Showing 15001 words to 18000 words out of 36565 words

Chapter 6 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt

27 Nov 2024

2107

other ways. Amma maganan kisa ki cire shi pls, kinsan makomar duk wanda ya kashe rai ba tare da sharuɗɗa uku da musulunci ya yarda dasu ba toh wuta ce makomar sa. Try and ask Ummi, I knw she might tell u okay?"


Kai kawai Khansa'u ta gyaɗa tana ayyana irin azabar data tanadarwa Zayyad, muddin bai samu Abba ya ya sanar dashi ya fasa ba....






_______________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/3, 7:55 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_








By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




The writer of


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_










21 & 22...




_________Yammaci ne mai ɗauke da sassanyar iska tana kaɗawa sosai, yayin da hadari ya tattara komai nasa ya tsaya a tsakiya yayi baƙi, wanda ke nuni da ako wani lokaci ruwa kan iya sauka. Zaune take tsakiyar ƙaton royal bed ɗin ta, gefen ta plate ne mai ɗauke da chips da ƙwai sai zoɓo dake hannun ta, gaba ɗaya ta tattara hankalin ta kan film ɗin da ake nunawa a MBC 2 wato (Alice in wonderland), wayar ta data soma ruri ce tasa hankalin barin kallon, sosai gaban ta ya mugun faɗi ganin mai kiran nata, saida ta kusa katsewa sannan ta ɗauka tare da karawa a kunnen ta.
_kada ki gasgata min labarin da nakeji baby, dan Allah ki faɗamin ba gaskiya bane ba_.
Shine abinda aka faɗi daga ɗaya ɓangaren, da ƙyar ta danne kukan dakeson taho mata tace "dear bamu gaisa bafa."


Bata kai ga rufe baki ba ya ƙara da cewa " _wani irin gaisuwa kikeson muyi, bayan kinsan yadda na daɗe ina nuna miki ƙauna, ke shaida ce nakan sadaukar da farin ciki na duk dan ke ki samu naki farin cikin, na nuna miki so iya so, abu ɗaya ya hana ban furta miki ba, gudun kar a samu matsala, gudun kada furta miki ya zamo silar rushewar alaƙar mu, ashe duk abin da nakeyi baki taɓa gani ba kuma baki taɓa lura ba? Yanzu ya tabbata aure zakiyi da gaske kenan?"_


Hawayen da tayi ta ƙoƙarin riƙewa ne ya gangaro kana tasa hannu ta share tace "ka yarda dani Zaid, wlh ban taɓa tunanin cutar dakai ko yaudarar kaba, amma kasan ba laifi na bane, meyasa baka furta min kalmar so ba har saida bakin alƙalami ya bushe? ka sani a bari ya huce shike kawo rabon wani, meyasa ka riƙe abin a ranka har saida Abba ya yanke wannan hukuncin, meyasa ka zaɓi wahalar da zuciyar ka akai na, wallahi ban taɓa gasgata abinda Nasreen ke faɗa min game da alaƙar mu ba sai da aka haɗa aure na da ya Zayyad...." Kukan da yaci ƙarfin tane ya hana ta cigaba da magana.


A ɓangaren Zaid kuwa shima hawayen yake fitarwa, chan cikin zuciyar sa na masa suka yana jin raɗaɗin zafin rabuwar da zaiyi da Khans, haƙuri ya soma bata har kukan ya sassauta sannan ya ƙara da faɗin _"na fahimce ki dear, sannan irin tamu ƙaddarar kenan, Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi yayi mana jagora_".


