Showing 21001 words to 24000 words out of 108344 words
Chapter 8 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt
haka, har zuwa ake a tazama tsuntsaye idan suka tashi suka nufi gabasa toh magana yayi akwai al'amun sa'a (Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama,Yasha fama da Jahilai), sai ilimi taurari shima tun wancan lokaci sukayi imani da shi, amma zuwan Musulunci ya haramta wa kowa, shi kam zaku iya duba cikin kitabu Tauhidi, sabida babu mugun ilimin irin masu ilimi taurari, bansan yadda zan muku bayanin ba but yadda malama tayi mana bayani ta tabbatar masu ilimi suna da mugun sani akan gobe shi yasa Allah subhanahu wata'ala yayi hani da zuwa gun masu duba tsafi, duk aka sasu a Shashi shirka_
*Idan nayi kuskure ku gyara min barnan da nayi Nagode 🙏🏽*
9.....
"Kaje kanemi ilimin kare kan da al'ummar kasar ka, tabbas zata zo. Zata rusa wani aikin zata."
Shiru tayi tana kallon wani gefe sannan ta cigaba da cewa.
"Ban san ta yadda zan maka bayanin ba, amma ka bata wannan zoben. Ya take taya zata zo ban sani ba amma zata zo abisa wani kyakkyawan fata kuma zata yi nasara"
'''' Tunda ta bashi zoben ya saka a cikin aljuhun rigarshi, bai kuma bin takan zance ta ba.
Mata da yawa an kawo su cikin masarautar musamman bangaren shi aiki, bai taɓa ganin wacce ta iya kallonshi ta gaya mishi magana sai Safinah, ita ce ta an karar dashi dukda yana sane, dan Bayan abinda Kakan Ghaniyu ta gaya mishi, Baban Ghaniyu ya bashi shawaran ya tafi niman ilimi Addinin, shine dalilin da ya sashi tafiya Saudiyya karantan Islamic law, a shemaranshi na biyu ne, ya dawo samu labarin mutuwar Hakeem, lokacin Ghaniyu yana shekarar shi ta karshe a makarantar horan Yan sanda, amma haka aka yanke mishi karatunsa, ya dawo yana kula da lafiyar Ashraf,
Abinda Ya fahimta shine ba mutuwa Hakeem yayi ba, kashe shi akayi, dan haka ya shiga bincike amma bai samu kome ba, da zai koma ne yake Ghaniyu suka tafi,
Bayan ya kuma nimawa Ghaniyu damar karasa karatunsa. Na dan sanda a nan Saudiyya, sai da suka kwashe shekaru uku, sannan suka dawo, rana da suka iso suka haɗu da Fahad.
Shima Fahad Baban shi yayi aiki da Sarkin Abdullahi mahaifin Ashraf, wani ziyara da ya taɓa kawowa Ashraf, har yaso gaya mishi wani magana, bai samu damar haka, toh a hanyar komawarshi gida aka sami gawarshi.
Dan haka Fahad ya basu shawara su shiga aikin tsaro kasar, amma dole sai Ashraf yayi amfani da ƙarfin ikon shi dan a basu aikin sirri,
Fahad ya karanci ilimin kimiyya computer, dan haka Ashraf da kanshi yaje har ofishin ministan tsaron da shugaban kasa, aka basu iznin shiga aikin.
Kuma dake suna da goyon bayan shi basu wani gardama ba, inda a ranar aka kirkiro, Jordan 26 Agent, inda suka sami wasu tsofin sojojin da yan sanda, da kuma masu aiki a lokacin, aka shiga basu hoto na musamman,
Sun same shekara biyu suna samun horo, kafin suka gama, Ashraf ya dawo ya cigaba da zama a matsayin Sarki, a idanun jama'a. A gefe guda kuwa yana aikin bincike sosai.
Babbar matsalarshi yana niman inda mahaifiyar shi take, tunda yana zuwa Oman kuma suma suna zuwa masa, kwatsam sai ga Alie ya kai Safinah zai sayar da ita, daga cikin mutanen da suka ja motar, har da Fahad shine Yaron kazab, shi yasa biya kuɗin ta.
