Showing 12001 words to 15000 words out of 36565 words
Chapter 5 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt
ta taddashi da alama ita yake jira, yana ganin ta kam ya buɗe motar, itama zagayawa tayi ta shiga nata mazaunin suka fice.....
___________________________________________✍️🖊️
*BABYLORH*❤🔥
(Shalelen Women Writers)🤞
07069929131
[9/26, 8:14 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(Shalelen Women Writers)*🌹
Writer of:
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading......
3. *KHANSA'U* _(the famous arabic poetess)_
17 & 18...
_______Koda suka dawo gida babu wanda suka sanar mawa domin babu wata alama data nuna wani abu ya faru, harkokin ta kawai ta shiga yi shi kuma ya koma asibiti.
Toh Khans ta cigaba da zuwa makaranta cikin jin daɗi, kuma sosai take karatu ita da kawar tata wato Nasreen, dan itama ba daga baya ba wajen son karatu. A ɓangare guda kuwa alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakanin su da Zaid, duk sanda ya rigasu fita lecture yakan zo ya jira su su gama su fito, harya gama karatun nasa, lokacin daya labartawa Khans ba ƙaramin baƙin ciki da tashin hankali ta shiga ba, dan ta kasa tantance alaƙar ta da Zaid, sau tari Nasreen kan faɗi mata sun kamu da son juna amma taƙi yarda da hakan, a cewar ta mutunci ne kawai, kuma dan yana da sunan masoyin ta ne. Sai a ranar ƙarshen shi a makaranta ta soma gasgata zuciyar ta kan ta faɗa soyayyar Zaid, yayin da wata zuciyar ke raya mata shaƙuwar da sukayi ce kawai tasa hakan, ita kanta tafi gasgata shaƙuwa ce.
Shi kanshi Zaid ji yake kamar karya tafi amma ya zamar masa dole, domin tun last week ya kamata ace ya tafi amma ya kasa, yana son Khans matuƙa, amma jin labarin ta yasa yake fargabar sanar da ita, sabida besan menene zai zama respond dinta ba, kuma bayason hakan ya taɓa alaƙar su da shaƙuwar su, shiyasa bai taɓa gigin sanar da ita ba.
Tun bayan komawar Zaid gida kuwa makarantar ta zamo tamkar ƙabari wa Khansa'u, duk da kuwa suna waya akai-akai da Zaid ɗin amma dukkanin su babu wanda ke gamsuwa da wayar, sun ɗauki lokaci mai tsawo kafin suka saba da hakan, zuwa lokacin har Zaid ya soma aiki a babban asibitin da mahaifinsa ya gina masa.
★★★★★
Kamar yadda suka saba gudanar da meeting duk bayan watanni uku tsakanin su, yau ma hakan ce ta kasance, amma abin mamaki a wannan karon harda yaran aka sanya cikin meeting ɗin. Su kansu Ummi da Mummy basu san meye dalilin su Abba nayin hakan ba, amma koma meye zasu ji.
Bayan kammala tattaunawa kan abin da ya tarasu ne Abba yayi gyaran murya kana ya soma magana kamar haka "Ehmmm nasan dukkanin ku zakuyi mamakin wannan taro da aka haɗa domin ku, toh wannan ba abin mamaki bane a gare ku, domin kuwa mun zauna nida Daddyn ku munyi nazari sosai sannan mun yanke shawara a kanku, wanda muke fatan hakan ya yazo alkhairi a garemu baki ɗaya. Kada na cika ku da surutu, dalilin tara ku anan ba komai bane face magana akan kai Zayyad da ƴar uwar ka Khansa'u, ina son ku ɗauki furucin dazai fito daga baki na a matsayin ƙaddarar ku sannan zanso kuyi magana biyayya akan hakan," ya ƙarasa yana gyara zama sannan yace "na baiwa Zayyad auren ɗiya ta Khansa'u..."
Ba Zayyad kaɗai ba, hatta Khansa'u da tunda Abba ya soma magana kanta ke ƙasa saida gaban ta yayi wani mummunan faɗuwa, Ummi da Mummy kam ƙasa sukayi da kansu, dan tunda wannan furucin ya fito daga bakin Abba tare da goyon bayan Daddy sunsan babu makawa saiya tabbata, saidai wani ikon Allahn.