Yadda kawai yayi maganar tasan zuciyar sa nayi masa zafi da ɗaci kan maganar, cikin kuka take masa magana kamar haka "kayi haƙuri Zaid, kada ka ɗauka hakan a matsayin yaudara wallahi ko kaɗan bani da niyyar yaudarar wani a rayuwa balle kuma kai, zan aura ya Zayyad ne kawai sabida biyayya badan ina sonshi ba, zan aura ya Zayyad ko dan nasa farin ciki a cikin zuƙatan iyaye na, duk da nasa akwai *ɓoyayyen sirrin* da suke ɓoye wa, nasan babu yadda za'ayi in aura ɗan uwa na, sannan zan aure shi da zuciya ɗaya, saidai bansan ko ƙiyayyar da nake masa zata hanani cutar dashi ba, wlh yadda nakejin tsanar shi a raina bazan iya misalta shi da komai ba. Zaid idan harni rabon kace ina mai tabbatar maka dako sama da ƙasa zata haɗe saina zama mallakin ka, idan kuma harni ba rabon ka bace ina mai maka fatan alkhairi da samun mace ta gari mai ilimi da addini da tarbiyya." tana gama faɗi ta katse wayar tare da kifewa tana wani matsanancin kuka mai taɓa zuciya da ban tausayi. Haƙiƙa duk wanda yasan Khansa'u a baya ya ganta a yanzu saiya tausaya mata, dukkan rayuwar ta ta sauya tun bayan rasuwar Zayd ɗinta, bacin ramar da tayi ga uban tunani data sanyawa ran ta tamkar a kanta aka fara irin wannan auren.


Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi, gefe guda shaƙuwa mai tsanani ta ƙara shiga tsakanin familyn biyu, saidai har yanzu babu wani sauyi a wajen Zayyad da Khans, sosai take iya bakin ƙoƙarin ta ta cusa soyayyar Zayyad cikin zuciyar ta amma abin yaci tura, musamman idan ta tuna da shi ɗin aboki ne kuma ɗan uwa ga Zayd ɗin ta. Kullum takan roƙi Allah ya cire mata duk wani aniya mara kyau data ƙudura kan Zayyad bayan auren su, takan roƙi Allah ya bata ikon zama ƙarƙashin sa tare da biyayya kodan samun lada wajen mahaliccin ta da kuma wanzuwar farin cikin iyayen ta. A haka kwanaki suka yita shuɗewa suna zama tarihi, yayin da kwanaki auren su Zayyad keta matsowa. Ana saura sati uku Mummy tazo da kanta ta ɗauka Khans zuwa gidan ta, nan Khansa'u ta fara shan gyara kala-kala wanda ta sani dama wanda ya zama baƙo a gareta, gefe guda ma Anty Jumayna na aiko mata dasu sosai, wani lokaci ma da kanta take zuwa ita da babyn ta *Ayaan*. Sosai ta sauya cikin sati biyu kacal ta koma wata kyakkyawar balarabiya, dama gata ba daga baya ba wajen kyau ga hanci tamkar alƙalami, ga cika data ƙarayi kai abin sai san barka.
A ɓangaren ango Zayyad ma ba'a barsa a baya wajen shirye-shirye ba, Abba ba sosai suka zage damtse wajen ginawa yaran nasu tangamemen gida, dan sun lura Zayyad bayi zaiyi ba, dan yadda yake abubuwa tamkar mace mara jini a jika.
Washegari ya kama laraba, tun safe Nasreen ke gidan su Ameesha wajen Khansa'u, kasancewar sunyi hutun ƙarshen semester abin yayi daidai da bikin, sosai Nasreen ke mata tsiya ita kuma ta cika tayi fammm in ranta yayi dubu kuma ya ɓaci, amma hakan baisa ta daina mata tsiya ba, babu yadda Khansa'u ta iya hakan yasa ta daina damuwa ma, dan idan da sabo ta saba da halin Nasreen. Sosai suma suke shirye-shirye duk da rabi da kwatan komai Nasreen keyi saidai Khans ta bita da ido, tun Nasreen na basarwa harta gagara saida ta yiwa Khans magana ta hanyar faɗin "wai ke me kike nufi ne? Kin barni ni kaɗai ina ta shiri sai kace bikina.."


Dogon tsaki Khans taja kana tace "idan kin gaji ki ajiye mana, aiba dole bane ko!"


