Showing 27001 words to 30000 words out of 36565 words

Chapter 10 - KHANSA'U Book Complete Hausa Novels by Bablor.txt

27 Nov 2024

2111

Abba sosai ranshi ya ɓaci, nan take ta kira Zayyad tare da ce masa yazo gida._








★★★★★★




Toh Alhamdulillah, kamar yadda Khans tayi alƙawarin gyarawa, bata saɓa ba. Sosai take iya bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta farantawa Zayyad kodan farin cikin iyayen ta. Shima Zayyad sosai yaga chanji daga wajen matar tasa da yawa, dan yanzu tana abinci, ta gyara ko ina na gidan har ɗakin sa, kuma takan yarda su kwana tare wani lokacin, saɓanin da da bata komai, gyaran gidan ma na ɗakin ta kawai takeyi. Har ƴar aiki Zayyad ya kawo mata dan ta riƙa taya ta aiki, dan a matsayin ta na mai ciki yawan aiki ba nata bane, duk da har yanzu bata san jiki bane, dan bai wuce wata 3 da ƴan ɗoriya ba, tana dai lura da yanayin yadda jikin ta ya chanza, ga ƙwadayi da take fama dashi, sai kuma magungunan da Zayyad ke kawo mata, wani lokacin kuma ya ɗauke ta suje asibitin sa ya duba ta ya dawo ta ita. A lokacin da cikin ta ya shiga wata na huɗu ne ta gane ciki gare ta, tasha kuka harta godewa Allah, dan har lokacin daidai da minti ɗaya bata taɓa jin son Zayyad ba, amma tayi alƙawarin sanya shi da iyayen ta farin ciki, zata raini cikin kuma ta haife da yardar Allah.


Yauma tafe suke a hanya sun dawo asibiti, ga mamakin Khans a maimakon su tafi gida sai taga ya ɗau hanyar gidan su, saida marin da Abba ya mata ya dawo mata, tasa hannu ta shafa wajen idanun ta suka kawo ruwa. Zayyad dake gefe na saida ya lura da hakan, sosai shima yaji ba daɗi har dai suka ƙarasa. Basu sami kowa a gidan ba sai Ayeesh da Haseena suka tabbatar musu da sunje taron ƙarshen wata, basuyi ƙasa a gwiwa ba, suka nufi gidan Daddy dan dama achan akeyi. Sosai kuwa akayi murna da ganin su, dan kuwa alamu sun tabbatar da Khans ta cika alƙawarin data ɗauka. "Sarakan yawo, daga ina kuke kuma wa yace muku muna nan? Nan nasan badan Allah kuka zo ba, wata ƙilama baku taɓa zuwa gaida Daddyn ku ba," Abba ya faɗa fuskar sa ɗauke da murmushi.


"A'a! Ya haka kuma, haka mukayi dakai basu taɓa zuwa ba, kuzu kunji ƴaƴana, zo ku zauna."


"Auuu! Haɗemin kai zakuyi kenan, toh shikenan, daga ina haka da ranan nan?" Abba ya kuma maimaitawa a karo na biyu.


Munje asibiti ne Abba, dawowar mu kenan mun biya ta gida, Haseena tace kuna nan." Zayyad ya faɗa yana sosa ƙeya.


"Subhanallahi! Waye ba lafiya ɗana?" Daddy ya faɗa yana dafa kafaɗar Zayyad ɗin.


Inda-inda ya somayi yama rasa me zaice, dan baisan ya furta asibiti bama, nan take kuwa suka gano komai, musamman ma Ummi da Mummy da tun shigowar su suka ƙyalla ido kan Khans suka ga komai.


"Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah sarki, Alh. Muhammad shi ya fara faɗomin a rai," Daddy ya faɗa fuskar sa cike da tausayi. Ƙasa sosai Zayyad yayi da kanshi ya share siririn hawayen daya taho masa da handkie ɗin hannun sa. "Meyasa kake kuka?" Khansa'u ta faɗa cikin sigar tanbaya a hankali.
"Ba kuka nakeyi ba, abu ne ya shigar min ido," ya faɗa yana sakar mata murmushi a ɓoye.


"A'a Zayyad! Ni yanzu ina ganin babu wani ɓoye-ɓoye kuma, ya kamata ace zuwa yanzu matar ka tasan komai game dakai," Mummy dake zaune ta faɗa tana mai tausaya Zayyad ɗin. Shidai Zayyad baice komai ba, kuma bai ɗago ya kalli kowa ya, Abba ne ya soma magana kamar haka ".....














```Ina masu buƙatar jin labarin Zayyad, toh ku tara dani idan Allah ya kaimu gobe ɗauke da labarin Zayyad insha Allah```
```Kuyi haƙuri yadda na yayyanke labarin, banaso yayi tsawo dayawa ne shiyasa.```












___________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/16, 8:18 PM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_






By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




🪶 _*WOMEN WRITERS ASSO...*_ 📚




The writer of:


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*
_(the famous arabic poetess)_






35 & 36....








