Showing 9001 words to 12000 words out of 108344 words

Chapter 4 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt

27 Nov 2024

4808

tashi zaune, a tsakiyar gadon zuciyarshi ba dad'i taya zai zauna a Oman Bayan shi yanzun baya kaunar dukkan wata alaƙa da mulki, sam ji yaƙe ina ma bai haɗa Nasaba da mulkin ba, da yafi mishi alkhairi. Zai iya cewa tun tasowarshi bai taɓa niman abu ya rasa ba sai ita, sabida ya taso inda ko kallon abu yayi za a kawo mishi. Da ace ya taso ne a gidan da basu kai haka ba, da bazai tashi a murdadden hali ba,
Wannan murd'add'en halin ya kai shi ya baro shi dan da bai nunawa Safinah ikon bala'i ba da yana nan tare da ita amma ina ya zauna sai juyata yake son ranshi,


Toh taya mazata amince min, ya jima yana saka da warwara, kafin kuma ya shiga ban daki yayi alola ya fito ya yadda sallah inda zai kai kukanshi gurin me dukkan, dan ya fahimci ba inda yake samun nutsuwa sai ya kai kukanshi ga rabbi.


Koda ya gabatar da Sallah ya jima yana kai kukanshi, tare da niman biyan buƙatar shi na rayuwa...


Ya jima a gurin sannan ya miqe, zuwa, dan ya fara jin barci.
***
Shakeni wuyar Mamie yayi cikin ɓacin rai yana kara matarsa yana cewa.
"Me yasa! Akan me zaku tashe ni, ina barci na, kusa min muradin wani bani Adam a cikin zuciyata, dole na ɗauki fansa kafin na koma makwancina, dole na cika mishi burinsa, ki tafi gidan ki kai wannan tukunya a matsayin kyautar da ita, Ni kuma zan bata kyautar da na shirya mata, sai na shayar da ita madaran bakin ciki wanda babu irinsu duk fadin duniya, kamar yadda suka sashi ya rasa rayuwarsa sai na sadaukar da ita na zubda jininta ga doran kasa, wucce ki fita kuma ki kawo min kawarki Salmah dan jininta zan sadaukar ga abin da nake bautawa."


Da sauri ta fita tana rike wuyarta tare da shiga ruɗani ganin abinda zata aika ta, jinin Salmah zata bada Innalillah.
"Na shiga uku! Yau na yadda abin da ya dame ni. Ina zan kai hakkin Salmah."
Haka ta dauki tukunyar tare da barin gidan, jikinta a mace.
Dole haka ta faru da su tunda sun nace sai sun jefa rayuwar wasu a matsala gashi Tun basu je ko ina ba tasu ce a matsala, garin k'iyayyar SAFINAH ta wulla kanta cikin cikin damuwa, taya zata kawo karshen bala'in da ta jefa mata rayuwarta, bazata kira haka da zanen kaddarta bane, sabida shi zanen ƙaddara Allah ne ke zana maka, ita kuma wannan ita ta zamawa kanta katon layi me girman gaske, ita kuma wannan ita ce ta zamawa kanta, bata jin badaru da Maryam zasu yafe mata, idan suka ji abinda ta aikatawa yarinyar da sukafi SO duk cikin yaransu, Domin son da suke wa SAFINAH daban ne a cikin yaransu, suna matuƙa mata wani irin sone na musamman.
Wannan dalili ya jefa mata k'iyayyar SAFINAH, dan gani take duk cikin Yaran badaru yafi fiffita SAFINAH akan sauran yaransa.
***
Tun da ta iso gidan dare yayi sosai, dan haka dakinta ta wuce, tare da kwanciya, ko sallah batayi ba,
Washi gari tana tashi. Ko sallah batayi ba ta fito daga gidan da tukunyar, sai gidan SAFINAH inda tasami me kula da gidan suka gaisa tace.
"Mutanen gidan suna nan kuwa?"
"Ayya Hajiya jiya sukayi tafiya."
Safe goshinta tayi cike da jimamin gulma tace.
"Ayyana ban sani ba, amma ga wannan a saka a cikin gidan furene me kyau zai kawata mata gidan. Kace inji Hajiya Kubrah."
Karba yayi tare da godiya, har ta shiga mota sai tayi tunanin kar ya bata matsala ta sai ta zuge jakarta ta ciro sabon yan dari biyar ta miƙa mishi take ya washe bakinsa, yana ta zuba godiya. Murmushi tayi tare da samun nasarar, sauran aikin ya ragewa Anim.
***
Yau kwana uku kenan da shigowar mu Poland, duk meeting din da suka shiga baya taɓa bari ya kai dare dan haka yau ina kwance a jikinshi da wata yakoluelwar riga, hannunshi daya yana aiki da laptop, daya hannunshi yana cikin rigata dai dai cibiyata, yayinda na Daura hannuna akan nashi, a hankali nake shafa hannunsa. Sumbatar kaina yace.
"Beauty! Kina son jiki kamar mage gaki da mugun tsoro, da zancen zamu haɗe yanzun zaki fara zaro min idanu."
Kwantar da kaina nayi cikin jikin shi ina murmushi mishi Sannan nace.
"My Man! Kaine ai baka da sauki da yanzun zance na amince wallahi da kuka zaka kyaleni, shi yasa tsakanin na da kai wasan kada kusadashine ruwa ne,"

