Showing 18001 words to 21000 words out of 36565 words

Chapter 7 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt

27 Nov 2024

2112

inba dariya ba, har cikin ta ya kusa ƙullewa, da haka sukayi mata sallama suka kama gaban su.
Suna tafiya kam ta tashi ta cire rigar tasa doguwar rigar bacci mai kauri da kwanta....










________________________________________✍️
Daga alƙalamin
💍BABYLORH💍
(shalelen women writers)
[10/9, 7:48 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_




_*WOMEN WRITERS ASSO...*_






By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




The writer of


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_






25 & 26...




_______Ba jimawa da tafiyar su anty Jumayna Zayyad da abokan sa suka shigo gidan, sun ɗauki ƴan mintina kafin suka bar ango tare dayi masa saida safe. Zayyad ya daɗe ƙofar ɗakin Khans yana tunanin shiga, fargabar sa ɗaya abinda zai shiga ya tarar, ya sani sarai bakin daya furta tsana toh tabbas zai aikata koma meye. Ya kai kimanin mintina 10 sannan ya shiga bakin sa ɗauke da sallama ciki-ciki, dan ba kowa ne zaiji ba. Kwance ya same ta akan gado tana sharar bacci, a hankali ya taka ya isa gare ta tare da tsura mata idanu, a hankali take fidda numfashi haɗi da ajiyar zuciya akai-akai. Ya daɗe tsaye kafin ya zauna bakin gadon ya ɗora ledar hannun sa kan side drawer, hannun ta ɗaya ya kama ya kira sunan ta a hankali.
Kamar a mafarki taji ana kiran ta da kuma muryar wanda bata ko mararin jin muryar sa balle ganin sa, a hankali ta buɗe idanun ta daga baccin daya ɗan sace ta, lokaci guda ta wani murtuke fuska tamkar wadda batasan meye dariya ba, da sauri ta fuzge hannun ta daga nasa tana mai matsawa kana ta tashi zaune, murmushi yayi dan yasan dole za'a rina, a hankali ya ɗago ya kalle kana yace "abinci na kawo miki, kada ki kwanta da yunwa."


"Bana buƙata," ta furta tana mai kau da kanta gefe.


Ƙara gyara zaman gilashin idanun sa yayi kafin ya ƙara cewa "kiyi haƙuri Khans, banaso in zama marar adalci a gareki, cin ki da shan ki yana wuya na yanzu, idan har bakici ba hakan na nufin rashin kulawa ta a gareki kenan, ki daure kici dan Allah badan ni ba."


"Ha'a! nace maka bana buƙata ko? Banjin yunwa ne idan da inaji ai zanci," ta ƙarasa tare da juya masa baya taja bargon ta.


Badan yaso ba Zayyad ya miƙe cikin sanyin gwiwa ta kama hanyar fita, har ya kama handle ɗin ƙofar, sai kuma ya jiyo ya kalle ta na ɗan wasu daƙiƙu, kafin yasa kai ya fice. Bai tsaya ko ina ba sai ɗakin sa, zuciyar sa cunkushe ya rasa me zaiyi yaji daɗi, wanka ya shiga yayi ya dawo ya sanya singlet da three-quarter, saida yayi Sallah kamar yadda ya saba a ko wani dare kafin ya kwanta, sosai ya daɗe kan sallaya yana kwarara musu addu'a kafin ya koma kan bed ɗinsa ya kwanta, ya daɗe kafin bacci ɓarawo ya ɗauke sa.




Kiran sallahr asuba ne ya tashe sa daga baccin daya dauke sa, cikin sanyin jiki ya miƙe ya nufi bathroom, wanka yayi haɗi da alwala sannan ya fito ya sanya dark-ash jallabiyya ya fito, jin ana ƙoƙarin tada iqama yasa bai tsaya tashin Khans ba saiya dawo. Ana idar da sallah ya dawo, dan baiso lokacin sallah ya wuce matar tasa, koda ya shigo direct ɗakin ta ya nufa, saidai bata kan gado, motsin daya jiyo a bayi ne ya tabbatar masa da tashin ta, ya juya zai fita kenan ya hangi ledar daya shigo da ita jiya, ajiyar zuciya ya sauke yana mai mamakin abinda ya hana ta ci, ko tana tunanin ya sanya wani abu ne? Toh amma me zaisa ya sanya mata abu aciki bayan ita ɗin matar sa ce ta Sunnah....
Fitowar ta ce ta katse masa tunanin sa, dressing mirror ta nufa direct ba tare data lura da mutum a ɗakin ba, sosai ya ƙurawa jikin ta kallo yana mai jin wani tsananin ƙaunar ta na shigar sa. A hankali take tsane ruwan jikin ta kafin ta ɗauki mai ta soma shafawa harta gama, perfumes ɗin da anty Jumayna ta bata ta ɗauka ta soma feshe ilahirin jikin ta dashi, duk abin da takeyi a idanun Zayyad, bai koyi ƙwaƙƙwaran motsin da zata san yana ɗakin ba. Juyowar da tayi ne ta lura dashi, wani uban ihu ta fasa tana kare jikin ta, ihu kawai take zabgawa tamkar wadda taga dodo, da sauri Zayyad ya ƙarasa inda take ya zagaye ta da hannayen sa yana furta "maintain dear! Ni me."
Sai a lokacin ta bar ihun tana ɗagowa tare da ƙare masa kallo kafin kuma ta haɗe rai, harga Allah ba ƙaramin tsoro taji ba, dan batayi tsammanin ganin mutum ba ko kaɗan, a hankali ta janye jikin ta daga hannun sa ta nufi wardrobe tana furta "meya kawo ka ɗaki na, inace kowa da nasa ɗakin?"
"Well, nazo tashin ki kiyi sallah ne."
"Toh nayi, shikenan?"