📖____________"Hakane Zayyad, ya kamata ta sani," saida yayi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa "


```Alh. Muhammad Usman, wanda akafi sani da Alh. Muhammad Shehu (wato takwaran Abba), haifaffen garin Katsina ne kuma yaya a gurin Hajiya wato Ummi, mahaifin su ya kasance mutum mai ɗumbun dukiya, ga ilimi Allah ya bashi, inda rabi da kwatan kuɗin sa yake sadaukarwa al'umma su. Ni kaina zan shaidi Alh. Muhammad akan halayyar sa da mutane musamman maƙwaftan sa, domin ya ɗauke su tamkar ƴan uwa. Sai dai Allah ya jarabce sa da wata azzalumar mata, tun bayan rasuwar mahaifiyar Zayyad, a lokacin yana da watanni 8 a duniya. Matar ta kasance tana azabtar da Alh. Muhammad da kuma ɗansa Zayyad, ta haɗawa Zayyad zagon ƙasa dan mahaifinsa ya kore sa a gidan amma batayi nasara ba, domin duk duniya Zayyad shine babban ɗa kuma mafi soyuwa a zuciyar sa. Wannan ke tsole mata ido, kuma yake ɗaga mata hankali, dan so take ita da ƴaƴan da zata haifa su su gaji dukiyar, duk yunƙurin ta na kashe Zayyad ta gaza samun nasara, hakan yasa take azabtar dashi, ta dake shi ta jijji masa ciwo, wata rana ma ta hana shi kwana gidan, sabida mahaifinsa matafiyi ne.```
```Ana haka Alh. Muhammad ya soma wata iriyar cuta wadda aka rasa ta mecece, har ƙasashen ƙetare an zaga dashi amma duk abu ɗaya suke faɗa, bayan cutar sa ta hawan jini, babu abinda suka gano tattare dashi. Kamar gaske, Alh. Muhammad ya soma samun lafiya, dan har takawa ma ya somayi, kwatsam wata rana ya fita shan iska tsautsayi yasa ya faɗi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar ɓarin jikin sa, yasha wahala matuƙa, dan duk lokacin da ciwon sa ya tashi ba ƙaramin jigata yakeyi ba. A kwana a tashi Alh. Muhammad saida yayi watanni goma a asibiti, a safiyar ranar asabar Allah ya ɗauki ransa. Karima (wato matar Alh. Muhammad) tasha kuka kamar gaske, a haka har akayi arba'in ɗin mahaifin Zayyad bata taɓa nuna wariya ga ɗan ta da Zayyad ba, ashe akwai abinda take ƙullawa.```


```Wata rana, bayan kusan wata biyar da rayuwar Alh. Muhammad Hajiya (mommyn Khans) taje gidan domin duba halin da ɗan ɗan uwan nata ke ciki, amma abin mamaki sai ta taji suna magana da wata ƙawar ta, jikin ta daya bata akwai abin da suke ƙullawa yasa ta tsaya daga bakin ƙofa, Karima da ƙawar tane suka ta saƙa da warwarar yadda za'ayi su ɓatar da Zayyad a duniya, a lokacin Zayyad baifi shekaru ɗaya da wata watanni tara zuwa goma ba, nan sukayi ta tunanin yadda zasu yar dashi, nan take kuwa ƙawar Karima ta bada shawarar a bawa area boys ɗin layin su fitar dashi, nan kuwa Karima tayi na'am da hakan, suka yanke shawarar da daddare zasu aiwatar da komai, in yaso sai suce ya ɓace.```


```Jin haka kuwa yasa hankalin Hajiya mummunan tashi, haka ta fito zuciyar ta cike da fargaba da kuma yadda za'ayi ta ceto Zayyad daga mugun manufar su akan Zayyad
Nan take ta yanke shawarar taje ta samu area boys ɗin, in yaso suyi yarjejeniya ta biya su. Hakan kuwa akayi, toh su da yake kuɗi suke nema, ai ba musu suka amince, a daren ranar kuwa suka aiwatar da komai ba tare da sun sanar da Karima komai ba. A taƙaice dai Zayyad tun yana shekara ɗaya da wata goma yake tare damu, daga lokacin ya samu kwanciyar hankali, duk da ba wayau gareshi ba a lokacin, amma har ya girma baya shiga harkar mutane balle kuma wani abu ya faru dashi. A lokacin da muka sanar da Zayyad cewa ba mune iyayen shi ba, muka sanar dashi tarihin rayuwar sa, yayi kuka matuƙa harya gode Allah, duk daga wannan rana kuwa magana ke yiwa Zayyad wuya, duk da cewa yana da wuyar sha'ani kafin ku saba, amma da zarar kun saba dashi shikenan, nasan kema kin fahimci haka ƴa ta.```


