Showing 6001 words to 9000 words out of 82304 words

Chapter 3 - UNCLE JUSTICE COMPLETE DOCUMENT by Ummu Sharif .txt

27 Nov 2024

4328

dama k'uma niba mai ra ayin kulla samarin bace.
Z'anyita zama agida, tareda iyayena. bama sai nayi aurenba, na haihu idan yaso I'ta khairat ta haihu sai nadauki d'an.ko yar, itakuma sai ta Haifa wani.


Ninarika azumi da zai zamemani garkuwa. daaga sharrin z'uciya da shaidan. domin dama nitun t'ashina mutum dayan mukataba k'ulla wata alaka, d'ashi kuma shima din ga dukkan alamu ba ra'ayinshi bane na iyayene.


Wato yaya k'halipha dan yayarsu a
Abbanmu ne Ammy Amina da suke *u.k* inna ga kuma dudu idan yayi yabani shekara biyu, da haihuwa. tun waani zuwa adaa sukayi, alokacin suka tadda anayimani b'ukin saukar alqur'ani mai girma. bayan munyi na I'salamiya, kuma sai maman fareeda tahada mun wani, agida inda duk dangi suka hallara har yan uwan mahaifiyata sunzo daga zamfara. baba Ammy Amina da Alhaji Alhaji Sameer mijinta da dansu daya k'halipha. sai yayan yayar maigidan ta datake riko, kasan c'ewar kar k'alipha yaitazama shikadai, kadaici, da rashin abokanan wasa. y'adameshi, yasa suka dauko rikon na'im da nadim.


Y'anda ita da mijinta sukaji inna fitar da ka'idojin karatu na, yasa tayima danta sha,awata w'anda shima atake alh sameer yadarsa hakan aransa.


B'ayan sunkoma gida da dare take gayamasa abunda kecikin ranta. atake nan yake gayamata kamar tasan abunda yake c'ikin ransa domin g'askiya yanayima k'halipha fatar hada iri dani. amma ta tambayi Abbanmu taji idan suriga da anyimun m'ijiba
bawani bata lokaci k'uwa tagabatar da b'ukatarta agun Abbana ayayinda s'hikuma ya wakillata, maman fareeda! da ta t'ambayar masa ra ayina taji idan na a'mince shibayada matsala idan yaso k'haliphan ya naimi soyayyah agutrina. amma yanason kar afara yimun maganar s'oyayaya kowani abu makamanchin h'akan har saina kai k'allah aji b'iyar na makarantar gaba da primary t'ukunnah.


To tundaga lokacin, k'halipha yakedan k'irnan akai akai, amma wata alaka da tajibanshi soyaya b'ata taba shiga t'sakanin muba mukan dai danyi fira irinta yan uwantaka. tareda bashi laba rurrukan na abunda kefaruwa, acikin f'amily dinmu.wannan kenan.


To ahakadai cikin f'argaba akayi nasar fitarda cikin akayimata w'ankin ciki alokacin kuma "uncle justice" yake tambayata y'aran nakecemas ai muntsaya g'idan mai martaba mun sauke su.
Baba mairo ce t'ace dashi y'akamata azuba mishi abinci yaci ganin duka duka yau t'unkarin safe baici komaiba. y'ace mata ah'ah shi bayajin yunwa, yanxu, araina nace, ainasani Auntie tanacikin wanna halin to bakuwa zai iyya sakama cikinsa komaiba.
sai wajen kamar misalign karfe 8:00 nadare, tukunnah, akafito da aunty raheema. zuwa dakin hutu, kama wani hukunci na Allah ta war ware kamar ba i'taba atake nan tace azubamata abinci taci.


B'aba mairoce ta taimaka mata zuwa toilet, ta gyra j'ikinta ta chanza kaya, taa waanke baki, suka fito kuma fitowar tayi dai dai, da shigowar "uncle justice" baki kawai yasake yana kallon ta! da saurinsa yaje ya tarbesu. baba mairo tasakar masaa ita, takoma toilet damin ta d'ankyara innada t'abaci Murna duk ta kamashi ganinta bakamar yanda yayi tsammaniba.


Ni kuwa nazuba mata abinci, nabata "uncle justice" ne yakarba yafara bata. ahankali tana amsa hartadanci da dama tukunnah nahadamata tea mai kauri t'ashanye, duka uncle sai murna yake yaushe rabonta da chin wani abinci haka, tun kafin samun cikinta wata biyu cikin na ukku k'enan


Ganin tadan fara samun natsuwa sai anan nima nagayar da ita, naimata yajiki, kuma nake cewa kuma yanxu aunty shikenan duk w'ahalar da k'ikasha da cikin nan naso kwarai ace little tasamu k'ani ko k'anwa Aunty Raheema tace akul dinki kar nasake jin ire iren wannan M'agana abakinki fareeda kefa malamce, anya bakida nafsine akanki da har k'ikeyin irin wannan maganar atake anan nafara i'stigfari nima t'ausayinki ne yasani fadin hakan amma Allah k'ayafe mani.