"Amm...aaa abincin dana kawo maki jiya naga bakici ba, meyasa."


Yana ambaton abinci taji cikin ta yayi wani irin ruri, dan rabon ta da abinci tun jiya da rana, sedai batason yasan tanajin yunwa hakan yasa ta dake tare da faɗin "dan ka siyomin abinci banci ba shine kake tuhuma ta?" Ba tare data jira cewar sa ba ta nufi inda ledar take ta ɗauka, ƙamshin kazar daya bugi hancin tama saida ya ƙara mata yunwar, amma sabida taurin kai irin na Khans ta gwammaci ta zauna da yunwa. Har gaban sa ta iso da ledar a hannun ta, ta kamo hannun sa ta zura masa ledar tace "ga shinan," tana gama faɗi ta tafi ta barsa tsaye tamkar wanda aka dasa, ta shige dressing room. Zayyad, tunda ta riƙe hannun sa yaji jikin sa ya ɗauki wani baƙon yanayi dako zai mutu Khansa'u baza ta taɓa bashi kanta ba, tunda ya rungume ta a jikin sa yayin da take ihun nan ya somajin sha'awar ta na taso masa, yayi ta ƙoƙarin dannewa amma yana neman kasa wa, baya son ya ƙuntata mata daidai da ƙwayar zarra, hakan yasa bazai iya ƙwatar haƙƙin sa ta halin ƙarfi ba, dan yasan ma wahala kawai zai sha, amma with time insha Allah zata bashi da kanta, saidai baisan ko kafin lokacin ya illatu ba. Daga haka ya fice daga ɗakin, ficewar sa kuwa yayi daidai da fitowar Khans daga dressing room, wata harara ta zabga masa tana raka bayan sa da tsaki. Shi ko gogan ɗakin sa ya nufa ya faɗa kan gado yana jizar leɓe tare da runtse idanu, lokaci guda kuma ya soma zufa numfashin sa na fita da ƙarfi, ya daɗe a haka kafin yanayin nasa ya soma raguwa, har yazo ya tafi, sai abinda da ba'a rasa ba, a hankali ya miƙe ya shiga toilet ya sakar wa kansa ruwa mai zafi sosai, ya daɗe kafin ya fito, cikin wata dakakkiyar shadda ƙirar getzner sky blue color ya shirya, da baƙin takalmi sau ciki haɗi da hula zanna bukar, sosai yayi wa kayan kyau kamar dashi akayi, sai zuba ƙamshi yakeyi tamkar angon gaske, wayoyin sa ya kwasa tare da car key ya fito, ɗakin ta ya nufa tare da kama handle ɗin ya murɗa, amma yaji ƙofar a kulle, mamaki ne ya kama sa na dalilin rufe ƙofar nata, a hankali ya soma knocking, amma taƙi buɗewa, ga shessheƙar kukan ta da yake jiyowa, sosai yake tausayin ta, baiyi ƙasa a gwiwa ba ya cigaba da knocking yana kiran sunan ta amma taƙi buɗewa, ga kukan ta da har yanzu bai dena fita ba. Dabarar data faɗo masa ne yasa shi fita waje, saida ya zuba wayoyin sa a mota sannan ya zagaya ta bayan gidan, cikin sa'a kam ya tadda window ɗin ta a buɗe, da ƙyar ya iya rarrashin ta ta buɗe masa ƙofar ya zagayo, tanbayar ta ya somayi me aka mata amma babu amsa, tanbayar duniyar nan yayi mata amma taƙi basa amsa, ya rasa ya zaiyi da ita, ita bata bar kukan ba sannan bata amsa ɗaya cikin tambayoyin da yake mata ba. Ganin lokaci na tafiya yasa shi gyara zaman sa yana fuskantar ta, "Bie~bie dan Allah ki daina kukan nan banaso, ki sanar dani abin da yake damun ki zan taimaka miki insha Allah, dan Allah badan ni ba."


