Showing 36001 words to 39000 words out of 108344 words
Chapter 13 - Masarautar jordan Book Complete Document by mai Dambu .txt
aka ce musu gender ɗin Male ne, ai tun daga London aka kira Ashraf, yana tsaka da aiki.
Da mamaki yake kallo number, a dakile ya dauki wayar.
"Assalamu alaikum! Abu Amir! Yanzun aka tabbatar mana da cewa namiji abin cikina."
"Na aike ku ne? Ko nace miki Ni nafi son namiji ne? Da mace da namiji duk wanda Allah ya bani ina so, dan haka Idan zaku yi shirme, kuma kiyi scanner karshe idan kika kuma wani abu ya sami abin cikin ki."
Karshe kiran yayi cike da bakin ciki ranshi a ɓace, shi bai ki duk yaranshi su fito daga jikin SAFINAH. Murmushi ya sake cikin farin ciki.
★★★
Kuka Natashah tasakawa Mamanta.
"Yanzun meye abin ɓacin rai dan na gaya mishi, kiji da wai duk mace da namiji duk daya ya ɗauke su, da wad'ancan shegun yaran wai ɗaya ne da d'an halak kiji da cikin babu dattin zina babu kome, shine yaƙe haɗa min da magajin jordan"
(Tirkash Inji Mommy Sayyid 🤣😂 ba Natashah ta balla August)
Nan Uwar tashiga rarrashinta tare da gaya mata duk rintsi Ashraf natane dan wannan yaran babu abinda zasu iya tunda cikin jikinta shine wanda kowa ya sani wad'ancan
Kuwa ba a san dasu ba.
Nan suka zauna suna karawa kansu zunubi, tare da cewa ai duk abinda ke faruwa Nannah tana sane bata iya tab'uka kome sabida tana tsoron Ashraf, shi yasa Safinah ta mallake mata, sosai suka zage Nannah wacce ita ta dauki nauyin zuwansu London, har asibiti Queen Mary, asibiti mafi kuɗi da shahara.
★★★
Abun ba sauki dan sosai Ummi tasa ido a kaina, tunda ta kwace wayata. Kuma nasan Ashraf zai nime ni, hankalina yayi mugun tashi, kar zanyi kuka duk yadda naso ganin na magance matsalarmu.
Shima duk ya shiga damuwa rashina, gashi numberta bata shiga, yazo suka haɗu da Dudu dakyar aka rabasu, dan rashin mutunci Dudu yayi masa, abinda yacewa Dudu shine ya sake fusata shi.
"Ina ganin girman kane sabida zuri'ar da suke tsakanina da Yayarka, shi yasa idan ka tabani bana ramawa, Abdullahi idan a cikin san-sanina ne baka isa ka taba Ni ba tare da an yanke hannunka ba, ita SAFINAH da kake hanani ganinta, zan zo har nan na dauke ta akan idona zata bini, bana son mukai ga haka ne shi yasa nake son ku bani aurenta dan kuma fi dacewa da ita, idan kuma kuka ki, tarihi zai mai maita kanshi a-a karkayi tunanin ta wancan hanyar hmm ta gangara Zan saita ƙwallona, kuma babu gargada jinin bakuraishe harbawa take daga ita har Kunamarsa"
Aikuwa Dudu ya sakeyowa kanshi.
Bayan motar shi ya hau tare da zama yayi Crossing leg dinshi tare da sukari motar da tafin hannunshi yace.
"Wallahi indai izza da mulki gadarsa nayi sai na auri yar uwarka, koda zan rasa kome da na mallakan sai na tabbatar maka Ni Balarabe ne bana tsallake maganata daga yau kafara kirga kwanaki Allah ya bawa me rabo sa'a"
Cikin fusata Abdullahi yace.
"Ni kuma na maka Alkawarin SAFINAH ta haramta maka I, kaman yadda kayi alwashi nima haka na riƙe maganata"
(🙄🤔😒 Alamarine ya zafafa)
Tun daga ranar Ummi tasani dawowa d'akinta sosai aka saka ido akaina fa.
Bansan make faruwa ba sai dai naji wai an min miji......... Wata sabuwa
Wallahi labari ba hatsaniya ai tamkar miyar kaza ce ba gishiri, ban sani ba ko kuna jin dadin labarin for me kome yayi min 🤣😂
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
16.
"A'ah Ashu tsoro nake ji bana son na zama sanadin da iyayena zasu tsane. A halin yanzun ya dace na gyara gobe na, amadadin haka sai bata musu nake."
