Showing 63001 words to 66000 words out of 108344 words
Chapter 22 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt
yaga jikina arawa, ya fahimci dagaske ake, cikin airport d'in yaje ya amso min meatpie, ɗin ya kawo min. Tureshi nayi ina fad'in.
"Jeka dashi bana so bana so"
Rungume Ni yayi cikin damuwa yace.
"Wallahi ban san zaki yi kuka ba, da ban hanaki ba, akiyi hakuri kinji"
Dakyar suka samu nayi shiru, a take na cinye,na fara zare ido ina niman kari, b'ata rai yayi al'amun babu wasa, haka na hakura amma dan niman fitina na kwanta a bayan mota na fara rera musu baitotin kuka.
Haushi kamar ya rufe Ni da duka, Ghaniyu bai kai mu gida ba, sai gidan abinci ya fita shi da Fahad da yaran nan Ashraf ya juya ya fara balbalin bala'i, Ni kuwa na kara b'are mishi baki l, dan Wallahi yau rigima nake ji shi yasa ana min abu kaɗan sai kuka. Bakin ciki ya kara kama shi, juyar da kanshi yayi.
Kuma abinda na Fahimta cikin ne yasani haka, domin kuwa ba haka nake ba, bana kuka sai an b'ata min rai yau nice nake kukan banza.
Suna shigowa suka mika min laidar,
Koda muka isa gidan babu wanda yace min uwaki SAFINAH, nima ina jin rigima ban bi takansu ba,
★★★
Rayuwarmu tana tafiya ce abisa tsarin Ubangiji, komai ma haka a sannu a hankali cikin ya fara tasawa, tunda gashi ya shiga wata shida ina niman na bakwai, zamanmu ya sauya domin kuwa Ashraf yana ƙoƙarin bamu hakkinmu har ita Natashah wacce take ganin kamar karfinta yasa Ashraf yake mata komai, idan taba kafafa kallonta nake sabida bazan iya maida mata martani ko raddi ba, dan haƙa kawai zata shiga yiwa kanta kirari da gwad'oso.
........ Abinda bata sanin ba, mijin da take ihu akan shi, nice nake bashi kowacce shawara musamman akanta da Mahaifiyarshi, sai dai ganin cikina fara fitowa Nannah ta bud'i baki tace min.
"Bani da Yadda zanyi dake ne, SAFINAH da ko numfashi sai na hanaki shaka, na tsani Tarayyarki da Ashraf, bana sonki bana kaunarki ki fita a rayuwarsa mana."
Shiru nayi tare da murmushi sannan nace mata.
" Allah ya hucci zuciyarki"
Tabbas ina cikin damuwa sosai. Sabida Nannah tana son D'anta ita kuma tana k'ina a bayan idanunshi.
Lokuta masu yawa Zuciya kan sarrafa rayuwar mai ita, a yayin da take saka aikata kuskuren da zaka share rayuwarka kana fatan kankarar biyayyar da ka mata.
Shatin ƙaddara daban yake da wanda ƙirƙira ta samar da shi. Zamu ƙira komi da ƙaddara amma a zahiri akwai silar da kan wanzar da faruwar ƙaddarar!
Ya kake ji a zuciyarka a yayin da ka himmatu wajan bata ko wani muradinta?
Rayuwarka na fama da dunƙulallan layin da ke amsa sunan sufuli ne👌🏻
Domin baka da ƘAWA ZUCIN da zaka kira shi naka!
Sai dai CI DA ZUCIN da zuciyarka ke ingizaka.
Ka killace tunaninka ka goge bauɗaɗɗiyar biyayyar da kan ƙara maida makaho bagidaje.
Babu ido mi za'ayi da fitila? Babu kunnuwa balle a nemi sautin isar da ƙara.
SA'A guda ta wadaceka aikata kuskure sai dai zata ci gaba da caccakar rayuwarka har shuɗewar mahangarka.
Ajiyar zuciya na sauke tare da mata fatan shiriya. Tunda na fahimci hakan sai na assaso mana rikici a tsakaninmu wanda yaja mana babban rigima sosai, har muka zauna a gabanta domin tayi mana shari'a, amma ido da ido ta nuna min nice me laifi sabida nice sama dashi, kuma ai na girme shi, taya zan maida hankalina irin nasu da Natashah. Dan haka idan bazan Iya zama dashi ba na koma gado inda na fito.
Kallonta nayi cike da baƙin ciki nace.
"Tabbas kin nuna min halinki nason kai da zuciya, idan halin mu ba d'aya dasu ba, dani da shi waye keda ikon akan wani wato Nannah yanzun bani da amfani! Sabida d'anki yana tare dake, ban tab'a ganin me son zuciya irinki ba, kuma bazan rabu dashi ba, idan kika ce zaki raba had'in Allah, wallahi mutuwa."