Bakin Khansa'u har karkarwa yake wajen furta "Abba ɗan uwa nane fah!"
Gyaɗa mata kai kawai Abba yayi alamar tabbatarwa kuma yana cikin hayyacin sa... Zayyad dakejin sa kamar ya nutse cikin ƙasa ne ya saci kallon Khans a hankali a ranshi yana mai baƙin ciki da wannan hukuncin, bai taɓa kallon Khans a matsayin mata ba a rayuwar sa, baya banbance ta cikin ƙannan sa, bugu da ƙari shi bashi da ra'ayin aure yanzu ma, ko da yana da ra'ayi ma Khansa'u tayi masa ƙarama sosai, bai san me zaiyi da ita ba saidai ya raine ta. Amma alƙawarin ne ya ɗaukar wa kansa, bazai taɓa tozarta Abba ko Daddy da iyalan su ba, zaiyi iya bakin ƙoƙarin sa yayi biyayya ga wannan lamari.
A ɓangaren Khansa'u kuwa tunani take anya Abba na cikin hayyacin sa kuwa, yo cikin hayyacin sa mana. Duk mutumin dake cikin hayyacin sa ai bazai haɗa ƴarsa da ɗansa daya haifa da cikin sa aure ba, idan kuwa hakane to hakan yana nufin akwai wani *ɓoyayyen al'amari* da aka ɓoye musu kenan, amma meyasa ba za'a barta ta fidda wanda take so ba, shin idan Zaid yaji wannan labarin me take tunanin zai faru..., Runtse idanun ta tayi tare da girgiza kanta dan tabbatar da abinda ke faruwa a zahiri ne kuwa, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta furta a ɗan bayyane kaɗan..,? maganar da Daddy ya somayi ne ya katse musu tunanin su yayin da yake faɗin "kuyi haƙuri yarana, nasan zakuji abin tamkar almara, kuma zakuyi zaton ko bamu cikin hayyacin mu, toh muna masu tabbatar muku da cikin hankalin mu muke, sannan kada ku sake naji wani abu mara dadi yaje ya dawo," ya ƙarasa tare da rufe taron da addu'a.
Tun da suka tashi taro ta koma ɗaki sai faman saƙe-saƙe kawai take a ranta, ta rasa gane me su Abba suke nufi, ko a zamanin jahilai a ina ƙanwa ta taɓa auren wan ta, sosai abin yayi mata wani banbaraƙwai, sammm baza ayi wannan ta'asar da ita ba, bugu da ƙari bazata taɓa iya zama da Zayyad a matsayin miji ba, domin ko a gida ya zaman su ya ƙare balle zaman aure, dan kulawa kam tana samun ƙulawar da duk wata ƙanwa take samu daga wajen ɗan uwan ta, amma matsalar miskilancin shi baza ta iya tanƙwara shi ba, sosai magana ke yiwa zayyad wahala, a lokacin rashin lafiyar ta bayan ta farfaɗo nema taga ya ɗan yi magana, duk da tayi mamaki matuƙa dan bata taɓa tunanin akwai abinda zai sanya yayan nata magana ba...., tana tsaka da wannan tunanin Ayeesh ta shigo tare da sanar da ita Abba na kiran ta.
Jiki a sanyaye ta miƙe tana mai fatan Allah yasa su janye maganar su, bata tadda Abba a parlorn sa ba hakan yasa ta shiga ɗakin nasa ɗauke da sallama, "Babban magana," ta furta cikin ranta yayin da taga Abba da Ummi zaune, sai Zayyad dake kan lallausan center carpet ɗin daya haska bedroom ɗin Abba ya sada kansa da ƙasa. Zama itama tayi kusa da Ummi tana opposite ɗin Zayyad ɗin.
"Zayyad," Abba ya faɗa cikin muryar da take nuna babu wasa tattare dashi.
Cikin sanyi Zayyad ya amsa da "na'am Abba."