Saida Abba yaja nannauyar ajiyar zuciya sannan ya cigaba da faɗin "wannan dalilin yasa na yanke shawarar haɗa auren ku, domin nason ke kaɗai zaki iya kula da marayen Allah ɗiya ta, duk da kuwa a baya kin nemi ki watsamin ƙasa a ido, amma yanzu Alhamdulillah naga kun daidai ta. Wannan zancen da nake miki, har yanzu Karima bata san Zayyad na raye tare damu ba, kuma har yanzu tana nan tanacin duniyar ta da tsinke, domin sosai nake lura da duk wani shige da fice nata. Kwanaki ma naji ance wai ɗan ta data haifa ma ya rasu, a dalilin haɗarin mota da yayi.


Tun da Abba ya soma magana har ya gama Khansa'u ke faman kuka tamkar wadda ranta zai bar jikin ta, kuka take sosai na nadamar abubuwan da tayi wa Zayyad da irin wulaƙancin da tayi masa, kuka take na tausayin Zayyad da kuma irin rayuwar da aka so jefa shi amma Allah ya kiyaye shi da tsarewar sa, ganin bata da niyyar dakatar da kukan ne yasa Daddy cewa "Ba kuka zakiyi ba ƴata, addu'a kawai zamu cigaba dayi, Ubangiji ya cigaba da tsare mu a duk inda muke da kuma sharrin masharranta, kai kuma Zayyad Allah ya ƙara maka haƙuri da juriyar rashi, nan dai ya ɗanyi musu nasiha da kuma faɗa kan saɓawa juna, kana yace su tashi su tafi.
Jiki a mace dukkanin su suka miƙe suka fita, har suka shiga mota Zayyad bai iya furta komai ba. Saida ya kwashi kusan mintina goma kafin yaja wata zazzafar ajiyar zuciya kana ya zaro hankie daga aljinun sa ya share idanun sa da sukayi jaa, sannan ya tada motar suka tafi.
Koda suka koma gida ɗaki Zayyad ya shiga, wunin ranar Khans bata ƙara sanya shi a idanun ta ba, tun tana saka ran fitowar sa koda zuwa masallaci amma shiru, kuma tana tsoron shiga ɗakin nasa sabida batasan da wani ido zata kalleshi ba. Ganin har an kira sallahr maghriba bai fito ba yasa ta yanke shawarar shiga duk abin da zai faru ya faru, dan duk abinda zai mata, baza taga laifin saba, don tayi masa shima. Saida tayi sallah kana ta jera masa abincin sa a dinning ta nufi ɗakin, bakin ta ɗauke da sallama ta shiga kanta a ƙasa, daga can ƙasan maƙoshi ya amsa mata wadda ke bayyanar da dasasshiyar muryar sa, zaune yake akan sallaya har ta ƙaraso inda yake. Durƙusawa tayi kan gwiwoyin ta a gaban sa, har lokacin bata kalli fuskar Zayyad ba, balle taga wani irin kallo yake mata, wasa ta somayi da yastun hannun ta kafin tace "ya Zayyad dama naga baka fito bane shine nace bari inzo in duba ka, kuma na gama abinci yana dinning yanzu haka."
"Yanzu nakeson in fito dama, tashi muje," ya faɗa yana miƙewa daga kan sallayar da yake. Itama mara masa baya tayi tanajin ta wani iri, dan ta kasa haɗa ido da Zayyad ɗin ma. Saida tayi serving ɗin shi sannan tayi serving kanta. Duk da ba wani yunwa yakeji ba, dan jin cikin sa yakeyi a cunkushe, yayi kusan loma uku kamin ya tsaida kallon sa ga Khans dake jujjuya cokalin ta yace "Khans yadai? Naga kinyi shiru kuma bakicin abincin."
Murmushin yaƙe tayi daga bisani tace ".....










____________________________________________✍️
Daga alƙalamin
*BABYLORH*
(shalelen women writers)
07069929131
[10/17, 10:24 AM] Babylor: 💍💍💍💍 *KHANSA'U* 💍💍💍💍
_(the famous arabic poetess)_






By
💍BABYLORH💍
*(shalelen women writers)*




_*WOMEN WRITERS ASSO...*_




The writer of:


1. *RUSHDAH*
2. *MARAICI NA*
loading.....
3. *KHANSA'U*. _(the famous arabic poetess)_






37 & 38....