Dariya Nasreen ta kwashe dashi wanda ya ƙular da Khans kafin tace "haba uwargida a gidan yayan mu Zayyad, me kuma yayi zafi? Maida wuƙar, ai bance miki na gaji ba, ko ni irin kice."


Throw pillow ɗin dake hannun Khans ta jefa mata yayin da Nasreen ta kauce tana sakin dariya. Khansa'u kam ranta yakai ƙololuwa wajen ɓaci, ji take kamar ta tashi ta rufe Nasreen ɗin da duka, hannu tasa ta share hawayen baƙin cikin da Nasreen ke ƙunsa mata. Nasreen kam bayan ta gama dariya ta gyara zama tana faɗin "duk wannan abin da kikeyi na ɗan lokaci ne, da kanki zaki zo ki cemin duk duniya babu wanda kikeso sama da Zayyad, kaiii amma zanso inga wannan ranar, ni kam saina tuna miki da abubuwan da kike faɗi kafin auren ku."


Nan fa Khans ta taso ta nufo Nasreen, ita kuwa ganin haka yasa ta miƙe tayi hanyar barin parlon, kiciɓis sukayi da Mummy na ƙoƙarin shigowa, nan kuwa Nasreen tayi bayan ta ta ɓoye tana ta ƙyaƙyata dariyar ta.


Ah ah! Ku tsayamin, meke faruwa ne, meye haka kukeyi kamar ƙananan yara?


"Mummy tun ɗazu yarinyar nan ke tsokana ta, na ƙyale ta na ƙyale ta amma taƙi bari," Khansa'u ta faɗa tana sakin kuka haɗi dana shagwaɓa.


Kai kai kaii! Kinga fa Nasreen ki dena taɓamin shalele na, inba haka ba kuwa zamu sa ƙafar wando ɗaya.


Nasreen dake bayan Mummy ne tace "Mummy nifa ba wani abu nayi ba, kawai daga nace uwargida a gidan Zayyad, shikenan ta fara dukana da pillow wai akan me zance mata uwargida, wacece amaryar?"


Waro idanu Khansa'u tayi kana tace "kiji tsoron Allah Nasreen, wlh Mummy ni ba haka nace mata ba."


"Na san baki faɗa ba, taho muje kisha maganin ki," Mummy ta faɗa tanajan hannun Khans zuwa kitchen yayin da Nasreen tabi Khansa'u da gwalo.










__________________________________________
Kuyi haƙuri kun jini shiru kwana biyu, hakan yana da nasaba da abubuwa da suka dan yimin yawa.


________________________________________✍️
BABYLORH💓💖
(shalelen women writers)
07069929131
[10/8, 10:20 AM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_






_*WOMEN WRITERS ASSO...*_📚




By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




The writer of:


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading......
3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_










23 & 24...






________Shirye-shirye daga ɓangaren biyu ba kama hannun yaro, ɓangaren Abba da Ummi sosai suka miƙe tsaye akan Zayyad wajen ganin yayi dukkan abinda ya kamata, kuma Alhamdulillah, abin sai san barka. Haka zalika ɓangaren Mummy, sosai takejin daɗin sauƙin kai da kara irin na Mummy, duk da dama chan basu nuna bambanci tsakanin su balle kuma yaran su, Khans ta samu dukkan abin da take buƙata wajen Mummy abin sai godiya.