"Kunsan dalilin da yasa na kira ku?" Dukkanin su girgiza masa kai sukayi alamar a'a.
"That's good, Zayyad me zakace game da wannan hukunci?"
Ɗagowa yayi a hankali ya saci kallon Khans dake zaune ta tsare shi da idanu tana jiran taji me zaice, "Ahh--amm Abba ni babu abinda zance akai, duk abinda kuka yanke daidai ne Abba."
"Ba haka nakeson kace ba Zayyad, kada ka damu da furuci na kona Daddyn ku na ɗazu na da mukace babu abinda zai hana hakan faruwa, ka faɗamin shin ka yarda da auren Khansa'u?"
Wata irin bugawa zuciyar sa tayi kafin ya ƙara ɗagowa a karo na biyu ya saci kallon Khansa'u, har lokacin bata ɗauke idanun ta akan sa ba, jiran amsar da zata fito daga bakin sa kawai takeyi.
"Na amince Abba."
"Innalillahi wa inna ilaihi, ya Zayyad kaima haka zakace, a ina ƙanwa ta taɓa auren yayan ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya, meya sanya kuke haka ne wai? Ummi kisa baki mana, wallahi.....!
Saurin doshe mata baki Ummi tayi tana auna mata harara kafin tace "meke damunki ne, waye sa'an ki anan da kike mana magana haka? Ki shiga taitayin ki."
Nan fa hawaye ya soma zarya a fuskar Khansa'u, kafin wani ya sauka wani ya fito, meke damun su Ummi ne wai, kodai mafarki takeyi ne? Idan mafarki ma nakeyi Allah kasa na farka kafin faruwar wannan lamari, ta faɗa a bayyane. Babu wanda yace da ita ƙala, illa gyara zama da Abba yayi yace "tashi kaje Zayyad, Allah yayi maka albarka."
Jiki a mace Zayyad ya miƙe zuciyar sa na masa wani raɗaɗi jin irin kukan da Khansa'u keyi, duk dan an haɗa su aure.
"Daughter, Inaso ki natsu ki saurareni, nasan abin zaizo maki wani iri ko? Kada ki damu, with time zaki fahimci komai, kada wata matsala da fito daga ɓangaren ki okay?" Bai jira amsar taba ya fice, sakamakon sallan da ake kira.
Baki buɗe tabi bayan Abba da kallo harya fice kafin ta kifa kanta kan cinyar Ummi ta saki wani marayan kuka, "Ummi meyasa kika kasa yiwa Abba magana bayan kinsan abin da yake shirin yi ba daidai bane, ɗan uwa nafa Ummi! A ina aka taɓayin haka, taya zan kalli wanda muka fito ciki ɗaya dashi matsayin abokin rayuwa na dindindin, Ummi akwai sake a cikin al'amarin nan, kada ki bari son zuciya ya kaimu ga aikata abinda zai zamo dana sani a garemu Ummi dan Allah, banason ya Zayyad wallahi, har gobe kallon ɗan uwa nake masa, kwatsam kuma saina wayi gari dashi a matsayin miji? Na roƙe ki Ummi kada ki bar hakan ta faru, idan ba haka kuma saidai akai masa gawa t...."
Da sauri Ummi ta toshe mata baki tana mai tausayawa ɗiyar tata, baza taso aurawa ɗaya daga cikin ƴaƴan ta wanda bayaso ba, balle kuma ɗiyar ta mafi soyuwa a gareta kuma mafi rauni cikin ƴaƴan nata, toh amma ya zatayi? Babu yadda za'ayi ta tunkari Abba akan ya janye maganar, domin Abba mutum ne mai kafiya akan abu. Rarrashin ƴar tata ta shiga yi tare dayi mata nasiha kan bin umarnin iyayi da kuma ribar dake tattare da hakan, da ƙyar Khansa'u tayi shiru tana cigaba da kukan zuci ganin daga Ummu har Abba sun kasa fahimtar ta.