"Didih"
Naji muryan Yarana, hawaye ne ya zubo min cikin tashin hankali nace.
"Mariamah!!!"
"Zaki yi yadda nace ko na maida musu yaran?"
"Wai meye yasa kullum kake bani matsala ne haka, kasan girman iyaye kuwa!? Da kake son na bata musu kaje da abinka kawai Ni ba zanzo ba."
"Ba damuwa karki zo, kiyi zamanki ma. Ni da nake da daman auren mata hud'u, balle ke gaba da zama."
Kashe kiran nayi tare da g
Cillar da wayar, na cigaba da kuka tunda shine abokinsa hirana, sam ban san wani irin son kaine yake dawainiyya da Magabatanmu ba tunda nace Ashu nake so ya kamata su duba lamirina bawai su zuba min ido nayita abinda bai dace ba.
Kifa Kaina nayi akan pillown ina kuka sosai.
Da dare na je har falon Abba na sameshi shi yana kallon network news, zama nayi can gefe kaina a sunkuye,wasa nake da harshen gyale na, hawaye ne ke zuba daga nuna.
Gyara zaman shi yayi Cikin nutsuwa sannan ya rage ƙarfin maganar da ake a tv.
"Safinah! Ba munki miki abinda kike so bane! Sai dai munyi dubi da irin rayuwar da zaki shiga ne,"
Zuciyarki da kwalkwarki baza su iya daukar kasadar dake cikin masarautar Jordan ba, tunaninki da nazarin ki bazai dauki bukatar alummar cikin masarautar ba, SAFINAH ina ganin kiyi hakuri da Alhaji Nuhu, shine mijin da ya dace dake. Ba Ashraf ba, idan kuma aka yi dubi da rayuwarku da bambanci domin duk wanda aka daura shi shugaban al'umma sai ya take gaskiya dan wata dalilin shin zaki iya jure masifar da tasa uwa tafiya tabar d'anta? Zaki iya jure masifar da ya raba miji da mata!? Indai zuciyarki tana da adalci bazata rabamu dake ba, SAFINAH ki zauna damu hankalinmu zaifi kwanciya muma zamu fi samun nutsuwa ace kina kusa damu, badan ina Mahaifinki ba sai dan abokin shawaranki."
Kukana ne ya tsananta, dakyar na mike tare da gyad'ana. Kuka nake me mugun cin zuciya.
A haka na isa d'akina na kwanta, duk inda naso abin ya kasance yaki yuwa har Dudu da Umma nasamu, da maganar. Ita Umma yasameta su akan su bar i mu auri Ashraf.
"Maman Safinah! Yarinyar nan tafi ku gaskiya tunda tace muku Ashraf take so kubarta takoma hannunshi, ita Kuma uwar Ashraf ɗin idan har ta cika Uwa dole taso abinda d'anta yake so ba wai tace muku. Ku raba abinda Allah ya haɗa ba, Safinah ba Yarinya bace amma tunda tace muku shi ta zaba a abokin rayuwarta kamata yayi kubata shi."
"A'a! Amnah ki kyaleta kawai son zuciyarta ce kawai amma ita ba tsara Ashraf bace, kuɗi! Mulki! Nasaba! Uwa uba d'auk'ak'a, shi ba sa'anta bane, tayi hakuri Allah ya Kawo miji tayi biyayya kawai."
"Maman Safinah! Zaku sak'e tura ta cikin wani irin hali kodan Albarkacin yaranta ku kyaleta ta koma kansu, Bazawara ce ita addini ya bawa daman zaben Abokin zamanta ku iyayenta naku addu'a da bincike, kuna son kanku."
"Don Allah Amnah ki bar maganar nan ta auri Nuhu."
"Toh tabbas duk abinda ya biyo baya kune sila sabida tsoron karta kwace dukiyar ta, takwace mana."
"Ni kam fita daga d'akin korafin yar dakinki bai karbu ba."
Hmm duk yadda muka zata ba haka ba ne, domin kuwa Abba shi bai ja ba, Ummi ce ta kafe kai da fata. Kuma taki sauraro kowa.
Gaba bikin yana karatowa, dan haka na kashe wayata na zuba musu.
Sosai Al'amarin ya zafafa. Dan haka yau laraba na fito wanka daure, taje kaina nayi sosai sannan, na ciro pant da bra dina na saka. Zuciyata ta gama raya min abinda, ina gamawa na zauna sai da na busar da gashina sannan na fito daga d'akin sanye da hijab har kasa, Ummi na zaune tana haɗa wani tsimi na shiga mika min tayi na amsa ba musu na shanye. Sannan nace mata,
"Ummi zanje Salon!"