Aunty tace namika mata cooler abincin, nahadomata da ta miyar da p'late namika mata, malemalin tuwo hudu dama nasaka da zamu zo, Aunty tachi daya, saura u'kku namika mata tashi t'ayi ta wanko h'annu tadawo saman shimfidaar carfet din damukazo dasshi dazu, t'azaunada ido tayima "uncle justice" umurni kkamar wani yaro y'akaraso inda take.
alokacin nikuma nakabbara sallar magriba, dabansamu nayita c'ikin lokaciba, ayayinda baba mairo tafita tazubarda kayaan k'azantar dasuka bata a toilet din.
da hannunta tafara dibar abincin tafara bashi yana karba nikam kobayan, danagama sallah. banjiyoba na kallesu bama ballantana nasan irin wainar dasuke toyawa. kaf y'achinyeshi kuwa dama nasan za ayi haka amma d'onma yana asibitine d'omin idan agidane aka ida malemali hudu zuwa biyar y'ake cinyewa y'atashi su maman fareeda ne tareda ummu salma da baba mairone sukayi sallama suka shigo, wanda duk dashogowarsu bai saka Aunty raheema, tayi niyar daina ciyar da "uncle justice" ba diba wanda dama shima annashi bangaren hakan badamunsa yayiba, hakanan kuma sumadin su maman fareedar hakan badamunsu yayiba. inda sabo kowa yasaba da halin "uncle justice" din kusan sunsaba ganin haka haka kuma kowama a f'amily y'asani idan har aunty naga wuri kuma l'afiyarta klau to tabbas "uncle justice" baiya chin abinci da hannunsa.
sam sai dai tarika bashi, wanda koda alokacin b'ukukuwan sallah ne, kuwa wanda duk family suke haduwa afada, a inda akehada kwarya kwaryar liyafa ta dangi kawai nakusa d'ana nesa ayita nisha did a annashuwa da k'uma sadder da zu,munchi da kuma wanzar da k'auna,
inna matukar son w'annan taron nagidan mai martaba inda nima k'aina idan akace sallah saura kwana u'kku nake t'atara yinawa y'inawa natafi gidan k'asncewar akwai yara yan mata, d'ayawa agidan yasa wanda yakasance cewar wasunsu j'ikokin gidanne wasunsu k'uma ya'yan yayye ne dakannan da yan uwan mai martabar ne, rikonsu ake agidan.