"Ba wani nan, Beauty kina b'oye min wani abu, baki san Ni likita bane hala ko kin manta ne, sam baki samun nutsuwa dani, dan haƙa yau sai naga kin samu nutsuwa zan kyaleki."

Rau+rau nayi da idanuna, tare da rike hannunsa nace.
"Wallahi Ni dai ina samun nutsuwa da kai don Allah kar a kuma."
Dariya shi ya gimtse tare da jan hancina, yace.
"Hey! Lady ba zan fasa abinda nayi niyya ba, dan haka ki gama kukanshi an jima sai mun sake kulawa Sama jannati."
Miqewa nayi zan gudu ya riko hannuna yana dariya yace.
"Duk inda kika shiga zan biki dan Ni ɗin ai dai dai dake ne, yarinya ina son ganin yadda kike jan.."
Kamar zanyi kuka nace..
"Don Allah kabar fadan haka, wallahi kunya kake bani.".


"Wayyo Allah na, Beauty Ni kike jin kunya, lallai kuwa. Toh zo na cire miki kunya tunda ban cire ba a can rana, yau kuwa sai na cire naga karshe Kunya."
Aikuwa ya shiga min chakulkuli. Dariya nake har da shudewa, gaskiya Dr Zaki karshe ne a duniyar jiyar da mace soyayya. Bai wani damu da ya nome Ni ba, amma yana nuna a cikin birnin zuciyarshi nice babu wata umma akwai toh ya cireta, ya kuma bani zuciyar.
"Don Allah Baby! Ka bari zanyi fitsari wallahi."
"Karki damu kiyi sai muje kiyi wanka tunda kin bata mu."


"Wayyo cikina zai fashe wallahi ciwon yake min."
Murmushi ya sake, cikin son sanin inda yake min ciwo yace..
" Ina ne ke ciwon nuna min."
Yana cigaba da min chakulkuli, duk na firgice da dariya, dan ya kyaleni na nuna mishi gefen marana, bai fasa sai ma sauya salon chakulkuli da yayi ya shiga daura min tashi karatun zilewa nayi na fadi kasa, ina sauke numfashi.
Kankance idanunshi yayi a raina nace.
*Kai jama'a na hadu da aiki kai kuma naka kalar kenan*
Biyo NI capter din yayi tare da cigaba da murkushe ni.
"Wayyo Dr! Don Allah kabarni bazan kuma ba, wallahi na gaji da salon ka."
"Hmm Ni kuma ban gaji dake ba, ko nace naki wayon, haka kike min kina guduna."
"Allah bani kuma gudun ka."
"Kamar da gaske, Kuma kina ganina zaki fara zare ido kamar mara gaskiya, kawai rufeni idanunki na baki candy pop."
"Allah na koshi dan wannan candy pop ɗin bayi da dadi kai kaɗai kake jin daɗin sa, Ni kuwa bana jin daɗin sa."
"Hmm, zan koyar dake yadda ake jin daɗin, Allah kuma kika dame ni lokacin da kika kwarewa
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*


Oum Muwaddah......