_Toh fans! Me tunanin ku ya kawo kan wannan hukuncin da Abba ya yanke mana, me zakuce game da hakan._
_Team Zayyad na tayaku murna, amma ya kamata Ku sanar damu hikimar yin hakan, domin auren wanda kuka fito ciki ɗaya haramun ne._
_Team Dr. Zaid ina tayaku jaje kan wannan lamari tare da fatan alkhairi akai._
_________________________________________✍️
Babylorh ce❤🔥💞
*(Shalelen Women Writers)*💋
07069929131
[9/29, 9:39 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_
By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*
The writer of
1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_
19 & 20....
________Koda Zayyad ya fita, direct sashin su ya koma tare da shiga ɗakin sa, kan bed kawai ya faɗa ya rasa meke masa daɗi, harga Allah baiso wannan haɗin da Abba yayi ba, amma bazai iya watsawa Abba ƙasa a ido ba, dan irin halacci da adalcin da Abba yayi masa ba kowa ne zai iya shi ba, duk da yasan Khansa'u daidai da minti ɗaya bazata so shi a matsayin miji ba, amma zai jure dukkan wani wulaƙanci daga gare ta, dan alƙawarin zuciyar sa ne baza'a taɓa tozarta ko wulaƙanta ɗaya daga cikin iyalan Abba a gaban sa ba, balle kuma shi ya wulaƙanta su. Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ci gaba da tunani, ganin tunanin bazai fusshe shi ba yasa ya miƙe tare da nufar bathroom yayi wanka haɗi da alwala ya fito, sallah yayi gami da addu'o'in nasara da fatan alkhairi akan wannan al'amari dake shirin faruwa. Ya daɗe sosai kan sallaya yana nema masu zaɓin Allah kafin ya miƙe ya kwanta..
Washegari da wani matsanancin ciwon kai da ciki Khansa'u ta tashi wanda yayi sanadiyyar rashin zuwan ta makaranta, har su Haseena da Ayeesh suka wuce makaranta bata fito ba, dama Abba yana rigasu fita hakan yasa bai san da rashin fitowar taba. Sosai Zayyad yaji babu daɗi ganin irin halin da ƴar ƙanwar tashi keson jefa kanta akan shi, yanason faɗa mata gaskiyar shi ɗin ba yayan ta bane na jini amma yana tsoron faɗan Abba, dan Abba yace ko mutuwa tayi sai ankai gawar ta gidan Zayyad sannan za'a kaita makwancin ta. Mahfouz da yaji shurun yayi yawa ne yace "mom wai ina Khans ne?"
"Tana ɗakin ta mana, ka ƙyale ta zata fito idan yunwar ta kusa kashe ta."
Jikin Mahfouz ne ya basa ba lafiya ba hakan yasa ya miƙe yana faɗin "gaskiya Ummi ba lafiya ba, bari in duba ta." Ya faɗa tare da ficewa daga sashin dinning ɗin. Tun daga corridor yakejin shessheƙar kukan Khansa'u har ya isa ɗakin, knocking ya somayi amma shiru ba'a buɗe ba, ga kuma kukan ta da har yanzu bai dena fita ba. A hankali ya murɗa handle ɗin bakin sa ɗauke da sallama, chan ƙarshen gado ya hango ta tana murƙususu, da sauri ya ƙarasa tare da tallafo ta, wani zafi jikin ta yayi wanda ya ƙara tsorata Mahfouz. Daga ɗakin ya soma kwaɗawa Zayyad kira, Zayyad wanda dama jiran abinda zaisa yaje ya ganta yake ya miƙe a sukune ba tare daya ankara da kallon da Ummi ke masa ba. Ko ƙofar mai iya maidawa ya rufe ba ya nufi inda suke a zaune, da sauri ya amsheta yana faɗin "Mahfouz ɗakko first aid box a ɗaki na kan bedside drawer."
Da "toh" ya amsa yana ficewa. Fitar sa ba daɗewa Ummi ta shigo itama tana tanbayar "meke damun ta?"
"Ban sani ba Ummi."