*⚖️UNCLE JUSTICE⚖️*


*STORY WRTTING BY UMMU SHAREEF*


*DEDICATED TO UMMU SAYYID*


*A FIRST TIME WRITER*


*WANAN LITTAFIN NAKUDINE*


*KIBIYA 300 TA WANNAN ACCOUT NUMBER HAFSAT ABUBAKAR SADEEQ FIRST BANK 3195366407*


*KO KITURODATA TA 300 KO KATIN WAYA NA 200 ZUWA GA WANNAN LABAR TAREDA TURO SHAIDAR BIYA* *08036833612*


*ZAKITURO DA SHAIDAR BIYAN KUDINKU TA* *WANNAN LAYIN [08036833612]*


*KIBIYA HAJIYA KIKARAN TA ZAKI KARU DA ABUBUWA DA DAMA WA NAN LABARIN*


*LABARIN KUMA* *KAGAGGE NE BA AYISHI DOMIN WANI WATA KO WASUBA.*


*IDAN KINSIYA KINKARATA KIKABAMA* *YAR UWARKI KAWARKI KOKIKA TURA A GROUP* *HAJIYA NAYAFEMIKII*

*IDAN KINA DA HALI DAN ALLAH KIBIYANI HAJIYA TYPING AKKWAI WAHALA*


*DUKKANMU MASU* *LAIFINE ALLAH YA YAFEMANA*

*FREE PAGE*
*x*




M'unsauka jidda, damisalin karfe shidda na asuba, bayan yanshige da fice takwas zuwa tara mukama hanyar madina a madina k'wnanan mu biyu muka dauki hanya zuwa cikin garin makka, a mustalifa muka tsaya mukayi wanka muka dau harami umara, sai alokacin naga yanayin tsarin zaman namu yachanza, inda "uncle justice" da daddy suka kasance agaba, ayayinda nida Aunty Raheema muke atsakiya, sai baba mairo da little a seat din karshe abaya, duk daya kasance tafiya ce mai nisan gaske, amma ahakdai muketa tasbihi a zuciyoyinmu, a yayinda "uncle justice" nashi yake dan baiyane shida da daddy. nidai lokaci lokaci nakan danyi dariya aciki aciki. don banason Aunty tajiyoni duk da haka saida tajiyoni din kuwa, tajiyo takalleni, acikin mamaki ita kanta tasani wannan bashine zuwana hajji ko ummura nafarkoba, ballantana kotace tsananin murna ne yasakani dariya nikadai, nikuwa azahirin gaskiya "uncle justice" ne nakeyi ma dariyar keta ganin ko dazun kafin mushiga harami sai wani nanikema Aunty Raheema yake, amma yanxu komaganar k'irki bayaso t'ayimai saidai k'aji yace uhmmmnn na masu sallah araina nace wani wan wani rahi wan tudu, wata kila dalilin kenan da sam bayabari suna zuwa aikin hajji tare.
Gundun kar yasha lilon banza ita saidai tawuto cikin tawagar gidann sarki.


Wata dariyar nakuma k'yalkyatawa dana tuno dahakan Aunty Raheema takasa shiru, tana tambayata k'e l'aifiyar ki kuwa dariya haka nace mata nima wani shirmen little da daddy ne natuno, itama tadanyi dariya, tace ai wani lokachin idan suna dramar su yanda kikasan zamanin su golobo da yar mai albasa, d'uk mukasa d'ariya.
Mun iso kusan asuba sabodahaka wanka kawai mukayi muka wuce aharami, munada kwana biyu da zuwa makka su Ammy suka iso da khalipha, ayayinda su mai martaba tawagar su mai martaba sai sallah, saura kwana hudu zasu iso.


Kusan a hotel daya muke dukkan mu harda su kalipha, ranar sallah munzagaya sosai a wurare daban daban, nashakatawa kuma kusan duk inada mukaje sai Ammy ta umurci nida khalipha da muzo tadaukemu hoto tare, wannan kuwa yasa har araina nafara zargin wani abun daban, munyi shirin komawa gida ranar lahadi inda yakama exactly twoo weeks mukedashi a saudiya, to tun jumu'a da dadare kalipha yamatsamun sai narakashi yayima yan uwa abokanai da classmate din shi tsaraba. kusan kasan cewar nitun amdina nayi tawa tsarabar domin inna son kayan madina sosai fiye dana makka, ko jidda, kayansu mostly are "uniqe" sunada high quality, sai dai da akwai ban bancin farashi na madina sunfi tsada sosai fiye da na makka ko jidda,
munshiga manya manyan shaguna, na tayashi ya zazaba amma saidai wasu yakance na barshi shi zai zaba da kanshi. na matar da yake masifar so ne zai aura. yazazabi wasu yan ubansu jalabiyoyi masu matsakaicin tsawo da English wears da Pakistan daa sari ganin duk ba size dina bane yasa nasamu relief, domin ni sam bana son koda badan uwana bama naga maganar soyayya tashi ga tsakaninmu dasu, bashiry mataba.


K'wayane suna tsokanata da cewar banida "feelings" saida muka zo wurin gold yazabi wani dubai masu kayua nima kuma yace nazaba inna dasu amma duk daha banmaida hannun kyuataba nazabi wasu englis gold sirara kasancewar nibana son nazabi abunda yakeda hayaniya sosai, ya dauko wani yakaramun dashi yace wannan na alkawarine. inna son dan Allah duk sanda zan naimi taimakonki zaki taimaka mun,
domin da akwai wani abunda yane so araina Allah yabanishi cikin tsananin rudani da bugun zuciya nazubamishi ido, ganin kamar na razana ne yasaka yace ah bafa wani abubane wanda zai bata miki rai ba. ko yabata miki cikar burinkiba ko yatarwatsa miki tasarin rayuwarkiba, sai asannan nayi ajiyar zuciya naji wani relief domin nasancewa khalpha yasan komai ayanayin tsarin rayuwata.