MJ
BOOK-2
19-2-2020


✋🖕
Shafar fuskana yayi a hankali, lumshe idanuna nayi, tare da kwanciya sosai a jikinshi.
"Baby baka hakura bane!?"
Na tambaye shi, muryata na rawa.
Sumbatar kumatu na yayi tare da gyara min kwanciyata a jikinshi yace.
"A'ah ai ba zan iya fushi dake ba, kwanta ki huta."
........ Wannan halin ko ina kula da Dr yake min ya fara damun rayuwata, dan kuwa a cikin lokacin ƙalilan na zabge, na fita hayacina, babu shiri muka bar Oman, dan ha fahimci Dr so yake zuciyata ta buga haƙa muka dawo tattaro zuwa naija.
Dr Shabhan ne yazo ya dauke mu, muka nufi gidanmu. Tun daga nesa naga gidan ya koma kamar irin tsohon gidan nan. Duk wasu flower da aka saka a gidan ya mutu, kamar ba a mishi ban ruwa, haƙa Dr Shabhan ya shiga da motar shi ciki damu,
Tunda na kalli gidan sai da zuciyata ta buga, tsabar tsoron da gidan ya bani, bakina dauke da addu'a na amshi key na nufi gidan. Wanda yayi yanar gizo gizo.
" Gidan nan naku akwai matsala! Ina shigowa da motana na fahimci hakan."
Dariya Dr yayi sannan yace.
"Babu komai Wallahi, kawai kana dai tunanin hakan ne."


Duk yadda Dr Shabhan yaso fahimtar da DR yaki fahimta. Yana fita daga gidan, Me gadin ya bishi da mugun kallo tare da idanunshi da suka koma ta kare.
...... A sannu na shiga gidan na samu yayi kaca-kaca, ga hotunan mu a farfashe. Kome na gidan a juye fa. Safe goshina nayi sakamakon ganin wulgawar wani bakin kare, cikin yan second.
Sunan Allah na shiga kira a hankali har na shiga d'akina. Shima an lalata min kome, Ni abin ma tsoro ya fara bani,


Wasu irin abin mamaki nake gani dukda bakina dauke yake addu'o'i.
Dafani aka yi aikuwa na fasa ihu, da sauri ya rungume Ni tabaya yana cewa.
"Beauty!!! Nine fa"
Da hanzarin na juya tare da shigewa jikinshi, ina rintsa idanuna.
Ajiyar zuciya nake saukewa. Cikin damuwa nace.
"Nikam,"
"Ke kam! Me?
Cikin wani irin murya nace.
"Gidan tsoro yaƙe bani"
"Kai nifa banga abin tsoro ba kawai idanun ku na nuna muku wani abu na daban ne."


Duk yadda naso ya fahimta yaki dan haka na hakura muka fara gyaran gidan, sallah ce take tsayar damu, dake tasowarshi asuba ce sai muka iso karfe sha daya na safe.
Biyar na yamma muka gama aikin har da girki, tare muka ci sannan muka yi wanka gidan Ammah ya tafi yabarni a gidan, dake Ni ɗaya ce sai na kunna ta. Naga ana film din wani horror bai min ba sai na mai dashi zuwa, Saudi one sun kuwa saka karatun Alkur'ani. Cikin suratul ma'edah. A sannu barci yayi gaba dani wajen biyar da kwata.


Barcin ba wani nisa nayi ba, amma ba fara wani rudaɗɗaɗiyar mafarki na wanan karen da naga kamar gizo shi na bina da gudu, sai da yayi wuf zai kamani naga anyi sama dani, shi kuma yana kasa sai haushi yake.
Cikin salati na farka, dai dai Lokacin da aka wucce wuf ta window na, mikewa nayi naga ashe ina kwanciyar aka dauke wuta. Fitowa nayi na hango mai gadi yana zaune, amma kanshi a sunkuye. Kiranshi nayi da cewa,
"Malam Ali!"
Bai d'ago kai ba, na kuma kiranshi, amma yaki d'agowa sai da na isa inda yake na fara magana da cewar.
"Malam Ali ya ina magana kaki amsa min ko ba kaji ne?"
"Bani ne bana ji ba! Kece baki ji! Sai da na gargadi akan kowani namiji Safinah baki ji ba."
D'ago bakaken idanunshi yayi baya nayi tsoro ya kamani,
Horn din Dr yasani manta abinda na gani, dan shima mikewa yayi yaje ya buɗe get din sam na manta abinda na gani har Dr ya shigo gidan, gabaki d'aya kaina ya kule, ina ƙoƙarin tuno abinda na gani amma nakasa,
Jan kafaffuna nayi naje na bude mishi, fuskarshi ɗauke da murmushi ya fito yana cewa.
"Beauty! Ina can zuciyata tana gareki, gaya min keke faruwa?"