Buge min baki yayi da bayan hannunshi, kallonshi nayi tare da sunkuyar da kaina, kwalla na sauka a idanu a, tabbas bazan tab'a zubda darajar mijina a gaban kowa ba, dan na lura abinda ake nima kenan asa shi ya sake ni, dake ta horani Tuni na d'ago dan na fahimci tsiyar da ta shirya min.
Duk abinda zan gaya muku bazaku gane ba, domin baku san yadda uwar miji ba larabiya take ba, tunda ba sona take ba, toh kuwa zan iya cewa watan cin Ubansa ne ya tsaya, ranar da akayi haka kwana nayi ina kuka sosai, gashi zuciyata taki bawa Ashraf laifi, gani nake duk abinda ya faru nice sila, kuskure d'aya tak ya ruguza min kome na Rayuwata. Wani irin tukikin baƙin ciki yasani mik'ewa da sauri zan bar falon Jiri ya kwashe Ni zan fad'i ya tare ni.
"Karki kuskura kija min asarar wallahi sai na baki mamaki, tunda baki da hankali, kome sai kin saka kishi a ciki, wallahi ki shiga hankalinki, abinda nake gudu kenan nace kiyi baya da kowa, duk son da nake miki ba zai hanani dakatar dake ba, sabida Uwata ce. Kuma dud duniya babu mace me darajarta, sai ke da kike biye mata, sai Yarana, dan haka ki shiga hankalinki, dan bazan dauki reni ba, sabida haka nace miki ki nesanta kanki da ita, yanzun zaki gaya mata magana ance miki Ni sakarai ne da zan zuba miki ido ki wulakantamin ita, wannan ya zama na farko dana karshe, indai har zan gaya miki magana ki bijire min toh ba makawa duk abinda ya biyo baya zan dakatar dake, amma baki ji ba sabida taurin kai, dan haka muje ki kwanta."
A ranar nayi kuka fiye da komai a rayuwata dakyar nasha ruwa a cikina na rasa wanda zan kira na gaya mishi matsalata, haka na cigaba da ganin bakin ciki, idan yau naji dad'i gobe akwai bakin ciki. A haka muka had'a sati biyu.
Ina zaune bayan dawowarmu daga siyayyar kayan baby garin bud'e handbag d'ina naga wannan kwalbar, shine na fito na kawo mishi na bashi, tare da mishi bayani, yace.
"Ki ajiye zan zo na amsa, wannan fatalwan ne ki ajiye shi zanzo anjima na amsa."
Tsorone ya kamani kamar zan fashe da kuka nace.
"Don Allah ka rike a hannunka"
"Na dai gaya miki karki bari ya fashe"
Haka na maida d'akina, na ajiye ina jin tashin hankali. Ashe duk maganar da muke a kunnen Natashah da Nannah.
Kallon Natasha Nannah tayi, suka gyad'a kai.
🤔🤔🤔🤔
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah
2️⃣8️⃣
Murmushi Natashah tayi cike da farin ciki, suka juya d'akunan su. Kowacce tana farin ciki, akan samun wannan babban damar dan tabbas suka fasa, dole Ashraf ya rabu da SAFINAH. Lallai su Nannah da Natashah sun aikata mugun kuskure, dan dasun san waye a cikin kwalbar da basu yi yunkurin tada shi ba, Ni nasan bakar wahalar da nasha dukda bansan ya aka yi Ashu ya rabani da shi ba, amma tabbatar ba haka kawai Allah ya rabani dashi ba.
Nice me laifin da nafi nasu domin kuwa, dana tashi sai na saka a sama mirror nayi wuccewa ta. Dake ina aiki ne sai ban mai da hankalina akan kwalbar ba.
Ina sai ga Natashah ta shigo tana son na bata, aron wayata ban d'ago na dub'eta ba nace.
"Ki duba kan mirror d'in yana gurin."
Dake bashi ta zo d'auka ba ta suri kwalbar tayi tafiyarta.
Babu abinda yake tagayyara da rayuwar mutum kaman sharri, musamman idan ka had'u da munafukai (🤣😂🤔🤭 Toh Allah ya rufa mana Asiri) toh magana ya kare, domin kuwa duk hanyar da suka sannan zasu cutar da kai sai sun nima, ina mamakin yadda su Nannah suke ƙoƙarin cutar dani, ba tare da tunanin hakkina ba, dan da sun san fitinar da zai same su a fasa kwalbar da har duniya ta tashi bazasu taɓa da bazasu d'aukar kwalbar ba, amma dake ance duk wanda Allah ya yankewa kazar wahala, sai ya fiye da jib'i.