Share hawayen ta tayi ta gyara zama itama kana tace "dama ficewar ka kayi, da yafi, faɗa maka damuwa ta bashi da wani anfani dan ba magance min shi zakayi ba."


Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "me zakici in kawo miki?"


"Banason komai, ka barni da yunwa ta inma kashe ni zatayi ta kashe ni, tunda baka da asara."


Bayajin daɗin kalaman dake fitowa daga bakin ta, yadda take masa magana tamkar ƙanin ta ko sa'an ta na mugun ci masa rai, amma bazai taɓa karya alƙawarin daya ɗauka ba koda hakan zaiyi sanadiyyar shafewar tarihin sa a doron ƙasa. Ba tare da yace da ita ƙala ba ya miƙe ya fita, sai bayan kusan 45mins sannan ya dawo hannun sa ɗauke da leda guda biyu, ajiye mata su yayi akan ɗan ƙaramin table ɗin dake ɗakin ya fita, kasancewar jiran shi akeyi zasu sallami baƙin da suka hallara wajen auren nashi...




Tana daga bayi ta jiyo shigowar Zayyad wanda bai daɗe ba ya fice, sai kuma taji yayiwa motar sa key ya fita. Koda ta fito gaba ɗaya ɗakin ta gauraye da wani daddaɗan ƙamshi na abinci, nan take cikin ta yayi wani irin ruri, babu shiri ta nufi inda ledar take ta buɗe. Takeaway biyu ne a jiki, gaba ɗaya ta fito dasu tare da buɗewa, fried rice ne a takeaway ɗaya, sai ɗayan kuma papper chicken, ɗaya ledar kuwa yoghurt ne guda biyu sai ice cream roba biyu shima. Abincin ta soma kaiwa hari, kona bakin ta bata cinyewa take ƙara danna wani, sai da ta cinye shi tasss tayi nak abin ta ta ƙara korawa da milk sannan ta miƙe. Dressing room ta shiga ta soma duba kayan da zata saka, karap idanun ta suka sauka kan wata navy blue ɗin atampa Holland mai matuƙar kyau ɗinkin riga da skirt, sosai kayan sukayi mata matuƙar kyau musamman yanda aka ƙawata ɗinkin da stones masu matuƙar ƙyalli, bata wani tsaya kwalliya ba ta kashe ɗaurin ta ta shafa lip gloss ta fito. Saida ta gyara ɗakin tsaff sannan ta kwasa kayan data gama cin abinci ta fito dasu, dustbin dakai takeaway ɗin, sauran yoghurt da ice cream ɗin kuma ta sanya su a freezer ta dawo parlor. Zama tayi bisa kyawawan kujerun da suka ƙawata parlon nata bayan ta kunna TV, nan ta hau kallon ta hankali kwance.....










__________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
_(shalelen women writers)_


07069929131
[10/11, 1:05 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_




_*WOMEN WRITERS ASSO.....*_




By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




The writer of


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_






27 & 28....




_________Zayyad bai dawo gidan ba sai kusan ƙarfe 12:30 na rana, kasancewar abubuwa da suka sha kansa game da hidimomin bikin da kuma abokan sa. Saida ya biya ya amso musu takeaway sannan ya shigo gida, kwance ya sameta kan kujera tana bacci, kamar zai tashe ta sai kuma ya soma tunanin abin da zai biyo baya, ganin lokacin sallah yayi yasa ya soma bubbuga hannun kujerar da kanta ke kwance haɗi da kiran sunan ta, firgigit tayi ta farka, karap idanun ta suka sauka kan na Zayyad da yayi mata rumfa, ko wannen su samun kanshi yayi da kasa ɗauke idon sa akan ɗan uwan sa, har kusan minti ɗaya kafin Zayyad ya dawo hayyacin sa, nan ya soma kame-kame yana sosa ƙeya, Khans kam tsintar kanta tayi da jin haushin kanta data tsaya tana kallon sa, ji tayi kamar ta rufe Zayyad ɗin da duka dan haushi amma ba dama. Ba tare da tace dashi ƙala ba tayi wucewar ta ɗaki, sororo Zayyad ya tsaya ya bita da ido, yana mamakin wannan mugun halin da Khans ta samo, duk ta inda yabi wajen shawo kanta saita zille. Kitchen ya nufa da kayan hannun sa ya ajiye sannan ya fito, shima nasa ɗakin ya shiga, yayi wanka ya shirya cikin navy blue T-shirt wadda aka rubuta sunan sa a baya da manƴan baƙaƙe kamar haka (DR. ZAYYAD), farin three-quarter ya sanya kana ya nufi masjid, dan zuwa lokacin har an soma kiraye-kirayen Sallahr azahar.