Hotonta ya ɗauka ya turawa Ashraf, yana ganinta. Ya fara binciken akanta anan ya fahimci yar jarida ce, kuma ta b'oye bayyanta. Sake turawa Fahad sako yayi akan daga wani yanki tafito.
Shi kuma ya turo masa da cewa.
Daga Senegal, murmushi yayi bai kuma bin takanshi ba,dan shi yasan koma a binciken da yayi dukda rufe information ɗinta, sai da yasan yadda yayi hanking ɗinta ya fidda kome akanta, printing din hotonta.
Tunda ta shigo gidan yake jiran ta inda zata fito mishi, bata fito ta ko ina ba sai ta masa katsalanda a cikin al'amuran shi, haka yayi mishi dad'i, ita ce mace ta farko da ta sanya shi farin ciki ta hanyar gaya mishi gaskiya, taurin kai, kafiyarta haka ya matuƙar burgeshi.
Gabaki d'aya rayuwarshi babu mace dan shi abinda ke gabanshi ya hana shi fahimtar wata mace.
Sannan shi bai fara sonta bayan ya sameta ba a'a sonta ya fara ne daga lokacin da Fahad ya turo mishi hotonta, Dan Koda ta fara aikinta da gaya yasa aka ki bata d'aki, kuma ya shiga bata aikinta wahala, kuma sai yaga bata damu ba.
Da kuma tasowa tsoma kanta Cikin sha'anin shine ya sa ake ta bata wahala, dan Ghaniyu yasha mishi magana da a sassauta mata, akan haka sai da ya bawa Ghaniyu hutun sati biyu, dan haƙa ya cigaba da zuba mishi Ido,
Abubuwa da suka faru daga farkon labari har zuwa, rape ɗinta da yayi. Lokacin da Ghaniyu yazo ya samesu fita yayi yaje ya tawo da Fahad da kuma, Azrah ita tazo ta sanya mata kaya, Ghaniyu ya dauke ta zuwa can shashin bayi, Fahad kuma da wasu kartin maza suka riƙe Ashraf wanda suna tashinsa ciwon ya kuma tashi,
Danne shi sukayi aka fara aikin, basu fadi wanda ya turo su ba, a haƙa suka fita.
Bayan ya farka ne yake gaya musu mafarki da yayi, sunkuyar da kai yayi tare da rike kanshi.
"Na cuci kaina na zalunci yarinyar da bata zo dan cutar dani ba."
"A'a Sultan ka bar fadan haka, kaddara ce kuma babu wanda yafi karfin haka "
Sun ɗauki lokaci suna nuna mishi yarda da suka yi da shi.
Sai abubuwan suka faru daga lokacin har zuwa yanzu.
Tunda da abin ya faru ya shiga damuwa, a hankali ya fara fahimtar sauyi daga gare ta musamman yawan amai ko tayita amai, dukda yaso ta bashi haɗin kai a dubata taki, karshe har ta zuba mishi guba, a cikin abinci.
Bayan an rufe ta yasa aka dauko mishi kayanta nan yaga passport ɗinta, wani abinda Safinah bata sani ba, ai Ashraf yasan cewa guba zata sa mishi, dan haka da ta kawo shayin bai sha ba, sai ya zubda a kasar table, sannan bakin shi dama ya kuntso kumfan brush ɗin da yayi (🤪😜😂🤣 mugu) da taga yasha dan har kekenshi take, shi kuwa bayan wasu lokuta ya fara fidda kumfan, ganin haka ai kuwa ta fara ihu, kuma dama sunganta. A Cctv shi da Ghaniyu da Fahad, ganin yadda ta rude ga Ashraf a kwance, su Ghaniyu suka fita da ita zuwa gidan kaso.
Shima ya tashi yana wani murmushi miskilancin, sannan yace.
"Zan kwanta dan nasan yanzun motar asibiti zasu zo, Kuma Hikimarku tayi dan bansan iya mutane da aka kashe sabida Ni ba."
Yana kwanciya sai ga Ukshe da Abu Zarri
A hanzarince suka nufi dashi.