B'ayan munkoma g'ida muka shiga hadar hadar hada yanamu yanamu zuwa gida
yau asabar inna k'wance ne asaman jikin ummina tannayimani tsifa tunda dama ni mutunce mai som kanana kitso, kasancewar inna da cikar gashi da tsawo shine dalilin da yasa idan nayi kitso yakanyi sati biyu harma ukku wani lokacin, kan nakoma yin wani. muna yar fira amma galibi firar tamu tafi raja,a akan karatuna. da ire iren kawayen danake haduwa dasu da halayensu, dama lokaci lokaci ummi na takanyi mun ire iren wadannan tambayoyin, domin son sanin koda akwai masu gurba tataciyar tarbiya anake tare a su kasan cewar zamani yanxu yazama sai addu,a tareda sanya ido daga iyaye.
Muna haka abba yasamemu natashi da sauri nakarbi kayan da suke a hannunsa atake kuma har muna hada baki da maman fareeda gurin yimasa sannu da zuwa, sakon hannu nah kuwa maman fareeda ta umurceni da inje inkaiwa ummu salma, dama sunriga sun saba da ko aranar a baranar girkinki bane aka iya baki rabo ba dole sai mai girki bace zatayi girkiba ko rabon abu idan ankawo
naje nasamu ummu salma, a kitchen tana ta kokarin hada abincin dare ita da khairat ayayind ita khairat din tanata kicinniyar hada drinks dama nima hutune aakabani nakwana biyu a kitchen din ganin muna gab a fara jarabawa yasa ummina tace an daga mun kafa a hidimar gidannan domin nasamu natsuwar yin karatun jarabawa, sosai nayi sallama nashiga nace umma salma sannu da aiki bata kaiga amsawaba naji rankwashi mai shiga rai asaman kaina, da karfi cikin sauari nasaki ledar hannuna tuni kifin tarwadar dake cikin ledar suka zube a lokaci daya kuma inna mai taba wurin tare da yarfe hannu na ayayin da ummu salma ke bina da wani mum munan kallo, tuni nama kuwa har hawaye sun cika mun ido, waike wace irin yarinya ceke dashegen mantuwa, saunawa zangaya miki bakyui mace idan tana tsifa tshigo madafi, ba kallabi har yaushe zakiyi wayyau ke ce babbaba amma sai tarin wauta, cikin ranki sai dana bari tagama fadan tukunnna natsugunnah har kasa nabata hakuri. wata tsawa tadakamun tuni jikina yafara rawa tace bazaki fitaba sai kinbatamun sanwa, k'insan illar gashi kuwa idan yashiga cikin abinci wani zai iya wuni y'ana amai, idan har yaga g'ashi acikin abincin sa tuni ummina haar tajiyomu tashigo kitchen din, tace habamana mamaan khairat k'ema kinsan mantawa tayi. ayimata afuwa dama ke ai bakwa gaanin laifinta kome zatayi adai y'iman afuwa dai kar ahanaumu wannan kyakykawar sanwar da tun kafin asauke kamshi yacika ko inna acikin gidan.


Dukkan su sukayi dariya ummina kuwa tariko hannuna muka bar wurin yau muka fara exams. inada muke rubuta jarabawar first semester, anan school of nursing, and midwifery saboda haka tunda wuri yau zan fita, amma tun jiya jin jikina nake yayi matukar sanyi.dama haka nakeda tsoron jarabawa, tun muna secondary school, duk idan zamu fara jarabawa sai nayi dan gajeren zazabi, na tenshin duk da dai cewa bawai inna tsoron bane. domin ban iyaba ko banyi karatuba ah'ah inna da kokarina dai dai misali, "resuld" dina nayin kyua hallita tace haka inna da yawan tsoro ne, kuma ma gashi balaifi abbanmu yana kokari sosai wurin siyamana kayan da yadanganshi harakar ilami. ga kuma tun jiya nakasa chin wani abincin kirki. sai mai ruwa ruwa, sanin halina na far gaba yasaa maman fareeda tun dasafe da hadamun kunnu gyada, maidan kauri. tun da safe ta tsareni sai nashanye kafin infita.

Mungama exams, ranar alhamis ranar jumm,a saai naji sallamar "uncle justice" dama muna dakin ummina dukkanmu hadda su khairat Abba ne kawai baya nan saiga "uncle justice" yayi sallama wata irin faduwar gaba tasameni, har saida na dora nannunah nadama asman hanuna nadamah asaman kirjina.
A raina nace ya Allah inna tsananin tsoron wannan halitatar taka, inna ga hakan bairasa nasaba watakilla da yanda jininmu bai hadu dana juna ba kuma ni tunda nake bantaba ganin yana dariya ba, hana rantsuawa nataba gani sau biyu yana murmushi ga yanayin girmna jikinsa da yataimaka yafito da tsawonsa ga fadi ga karfi domin duk illahirin jijiyoyinsa sun fito ko inna ajikinsa radau.