Kallon Malam Ali nayi naga baya gun, rungume shi nayi tare da kwantar da kaina a kirjinshi nace.
"Babu!"
A takaice, janye Ni yayi ya dawo dani gabanshi, yace min.
"Muna da bakuwa fa"
Juyawa nayi na hangonta tana zaune, a bayan mota sai wani d'aga hanci take.
"Wacece ita!?
"Yar gogg."
"Goggo Aminah ko? Hmm kace ta fito."
Magana ya mata ta fito tana yatsina fuska, tabe baƙi tayi sannan tace.
"Toh kayan fa? Waye zai dauka min!"
Juyawa yayi zai je kamar zan rike shi sai na kyaleshi, ya sauke mata kayanta muka shigo gidan,
D'akina na wucce bani takansu ba, dan matukar nayi haka tabbas bani da adalci, kuma kamata yayi na amshi ta, amma bazan iya ba kuma bazan wulakanta ta ba, nuna Mata dakin kusada nawa, ta saka kayanta.
Sannan ya shigo d'akina ya dame Ni na fito daga ban daki, ina tsaye zuwa gabana yayi ciki sanyin jiki yace min.
"Kiyi hakuri!"
Murmushi nayi sannan nace..
"Name fa!?
D'ago hannuna yayi ya daura a gefen fuskarsa, yace..
"Kiyi hakuri dai, na kawo miki wata gida."
Murmushi nayi tare da kai ɗaya hannuna din na tallafe fuskarshi nace.
"Ko ɗaya idan nayi haka na zama mara imani tamkar butulcin zan kira Kai na tunda ta ko ina. Allah ya bani nasara yan uwansa nima yan uwana ne, don Allah karka saka komai a ranka ina tare da kai."
Jan kumatu yayi sannan yace.
"Allah ya bar min ke!"
"Tare da kai!"
....... Kitchen muka shiga tare muka fara girki abincin dare, muna cikin aiikn muka ji kiran sallah rage wutar muka yadda abincin zai nuna, a d'akina mukayi sallah sannan muka tare, bakuwarmu na gani dauke da abincin da ko d'and'ana shi ba muyi ba, ta shake har yayi soro.
Ban kalle ba , nayi wucce wata kitchen na sauke sannan na juye na fito mana dashi, akan kafet na ajiye mana, dan jollop ɗin taliya ce,
Gabanshi na shiga na zauna, tare da ɗaukan abincin na kawo gefenmu muka fara ci, tsaki yarinyar tayi dan bata wucce Sa'ar Nanah ba,


Ni yake bawa abincin a sannu ina ci muna hira, yana gamawa ya na juya na fara bashi. Kamar yadda ya bani, muna gamawa na tashi zan Kai kwanikan ya amsa ya dawo dani, ya sannan ya dawo tare da tissue, ya goge min hannuna,


Nan muka cigaba da kallon labarai, har wajen tara sannan muka tashi zuwa cikin, wanka mukayi sannan ya sani nayi alola muka yi sallar Isha tare da shafa'i da wutir.
Muna idarwa ya riko Ni tare da zare min hijabi na, rage wutar d'akin yayi sannan muka kwanta.

"Kiyi hakuri da abinda Sa'ima tayi mana, bana son ace daga zuwanki har an fara samun matsala daga gareki, zata zauna na wata shida ne, yazo service idan tagama shikenan da."
Murmushi nayi tare da janye jikina daga nashi nayi rubda ciki, ina Son jin zafin abinda yayi min amma ba halin haka dole na juya mishi baya, yana tabani nace.
"Please barci nake ji."
Matsowa yayi ya kwantar da kanshi akan bayana, sannan ya zagaye hannunshi inda ya turani cikin jikinshi, lumshe idanuna nayi kwallar da nake b'oye suka fara sauka a kan matashin.
Jin yadda nake jan hancina ya fahimci kuka nake, amma bai hanani ba, sai ma kara k'amk'ame ni da yake.


A hankali barci yayi gaba damu.
00:1am na tsakiyar dare, agogon d'akin ya buga "katttt"
Gyara kwanciya nayi ɗan har lokacin ina kwance ne Dr na sama na.
Juyawa nayi a sannu, sai naji anan magana ƙasa-ƙasa, haɗe da kukan jarirai, abin mamaki Kuma a cikin d'akin nake jin maganar, sake ware idanuna nayi ina niman inda ake maganar, kuma abin damuwar sam baka fahimtar Abinda ake cewa. Jin digar abu a kumatuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login