Bai daɗe ba ya dawo da first aid box ɗin ya miƙa wa Zayyad, jikin sa har ɓari yake wajen amsa, da gaggawa ya soma bata taimako, nan take kam ya gano matsalar, abinci yasa aka kawo mata bayan yayi mata allura. Mahfouz da kansa ya fita ya kawo mata abinci, da ƙyar da rarrashi taci kuma bawai dan batajin yunwa ba, sai dan Zayyad dake wajen. Hakanan taji batason ganin shi, batason ya raɓe ta ko ƙadan, sabida sanadin haɗa auren su ke neman ruguza soyayyar Zaid dake cin ta a rai. Shi kuwa Zayyad yayi hakan ne gudun faruwar matsalar zuciyar ta, a iya binciken da yayi ya gano rabon ta da abinci kusan tun jiya da safe.
Wunin ranar dai haka Khansa'u tayi shi babu walwala, ga wutar ƙiyayyar Zayyad dake ruruwa daga chan ƙasan ruhin ta, daidai ta minti ɗaya batason jin koda ƙamshin turaren sa. Ta rasa wa zata faɗawa damuwar ta taji daɗi, Nasreen dake taimaka mata da shawarwari, a wannan gaɓar itama ta rasa me zatayi, dukkanin su babu wanda ya kawo Zayyad ba ɗan gidan bane, a cewar Khansa'u ma wai asiri yayiwa ƴan gidan ya rufe bakin su.
Toh a kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, yau kimanin watanni uku da faruwar wannan lamari, abubuwa da yawa sun faru tsakanin watannin nan ciki kuwa harda sa ranar Zayyad da Khansa'u da akayi, watanni biyu masu zuwa. Tun Khans na ɗaukar abin da wasa har zuciyar ta ta fara gasgata su Abba basa cikin hankalin su.
Kamar yadda Mahfouz ya saba kaita makaranta ya ɗakko ta, tun bayan da aka sa ranar auren su, yauma tafe suke a hanya babu mai cewa da wani ƙala, wanda ba haka suka saba ba, haka har suka isa gida babu wanda yace da wani ko sannu.
Zaune take yau ma a ɗaki kamar yadda ta saba zama ta faɗa duniyar tunani har Haseena ta shigo bata sani ba. Firgigit tayi yayin da taji hannun mutum a jikin ta, ganin Haseena ce yasa ta koma ta kwanta kamar yadda take, cike da tausayawa Haseena tace "Ukhty meya sanya kike ɗaurawa kanki damuwa hakane, meyasa kikeson sanya kanki cikin yanayin da likitoci suka hane ki daki shiga?"
"Hmm, bazaki gane ba Haseena, ki ƙaddara kece a akace ki auri ya Zayyad, yaya zakiji? Haseena tayaya Zayyad zai zama mijina, bayan kinsan ciki ɗaya muka fito, ko ku a makaranta ance muku hakan zai iya faruwa?" Ba tare data jira amsar Haseena ba ta ƙara da faɗin "wallahi Haseena na yarda Abba ya zaɓamin koma wanene zan aura, amma ba ya Zayyad ba." Ta ƙarasa maganar da wani matsanancin kuka mai taɓa zuciyar mai sauraron ta.
Sosai ƴar uwar tata ta tausaya mata itama zuciyar ta cike da tunanin abinda su Daddy da Abba suka yanke wanda ba daidai bane a musulunci. Kafaɗar ta ta dafa kana tace "kiyi haƙuri Ukhty, ni a ganina wannan keɓewan da damuwan da kike ɗaurawa kanki bai dace ba, nasan cikin mu babu wanda zai iya tunkaran Abba da wannan maganan, why not ki samu Ummi ko Mummy ki fahimtar dasu rashin dacewar hakan, kinga idan akwai wani abu a ƙasa ma saimu sani."
"Haseena basu da niyyar sanar dani komai, kuma ina mai miki rantsuwa da idan ba'a kaiwa ya Zayyad gawa ta ba toh shi sai an bar gidan da gawar sa, saidai In nima a kashe...."
"Meye haka kikeyi sis, kinsan me kike faɗa kuwa, ya kike abu kamar wacce bataje makaranta ba? Kamar yadda nace kiyi ki gwada mu gani, idan har shawarar batayi ba then we shall think of