Zuciyata ke bugawa kamar zata fito, tsabar tashin hankali musamman da ta tsare Ni da manyan idanu, wai na shiga ruɗani.
Had'iye yawu nayi tare da b'oye halin da nake ciki.
"Kina da kuɗine ko na baki?!"
Dan karya zargi wani abu sai na ce mata.
"A'a Ummi dama ina tunanin ko zaki bani ne."
"Ki bud'e wancan sif ɗin zaki ga kuɗin ki ɗauki yadda yayi miki Allah yayi miki albarka,ya kareki daga sharrin mutum da aljan"
Tausayi tabani na kasa motsawa, sai da tayi min magana a karo na biyu naje na ɗauki kuɗin.
"Allahumman Amin, Ummina Kiyi hakuri dani."
Murmushi tayi sannan tace.
"Allah ya jibanci alamarinki"
"Amin Ya Allah, Ummina sani na dawo."
Da sauri na fita naje na ɗauki wayata ina fita daga gidan. Sai da nayi tafiyar kafa, Kafin na kirashi kamar jira na yaƙe sai gashi ya kirani, cikin juriya na dauka.
"Assalamu alaikum"
"Waalaikumun Salam! Kin fito ne!?
"Eh gani a Bayan layinmu"
"Ok ga wani toyota nan zai dauke ki."
"Ok"
Juyawa nayi motar tayi parking a gabana, drvn motar ya fito ya bud'e min na shiga, sannan ya tadda.
Bamu tsaya a ko ina ba sai wannan gidan da ya kaini, suna filin gidan shida yaranshi da ma'aikatan gidan yaranshi na wasa da yan kuikuiyom kare, sai dariya suke, a hankali na zaro kafana na fito a ina kallon girka girkan karanukan gidan wani suke kaɗai min wutsiyar su. Kallon agogon wayata nayi, naga sha biyu saura.
Watsewa ma'aikata ya riko hannun yaranshi, murmushi yayi min.
"Barka da zuwa Mrs Hashim"
Ban ce mishi kome ba, tunda muka shiga ya kawo min abin sha, yaga ban taba ba.
Murmushi yayi sannan yace.
"Nafi karfin ciyar dake maganin barci dan biyar buƙata ta, idanunki biyu komai zai faru."
D'ago fuskana nayi me cike da damuwa nace.
"Ashraf!?"
"Shhhhhi!? Kamar yadda kika bani ciwon kai, get ready da hukuncina dan na rantse sai na rama kome da aka min yau sai na sauki fansata."
Gyad'a kaina nake idanuna na cike da kwalla. Na cin amanar iyayena,
Hawa jikina yaran sukayi cike da murna suka shiga bani labari sai na manta da kukan da nake, na cigaba da biye musu, tashi yayi ya barmu, nan wanka yayi cikin farar jallaɓiya sabuwa kal da ita, sai farin hula malam tab'ani kasha hadisi. Sannan yayi wasa da turare kafin ya fito.
Sumbatar yaranshi yayi sannan ya kalle Ni tare da kashe min ido, yace.
"Ke kinyi katuwa! A can zan baki naki rabon. Kishiga kiyi salla da wanka ina zuwa ki tabbatar kin kintsa kome kafin nazo."
Tura mishi baki nayi tare da dalla masa harara, lumshe idanu yayi sannan yace.
"Zaki biya"
Haka ya fita ranshi fari nawa baki, ji nake kamar na gudu dan abinda nake shirin aikawa babban kuskure.
Me kula da yaran ce ta shigo ta kama hannunsu suka shiga wani daki, daga nan ban kuma jin duriyarsu ba, nima Dakin na wucce ina shiga naga wata rigar barci tare da wani turare.
Ban daki na shiga nake nayi wanka sannan na fito daure da towel, na zauna akan stool na shiga gyara gashina, sannan na ɗauki rigar na kalla sai kunyar kayan ce ta kama Ni, dakyar na saka. Sannan na daura hijab dina akai.
Salla na gabata, ina cikin addu'a ya shigo da katon leda, har guda biyu ya ajiye a gabana.
Daura kanshi yayi akan cinyata, tare da sauke ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah! Na kusan cika cikekken namiji kamar kowani namiji."