Daga nan har abinda ya faru na barishin Masarautar da ita,
Lokacin da yaji labari bata da lafiyarta, yasa aka dubata nan suka tabbatar da tana da ciki na kusan sati Uku shi kuma yana don maida Ita gaban iyayenta, gashi ya son zuwa amsar takardun shi a Saudiyya. Kafin su bar kasar sai da yayiwa Dr Fu'ad magana, shi Kuma ya haɗa shi da Hameeed.
Da farko Hameeed yaso bayyana mata gaskiya amma ganin tana cikin damuwa yasa shi yasa bai fada mata aiki aka sashi ba.
Koda Ashraf ya dawo ya samu tayi nisa a soyayyar Dr, abin ya bashi haushi, duk yadda Dr yaso mishi bayani yaki sai da ita ta nuna bata yinshine, yasa shi hakura.
Amma maganar gaskiya Ashraf bai so ta auri Dr ba. Amma ganin haka zai iya haifar mata da farin ciki ya sashi, hakura sai zamanta da Dr shima dai ya kai zuciya nesa ne, amma kullum sai yaje Asibiti jin yaushe zai sake ta. Abinda basu saka shi cikin tsarin ba Anim wanda fatalwansa ya sabbin rayuwarta..
.....
Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara kwanciyar shi.
Yana tsananin kewar tsiwar rigimarta yanzun yasan tunda tace sai ta nime shi.
***
Ina kwance inda nayi sallah ban kara motsawa ba, barci yayi gaba dani. Saboda jiya ban samu barci ba.
Shafa min kan da ake ne ya taddani a barci, a sannu na buɗe idanuna, Ummi na gani tana zubda hawaye.
Tashi zaune nima ina kallon ta, yadda take kuka taba bani hakuri, murmushi nayita na ciwo, sannan na shiga labari abinda Hameeed suka min, ita ma kuka take ta bani labarin haukacewar da Mamie tai sakamakon Kama aljani ta.
Hakuri tayi ta bani tare da gaya min sharrin Mamie ce.
***
Lokacin ya tafi dan har na koma gida, na cigaba da zaman idda, sam bana jin daɗin kome.
Kwanciyar tashi asarar me rai, yau nice saura wata ɗaya na gama idda.
***
"Don Allah idan laifi na maka ka gaya min. Kusan wata uku da zuwa na amma kamar wa."
Mika mata hannu yayi, ta tsaya tare dayi ƙaramin tunani kafin ta taka zuwa gabanshi, sanya hannunta tayi cikin shi sannan ya ajiye ta bisa cinyar shi..
"Natasha ba lallai bane ki gane halin da nake ciki ba, saboda ke Ni kike so? Ni kuma zuciyata yana gareta, taya zaman mu zai haifar da da mai ido.
Gashi ta kusan gama iddarta ina so samu ne, zan sawwak."
Rufe mishi baki tayi da hannunta.
"Wallahi zan iya zama da kai Indai zaka rike aurena, ka rufa min asiri, kasan ba karamin abu bane zai sa miji ya saki mace, a cikin tarihin masarautar mu ba a taba samun ba, don Allah karka sa a min kallon wacce bata san darajar kanta ba, don Allah kayi hakuri Ni na yafe ma bazan kuma maka magana ba tunda ba kaso, Allah ya baka Safinah."
Yadda tayi maganar sai da tsigar jikinshi ya miqe, sabida muryanta rawa.
A hankali yake kewaye hannunshi a tsakanin k'uib'inta zuwa shafafeffen cikinta tare da manna mata, kasancewarta me karancin shekaru, dan haƙa ya dauke ta zuwa other room (🙄😜 Yau ma nasan haushi zai kama wasu naki leka d'akin Don Allah ku rabu dani bazan leka ba wato kai ena Kubar turani 😏)
(A fito lafiya AshTash)
***
Muna zaune a falo yau na tashi da kewar Yarana da suke gurin Nannah, kamar wanda aka wurgoshi na ganshi a kaina!
Waye kenan
Assalamu alaikum
_kuyi hakuri ina ta zirga zirga ne Insha Allah zaku samu zuwa dare Nagode 🤝_
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
10.A firgice na tashi ina kallon shi.