📖____________"amm y...ya Zayyad, dama... dama...," Sai kuma tayi shiru. A hankali Zayyad ke karantar ta, yana son gano abinda yasa taƙi sake wa, sai da ya ɗauka cup ɗin ruwa yasha sannan yace "faɗi ko menene, zan fahimce ki insha Allah."
A sannu-sannu tabar kujerar da take zauna ta taka har inda Zayyad yake kana ta durƙusa gaban sa, "ya Zayyad, nasan a a zaman mu dakai na ƙuntata maka, haƙiƙa na cutar da kai mijina, dan Allah ba dan hali na ba, ina roƙon ka da girman Allah ka yafe min, wallahi nayi nadamar hakan, ina so in wanke kaina sannan in zamo mata ta gari a gare ka, dan Allah ya Zayyad kayimin wannan alfarmar, bazaka ƙara samu na da wani halin banza ko bad intentions akan ka ba," ta ƙarashe tana haɗa hannayen ta biyu yayin da hawaye ya gangaro kan fuskar ta.
Toh Zayyad dama bai taɓa riƙe ta a zuciya ba balle kuma har abin da take yi masa ya dame sa, yaji daɗi matuƙa da bai sha wuya sosai ba kafin ta sakko, dan ya yafe mata ba wani abu bane, ko da kuwa ba nadamar gaskiya tayi ba ya san wata rana zatayi, ƙoƙarin shi ɗaya yanzu, shine ya dasa soyayyar shi a zuciyar ta, dan har yanzu bashi da tabbacin son sa ya kamata.... Jin yayi shuru ne yasa Khans ɗagowa kana ta dafa kan cinyoyin sa tace "nasan yiwuwar hakan da wuya, dan Allah ya Zayyad ka taimaka ka yafemin, ta haka ne kaɗai zan iya samun rahamar Ubangiji na."
Murmushi yayi wanda ya bayyana kyawun sa sosai sannan ya miƙe tsaye, hannayen sa yasa ya ɗago ta itama kana yace "ya kamata ki san cewa mijin ki bai taɓa ƙullatar ki a rai ba, balle kiyi tunanin idan kin nema yafiyar sa bazai yafe ba. Allah SWT ma muna masa laifi, kuma idan mukayi tubar gaskiya muka nemi gafara yana yafe mana, toh wanene Zayyad da bazai yafewa matar sa rabin ran sa? Na daɗe da yafe maki matata, sabida haka ki daina damun kanki ko kaɗan, sabida kada ki mana asarar wannan," ya ƙarasa yana shafa cikin ta daya tafi flat, tamkar ba ɗan mutum ne aciki ba. Da mamaki takai idon ta kan hannun sa dake kan cikin ta kana ta ɗago ta kallesa. A idanun ta ya gano tanbayar da takeson yi masa, hakan yasa ya saki dariya tare da manna ta da jikin sa, ya rungume kayar sa, ko ince kayan sa. A hankali yake mata raɗa (whispering) wanda ni kaina banajin me suke cewa, sun ɗauki lokaci mai tsayi a haka kafin yaja hannun ta zuwa ɗakin sa, wanka ya shiga yayi ya haɗo da alwala, itama shiga tayi tayi alwalar yazo ya jasu sallah, zassha'awa🥰. A taƙaicen taƙaicewa dai tun daga wannan lokaci rayuwar auren su ya sauya gaba ɗaya. Kulawa babu irin wanda bata ba Zayyad, ta mai dashi shalelen ta tako wani fanni, sosai kuwa yakejin daɗin hakan, nan shima ya zage damtse wajen ganin ya faranta mata.


Toh a kwana a tashi ba wuya wajen Allah, yau cikin Khans yayi kimanin wata biyar, dan har ya bayyana gashi ƙarami, idan ba ka lura da kyau ba bazaka gani ba, sosai cikin ya zauna ɗass acikin ta yayi mata matuƙar kyau. Zaune suke a harabar gidan sanye da kayan sport, Khans sai maida numfashi take kamar wadda tayi gudun famfalaki, Zayyad dake gefe sai dariya yake mata kamar zai kifa. Ruwan dake kusa da ita ta ɗauka ta ɓalle marfin gorar ta kafa kai, saida tayi rabin ruwan sannan ta ajiye tana sauke numfashi kafin tace "gaskiya baby na gaji, daga yau ka riƙa yi kai kaɗai, ni bazan iya ba, nayi wanda zan iya." Dariya kawai Zayyad keyi kafin yace "ke kika ce zakiyi ai, ni bance ki tayani ba."


"Oh hakama zakace?"


"Sorry ma'am, ki shirya da yamma insha Allah zamu fita."


Tsallen murna tayi tana dariya, dan a tunanin ta gida zasuje, dan tunda aka sanya ranar auren Haseena da Ameesha bataje ba, "shikenan sai ka shigo, nikam kaga tafiya ta," ta ɗauki robar ruwan ta tayi ciki.
Da kallon ƙauna kawai Zayyad ya bita kafin shima ya miƙe yabi bayan ta.


Da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar kowannen su ya shirya tsaff, kasancewar su atampa atampa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login