*⚖️UNCLE JUSTICE⚖️*


*STORY WRTTING BY UMMU SHAREEF*


*DEDICATED TO UMMU SAYYID*


*A FIRST TIME WRITER*


*WANAN LITTAFIN NAKUDINE*


*KIBIYA HAJIYA KIKARANTAZAKIKARU *DA ABUBUWA DA DAMA*
*WANANAYAN LABARIN*


*LABARIN KAGAGGENE BA AYISHI A*
*DOMIN WANI WATA KO WASUBABA*


*IDAN KINSIYA KINKARATA KIKABAMA YAR UWARKI, KAWARKI, KOTURAWA A GROUP NAYAFEMI,*


*IDAN KINA DA HALI DAN ALLAH KIBIYANI TYPING AKKWAI WAHALA.*


*KIBIYA 300 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 3195366407 HAFSAT ABUBAKAR SADEEQ FIRST BANK*


*KO KITURO KATIN WAYA NA 200 TA WANNAN LAYIN TAREDA TURO SHAIDAR BIYAN KO DATA TA 300 08036833612*


*DUKKANMU MASU LAIFINE ALLAH YA YAFEMANA.*


*FREE PAGE*
*xi*


D'uka suka hada baki gurin amsa masa sallamar sa, saida y'ashigo yasamu wuri yazauna, san naan yagaida umma salma, sannan suka gaisa da Maman fareeda, ayayinda khairat sadeeq da aslam duk suka gaiyar dashi, nikuma d'ama inna kwance ne asaman doguwar k'ujera, nakoyi sauri na rufe i'dona adole ni barci nake.


J'in umma salma tayi gyaran muraya, yasa nayi saurin tashi z'aune d'omin nasan cewa gargadi biyu take mun, nafarko saboda ba mayafi ajikina, nabiu k'uma bangaiyar da "unle justice" ba tunda su sunsan cewa ba barci nake ba.
domin nicema mai basu labari kafin s'higowarsa najuya batareda nakalleshiba nadan rusuna nagayar dashi, fuskarshi k'adaran kadahan ya amsamun, natashin kawai nashige d'akina tareda khairat a yayinda sadeeq da aslam suka fice kofar gida. wurin buka basket ball.


Ummaa salma tatashi takawo masa ruwa, ta barshi suna kara gaisawa da maman fareeda, ya kira sunanta kasan cewar har yan g'idan mai martaba dahaka suke k'iranta dan Allah wani dan taimako nikeson k'iyimani idan da hali tayi shiru tareda zubamai ido.

U'humm inna jinka "jawad" saida yadan nisa alamun damuwa duk sun baiyana ataredashi, t'ukunnah yace wata alfarma nake naima, k'ibamu aron yarki mutafi changidan domin tadanyimana yan kwanaki, domin maman su daday ce kuma balafiya munje asibiti sunce shigar cikine, amma shima kamar wancen sunce yana cikin hadari, Maman fareeda tanuna j'imami da damuwa tarda yimasa fatar Allah yakara sauki, yara kuma Allah yasa masu amfanine ya inganta raida lafiya cikin natsuwa y'ace amin
shirune yadan biyo baya zuwa chan ummina tanisa tace toh amma auta mai zaihana kaje gidan mai martanba asama maka wata daga cikin dangi, domin kaga mutanen nan dai dai gwargwado sunyimun k'awaichi, duk sanda bukatar hakan ta taso basu nuna g'azawarsu, karfa mukure hakurin su, mana jawad.
"Uncle justice" shima yayi wani j'im nadan wani lokaci shima kanshi yana duba lamarin, z'uwa chan yanisa yace to amma nida maman su daddy da sukansu y'aran duk munfi gamsuwa da zuwanta, saboda ita kadaice mai iyamana muduka ummi tace to ko cikin kannanka dake gidan mai martaba, dakaje kabukaci daya tazomuku yadan kauda k'anshi gefe yace kinfa san su wadan chen basu aje komaiba sai bama masu aiki umurni, da order dasaka aikin y'ikaza, yikaza ummina tadanyi dan t'saki tace dahakan kam.
toh amma kaima daine jawad, kafiya yawan chi duk wani abu mai nauyi shine abinchinka, sukuma y'aran yanxu yawanchinsu sai bakar kyuyah da shegen lalaci,
ummu salama ce tashigo da tray na coololin abinci, ayayinda khairat kebinta da tray na kunnun aya da cups. sai fruits yankaku tayima uncle bismillah, bawani j'an aji kuwa yaja cooler abinci yafara aunawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login