*5 DAYS LATER*


Duk da an kammala shirye-shirye sai dai abinda ba'a rasa ba, hakan baisa sun daina hidimomi ba, yayin da a ɓangaren Khansa'u ganin abin take tamkar a mafarki, tayi kukan har saida hawaye ya koma yana fita da ƙyar a idanun ta, ba komai take tunani ba illa zaman da zasuyi da yayan ta Zayyad, gashi duk wanda ta tanbaya tsakanin su Mummy sai suƙi faɗa mata matsayin Zayyad a gidan, haka ta cigaba da tunane-tunanen ta, tabi tachan ta ɓille ta chan.
Toh Zayyad ɗin ma kusan hakan take a wajen, ko ince kishiyar hakan, fargabar sa guda, shine yadda Khansa'u zata kalle sa a matsayin miji, domin ko ƙwayar idanun ta ya kalla babu abinda yake gani sai tsantsar ƙiyayyar sa a gare ta, ƙarara take nuni rashin so a garesa wanda bai taɓa tunanin hakan daga gareta ba. A da ko wuni Khans tayi bata ganshi ba saita tanbaya saidai In yana hospital, wani lokaci har driver take sawa ya kaita wajen yayan nata, irin kulawar da Zayyad yake bata matsayin ƙanwa, da irin wanda take bashi a matsayin ɗan uwan ta, bai taɓa tunanin dan an haɗasu aure zasu rushe ba, harga Allah bazai ce baya son Khans ba, domin ta haɗa duk abinda namiji ke fatan samu wajen mace, toh amma akace son maso wani wahala ne, baya taɓa tunanin ko nan kusa Khansa'u zata ƙauna ceshi, amma ya ɗauki alwashin dukkan abinda zatayi masa zai ɗauka insha Allah, da waɗannan tunane-tunanen dai kawai yake yawo yayin da in ya tuna da Allah kuma sai yayi godiya ya nema musu zaman lafiya da fatan albarka wa auren su...




*RANA BATA ƘARYA* _(sedai uwar ɗiya taji kunya)_.
A yau Juma'a da misalin ƙarfe 1:30 na rana, (wato bayan sallahr juma'a) dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren *ZAYYAD MUHAMMAD* da ƴar uwar sa *KHANSA'U MUHAMMAD SHEHU* kan sadaki naira dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba. Nan fa aka soma yiwa Zayyad fatan alkhairi, gefe guda kuwa Zaid ne tsaye shima ya halarci ɗaurin auren, inda yakejin zuciyar sa tamkar ta tarwatse (nikam nace Allah ya baka haƙurin rashi Zaid).



★★★
"Haba Khans, meyasa kike haka ne wai, ya kikeso muyi? Kinsan dai idan Mummy tazo ta ganki haka baza taji daɗi ba, dan Allah ki tashi kiyi wanka ki shirya, mu kaɗai ake jira, koma menene sai muyi magana daga baya, amma yanzu ba lokacin magana bane, ɗazu ma dana fita Mummy ta tanbaye ni ke nace mata kina wanka, yanzu so kike ta shigo taga akasin haka? Dan Allah ki tashi." Nasreen dake zaune ta faɗa cikin ƙaguwa.


Kallon ta kawai Khans tayi kana tayi murmushi wanda yafi kuka ƙuna tace "consider yourself as me Nasreen, na tabbata kema hakan zakiyi ko fiye da hakan."


"I can feel your pain dear, bt this is not the right time to talk about this, ki fahimceni jiran mu akeyi, wallahi nasan bakyajin daɗi, kuma Allah yana tare dake, tashi dan Allah."


Babu yadda Khans ta iya hakanan ta miƙe ta shiga bathroom tana sharar hawaye mai tsananin ƙuna da zafi, ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta fito, da taimakon Nasreen ta soma shiryawa kana ta fito mata da kayan da zata saka, ita kuma ta fita kiran mai kwalliya. Khansa'u ta daɗe a tsaye tana kallon kayan kafin tayi jahadin sanyawa, tana gama sawa daidai su Nasreen sun shigo tare da mai kwalliyar. "Wow!" Kawai Nasreen ta furta daga bisani tace "kinga yadda kika fito kuwa? Sak amarya."


