fita,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login