Bayan mun gama cin abinci, dan ana gama abinci Ashraf da kanshi yake dauko mana namu sama, kuma idan ya hauro bazai sauka ba sai gobe, dan tunda cikina ya shiga wata bakwai, yake kaf-kaf dani ba iya Ni ba har Yaran, wanda yanzun harshensu rike turanci sosai, kiri kiri. Uban yake nuna min adawar shi da turancin,(🤣😂) sabida kishin kabilarshi da harshensa, shi yasa da yake cewa idan zai sakasu a makarantar, shi Yemen zai kasu ko riyad, dariya yake bani. Dan haka na daina musu turanci na koma larabcin baki d'aya, duk son Ashraf da turanci sai da ya kalubalence ni akan haka, yace dama Shuwa nake koya musu yafi turancin.
Muna gama hira ya tattara yaran zuwa d'akina, yayi musu addu'a sosai, sannan ya zauna a kusada su har suka fara Barci, zaman shi bawai dan ya kalle su bane, Surori hud'u na ciki Alkur'ani yake karanta musu, Kahf,Yaseen, Dhuka, Rahama, sai ya rufe da falak da nasi. Sannan ya rufe Alkur'ani ya tashi, dan har sun yi barci, ya shigo d'akina. Ina goge jikina da Towel, amsa yayi ya taya Ni goge bayana, sannan ya d'auki ma busa ya busar min da gashina, ya ajiye ya shige ban d'aki yayi wanka, kafin ya fito har na kwanta, kayan shi ya saka. Sannan ya hauro inda nake yayi min addu'o'i, kafin ya kwanta a bayana.
Koda muka kwanta najima ina jin addu'o'in sa har nake cewa a raina.
*Yau lafiya Ashu yake wannan addu'o'in*
Ashe jikinshi ne yake bashi akwai matsala, shine yaketa addu'o'in. Domin niman kariya, kuma dama dabi'unshi ne. Ɓalle kuma yadda sukayi da Anim.
....... Wajen karfe biyu saura Natashah ta farka, kwalbar ta dauka. Sannan ta gama kallon shi, sannan ta fito Tsabar mugunta, a gurin da take tsaye ta kwala kwalbar da kasa, tasa ya fashe.
Wani irin rugugi gidan ya fara kafin wani irin iska ya taso, zata zura a guje iskar Yahaya cikin guguwar, ya fara juyata sosai. Sai da iskar ta gama wasan kura da ita, sannan ta makata da kasa, a hankali iskar ke shigewa hancinsa.
Sai da ya shige cikin jikinta tsaf sannan ta bud'e farin idanunta wanda suka koma kalar ta zombia. Tashi tayi cikin iska ta nuna d'akinta da yatsar hannunta. Buɗewa kofar tayi sannan ta shige.
★★★
Washi gari...
Dake ba saukowa muke ba, iyakar mu, sama dan tun ranar da muka same matsala dasu Nannah ya hanani saukowa indai ba asibiti ba, zan tsaya na gaisheta sannan nayi wuccewa ta, dan tunda tace bata sona da D'anta sai naji dukduniya bani da abinda nake so sama dashi, kuma nake k'iyayye duk wata sharad'insa, haka ya kara mana fahimtar juna.
Saukowa yayi ya d'auki abin karyawarmu zai kai mana, ya kalle Kofar na tasha yaga yayi gizo gizo. Tsinkewa zuciyarshi tayi *badai fasa kwalbar SAFINAH tayi ba*
Abinci ya kawo mana sannan ya mika min hannu tare da cewa.
"Bani kwalbar da na baki"
Dakyar na mik'e sabida girman cikin, ina shiga inda na ajiye babu shi babu alamar shi.
Juyawa nayi na kalle shi cikin tsoron masifar shi nace.
"Ban gani ba."
Kamar ya rufe Ni da duka yace.
"Kina da hankali kuwa, ki ajiye abu kice baki gani ba, tsabar rashin sanin ciwon kai, wato fasawa kikayi kowa ya mutu ko"
"Kaga nifa ban san inda yake bane, kuma taya zan fasa abinda zai cutar dani, wallahi a sani na a nan na ajiye kuma na cigaba da aikina Ni ban."
Dakatar dani yayi tare da kura min ido yayi. Kafin yace min.
"Bayan dawowarki d'aki wa..."
Ihun Nannah muka ji Dukkan muka fito daga d'akin, da sauri ya sauko kasa. Ganin Natashah shake da wuyar Nannah, yasa shi turus cike mamaki.