Dariya ya bani sosai sannan nace.
"Dama baka cika namijin bane?"
Juyar da kanshi yayi cikin kallon kurilla yace.
"Eh! Amma zan duba idan muka haɗe a can, kinsan Allah ban samu sallah ba, bari nayi kafin ki warware min alola na, kema ya kamata kiyi nafilla niman gafarar Ubangiji, dan nima idan nayi idar da sallah zanyi."
Jikina ne yayi mugun sanyi cikin jin ba dad'i nace.
"Toh tunda abinda zamu aikata bai dace ba kawai mu hakura mana, Ni kaina bana son sabawa iyayena, kuma."
Mikewa yayi ya shiga gabatar da Sallah azhar, bayan ya idar lokacin nima na gabatar da nafilla kamar yadda ya umarce Ni,
Bayan mun idar ya dauko kayan cikin ledar ya ajiye mana janyo Ni yayi jikinshi, ya shiga ciyar dani namar rago wanda aka mishi gashin biebe'q' (oho🤷🏽♂️ idan kun fahimci suna sai ku gaya min sai na gyara, amma abincin Mutanen Jordan ne,)
Yana gama bani namar, sai ya janyo wani takeaway ya buɗe fruit ne a cikin musamman inabi me sanyi da danginsu kiwi blueberry da sauran dangin berry,
Shima sai da na kauda kaina sannan ya bani madara, rike hannunsa nayi cikin shagwaɓa nace.
"Zaka fasa min cikin ne, sai dura min kake fa."
Murmushi yayi sannan yace.
"Bazan fasa miki ciki ba! Idan nayi haka ina zan ajiye kiyaye na fa!?"
Share shi nayi dan ban ciki da rashin kunya,
Zare Ni yayi daga jikinshi, ya mai dani gefe, sai da yaci abincin yadda yake ci a yangance. Sai ya burgeka dan Ashraf ba dai mad'e ba kamar mace, yana cin abinci yana kunshe idanu kamar namiji ba.
Yana gamawa ya miqe tare da kwashe kayan ledojin da muka b'ata, ya kai waje sannan ya dawo durowa yaja tare da ciro asiwaki ya ya bare ledar su yasaka a baki, ya cigaba da taunawa. Jikin madubi ya koma ya shiga gyara fuskar shi, su kasumbar da ta cika masa fuska sai da ya cire su tas, sannan ya koma ban daki yasaka removen cream, ya shiga cire wasu gashin da suke hannuwan shi da na gefen kirjinshi, har da na kirjin nashi domin Ashraf yana da matukar suma, kuma suna kwance ne lub-lub, yana gamawa ya fito. Daure da towel alamun ya watsa ruwa dan har kana iya hango yadda gashin suka kwanta, goge jikinshi ya fara ba tare da ya kalle yadda na zuba tagumi.
Sai da ya gama sannan ya bud'e durowa inner wear ya ciro pjyam dinshi blue black tare da, wata farin shirt wanda aka rubuta sunnil, abin busar da gashi ya mika min.
A hankali na mike ba laka a jikina na amsa tare da, haɗawa na shiga busar mishi da gashin sa.
Ina gamawa na ajiye, cak naji anyi sama dani. Zaro ido nayi tare da sake yar karamar kara, Yau gani a hannun Ashraf.....
_Kuyi hakuri bazan iya page uku ba wallahi biyu nayi alkawari, shima idan babu uzuri._
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
17. ```Hey! Yau sai kunyi hakuri pagen nayi rashin Kunya 🙈🤭🤧```
A gado yayi min ma sauki, tsoro da ajiyar zuciya na sauke lokaci guda, ina ƙoƙarin zare jikina a nashi, jibga min nauyin shi yayi.
Cikin kankanuwar Murya nace.
"Ashu!!!? Ka.."
Rufe min baƙi yayi da hannunshi tare da mikewa ya kashe wutar d'akin, sannan ya dawo kusadani ya kwanta yana bina da wani shu'umin kallo.
Lumshe idanuna nayi tare da sauke ajiyar zuciya babu iyaka cikina kuwa d'ura ruwa yayi sai bada kululu, yake tsabar na ɗauki hanyar da ba bullews zata ba.
Matsowa yayi sosai kusadani, ya daura hannunshi a fuskana. Bude idanuna nayi ina kallon Yadda ya lumshe idanunshi, zara zaran Eyelash dinsa sun kwanta, shagala nayi da kallonshi. Har ya buɗe idanun Iska ya hura min.