"Don Allah ki yafe min! Safinah nayi da nasanin biyewa Ashraf."
Ban kalle inda yake ba na yi zama na ina gyara farcena, ganin baki kulashi ne yasa shi matsowa kuwa dani zai tab'a Ni na saka mishi tsawa tare dace.
"Wallahi ka kuskura ka taba sai na baka mamaki. Kuma ka fita mana a gida Hameed ko nasa a fitar min da kai, kaje Ashraf ya cigaba da juyaka."
Ya kasa bani hakuri haka yaja tsunami rayuwar shi ya fita daga gidan mu.
Kwallar da suka tawo min na maida dan nayi alkawarin bazan kuma wani kuka ba, kuma dole nima na rama duk iskancinsa da suka min.
***
Rub da ciki yayi bayan ya gama turmusa Natasha wacce take matsar kwalla, idanunshi jajjur ajiyar zuciya yaƙe saukewa,. tsabar damuwa da bakin ciki bawai dan bai same yadda.yake so bane kawai kishin Dr yake
Musamman yadda ya fahimci mata daban daban ne,.wasu duk gyara da zasu yi bazasu kai wasu bata tabbas SAFINAH mace sama da kasa, mace da duk namiji da ya rabu da ita sai ya fahimci haka, sau d'aya ya makale mata ya fahimci ita tana cikin mata na musamman.
_Yanzun haka Hameed yaji lokacin da ya aureta?_
Haka yayi ta sakawa da kuncewa.
Tashi yayi tare da saka kayan shi ya fita daga d'akin.
Binshi tayi da ido kwalla na kuma sauka a idanun ta.
***
"Hameed! Baka kyauta min ba, karasa wacce zaka yaudara sai Safinah yarinyar da ta yarda da kai sama da kome shine ka zauna ka cutar wai kana gaya min maganar banza."
Haka Ammah tayi mashi wankin babbar bargo.
Ya Kuma tashi ya bar gidan likita ba sauki ba, shi kanshi ya san yayi kurakurai amma dole ya nemi ya yafer Safinah.
***
Wani abin takaici shine jinin karshe da zai tsarkake ni daga rayuwar Hameeed yaƙi zuwa dan har kowa ya shiga tambayata ko na gama idda, shiru nayi ban kuma cewa musu cikanku ba.
Duk yadda bawa yaso da rayuwarsa ya kasance sai kasamu matsala, rayuwar da babu tsarin Allah a cikin sa shirme ne, kuma duk rayuwar da babu jarabtar banzan rayuwa ce, kai kanka kaji cewa Allah ya halicci kane dan ya gwada ƙarfin ikonsa da buwayarka, shi yasa a cikin Alkur'ani (Allah subhanahu wata'ala
Yace ku zaga duniya kutafi kuga abinda baki taba gani ba, tayi hakan ya zame muku Aya da izinin.)
Ai basan munje da nisa ba ko a iya inda muke munji kuma mun bika, don koda a Film ban taɓa kawowa Ashraf zai buga wasa dani ba, shine coach din, shine reapre, sannan ya haɗa team. Ba kome ya janyo haka ba, sai dan ya fitowa cikin mugayen mutane.
Sam babu tausayi ko imani sai tsantsan son kai, da mulki, indai har na sanya shi ya bar wasu dabi'a tabbas dole na gama idda domin na saita shi yadda zan zan ji daɗin. Ya ajiye izza da mulki,
*Ta ya?*
Na tambayi kai na! Lumshe idanuna nayi kafin na kuma buɗe su, akan window d'akina.
Hanyar sanya shi fita niman kuɗin aurena, matukar Ashraf ya iya kawo Sadakina a cikin wata uku, zan iya auranshi, amma dole yayi wasa da hankali shi nima, yadda zai fahimci nima ba saukine dani ba.
Lumshe idanuna nayi tare da gyara kwanciyata, ina jin na kama Ashu dam a hannuna zan amince masa ne bawai dan ina sonshi bane, sam bana sonshi sai dai ya zame min dole na gyara halayyar shine.
Sai da nakusan cinye