Kwala min kira yayi, tare da cewa na sauko mishi da wayarshi.
Da sauri na sauko da wayar na mika mishi, Ghaniyu da Fahad ya kira tare da gaya musu halin da ake ciki.
Nuna min hanya yayi na koma sama, duk sona da na tsaya, amma fir ya korani sama, haushi da tausayin Nannah suka cika min, zuciyata domin tana cikin mugun yanayi, tsabar Ashraf ya nuna mata kurenta yaki kwatarta a hannun Natasha,
Shigowar su Ghaniyu suka rufawa Natashah, dakyar suka kwace Nannah wacce ta suma. Gashi ta jigata, maida Natashah d'akinta sukayi. Sannan suka dawo kan Nannah suka watsa mata ruwa, ta farka tana tari.
A firgice ta mike zata zura gudu, Ya rikota tare da zaunar da ita bayan ya kalli su Ghaniyu. Mik'ewa sukayi tare da barin falon, ya kalleta sannan yace.
"Ban san irin k'iyayyar da kike nunawa Safinah har ya girma haka ba, laifin me tayi miki kika tsaneta haka!? Me ta tsare miki ne haka!? A sanina Yarinyar bata da matsala da kowa sai ke, kuma nayi imani da Allah kece kika tura Natasha ta dauko miki kwalbar dan ku zalunci SAFINAH, Ammyna Safinah bata da hakkinku shine abin ya koma muka duk duniya babu wanda ya isa raba Natashah da fatalwar Anim, sabida duk wanda ya bud'e haka karshen sa zai koma, sannan keda kika sakata duk lokacin da ta ganki zata nemi kashe ki"
(🤣😂🤭😎Mugu d'an masara ana goyanka kana karya uwaka)
Yayi mata wannan bayanin ne dan ya cusa tsoro a zuciyarta, dan kar gaba ta, amma tabbas akwai inda za a magance matsalar. Kuma yana son Natasha tabawa Nannah wahala yadda zai tsorata.
Wato Ni dai Ashraf ya hanani sauka sabida cikin shi, dani kaina. Yaranmu ba ya hanasu sauka, dake ba wai yana yawan magana bane, idan suna rikicinsu sau d'aya yake kallon su tuni sun shiga hankalinsu, kuma zai zauna ya musu hira har dasu tarihi, amma haka bai hana shi cusa musu akidar shi na rashin son hayaniya da kuma uwa uba, Body language, dan wani lokaci da yayi musu Magana da baki ya gwammace yayi musu da ido, kuma suma sun san halin shi, sosai. Abinda ya kara birgeni da shi yadda ya koyawa yaran dabi'a irinta. Sarautar ga dan banza fi'eli, abinci ma idan zan bi tasu ko abinci ma a baki zan basu yaran masu niman 3yrs.
Haka Ashraf ya rabani da kasa, Nannah kuwa tana shan bakar wahala a hannun Natashah, musamman idan Ashraf baya nan. Toh wallahi kamar Natashah zata kasheta. Ni masifa ya dame Ni, dan haka nasa shi a gaba. Da kukan banza dan ya taimakawa Nannah, bawan Allah nan ya share ni, Ni kuwa na hanashi barci kuma kunsan sha'anin cikin. Ni kuma nayi haka ne sabida wahalar da take sha. Tayi banza dani haƙa na hakura na zuba mishi ido, cike da takaici, da na ishe shi da mita.
Yace.
"Zo ki bani hakkina ai nayi ƙoƙari ma, kusan kwana biyu babu, sauke nayi"
Wallahi bansan lokacin da na sauka a gadon ba na shiga bashi hakuri, sabida yanzun ina wahala da cikin ga kuma fitinar Ashraf, duk lokacin da aka yi haka sai naji kamar zan juye cikin tsabar ciwon baya da mara.
Shi yasa da yace na bashi hakkinshi na lallaba na sauka a gadon zan koma kasa na kwanta.
Zan iya cewa wannan dalilin ya janyo mun kara had'ewa da mijina, sosai fa rawan jikin da yake akaina ba iya ka.
A gefe ina ganin farin cikin shi akan lalurar da su Nannah suka samu,
Duk Nannah ta lalace ta kuma fita hayacinta, hmm natasha kan ba a cewa kome, dan ta koma kamar horror, fatar jikinta ya tattara ya koma kamar na tsofi, gashin kanta kuwa kuwa ya tsaya tsage tsage, bata da kyan gani.
Ashu sun tafi airport dauko malamin da zai duba Natasha, Ni kuma ina falo Ni da Yara muna karatu naji ihun Nannah,