Harara Khans ta watsa mata tana miƙewa, wayar ta ta ɗakko tana son kiran Haseena, amma me? Message ta gani kan screen ɗin wayar ya shigo awa 2 da suka wuce. Ganin daga inda saƙon ya shigo ne yasa ta saurin buɗewa, saƙo ne kamar haka _"Assalamu alaiki ƴar uwa! Ina mai matuƙar tayaki farin cikin kasancewar yau a ranar auren ki, ina miki fatan alkhairi tare da fatan Ubangijin talikai ya baku zaman lafiya. Happy married life in addy.! Saƙo daga Zaid.."_
Kuka ne ya taho mata da ƙarfi wanda ta kasa danne shi har saida ya samu nasarar zubowa, duk yadda kakai ga rashin imani ka kalli Khansa'u a wannan lokacin saika tausaya mata, jin ƙafafun ta ta neman yaada ta yasa ta durƙushe kan gwiwoyin ta, da sauri Nasreen dake fitowa daga toilet ta matso tare da kama ta tana tanbayar ta ko lafiya? Sosai Khans ta bawa Nasreen tsoro dan bata taɓa irin wannan kukan ba, nan itama ta soma taya ta, ganin Khans bata da niyyar tsayawa yasa Nasreen karɓar wayar dake hannun ta, saida ta karance shi tsaff, kafin wani siririn hawaye mai ɗumi na tausayin Zaid ya zubo mata, yayin da gefe guda bataji daɗin shigowar saƙon ba, dan sunsha wuya kafin su shawo kanta tabar kuka, ga kuma wani kukan ya kunnu. Ameesha da shigowar ta kenan taga suna kuka yasa ta fice cikin sanɗa ba tare da kowa ya ganta ba, babu jimawa ta dawo ita da anty Jumayna, faɗa ta soma yi musu kan su kaɗai ake jira amma sun tsaya suna kukan shashancin banza da wofi, da kanta ta ɗago Khansa'u ta zaunar da ita bisa stool kana tayiwa mai kwalliyar alama da ta soma aikin ta. Ba tare data damu da wata shegiyar kwalliya ba ta cigaba da hawayen ta, da ƙyar mai kwalliyar ta shawo kanta aka soma, cikin ikon Allah kuwa har aka gama bata ƙara yin wani hawayen ba, Nasreen da Ameesha suma saida akayi musu sannan duk suka miƙe suka fita, amaryar na tsakiyan su kanta ƙasa. Ba laifi tayi ƙoƙari wajen danne kukan ta har yamma, lokacin an soma hada-hadar yin sallar maghriba, wani sabon wanka ta kuma yi, anty Jumayna ta feshe ta da turaruka masu sanyin ƙamshi wanda saika matso kusa da ita sosai zakaji, gefe anty Jumayna ta ɗan matsa tana ƙarewa Khans kallo a zuciyar ta tana faɗin "da yanzu da Zayd za'a ɗaura.., Allah yaji ƙanka da rahma."
Da mamaki Khans ta kalle ta kafin tace "anty wa kenan?"
Ita kuwa anty Jumayna bata ma san abinda ta faɗa ya fito fili ba, nan ta wayince tare da cewa "babu komai, wancan farar rigar zaki saka kafin na dawo." Tana gama faɗi tayi waje abinta, tabar Khansa'u baki buɗe.


Bayan sallahr Isha'i aka soma shirin kai amarya gidan ta, manyan motoci ne na alfarma Zayyad ya aiko dasu, a gurguje aka ɗauka amarya da babbar ƙawar ta Nasreen, sai dangi da abokan arziki.
Alhamdulillah, gidan amarya yayi kyau matuƙa gaya, ba ƙaramin kuɗi aka kashewa gidan ba, saidai muce Allah yasa rai akayi mawa.


.....ƴan kai amarya basu wani jima ba duk aka watse, sai su anty Jumayna da Ameesha da kuma ƙannen Khans wato Haseena da Ayeesh sai Nasreen, wani wankan anty Jumayna ta ƙara sanya Khansa'u tayi, a wannan karon wani fitinannen turare mai matuƙar ƙamshi ta sanya mata a cikin ruwan wankan, nan dai tayi wanda ta fito suka bata waje ta shirya cikin grey Abaya da mayafin ta, sosai kuwa tayi kyau matuƙa, tsokana kam tasha shi wajen Nasreen harda na Allah ya isa, da haka sukayi mata sallama tana ta faman kuka wiwi da hawaye, Nasreen kam me zatayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login