A ɓangaren Khansa'u itama tana shiga ɗaki toilet ta nufa, wanka tayi haɗi da alwala sannan ta fito ta shirya cikin white Dubai Abaya mai matuƙar kyau da sheƙi, sallah tayi itama kana ta koma gaban mirror, gashin kanta ta soma gyarawa harta gama ta naɗa mayafin abayar. Wayar ta ta soma nema tayi game amma bata ganta ba, sai a lokacin ta tuna da ta baro ta a parlor, nan ta fito ta ɗauka juyawar ta yayi daidai da shigowar sa ɗauke da sallama, ciki-ciki ta amsa tayi ciki abinta ta faɗa gado ta soma buga game.
Murmushi kawai Zayyad yayi ya shiga kitchen, gaba ɗaya takeaway ɗin ya juye masu a plate ɗaya ya haɗo masu da yoghurt da ruwa ya nufi ɗakin nata, (hmm nikam nace su ya Zayyad ko yaushe ka samu fuskar cin abinci tare da ita oho). Koda ya shiga game ɗin ta take hankali kwance dan bata ma ji shigowar sa ba, sosai kuwa abin ya taɓa zuciyar Zayyad amma ya basar, dan a tunanin sa taji sallamar sa amma taƙi amsawa. Kan centre carpet a ajiye tray ɗin a abincin kafin yayi mata magana, a wannan karon batayi gigin maimaita abinda tayi na ƙin cin abinci ba, amma fa taƙi yarda suci, juyin duniyar nan tace baza taci abinci dashi ba, kuma baza taci ragowar sa ba, sedai in ya yarda ita taci ta rage masa. Zayyad dai baice komai ba ya tura mata tray ɗin gaban ta yaja gefe, dan yanzu al'amarin ta ya dena bashi mamaki, ba kunya ba tsoron Allah kam taja abinci ta soma ci, saida taci mai isarta sannan ta sha ruwa ta miƙa masa. Da yake shi ɗin ba baƙon zafi bane yasa hannu ya amsa ya soma ci, saida ya cinye tasss tana kallon sa tana wani yatsine fuska harya gama shima ya kora da ragowar nata ruwan. Haushi sosai ya bata amma bata nuna ba, da kansa ya kwashe abubuwan da suka ci abincin ya fita dasu.


Toh haka zaman su ya cigaba da wakana na yau daban na gobe daban, amma abin godiyar shine Khans bata taɓa yunƙurin cutar da Zayyad ba, shima kuma yaji daɗin haka, hakan yasa ya ƙara zage damtse wajen shanye dukkan wani rashin mutunci da wulaƙanci nata. A haka har suka ɗauki kusan sati biyu, babu wanda yazo mata daga ita, sannan Abba ya hanata zuwa yace saiya nemeta. Harta ga ƙawar ta Nasreen kuwa, kiran duniya ta mata amma taƙi zuwa, sau tari takan zauna taci kukan iya kuka har ta godewa Allah, Zayyad kam Allah ya isa babu irin wanda bai sha ba, dan a cewar ta shine silar faruwar komai.
Toh! Yau ma zaune take riƙe da wayar ta a hannu tana kiran Nasreen a karo na sau ba adadi, saida ta kusa katsewa sannan Nasreen ta ɗauka da muryar bacci, nan fa Khans ta fashe da kuka tana faɗin "haba Nasreen, yanzu kema kin biyewa tsarin su Abba, sau nawa kike ganin kirana a wayar ki amma baki biyo baya? Baku san halin da nake ciki ba amma babu wanda yayi gigin zuwa duba ni, yanzu in ma mutuwa nayi saina ruɓe sannan zaku sani?"
Da ƙyar Nasreen ta iya danne dariyar dake cin ta tace _"oh oh! Sorry Mrs Zayyad, yau nake shirin zuwa gidan ki wlh."_


"Nasreen dan Allah da gaske? Bana son wasa pls"


"Tsaki Nasreen ɗin tayi kana tace _"ni sa'ar wasan kice?"_


Murmushi kawai Khans tayi tace "dan Allah kada ki shanya ni, ina jiran ki sai kinzo."


Daga haka suka katse wayar, nan Khansa'u ta tashi ta shiga kitchen, jollof ɗin taliya da busasshen kifi ta ɗaurawa Nasreen ɗin, dan shine best food ɗin ta, tana gamawa ta haɗa zoɓo shima, ta sanya a fridge ta nufi ɗaki, wanka tayi ta shirya tsaff, cikin pink ɗin shadda ɗinkin doguwar riga ta kashe ɗauri. Ba jimawa kuwa taji ana doorbell na ringing, da sauri ta tafi dan tarbar ƙawar tata, tana buɗewa kam suka rungumi juna suna dariya, har saida Nasreen ta gaji tace "sake ni da Allah, kada ki ɓalla masa ni."


Dukan su suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login